Friday, 6 April 2018




TAMBAYA TA 75

Home TAMBAYA TA 75

*_KARAWA AMARYA YAWAN KWANAKI, SABODA HONEY MOON?_*

                                *Tambaya:*
Tambaya meye hukuncin mutumin da yana da mata sai yayi amarya sai yayi mata visa suka tafi wata kasa wata daya a matsayin honey moon, to meye hukuncin daya matar, ya zalumceta kenan?

                                     *Amsa:*
To dan'uwa Anas R.A ya rawaito cewa: "Yana daga cikin sunna In mutum ya auri budurwa kuma yana da wata matar, ya yi mata kwana bakwai, in kuma bazawara ce kwana uku" kamar yadda ya zo a Sunanu Attirmizi a hadisi mai lamba ta: 1139, wannan sai ya nuna kari akan haka ya sabawa sunnah.

Amma Idan Uwar gida ta bada izni ya halatta ayi kari akan haka, tun da ya halatta mace ta sarayar da hakkinta na kwana, kamar yadda Saudatu ta bawa Nana A'isha kwananta, lokacin da girma ya zo mata, ta ga Annabi ﷺ bai damu da ita ba sosai, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 4914, wannan sai ya nuna halaccin sarayar da hakkin kwana, da yiwuwar yiwa amarya kari idan uwar gida ta yarda.

Allah mafi sani

31\1\2016.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: