Friday, 6 April 2018




TAMBAYA TA 67

Home TAMBAYA TA 67

*_MENENE HUKUNCIN WANDA YA YIWA DAN'UWANSA KAZAFI?_*

                                *Tambaya:*
Assalamu alaikum malam, menene hukuncin musulmin da ya yiwa dan uwansa musulmi kazafi?

                                     *Amsa*
Bai halatta mutum ya yı wa dan'uwansa kazafi ba, Allah yana cewa a Suratul Ahzab aya ta: 58 (Kuma wadanda suke cutar da Muminai maza da muminai mata, da abin da ba su yi ba, to tabbas sun daukarwa kansu karya da zunubi mabayyani). Wanda ya jefi wani da zina za'a yi maşa bulala tamanin mutukar bai zo da shaidu hudu ba wadanda za su tabbatar da abin da ya fadi kamar yadda aya ta: 3 a Suratun Nur take tabbatar da hakan, sannan ba za'a amshi shaidarsa ba har abada sai in ya tuba, kamar yadda ya zo a aya ta hudu a Suratu Annur.

Allah ne mafi sani.

10/2/2016.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: