Friday, 6 April 2018




TAMBAYA TA 73

Home TAMBAYA TA 73

*_SHAFA FUSKA BAYAN KAMMALA  ADDU'A !!_*

                               *Tambaya*
Malam menene hukuncin shafa hannu a fuska bayan gama addu'a.

                                   *Amsa:*
To dan'uwa hadisi ya zo daga Umar- Allah ya yarda da shi- cewa: "Annabi ﷺ idan ya daga hannayansa ya yi addu'a ba ya mayar da su, har sai ya shafa su a fuskarsa"  Sunanu Attirmizi: 3386.

Wannan hadisin ya zo da hanyoyi masu yawa, saidai dukkansu suna da rauni, wannan yasa malaman hadisi suka yi sabani game da ingancin shi, Ibnu Hajara ya kyautata shi, saboda ya zo ta hanyoyi da yawa, kamar yadda ya bayyana haka a Bulugul-maraam a hadisi mai lamba ta: 1345.

Akwai wadanda suka raunana shi saboda suna ganin hanyoyin da yazo da su masu yawa, ba su kai su karfafe shi ya zama Hasan ba, wannan shi ne ra'ayin Ibnu Taimiyya kamar yadda ya bayyana haka a Majmu'ul fataawaa 22\509, haka Albani a Silsila Sahiha 2\146.

Malaman Fiqhu sun yi sabani game da shafar fuska bayan addu'a, wasu sun tafi akan mustabbancinsa, saboda sun gamsu da kyautatawar da Ibnu-hajar  ya yiwa hadisin, kamar Ibnu Bazz a daya daga cikin fatawoyinsa, akwai kuma wadanda suka tafi akan cewa ba za'a ayi ba, saboda rashin ingancin hadisan da suka zo akan haka.

Abin da na fahimta a wannan mas'alar shi ne ba za'a aibanta wanda ya shafa fuskarsa ba bayan addu'a, tunda yana da magabata .

Allah ne mafi sani

3\2\2015.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: