Friday, 6 April 2018




TAMBAYA TA 29

Home TAMBAYA TA 29
TAMBAYA ========= 👇 Assalamu Alaikum MALAM ,ya aiki ,ya yau da gobe Allah kasa mudace Amin,tmvy ta farko ita idan yaro dan shekara 4 baya fahimtar karatu,wane mataki yakamata mutum ya dauka dan ganin ya samu karatu mai amfani, 2 )Shin ko ya hallata mutum yasa ma dansa ASHEER kuma minene ma'anarsa? Nagode AMSA ===== 👇 To wasu mutanen haka Allah yake halittarsu tin suna kananan yara, wadanda basa fahimtar komi a karatu. Irin wadannan yara a kasashen da sukaci gaba kamar China, suna koya musu sana'o'in hannu ta yadda zasu dogara da kansu. Sabida idan maganar ilimi ne bazasu taba fahimta ba gaskiya. Amma sai ana koya musu abinda nan gaba zasu dogara dashi a matsayinsu na Dan Adam wanda ba yadda za'ayi ya rayuwa face yaba da bukata ta yau da gobe. Amma duk da haka wannan bazai hana kuke masa Addu'ah ba, misali. Kuma karanta masa WA'ALAMNAHU MINLADUNNA ILMA. Ana tofa masa a ruwa yana sha. 2. Ban san ma'anar wannan sunan Ba gaskiya. Allah shine masani. ✍ ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876

Share this


Author: verified_user

0 Comments: