TAMBAYA TA 35
Post By:
Hausa Novels
Tambaya Mabudin Ilimi
TAMBAYA ======== đ Don Allah mallam ya halatta Wanda ba musulmi ba ya baka kyautar kudi ya halatta ka amsa ka kashe. AMSA ===== đ Ya halatta wanda ba musulmi ba idan ya baka kyautar abinci ko ruwa ko kudi ka karba. Wani lokaci manzon Allah saw yana halin tafiya shi da sahabbansa, sai ga wata Arniya ta kawo musu ruwa sukayi alwala, anan ne kuma manzon Allah saw yace, DUK WANDA YAYI MUKU ALKAIRI, SAI KU SAKA MASA, anan ne kuma sahabban manzon Allah saw suka dakko dabinon da sukayi guzuri sukayi ta baiwa wannan matar. Sannan Allah ya halatta mana cin abincinsa a cikin al'qurani mai girma, cikin suratul Baqara, matukar dai ba wani gunki suka yankewa ba ko kuma ba sun yanka Dan wata al'adarsu Bena, wadda wannan al'adar ta sabawa tarbiyyar da musulunci ya bamu. duk da cewar basa bismillah a lokacin da zasu yanka, idan kazo zaka Ci sai Kayi bismillah kawai kaci kayanka. Sai dai musulunci ya nuna mana idan zamuci abinci a kwanansu sai mun wanke wannan kwanan da hannunmu, Sabida Su kafirai najasa ne, kamar yadda Allah ya fada mana, sannan ba mamaki suna zuba giya a kwanon. Allah shine masani. ✍ ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876



0 Comments: