Friday, 6 April 2018




TAMBAYA TA 70

Home TAMBAYA TA 70

*_ZA KA IYA AURAN KANWAR MAHAIFINKA !!_*

                                *Tambaya*
Assalamu Alaykum malan ina da tambaya kamar haka: Kakana wanda ya haifi babana yana da Qani wanda suke baba daya amma ba mamarsu daya ba, toh zan iya auren diyarsa? na kasa fahimtar amsar,  don Allah a taimaka min na bashi amsa zuwa safiya,nagode,

                                    *Amsa*
To dan'uwa ya halatta ka aure ta, saboda kamar yadda malamai suke cewa: duk makusantan mutum ya haramta ya aure su sai nau'i hudu kawai ya halatta ya aura wato: 'ya'yan baffa, 'ya'yan gwaggo, sai 'ya'yan kawu da 'ya'yan inna, kaga ita wannan da kake so ka aura tana makwafin 'yar baffa ne, don haka sai ya halatta a aure ta.

Allah ne mafi sani.

Don neman Karin bayani duba: Majmu'ul fataawah na Ibnu-taimiyya 32\62

3\2\2015.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: