TAMBAYA TA 25
Post By:
Hausa Novels
Tambaya Mabudin Ilimi
TAMBAYA ======== đ Ina da Tambaya kamar haka a wana watani akiyin azumin tashu'a da ashu'ra kuma inasu kamin bayanin falalar su dan allah Nagode. AMSA ====== đ Hadisi Ya tabbata daga Manzon Allah saw yace, Azumin da yafi kowanne falala Bayan Ramadan shine watan Allah ALMUHARTAM. Sabisa haka a watan Almuharram ake yin wannan Azumi na Tara da goma ga wata. (TASU'A DA ASHURA) Sabida an sami hadisi daga Abu Qatasatal Ansari Allah ya kara masa yarda yace, Manzon Allah saw ya sami yahudawan garin madina suna yin Azumi na Ranar Goma ga watan Almuharran, sai Manzon Allah yace, Azumin me kukeyi? Sukace muna yin AZUMI ne Sabida a dai dai wannan Ranar ne Allah ya tseratar da Annabi musa daga sharrin Fir'auna, kuma a Ranar ne Allah ya halakar da Fir'auna din. Sai Manzon Allah saw yace, mune mukafi chanchanta da Annabi musa akan haka. Sai dai shi Manzon Allah saw yana son ya sabawa yahudawa a dukkan Al'amarin sa, sai yace, idan Allah ya kaimu shekara mai zuwa da rai, zan azumci Tara ga Wata. Sai dai Allah baisa ya kai shekara mai zuwa da rai ba. Allah ya karbi abinsa. Sabida haka, IQIRARI da Manzon Allah saw yayi, shine ya tabbatar da azumtar Tara ga watan Almuharram. Daman ya sunnanta mana Azumin goma ga watan Almuharram, Sabida haka kenan ya zama Tara sa goma ga watan Almuharram ne Za'a azumta. Ga Wanda zaiyi daya kuma, sai dai yayi na goma ga wata, Sabida shi Annabi yayi. Amma mai Neman dimbun lada, shine Wanda ya azumci duka Sai dai nasan Za'a yada hadisai na karya akan falalar Almuharram. Allah ya rabamu da masu yada karya su jinginata ga Allah ko Manzon Allah saw. Sabida haka sai Mu kiyayi 'yan uwa, akwai masu cuwa-cuwar Addini. Allah shine masani. ✍ ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876



0 Comments: