*_DAGA HANNU SAMA LOKACIN ALKUNUT !!!_*
*Tambaya*
Assalamu Alaikum, Malam Jamilu, akwai hujja akan daga hannaye lokacin yin alqunut a sallah, musamman alqunut ta lokacin masifa ? nagode
*Amsa*
Wa l'alaikumussalam, To dan'uwa, zance mafi inganci shi ne mustahabbancin daga hannu yayin alkunutu, saboda Annabi ﷺ ya daga hannu a sallar asuba lokacin da ya yi addu'a ga wadanda suka kashe mutum saba'in makaranta, kamar yadda Dabrani ya rawaito a Mu'ujamussagir a hadisi mai lamba ta: 111, kuma Albani ya inganta shi a Irwa'ul-galil 2\181.
Sannan an rawaito hakan daga Umar da Usman da Ibnu Mas'ud, da Abu-hurairah.
Don neman Karin bayani duba Attalkis na Ibnu Hajar 2\40
Allah ne mafi sani.
1/2/2015
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.



0 Comments: