TAMBAYA TA 24
Post By:
Hausa Novels
Tambaya Mabudin Ilimi
*_BABU ZAKKA A DUKIYAR WAKAFI !!!_* *Tambaya* Assalamu alaikum, Malam ya halatta idan aka gina masallacin Jumu'a sannan aka gina shaguna ajikinsa domin su dinga kawo masa kudin gudanar da shi, to malam idan kudin yakai nisabi za'a iya fitar musu da zakkah? Allah ya kara basira ameen. *Amsa* Wa'alaikum salam, To dan'uwa duk dukiyar da babu wani ayyanannen mutum da ya mallake ta babu zakka a cikinta, don haka babu zakka a wakafi, ko dukiyar da mutane suka hada saboda taimakekeniya, in wata matsala ta samu wani daga cikinsu kamar hadari. Ko da kuwa ana juya kudin suna kawo riba, shagunan masallaci wakafi ne, don haka ba za'a fitar musu da zakka ba. Don neman karin bayani duba Fataawa Allajnah Adda'imah: 9\291. Allah ne mafi sani. 29\1\2016 Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa. Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ. Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci. ______________________________________ » Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp). Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.



0 Comments: