*_HUKUNCIN YIN MASALLATAN JUMA'A GUDA BIYU A GARI DAYA?_*
*Tambaya*
Assalamu alaikum
MALAM TAMBAYA : YANZU ZA KA GA DAN KARAMIN GARI, AMMA SAI KA GA SAMA DA MASALLACIN JUMA'A DAYA A CIKINSA, SHIN HAKAN YA HALATTA ?
*Amsa*
Wa'alaiku musalam, To malam babu wani hadisi ingantacce da ya hana hakan, saidai malamai sun yi sabani a cikin mas'alar zuwa maganganu guda uku: wacce ta fi inganci daga ciki, shi ne ya hallata ayi sama da masallacin juma'a guda daya a gari daya, mutukar akwai bukatar hakan, kamar ya zama masallacin farkon ba zai ishi mutane ba, ko kuma za'a samu wata fitina idan aka hadu wuri daya, ko ya zama akwai nisa tsakaninsu, ta yadda mutane za su sha wahala, wajan isowa zuwa gare shi.
Idan babu bukata abin da ya fi shi ne yin masallaci guda daya a gari daya, saboda daga cikin hikimomin shar'anta juma'a akwai samun hadinkan musulmai, da kuma nishadantar da juna, da samun lada mai yawa, hakan kuwa zai fi tabbatuwa idan suka yi sallah a masallaci guda daya, wannan ita ce maganar Ibnu Taimimiyya da Ibnu Bazz da kuma Ibnu Uthaimin, da wasu manyan maluma Allah ya yi musu rahama.
Allah ne mafi Sani.
4/6/2013
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.



0 Comments: