*_MAZIYYI YANA KARYA ALWALA?_*
*Tambaya:*
Assalamu alaikum wa rahmatullah malam ina yi maka fatan alkhairi mal. Tambayata anan itace mutum ne yayi alwala yayi komai sai da yaje masallaci ta tayar da sallah sai maziyyi ya fito masa shin malam mutum za sallame sallar ne ko zai karasa ta kuma yay hukuncin sallar tasa idan ya karasa allah ya karawa malam lafiya da wadatar zuciya na gode
*Amsa:*
Wa'alaikum assalam, ya wajaba ka yanke sallah, ka saké Alwala, an rawaito daga Aliyu R.A yace: "Na kasance mutum mai yawan maziyyi sai na umarci Mikdad ya tambayar min Annabi ﷺ sai ya ce maşa: Idan ya fito ka sake alwala, ka wanke azzakarinka, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 266".
Allah ne mafi sani
9\2\2016.
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.



0 Comments: