Friday, 6 April 2018




TAMBAYA TA 3,188

Home TAMBAYA TA 3,188

*Asssalamu Alaikum*
.
.
*Tambaya ta 3,188:*
=
Inaso agayamin Sharuddannan wadanda akeso hijabi yacika???
=
=
Amsa
=
_Toh wadannan sharuddan guda takwas sune kamar haka na farko: Dolene mayafin yazama ya game dukkan jiki in banda fuska da tafin hannu. Duk ga6arda ba fuska ko tafin hannuba to anaso dole se hijabi ya rufesu. 2-Kuma dole ne shi mayafin yazama ba kayan ado bane shi kansa kenan kar yazama kwalliya yana daukar ido kamar yadda akeyin kashi 99 cikin dari na hijabinda mata sukeyi a yau duk kayan ado ne. 3-Kuma yazama yalwatacce wadatacce karya zama ya matse jikintaba kamar irin wani hijabi da akeyi yanzu me kamar riga kana ganin duk surar matar shima wannan kaga be cika sharadi ba. 4-Kuma yazama me duhune bame shara sharaba yadda ze zama ana hango surar jikinta. 5-Kuma kar yazama an fesheshi da turare dazarar turare me qamshi ya zuba akan hijabi to shikenan ya kwace mishi sunanshi yakoma wani abu daban amma dai baza'a kirashi hijabi ba. 6-Kuma kar yazama yayi kamada kayan maza, inhar hijabi yayi kamada tufafin maza to shikenan ya tashi daga hijabi yakoma wani abu daban. 7-Kar yazama yayi kama da tufafin kafirai, inhar yazama wannan abinda kikasa matsayin hijabi yayi kama ko irin tufafine wanda kafirai suka shahara dashi kamar irin gown dinnan damata suke sakawa shima wannan baza'a kirashi hijabi ba. 8-Kada yazama tufafin shuhura wanda yake saboda tsabar tsadarsa duk inda kika wuce sai an kalleki. Kokuma yazama saboda tsabar arharsa duk inda kika shiga sai an kalleki*****_
        _Wadannan sharuddan takwas sune duk abinda yacikasu ya halasta akirashi hijabi a shara'a, koda gyale ne ko mayafi ko menene matukar ya cika wadannan sharuddan. Ba dole se ansaka irin wannan hijabin wanda mata suke sawa a yauba musamman anan kasar hausa kokuma abaya ko lufafa da ake amfani dasu a wasu wajaje ba dole se wadannanba, ko babban gyale ne inhar yacika wadannan sharuddan to yazama hijabi a shara'a. Kuma duk abinda mace zatasa matukar yakasa ciki wadannan to a shara'a batasa hijabi ba sedai a al'ada, dan haka mafi yawan mata a yau zancen gaskiya suna dai saka lullu6i ammafa ba hijabi suke sakawaba. Allah ta'ala ya shiryar damu*****_
=
=
Allah Yasa mudace
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
*مجلس تعليم الكتاب والسنة*
📓📔
Watsaps
08036222795
09031200070
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook ta wannan hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
.
Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka wa atubu ilaika

Share this


Author: verified_user

0 Comments: