Friday, 6 April 2018




TAMBAYA TA 34

Home TAMBAYA TA 34
TAMBAYA ======== 👇 Assalamu alaikum mal Allah ya taimakika tambayata mal shin yahalata mace mai haila tadau alkur,ani . Tambayata ta biyu azumin wata acikin wata sha uku da sha hudu da sha biyar ga mace maiyin haila intayi lisafi aranakun hailarta zata zo ziyu ayisa kafin kwanakin ko bayan gama hailar kokuwa sai lallai sai sha uku zuwa sha biyar din AMSA ===== 👇 Na farko dai bai halatta mace ta dauki Alqur'anin ba alhalin tana jini, Wannan itace fatawar da yawa daga cikin Malamai suka bayar, kamar mal usaimin da sauransu, Duk da cewar wasu malaman suna ganin babu wani dalili kai tsaye da ya nuna cewar Dan mace tana jini bazata dauki Alqur'anin ba. Sukace Kalmar LA YA MASSUHU ILLAL MUDAHHIRUN "tana magana ne akan mala'iku ba mutane ba, da cewa akayi MUDAHHARUN to da anan mutane ake nufi, maimakon HA sai Allah yace MUDAHHIRUN wato MUDAHHIRUN Ba MUDAHHARUN ba. Sannan wasu malaman sukace mai haila zata iya daukar Alqur'ani, musamman ma idan tana tunanin har batayi Na Tilawa ba wannan haddar zata iya zubewa. Amma dai magana mafi inganci, itace maganar da mal usaimin na cewar bazata dauki Alqur'anin ba. Dan wasu malaman ma suna ganin mai haila bazata karanta Alqur'ani ba koda kuwa ba tare da ta daukeshi ba, sai dai addu'o'in da suke cikin Alqur'ani, Wannan zata iya yi, da niyyar addu'a, ba da niyyar Tilawa ba, kamar RABBANA ATINA FIDDUNYA HASANATAN WA FIL AKIRATI HASANATAN WAQINA AZABANNAR" da dai sauransu. Na biyu kuma bazata rama wannan Azumin ba, tinda Azumin nafila ne ba na farillah ba, sannan idan yazo mata a irin wadannan kwanaki alhalin tana cikin jini, za'a rubuta mata lada kamar tayi wannan azumin. Sabida fadin manzon Allah saw, inda yake cewa, idan mutum yayi tafiya ko bashi da lafiya, za'ake rubuta masa ladan abinda yake aikatawa kamar yana zaman a gida lafiyarsa lau. Allah shine masani. ✍ ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876

Share this


Author: verified_user

0 Comments: