TAMBAYA TA 38
Post By:
Hausa Novels
Tambaya Mabudin Ilimi
TAMBAYA ======== 👇 Assalamu Alaikum,,mungode malam Allah yasaka da mafificin alkhairi,,Amin...Malam dan Allah miye hukuncin iyayen da duk kulawar da yakamata ace sunba yaro basa bashi,,dukansu suna raye amma wani marayan yafita gãta,yarinyar macece amma hatta kudin makaranta ita take nema kuma wallahi iyayen suna samu,ba kamar ubanma shiyafi nuna ko inkula kuma yarabu da uwarta tintana yarinya...nagode malam AMSA ====== 👇 Duk yaron da ka ganshi, wata rana zai zama babba, Sabida haka yana bukatar kulawa kamar yadda ya kamata, Sabida da wannan ne zai girmama iyayensa a lokacin da girma yazo musu, a lokacin da basu da wani gata wanda ya wuce wannan Dan ko yar tasu, amma duk lokacin da wannan yarinya ko wannan yaron ya fahimci basu saukar da hakkinsa akansu ba, har ya fahimci haka, to tabbas ba makawa idan ya girma zai gujesu, bazai basu kulawa ba kamar yadda ya kamata. Sabida haka, ya kamata iyaye kuke saukar da hakkin da Allah ya dora muku akan yayanku, kuma duk uba ko uwar da basu sauke hakkin da Allah ya dora musu akan yayansu ba sai Allah ya tambayesu a ranar Alkiyama, tambayar kuma azaba ce. Allah shine masani. ✍ ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876



0 Comments: