Friday, 6 April 2018




TAMBAYA TA 6

Home TAMBAYA TA 6
TAMBAYA ======== 👇 Assalamu alaikum inayi wa mlm fatan Alkairi Allah saka maka da Alkairan duniya Dana lahira Tambaya ta shine mlm akan dalilin dazan fada ya kamata inne mi mijina ya sauwaka min saboda dalilan nan Shine nayi karatu a gaban iyaye na INA gamawa nasamu aiki sai kuma nasamu mijin aure kuma ni kadai suka Haifa sai mijin yace bazanyi aiki ba sai nace toh saina gaya wa iyaye na sukace basu yadda ba inkarfinsu yakare wa zai tallafa musu sai nace Akwai Allah suyi hakuri zai wuce suka yadda nayi aure shekara 15 kenan Amma mijina bayaban komi daga dukiyarsa sai abinci duk dahaka nagode wa Allah bantaba nunamar ba Amma yaran mahaifina ya kwanta ciwo har zawan sati 2 ba kudin kaishi asibiti har ciwo yayi yawa ajikin Sa Allah ya kaddara kwanan Sa ya kare Amma bai bani komi ba Dan inyi jinyar mahaifina Amma yaran kannensa inbasu da lpy ni yake barwa kudi inzai fita inbasu ko biki ko wata hidima a dangi na bayaban komi wani lokacin ma da kafata nake zuwa bakuma bashi da halin kudin ba toh yau gashi mahaifiyata bata da lpya bawanda ya taimaka min saudai inkarbi bashi gun nervous dina shine nace zan iya Neman saki domin inyi aiki insamu abinda zan kula da mahaifiya ta. AMSA ===== 👇 Ae Kin bar kashi tin ranar kwasa. Da tin a baya da yace miki bazakiyi aiki ba, da bazaki yarda ba ki amince masa hakan ba, tinda har kin sami aiki kamar yadda kika fadi, kinga yanxu idan akace ki nemi saki ma ba lalle bane a irin wannan lokacin da aikin gwamnati yake wahala ki samu ba. Sabida nasan ba mamaki soyayyar da kike masa ce tasa kikabi ra'ayinsa, alhalin ga abinda iyayenki suka hango miki, kinga Ni namiji ne amma wallahi nasan wasu Mazan basuda kirki, Sabida haka yanzu kuma kinzo gidansa kinga zahiri, Alhalin kuma a baya kina tunanin ko zai iya wadataki, amma yanzu gashi ba abinda yake miki in banda Ci da sha kamar yadda kika fadi. Kullum ina fadawa mata cewar ya kamata Su sani cewar duk wanda yazo yake miki hidima tin kina gidan iyayenki, to wallahi idan ya aureki ba lalle bane ya Dore da wannan hikimar da yake miki ba. Ke kuma Sabida mace ce, kina tunanin wai zaki sami komi daga gareshi. To ba haka bane. Wanda zai fito yace miki yau akwai ko babu, ko gaskiya bani da halin da zan iya yin kaza da kaza ba, Wannan shine wanda yake nuna miki zahiri, kuma har kullum ina Jan hankalin mata, soyayya a titi ba gaskiya bace, sai an shiga gida nan ne zakiga gaskiya idan har da gaske yake. Amma wata matar idan ta dauki SO ta dorawa saurayi, anan ta yarda akansa ma zata iya batawa da iyayenta akansa, sai bayan taje gidan zata gane tayi mistake a rayiwarta. Allah shine masani. ✍ ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876

Share this


Author: verified_user

0 Comments: