Friday, 8 June 2018




dan talaka 1 complete

Home dan talaka 1 complete

[9:41am, 14/05/2017] Queen yarmama: *⚽DAN TALAKA⚽* 1-5 By Maryam yarmama *FANTASTIC STARS WRITTERS* 🍀F S W🍀 *dedicated to* _salma ali wadah_ _asykhaleel_ _classic feedoh_ _anty khady_ *bismillahi rahamanun rahim* _wannan littafin banyishi don cin mutuncin wata ko wani ba,nayishine don fadakarwa,kuma kirkirace_ _wannan labarin yana cike,da abin tausayi,soyayya,kiyayya,fadakarwa,nishandartarwa,tsantsar darasi,cin amana da wulakanci_ _duk mai karanta littafinan sai ya tsuma mai zuciya_ *BAZAN MANTA DA DUK MASOYANABA,INA ALFAHARI DAKU ADUK INDA KUKE,HARMA DA MAKIYANA* _ubangiji Allah yabar zumunci_ *👤FARAWA👤* _jerin sunaye_ *FARUK DAN TALAKA *PRINCESS ZAITUN *SAFEENA *INNA FURERE *ALHAJI AMINU *AMMITA *SUWAIBA *🌈WURARE🌈* *Abujah villa *kauyen nassarawan kuki *united state of america(u.s.a) *kauyen adamawa *nassarawar kuki* Garine maicike da iska,dan karamin kauye da ake karaicin ruwa,garin akwai hadin kaida dadin zama ga wanda yasaba Wani matashin saurayi nagani,fari sol dashi,kyakyawa ajin farko,dan dogone,ga hanci ,idonsa dara dara,gaskiya idan bakayan da ka gani ajikinsaba bazaka taba tunanin dan kauye bane,tafiya suke da abokansa su uku Dayan na gefensa yace, *faruk* ashe yau wadansu yan birni sunzo su siya fili su gina gidan gona,wani alhajine bashida mutunci wai har kamfani zaiyi a garin nan, Kallonsa faruk yayi yace sallau,ka daina shiga lamarin wani,kayi rayuwarka,karka taba shiga lamarin wani inbashi yashiga nakaba Muntari yace aboki kayi gaisuwa,ai sallau da uban tsegumi yake,muyi sauri muje ku rakani zance kar larai tayi fushi Wani huci faruk ya fitar yace kaidai Allah ya shiryeka,ni fa gani nake soyayya bata lokacine,wlh kuma agarin nan ba macen da tamun,banda lokacin kula mace Dariya muntari yayi yace ayyah,aboki bakasan soyayyaba,soyayya ruwan kan hanya ,bakasan lokacin dazata riskekaba,munanan dakai Tsaki faruk yayi yace shirmen banza,komai kuce soyayya,nifa banda ra,ayin aure,kunga zanje gida in taya innata aiki, Dariya sallau yayi yace nidai mu hadu a *shaye shaye chamber*anjima A hankalo faruk yayi gaba yace kokuma chamban gulma ba. Wani gida naga faruk yashiga wanda an kewaye da langa langa,gidan jar kasa,wata matace itama fara,zata kai shekara talatin da biyar,bata wani tsufaba,amma talauci ya nuna ajikinta, Da sallama faruk ya shiga gida murmushi dauke akan fuskarsa,yace inna sannu da aiki Da damuwa akan fuskarsa tace sannu tilo da zuwa Tuni faruk ya nemi annurin fuskarsa yarasa sakamakon inna daya gani ranta amatukar bace,durkusa wa yayi yace innata meke faruwane? Hawayene yafara shatata a idonta,tace faruk wani mugu azzalumi yazo ya mana gargadi wai mutashi daga gidannan za,su gina kamfani.wai maigari ya anshe kudin gidan Faruk yace me?shine yasaki kuka,wlh ko za,a mutu inna hawayenki bazai zuba a banzaba,saina dau miki fansa Kuka inna tasa tana a a,faruk karka yarda kayi fada,banason yawan hayani,ka barsu da Allah,ai bamu kadai aka cutaba mutane diyawa aka cuta,inkasan na haifeka karka yarda kayi fada ,gobe ma yarshi zata zo ganin wajen. Cize lebe faruk yayi shiyasan zafin da yakeji,kasa ya iba ya dunkule hannunsa,yanajin zafin yadda mahaifiyarsa take kuka Suwaibace tashigo gidan,yarinyar yar kimamin shekara,sha shida da haihuwa,hannunta dauke da littattafan islamiyya a hannunta,durkusawa tayi tagaida inna Sannan ta gaida faruk dafe kirji tayi tace yaya naga motocin rusau sunzo ana rusa gidan makotanmu,Allah yasa ba namu,yanzu yazamuyi? Ran faruk bace dayaji umma na kukan ina zasu sa kansu,bayan wannan shine gidansu kwaya daya tak A guje yafita,ranshi abace,yaga manya manya motoci ,alhaji aminu ,aka bude mai mota ,bodyguard na takemai baya,a yatsine yake kallon mutanen kauyen domin arayuwarsa ya tsani talaka,ko yayansa bayaso su rabi talaka,hakama duk family dinsu basu dauki talaka abakin komaiba Wannan kenan By Maryam yarmama [9:44am, 14/05/2017] Queen yarmama: *⚽DAN TALAKA⚽* 5-10 By Maryam yarmama *FANTASTIC STARS WRITTER* 🍀F S W🍀 *dedicated to* _salma pinky_ _asykhaleel_ _classic feedoh_ _anty khady(my dohta)_ Alhaji aminu ya nufo wajen,da ma,aikata suke aikin rusau,yana bada umarnin ayi sauri a fara rusau Faruk ne ya nufo wajen,cikin bacin rai yace alhaji A fusace alhaji aminu yajiyo yana wani *dan talakan* ne yake kirana uwa yana kiran kare. Hado ido faruk yayi da alhaji aminu yace nine nan,dama akan maganar rushe gidajen nan ne,ba,a nemi shawararmu ba za,a rushe mana gida,to kasani bazamu taba yardaba,ka canza ra,ayi. Alhaji aminu ranshi ya bace matuka,yace hhhhhhhh kai kana *dan talaka*zakazo kana nunamin abin dazanyi,kaje ka tambaya waye alhaji aminu Faruk yace bana neman sani,domin bashida amfani awajena,nidai akan maganar hakkina nake magana,ba ruwana da wani saninka,bawanda ya isa ya rusamana gidanmu Bodyguard din, alhaji sunusi sukazo wajen da niyyar dukan faruk,cikin bacin rai alhaji aminu yace,ku kyalesa,kuci gaba da aikinku,asannu *princess*zatazo tayi maganinsa Budemai mota bodyguard sukayi,cikin fushi yashiga,akaja motar suka fita daga kauyen. Samari dayan matan garin suka cika da mamaki,don kowa yasan alhaji aminu bashida imani,saima yarsa *princess*da bata dauki kowa abakin komaiba Alhaji aminu yanufi airport yahau jirgi ranshi abace,yanufi gidansa dake abuja villa, Yana fitowa daga motar ,yashiga gidan,damatarsa yafaracin karo,a tafkeken falo,cikin mamaki tace alhaji mekuma yafaru ,tun da mukayi aure dakai,bantaba ganin bacin ranka ba sai yau,wai meke faruwane alhaji? Cikin fushi alhaji aminu yace,wlh wani dan iskan yarone ya mugun batamin rai,a kauyen nassarawar kuki, Salati amarya tasa tana agarin yaya haka tafaru, Shiru alhaji yayi yace ku kiramin *princess* Yaran gidanne yanmata suka fara fitowa,da samarai zasukai su goma,sai kwasar gaisuwa suke Dakyar alhaji aminu yake amsawa,shi burinsa yaga *princess*ko yaji sanyi arayuwarsa,don bawanda yakeso kamar *princess* Takun tafiya da taunar cingum,kakeji kas, kas Cikin murmushi alhaji yadago da idanunsa,da yar lele yayi arba tana sakkowa,murmushi takeyi *nikuma nace in wannan ce princess,gaskiya ta mugun haduwa* Yarinya yar fara,doguwa,coca cola shape,ga yalwar gashin gira dana ido,gata da dogan hanci,dakaramin baki pink,idonta dan dara dara,gashinta dabatasa dankwaliba har gadon baya,sanye take da wando jeans,da farar riga wanda aka rubuta *princess* Duk gidan suna kama,sosai,saidai princess tayi musu zahrah,don ita mahaifiyarta ta biyo a komai Princess yace ga alhaji aminu ,marainiyace tun tana da shekara daya mahaifiyarta ta mutu,tabarsu su biyu da yayanta mujaheed Karasowa tayi tafada jikin alhaji tana dady,waya tabamin kai? Alhaji yasaki ajiyar zuciya yace yawuce wani *dan talaka*bazagin duniyar da baiyiminba Azabure princess ta tashi tana what?who is he dazai tabamin dadyna,dad bani address din garin gobe saiya gane kurensa Amarya da uwargida da yayansu duk haushin *princess*sukeji ,saboda son da alhaji yake nuna mata tamkar gwal,tunba uwargidaba ta kullaci *princess*kullum si take alhaji ya tsaneta,haka yaran gidan daga yayannunta har kannenta bamai mata magana Adaren ranar princess bata ritsaba,saboda bacin rai wai wani kazami yazo,yabatawa mahaifinta rai Gari yana wayewa,taci kwalya acikin wani dogan riga mai guntin hannu wanda ya matseta ,dan siririn gyalle ta yafa,tadauki blue din takalmi mai tsini. Kiran kawarta tayi safeena ,suka hau jirgu suka sauka a airport,motane yazo yadaukesu,tunda princess suka shiga garin taketa toshe hanci,tana yamutsr fuska tacewa safeena,safeena ke bakyajin warin garinnan,wlh naki jinin talaka a arayuwata,Allah ya rabamu da talauci Princess tace mezai kaini ma in rabi talaka su ,watsamin talauci Murmushi safeena tayitace kamar nikenan wallahi banason talaka ya rabeni ko kadan ,ai ni duk dan talakan daya bude baki yace yana sona,sainasa an guntule bakinsa faruk da su sallau ana zaune a kusa da bishiyar dabino ,sansanyar iska tana kadawa, Motarsu princess ta faka,princess sai tishe hanci take da yatsine yatsine Muntari da sallau suka wangale baki,muntari yataba faruk yana aboki kaga wata kyakyawar fulawa kuwa,ai duk rashin son ya macenka dole kaso cikar nan Tsaki faruk yayi bai dago da idanunsaba yace zancen banza ,ba macen data isa in sota arayuwa, Princess ce suda safeena suka,fara doso wajen,cikin yanga da yamutse yamutse Kusan sumewa muntari da sallau sukayi, By Maryam yarmama [10:30am, 14/05/2017] Queen yarmama: *⚽DAN TALAKA⚽* 11-15 By Maryam yarmama *FANTASTIC STARS WRITTERS* 🍀F S W🍀 *dedicated to* Salma pinky,asykhaleel,classic feedoh and anty khady *this page is dedicated to _fantastic stars writters_ am pround of we,we are like one blood* Ahankali princess take tafiya uwa tana tausayin taka kasa, Harta wuce faruk bai dago idonsa yaga wacece ba,ko kamshin turarenta dayaji baisa yadago idoba Muntari yace kai masha Allah,amma aboki an barka a kallo,nasan wlh kana dago idonka kana arba da yarinyar nan zakaji kaunarta. Tsaki faruk yayi yace malamai kumin shiru,inkuna maganar matama wallahi haushi kuke bani,insokuke intashi inbarmuku wajen kuci gaba. Sallau yace yahakuri ,aboki baza,ayi hakaba Faruk yace wiwinnnan ya rage kuwa,sallau yace a a ba muntari ya shanyeba Faruk yatashi yace ba matsala,munshiga daji muje musiyo musha;dan yau akwai fada dayan yankinmu dana,yankinsu baba Sallau yace wlh aiyau akwai sara sa suka dan ubansu,sai sunyi bayani Princess ce tanufi wajen ma,aikatar,risinawa suke suna kwasar gaisuwa,a yatsine take amsawa, Ahankali tace wani dan iskan yarone ya batawa dadyna rai Daya daga cikin ma,aikatan yace ,ai ranki ya dade,kin baraso acan suda abokanansa,amma ga gidansunan kusa. Atare princess da safeena suka kalli gidan,safeena tabushe da dariya tana can you imagine princess?wani *dan talaka*yazo yaciwa dady mutunci,kalli gidan dasuke rayuwa,lalle kuwa yau akwai bala,i Princess ta yamutse fuska tana gaskiya bana,iyaji zan shiga gidanma,amma bari in daure,mushiga Ahankali princess take tafiya,harta shiga gidan batare datayi sallamaba, Suwaiba na daka,gero inna furere na surfe,dago kansu sukayi,atare inna tawashe hakori,ta kalli su princess dake yamutse fuska harda tufar da yawu,tace au baki mukayi,sannu da zuwa Princess ta dakatar da inna ta hanyar daga hannu tace,ki rike gaisuwarki bama bukata,ina tsinannen yaronki dayaciwa mahaifina mutunci Inna da sauri ta tashi tadafe kirji tana yata kiyi hakuri yarona ban tsine maiba,amma karki bari yazo yasami abinda kikemin Safeena tace ke tsohuwa ki iyewa bakinki,wlh ko yanzu kiji jiki,awani dalili zai nunawa dad dinmu yatsa,yana *dan talakan* Inna tace bayin Allah kuyi hakuri dan Allah,kubari yazo kwayi maganar nan,amma bana fatan yazo saboda ran kowannenku sai yabace,don gaskiya *tilo*baya jure ganin hawayena Suwaiba takalli inna tace inna kema kiyi shiru ki kyalesu,insu basusan mutuncin mutane ba,mu munada tarbiya Inna tace suwaiba kul kar inkarajin zancen nan abakinki kinji ko Princess taji ranta yabaci,wajen suwaiba tanufa,ta wanke fuskar suwaiba da mari,ta nunata da dan yatsa tana kisan dawa kike magana *yar alhaji aminu a.a maikudi* ce tsaye agabanki Dafe kunci suwaiba tayi tana kuka, Faruk ne yashigo gidan tundaga waje yakejin hayaniya,mutane suncika akofar gidan,matan aure sai lekowa suke, Faruk yanashiga,ko kallan inda princess take baiyiba,nufan inda inda inna take durkushe tayi tagumi yaje,yana inna meke faruwane?meyasameku Kafin umma tayi kokarin basa amsa,princess cikin zazzakar muryarta cike da izza da gadara tace tilo kake dasuna ko waye,ko tonice nabata musu rai,kazokayi abinda zakayi,kaima kuma kasha mari,kamar yanda kanwarka tasha Mari,kiris yarage tsohuwarka tasha mari,da bakinta ya subuce tafadi wata kalma datasha mari,kuma na mari banza Afusace faruk yajuyo yadaka mata tsawa heeey! Jikin princess yahau bari,don a tarihin rayuwarta bawanda yataba mata tsawa Faruk ya dunkuke hannu,saboda bacin rai kirjinsa har dagawa yake,yace keee aiko baki mari banzaba,don dakinyi kuskure kin mari kyakyawar fuskar uwata,dasaikinyi nadama wlh,dasaina guntule hannayenki,bakisan wanene faruk bane, Matsowa yayi,dab da princess,wani kwarjini ya mata,ta sunkuyar da kanta, Hannu faruk yasa yadago da kyakyawar fuskarta,yace ki kalleni dakyau, Dara daran idanunwansa yazura mata,kallon kallo akafara a tsakaninsu Hawaye taf yacikawa,princess ido,kiris yarage yaxubo, Faruk yace bacemin daganan banza,mummuna,inna kara ganin kafarki a gidanmu kinsan Allah saikinyi nadama,da faruk kike zancen Wlh dabadan mahaifiyata bazataji dadyba,dasaina miki duka ,kuma ni nasan mutuncin ya mace,banza ajawuya Hankadata yayi ,tayi taga taga kamar zata fadi,kuka princess tada tafita dagudu daga gidan,safeena ta bita abaya, Ihu gami da tafi yan kauyen suka fara,yanmata saijin son faruk suke,amma ba fuska Dagudu,princess tashiga motar ,tana kuka,tunda take arayuwarta ba,a taba mata cin mutunci kamar hakaba,tsanar faruk taji ya lunku azuciyarta,wlh saita dauki fansa Safeena ce tashigo motar,tace driver yaja sutafi,kuka princess take tamkar ranta yafita,harsukaje airport,suka hau jirgi Zazzabi mai zafi yarufe princess,ko iya daga hannunta batayi,safeena ta rude,alhaji takira awaya, Suna sauka a airport motoci sukazo tararta,alhajine yafito daga daya daga cikin motar,kamar yayi kuka Yana nashiga uku yar lele karki mutu,wayyo wlh saina dau fansa,dani yake zancen Asibiti suka wuce,aka dorawa *princess* drip Amarya da uwargida sunata adu,ar Allah yasa tama mutu, By Maryam yarmama [11:05am, 14/05/2017] Queen yarmama: ⚽DAN TALAKA⚽ 16-20 By Maryam yarmama *FANTASTIC STARS WRITTER* 🍀F S W🍀 *dedicated to* _Salma pinky,asykhaleel,classic feedoh and anty khady_ Princess har mafarkin abinda faruk yamata take,tata ihu da birgima,tana wayyo dady zai kasheni, Alluran bacci ake tayi mata,momin yarace da anty amarya suke jinya Momin yara(uwargida)ta ta tsaki tana yarinya saikace mayya ,aini yayi daidai da yaron yaci ubanta ,wlh dazan gansa dasai na zugasa, Anty amarya ta shekw da dariya tace rabu da shegiya yar katan uwa,aini naso yakasheta ko yayanmu sa samu shiga Haka kullum suke fada Alhaji yasa akaje aka kama faruk aka kullesa a cell,anata ganamai azaba,inna furere tashiga damuwa,faruk ne yake zuwa yayi aikin karfi ya nemo musu abinda zasuji gashi ankamasa *princess* ta warware aka sallamosu daga asibiti, Momin yara tace ammafa banso hakaba naso giwa ta mutu mun huta,amma intasan wata batasan wataba Motarsu tashiga harabar gidan,yaran gidan suka fito ,kowa dayaga princess saida ransu ya sosu,musamman, anty maryam da anty fatima,najib kuwa yafi kowa bakincikin dawowarta,don ya tsani yabudi ido yaga princess a gidan suda kamaludeen Itama harara princess tafara dankara musu,tayi shashinta,tanajin nishadi gobe,masoyinta zai dawo,faga kasar malaysia *uncle affan* Kowa ya hallaci dinning harda alhaji,kujera sunkai goma sha biyar a dinning din,duk sun zauna,princess ce bata wajen Alhaji yace maryam jeki ki kiramin princess Turo baki maryam tayi ta tashi tanufi dakin princess,ta kutsakai ciki,princess tana kwance tana chatting,bama tasan anshigoba Maryam ta kalli tafkeken hoton uncle affan da princess sunyi hoto sunsha kyau, manne a jikin bango Takaici gami da kishi yakamata,domin arayuwarta ba mutumin datake kauna kamar uncle affan, Agadare tace ke *zaitun* kitashi ubanki na kiranki Princess ta dago da kanta tayi murmushi tace ,wlh maryam kina bani mamaki,meye zakizo kimin shouting akaina ko kin manta da princess yar lelen baba kike magana Anty maryam tayo kanta tana karki kuskura kimin rashin kunya wlh donni ba sa,arki bace, Princess tace to anty anji,tafi dallah gani zuwa Anty maryam ranta yabaci ta hayo gadon tana wlh yau sainaci uwarki a gidannan Princess tace saidai kici uwarki momin yara donkin girmeni dawata uku saikita rainamin hankali Bugu anty maryam ta kawo mata,princess ta yi saurin kaucewa ta na ihun dadyna zata kasheni Alhaji da momin yara ne da anty amarya suka shigo, Princess ta rushe da kuka tanufi wajen dady aguje,tana dady dabaka zoba Allah ne yasan kadai dukan dazatamin Anty maryam tacika da mamaki tace wlh dady karya takemin zagina tayifa Alhaji yadakawa anty maryam tsawa yace kinci gidanku,kuma nafasa siya miki motar,yaja hannun princess suka wuce dinning Momin yara da anty amarya haushi yakamasu,suma suka nufi dinning din Alhaji yace princess zabi kujerar da kikeso kizauna Kujerar da kamal yake zaune tayi pointing Alhaji yace kamal tashi princess tazauna,ka koma,wani kujerar Kamal kamar yayi kuka wai kanwarsa ta biyu tana rainasa,wlh saitaci uwarta Ayangace princess tazauna,tayi pointing din amira tace yaki zokiyi serving dina Anty amaryata tace gaskiya alhaji iskancin yarinyar nan yayi yawa,gaskiya amira ba baiwarta bace dataza zuba mata abinci Alhaji yadakawa anty amarya tsawa shut up,nonsense amira taso kizo kizubawa yar lele abinci ,kar ranta yabace,did you get me A tsorace amira tatashi taje gaban princess tana zuba mata abinci badan ranta yasoba Hawayene yafara tsitaya a idon amarya,tace alhaji nikake kira da nonsense akan zaitun?tashi tayi yayinda kowa yakecin abincin,kowa sai daukan alwashi yake tunda alhaji yakusa tafiya saitasha duka By Maryam yarmama [11:59am, 14/05/2017] Queen yarmama: *⚽DAN TALAKA⚽* 21-25 By Maryam yarmama *FANTASTIC STARS WRITTERS* 🍀F S W🍀 *dedicated to* _salma pinky,asykhaleel,classic feedoh and anty khady_ *IYALAN ALHAJI AMINU* Asalinsu masu kudine,arxikinsa alhaji aminu yafara tundaga kakanni kakanni,alhaji aminu yakasance dane ga alhaji ibraheem maikudi,wanda yake ministan man fetur,kafin Allah yamai rasuwa,matarsa daya safaratu,sukansu sun kasance fulani usil,yayansu hudu ,badamasine babba sai hajara sai aminu sai zainab,sun taso cikin so da kauna,mahaifinsu aminu adaline,kowannensu yayi makaranta a kasar waje ,inda badamasi ya auri,yar saudiyya suna saudiyya da zama,sai hajara ta auri wani major soja suna maiduguri dazama,sai aminu dayafara auran momin yara ,ibo ce sunanta munnira,yar garin lagos ce,kamak suka fara haifa , bayan wata uku,alhaji aminu yakara auro mamansu princess ,balarabiya lokacin yaje saudiyya,sunanta mehfuza ,yar gwamman nan saudiyya,ta haifi mujaheed,bayan shekara daya,momin yara ta haifi najib,momin yara akwai kishi ta tsani ta budi ido taga mehfuza,ko kallon arziki bata mata Momin yara tasake haifan anty binta ,sai bayan shekara biyu aka haifi anty maryam ,anty maryam tana wata uku aka haifi zaitun wanda ake kira da princess,tunda tazo duniya alhaji yake matukar kaunarta,kullum yana manne sa ita,ko kukanta bayaso yaji, Princess tanada shekara daya a duniya,mehfuza ba ciwo ba komai ajali ya risketa,alhaji yayi kuka sosai,kamar tansa zai fita,yan uwan mehfuza sukazo suka tafi da mujaheed, Alhaji dakyar mahaifiyarsa safaratu tasa yakara auren anty amarya yar jahar sokoto sunanta hasiya,jininsu yazo daya da momin yara,amma kowa jin haushin kowa yake azuci,farkon haihuwarta ta haifi amira,sannan mama,sai yusif,sai momin yara takara haihuwa ta haifi umma sai baba karami shikenan alhaji aminu yace ya isa haka,yasa aka juyawa kowa mahaifa Andora princess karan tsana,abayan idon alhaji ata zaginta ,ahaka princess suka taso tagama karatunta a fannin,accountant,tana da shekara ishirin da daya aduniya,yayinda antu binta takeda shekara ishirin da uku ana shirin mata aure,dawani dan kanol,duk da haka alhaji baiso hakaba donyaraina arzikin gidan Wannan shine takaitaccen labarin alhaji aminu Washegari princess ta tashi da mafarkin faruk,tagumi tayi,tashiga toilet tayi wanka,tanaso taje tasamu dady ya kaita kurkuku taga halin da faruk yake ciki Tana fitowa ,tayi kwalya ta feshe jikinta da turare tanajin nishadi a zuciyarta yau masoyinta affan zai dawo, singlet fari tasa ta dora wando ja iya gwiwa,sannan ta tufke gashin kanta mai uban yawa da yellon ribom,riga top ta dora akai,kallan wandon ja,singlet din ciki yellow,ribon dintama yaro,tayi matukar kyau. Anty maryam ce acinyar momin yara tana kuka tana wallahi momy son affan zai kasheni,kitaimakamin kar princess ta kwaceminshi Momin yara tace haba maryam saikace ba mace ba,kinsan me za,ayi kiyi hanyar dazai kwana dake,saikuzo kimai karyar kinada ciki,inbai aurekiba xaki fallasashi(oh wata uwa) Rungumar momin yara anty maryam tayi tana that why i love you mum,ina maganin kin anso yanda bazai musa kwanciya daniba Momin yara tace tun yaushe,kamar karan mota nakeji, alamunya iso,kije kiyi wanka , Dagudu maryam tashige toilet din momin yara ta fesa wanka Wani kyakyawan saurayine yafito daga wani hadadden mota,dogene yanada dan jiki kadan,wankan tarwadane,yayi matukar haduwa,yanada gashin gira ,yatara gashi,kuma gashin yasha gyara,yana da dogan hanci da baki dankarami pink,yana da ido dara dara,daka gansa kasan ya amsa sunnansa *affan* Yaran gidanne suka fara fitowa suna ga uncle ga uncle, Murmushi affan ya saki,yana shakin hand dasu,shidai burinsa yaga *princess* Alhaji ya rungumesa yana welcome back my son ya kabaro su mahaifinka da yan uwanka dafatan komai normal Affan kamar bayaso yayi magana yace wlh suna nan kallau, Anty amarya ce take zuwa tana a a bakin malaysia nake gani ko na saudiyya Dariya affan yayi yana duka ina wuni Anty amarya tace lfy kl ya akabarosu Alhaji ne yace wai ina princess take,ita bazata zo ku gaisa bane, Princess ce take sakkowa daga upstair tana dad gani Sakin baki affan yayi, yana kallon yanda princess tagirma harta maganarta ta chanja,yau almost 5 yrs basa tare, saidai chatting kawai da turo hotuna,nan ya kwadaitu , Alhaji yayi dariya yace affan yadai kaga yanda yar kanwarka tazama ko?saima kaga maryam Affan yace ai girma ba wuya Ayangace princess tazo ta wuceshi tana uncle affan hi welcome back Affan yacika da mamaki,yaji takara burgesa Wajen dadi,tanufa,tace dad yakamata ace ansako wannan yaron faruk,ko ba komai yaci wuya Alhaji yace duk mekikace shi za,ayi bari inbuga waya asakesa Princess taji wani dadi aranta,batasan meye daliliba tace nagode dad,Allah yaja kwana By Maryam yarmama [9:28am, 15/05/2017] Queen yarmama: *⚽DAN TALAKA⚽* 26-30 By Maryam yarmama *FANTASTIC STARS WRITTERS* 🍀F S W🍀 *dedicated to* _salma pinky,asykhaleel,classic feedoh and anty khady_ _♥here is ur page *huraira yabo*you are part of me,i love the way you care about me,_ _the fans of *tarewar amarya hudah,*am going to use my time,to give you a vote of thanks,thank you for ur prayer and support,i love you so much,you are so many,i salute you all_ Wanka uncle affan ya shiga, Maryam tabi ta dayan kofa,tasa zunbulelen hijjabi,amma kayan dake jikinta ,wasu fitsararrun kayane,bangaren uncle affan tawuce,tana zuwa tawuce falonsa,tashige dakinsa,tacire hijjabi Uncle affan yafito daha toilet yana tsame ruwan jikinsa, Cikin karairaya,tace good morning uncle Tsawa uncle affan yadaka mata yace ke wacce yar iskace,waya baki dama ki shigomin dakina iye? Cikin rangwada maryam ta tashi ta dora hannu akan kafadarsa tana murzawa,tace uncle ina matukar kaunarka,zan baka duk me kakeso a jikina indai zaka soni,zamuyi rayuwa. Ran uncle affan yabace ya hankadeta chan gefe,yana nunata dadan yatsa yace ke maryam ,yaushe kika girma da harzaki,zokina gayamin wannan maganganun,to kisani uncle ne agabanki kuma *zaitun* ce tayi daidai da rayuwata,get out of my room Tsaki maryam tayi tazura hijjabinta tana magana ciki ciki,ta ajiye numbanta akan gadon tana duk randa kake da bukata ta ka kirani Kota kanta uncle affan baibi ba,yaci gaba da abinda yake Tana fita sukaci karo da princess zata zo wajen uncle affan,tsaki maryam tayi tabangaje princess da niyyar wucewa Cikin zafin nama princess ta rikota tana wakikewa tsaki?kuma meya kawoki dakin uncle affan? Maryam tace dallah malama sakeni,kije ki tambayi uncle affan din shi yasani ai Afusace princess tanufi hanyar dakin,tabude tashiga da sallama dauke abakinta,a hankali uncle affan ya amsa,murmushi dauke akan fuskarsa yace my dear kishigo Fuskarta a murtuke tashigo,tana uncle affan meya kawo maryam dakinka ? Uncle affan yace momynta ne ta aikota,ta gaisheni,kuma tanason ganina Ajiyar zuciya princess tayi tana uncle affan kasan yanda nake sonka kuwa,Allah yasa baka kula wata a malaysia ba Uncle affan,yazo ya durkusa agaban princess,ya rike hannayenta yana murzasu ahankali,murmushi dauke akan fuskarsa yace haba inada princess mezai kaini,in kula wata,ya mace Lumshe ido princess tayi ita tasan yanda takejin son affan aranta,a hankali taji yana kokarin kai hannu akan kirjinta,matsawa tayi tana zaro ido tana meye haka uncle? Matsowa uncke affan yayi,ya rungumota,yana haba princess kinsan son da nake miki bazan cutar dakeba,ina cike da sha,awarki kadan zaki bani kawai Fincikar kanta princess tayi ta tashi tsaye jikinta na tsuma,tace uncle affan bangane me kake nufiba,anya uncle son dakakemin na gaskiyane kuwa,anya baxaka karyamin zuciyaba kuwa Tasowa uncle affan yayi yace princess wallahi ina sonki,ai in munyi bawanda zaisani,kuma ai two month kawai yarage in aureki Girgiza kai princess tafara tana a a bazan taba amincewa ba,komin lalacina bazan tabayin zinah ba,hawaye taji ya taho mata ,fita tayi,ta nufi dakinta ta kulle kofa ta fada gado tana kuka A bangaren uncle affan yakasa jurewa,maryam ya tuno da dazu tamai tallan kanta gashi arha,tsaki yayi ,yadauki numban yasa a wayarsa,ringing biyu aka dauka,uncle affan yace hello maryam ce? A dayan bangaren akace eh dawa nake magana Uncle affan yace nine uncle affan kizo dakina yanzu ,ina jiranki. Kashe wayar yayi,yana tunanin dawani ido zai kalli alhaji yabatamai diya Ba,afi minti gomaba,saiga maryam tashigo,murmushi dauke akan fuskarta, Uncle affan ,ya kalleta,yace harkin zo Cike da karairaya maryam tace nazo ranka ya dade konayi lattine? Uncle affan yace ko daya, Maryam tahawo gadon,nan suka fada duniyar shedanu Tundaga wannan ranar maryam take zuwa suna sheke ayarsu da uncle affan Uncle affan,baikarawa princess maganar lalataba,saidai su zauna suta hirar soyayyarsu. Ahaka har yayi sati daya cur agidan, Princess ce zaune a falo,tana wayada da safeena,ta yaushe zaki dawo kasar ne? Safeena tace inaga nanda jibi Princess tace hmmm nima na dade ban fita wajeba,amma inasa ran,bayan aurenmu da yaya affan,zamuje honey moon malaysia Maryam ce tazo wucewa,cikin zuciyarta sai dariya take,tana zakiga aure,sai randa kikaga katin gayyatar auren uncle affan da maryam Wucewa tayi,tana wai ina anty binta tashigane ? Amirace tazo giftawa,ta harari princess Hada ido sukayi da princess,princess ta katse wayar da takeyi tace zonan amira. Dagudu amira ta falfala zuwa shashinsu,yayinda princess tabita tana wallahi har gadon uwarki saina biki nadukeki Aiko amira ta buya abayan anty amarya tana momy kinga wai anty princess ce xata dukeni Ran anty amarya abace tace mekika mata Kafin ta bada amsa princess tace uban wayace taharareni ni sa,artace Anty amarya tace keda kike raina yayanninki fa,ashe ba dadi? Princess tace bari wlh dadi yazo,sai narama agaban kowa zan zaneta Anty amarya tace ai alhajin yazo,wallahi yau koni koke agidannan,wasa kike da basakkwaciya Princess tsaki taja tace inma bararojiyace meruwa,fita tayi tana wallahi kowa sai yaji ajikinsa Anty amarya tace shegiya sai kyau uwa aljana *BALA,I A DAKIN UNCLE AFFAN* maryam ce tsaye,tana nifa kasan nayi dani don cikinka nasati dayane ajikina Uncle affan cikin rashin nuna damuwa yace ki zubar mana,ai bani nafara saninkiba balle kice cikina ne Maryam tace,hmmm affan kanaban mamaki,wallahi bazan zubar dacikinnanba,kuma Alhaji yana dawowa zan gayamishi,ince kamin fyade kamin ciki,kuma tsaf zai yarda, Uncle affan yace menene hujjanki,ai alhaji yasan ni nakwaraine Dariya gami da tafi maryam tayi tace hmmm,tokasani kasan meyasa duk kudin mahaifinmu bai barmu munje waje muyi karatuba harta princess din da yake lailayawa uwa gwal,tokasani yasan duk yawanci wanda yayi karatu awaje sune tarbiyyarsu take lalacewa,sune shaye shaye,bin mata ,dadai sauransu Jikin uncle affan yayi sanyi yace,maryam ki rufamin asiri dan Allah Maryam tace kokuma murufawa kanmu asiri mu auri junaba Uncle affan yace,haba maryam yakikeso inyi da princess,bayan da itanayi alkawarin aure Maryam tayi dariyar keta kazubata a kwandon shara,don maryam kadirkawa ciki ba princess ba *RANAR WANKA......* an hallara a falo,alhajine a tsakiya,princess tana kusa dashi,kowa dai ya hallara har,kaka safaratu(maman alhaji) Alhajine yace alhamdullillah,kamar yanda na yanke shawara cewa zan hada auren affan da yar lele;to yau Allah ya kawo ranar,inaso kowa in tambayesa ko yanason dan uwansa,zanfara daga kanki princess yar lelen baba kinason uncle affan? Lullube fuskarta tayi tace eh dad Kaka safaratu tace yar jakar uba,zaki auremin miji Dariya alhaji sukayi,yayinda momin yara suka murmurtuke fuska Alhaji ya kalli ,uncle affan da kirjinsa yake dukan uku uku,yace kaifa affan Uncle affan yaji duniyar tamai zafi,suna hada ido da princess,ta kashe mai ido,tayi dariya,tausayin tane gamida sonta ya kamashi,gumi ya fara tsattsafo mai, Su maryam anbaza kunne aji me affan zaice Alhaji yace affan kaifa nake jira Kaka safaratu tace hmm kodai kunyata kakeji,to ai kasakeni Yake uncle affan yayi yace dady kayi hakuri ,ba zaitun nakeso ba maryam nakeso Tashin hankali ba,asa masa rana By Maryam yarmama [4:17pm, 15/05/2017] Queen yarmama: *⚽DAN TALAKA⚽* 31-35 By Maryam yarmama *FANTASTIC STARS WRITTERS* 🍀F S W🍀 *dedicated to* _salma pinky,asykhaleel,classic feedoh and anty khady_ _♥this lovely page and sweet page,goes to *first lady*(umma shehu)the apple of buhari eye,i love the way you respect and love people,you are a star to me,that i will not let it go_ Alhaji yace affan wani magana kake fada haka,sokake kasa princess atashin hankali,in wasa kake kama daina,don da princess kukayi alkawarin aure Uncle affan ya tsunkuyar dakai yace dady,tabbas maryam nakeso itazan aura Princess tashi tayi hawaye na zuba a idonta,ta kalli alhaji ,taruga a guje zuwa bangarenta tana,kuka mai tsuma zuciya,da narka zuciyar mai sauraro Alhaji ya tashi yace affan kaban mamaki,amma kuje kuyi auranku,karku sani aciki, Kaka safaratu tace a a aminu baza,ayi hakaba,kasan abinda yaron nan ya hangane,kawai ku yanke auren tare da na binta sati biyu ayi agama Alhaji dayake mahaifiyarsane baya iya musawa,yace hajiya duk abinda kikace daidaine Allah yayi albarka zan kira ,yaya yazo daga saudiyya ayi maganar,tashi yayi ya karkade rigarsa ,yanufi dakin princess Kuka princess take uwa ranta zai fita,tana affan kaci amanata,kagama da rayuwata,kacuceni Alhajine ya shigo dakin a hankali yace yar lele,ki share hawayenki,kamar yanda banason inga hawaywn mahaifiyarki margayiya mehfuza,haka banaso inga hawayenki Tashi princess tayi taje wajen alhaji ta rungumesa,tana kuka tana dady,raina zai fashe,zuciyata tanamin zafi,inaji araina mutuwa zanyi ,uncle affan ya cuceni,dama ashe tunda baya sona,baya kaunata ,yasa nakamu da sonsa? Alhaji cikin tausayawa yace yar lele,kisamu wuri ki kwanta kidaina kuka Allah xai miki sauyi dawanda ya fishi komai,in Allah ya yarda dan gwammna zaki aura Ajiyar zuciya,princess tayi,ta saki alhaji ta kwanta, Alhaji ya kura mata ido kamar yayi kuka,yakeji,haka yafita daga dakin ransa abace A bangaren anty amarya da momin yara har kayataccen walima suka hada, Don murna,maryam jitake kamar tasa ruwa akasa,tasha tsabar farinciki , Princess ta tashi daga barcin da take,mai cike da mafarkin faruk,suna cikin lambu suna soyayya,faruk yana nine farin cikinki princess ,nizan kula dake har abada Tagumi princess tayi,tana oh meyasa wannan bawan Allah yakeso yashigomin rayuwata,bayan yasan niba tsararsa bace,tsaki tayi tashiga toilet ta dauro alwala tayi sallah,tana nafilfila,dayake bawani ilimin addini ne da itaba batasan me take fadaba,shafawa tayi,taxauna,a yar kujera,tana tunanin yaudarar da uncle affan ya mata. Princess ta ayyana a ranta baikamata ta kyalesa ahakaba yakamata ta cusamai haushi itama,kamar yanda ya karya mata zuciya,bata katse hanzarintaba taji muryar uncle affan yana sallama Ran princess inyayi dubu yabace ,azuciya ta amsa sallamar Uncle affan ne yashigo sanye yake da farin,jallabiya ,dayake ranar juma,ane, Uncle affan yace princess,kiyi hakuri ba laifi........ Kafin yakarasa ta katseshi tahanyar ya isa,mayaudari,azzalumi,kawa kalamanka ado da karya,duk abinda zai fito abakinka,bazan sauraraba,mugu azzalumi kazo kagani,ko na mutu da ciwon sonka,to gani atsaye gamgam,kamar soja abakin daga,Allah yaciremin sonka,kamar yanda Allah yama sauyi dani to haka nima nake roko Allah yabani mai sona tsakani ga Allah Uncle affan tundayake arayuwarsa bai taba sanin princess tanada masifa irin yauba,yace prin...... Princess ta katsesa ta hanyar cewa dakata dakata,banson jin kalamanka da in zauna dakai gwanda nazauna da bakin maciji Uncle affan yaji kalmar ta doki kunnensa hartamai zafi,a fusace ya fice,zuciyarsa yana tafarfsa Princess tazauna tana tunanin zuwa kauyen nassarawan kuki,taje ta duba faruk da mahaifiyarsa😳😳😳 Ji yanzu take tafara damuwa da lamarinsu faruk ,kuma yafara burgeta daga ganinsa zaiyi jarumta,kuma zaiga mutuncin ya mace By Maryam yarmama [6:35pm, 15/05/2017] Queen yarmama: *⚽DAN TALAKA⚽* 36-40 By Maryam yarmama *FANTASTIC STARS WRITTERS* 🍀F S W🍀 *dedicated to* _salma pinky,asykhaleel,classic feedoh and anty khady_ _this page, is dedicated to, *yarmama and hajur*novel group,thank you for ur love and support_ Washegari tun sanyin safiya,princess tayi wanka taci kwalya,cikin doguwar riga tayi rolling din kanta, Fita tayi tasa driver yajata zuwa airport tayi bizza,tahau jirgi zuwa garin nassarawar kuki Sauka tayi a airport,inda ma,aikatan alhaji aminu sukazo suka tareta,wani super market tashiga ,ta siya buhu bunan su shinkafa,da caton din su makaroni,da indomie,dasu faro water,da lemuka kala kala,a boot aka dinga zubawa Shigar kauyen,wani nishadi princess takeji,har motarsu tafaka a kofar gidan,tsoro da fargabane suka kamata harta kasa fita daga motar Driver yajiyo yace ranki yadade inaza,a shiga da kayan Princess tace ka kira yara su shigar da kayan cikin gidannnan,ta nuna gidansu faruk ,driver yafita daga motar,yafara umartan yara su shiga da kayan gidan Inna furere tana tsince shinkafar hausa,faruk na tayata ,suna hira, Sukaga ana shigowa da kaya ninki ninki Suwaibace tace wa yaran ku anya ba batan hanya kukayiba,mu yaushe rabonda muga irin kayan nan Faruk ya kalli kayan ya watsar yaci gaba da tsince shinkafar,inna furere taga sai shigo dakaya ake,tace wai nikam waya aikekune yara Dayan yaron yace watace hajiyace tana waje Kafin su rufe baki,princess tashigo bakinta dauke da sallama,yar karamar muryarta ya doki kunnen faruk Inna furere ce tayi karfin amsa sallamar,suwaiba a tsorace tagudu daki Princess ta durkusa,harkasa tana gaishe da inna furere Cikin sakin fuska inna furere ta amsa don ita bata ,rike mutum a zuciyarta,tace,lafiya kallau yarinyata,ya aka baro mutanen gidan Princess ta amsa lfy kl Princess tadawo da hankalinta kan faruk dake tsince shinkafa,ko kallon inda take beyiba,ransa abace ya murtuke fuska,pink din lebensa ya koma ja tsabar bacin rai,a hankali tace ina wuni yaya faruk Tsawa yadaka mata,ya tashi yana hey,duka shinkafar yabare,yace meya kawoki gidanmu?muna talakawa,marasa gata,meya kawoki gidanmu,duk cin mutuncin da kuka mana bai ishekuba? Ahankali princess tace a a yaya faruk nazo in nemi yafiyarka,nagane kuskuren da na tafka,talaka da mai arziki daya suke awajen Allah Faruk ya daka mata harara yace ashe kunsan da haka kuke,gallazawa talakawa,kuka tsani talaka,ki tashi kibar mana gida ki kwashe tsiyarki bamaso,Na Allah muke jira Inna furere tace tilo ka sausautama mana,haka tilo karka manta dan adam ajizine Faruk yayi buzu buzu da gashin kansa,wanda da a kwance yake luf luf,ya naushi hannunsa,shiyasan yanda yakeji,yanda suka kullesa a kurkuku Dasauri yanufi hanuar waje,da niyyar yaje yadan taba shaye shaye kohankalinsa ya kwanta,caraf yaji princess tarike mai riga,gwiwowinta akasa,tarushe da kuka mai sauti da tsuma zuciya Toshe kunnensa;faruk yayi don arayuwarsa ya tsani yaji kukan ,ya mace,bai juyoba bai yanke wani hukunciba Princess taci gaba dacewa yaya faruk dan Allah ka yafemin karka tafida fushina,kaduba maraicina,banda kowa sai mahaifina Tausayintane yakama faruk,juyowa yayi a sanyaye ya hadiye rai yace tashi na yafe miki Murmushi tayi tace nagode,zamu iya abota dakai Shekeke faruk ya kalleta yace,wannan kuma baki samu karbuwaba,domin bana abota da mata Princess taji sonshi yakara narkuwa azuciyarta matsala daya data tuno,alhaji yayi alkawali duk wacce ta auri talaka acikin yayanshi sai ya tsine mata ,kuma bashi ba ita har abada,koda princess ce,jikintane yayi sanyi lakas tace toshikenan Bai kulataba yayi ficewarsa,yayinda tazauna a kusada inna furere tana inna meyasa faruk yake da rashin kula da mutane? Murmushi,inna furere tayi,tace ai tilo haka ya taso,a halinsa ba abinda ya canja,amma yana darajarta ya mace,da ace ke namijice dayau kinshiga uku awurinsa Suwaibace tafito daga dakin,tana murmushi, Nan take princess suka hada ido da,ita jininsune yahadu;don suwaiba sa,ar amirace Princess tace,yan mata ya sunanki Suwaiba tace sunana suwaiba Princess tace wow kyakyawar suna nikuma sunana zaitun,amma ana cemin princess wato sarauniya Suwaiba azuciyarta tace wannan meta maidamu tadauka bamajin turancinne,a fili tace amma kinyi dacen suna Princess tace nagode ,hirane ya barke atsakaninsu,daga inna hare har suwaiba,sunji dadin zama da princess Labarin zaman doya da manjan da akeyi a gidansu tadinga basu,inna hare ta tausaya mata Suwaiba tadauki tulu tace inna,zanje diban ruwa, Princess tace yauwa suwaiba muje in rakaki Inna tace to adawo lfy,karfa kudade Tafiya suke suna hira duk inda ta gifta kallonta ake,bata taba tafiyar kafaba sai yau,ringing din wayarta taji,sunan dadynta tagani dauka tayi,tans hello dad Daga dayan bangaren akace princess ina kika shigane,? Princess tace ina gidansu safeena,sai gobe zandawo Alhaji yace yayi kyau kigaishe dasu Kashe wayar tayi sukaci gaba da hira, Princess tace suwaiba kinsan me nifa gaskiya son yayanki faruk nake,mexanyi ya soni don naga mata basa gabansa Zaro ido,suwaiba tayi tace tab,kima fidda rai indai yaya faruk ne,ba sauraran mata yakeba,mata nawane suke zuwa,kauyen nan nemansa,rabin matan garin nan namu sonsa suke,har yar maigari AMMITA wacce tafi kowa kyau da iya gayu a kauyen nan,,amma ko kulata bayayi,har magana taje gaban maigari,anzo an nemi yaya faruk yaki zuwa Kishine ya tokare, princess jiki a sanyaye tace ashe da sauran rina a kaba,niko inason ganin kishiyata AMMITA dinnan Suwaiba tayi dariya tace anty kenan,wannan yar iyayin nan kikeso kigani,ko abakin kogi kwalya take,gatada turancin karya Dariyane yakusa yakama princess tace zanso inga ammita kuwa Kogin garin suka nufa,yan matane kauyawa,kowacce tasha damara uwa zasuje dambe,kallo ya koma,kan princess Wata tace suwaiba ina kika samu baturiya yar birni Suwaiba tace budurwar,yaya faruk ce Atare yan matan wajen suka,ce budurwar faruk? Waigawa suwaiba tayi sakamakon jin karar barewar abubuwa Kayan kwalyan ammitane yabare,kishi ya motsa,tashi tayi Princess taga wata yar lukuta,ba laifi black beauty ce ammita,fuskarta yasha kwalya tayi kyau Princess ta ayyana tace ba shakka wannan itace ammita,saboda tafiyar datake na kasaita zai tabbatar maka da itace ammita Wajen ta doso masu take mata ,baya suna biye da ita,daradaran idonta ta seta akan na princess cikin turancinta na karya tace ,is who she(😂who is she) Dariyane ya kusa ya kwacewa princess amma ta matse,taseta nutsuwarta,tace au bakiji abinda,suwaiba tafada bane budurwar faruk ceni,ke kuma wace awajensa? Ammita ta dauki hannu da niyyar wanke fuskar princess da mari Ji tayi anrike hannunta,an watsar Faruk ne da muntari da sallau a tsaye *masu karatu kuyi hakuri zan tsagaita anan* By Maryam yarmama [9:35am, 17/05/2017] Queen yarmama: *⚽DAN TALAKA⚽* 41-46 By Maryam yarmama *FANTASTIC STARS WRITTERS* 🍀F S W🍀 *dedicated to* _salma pinky,asykhaleel,classic feedoh and anty khady_ _this lovely page is dedicated to, *FANTASTIC STARS WRITTERS*All,may Allah (s.w.t)restore peace in our group,amen_ Ran ammita yabace ta kalli faruk, Shima kallonta yake ransa a bace,idonsa,har wani jaaa yayi, Kwarjininsane yacikawa ammita ido,kawai taja kawayenta sukayi gaba Yayinda princess tayi murmushi tace nagode daba dan kaiba yau,danasha duka,saboda kasan karfin yan kauye da yan birni badaya yakeba,saita danneni Faruk azuciyarsa yace wannan yarinyar akwai uban surutu saikace aku,a fili ya kalleta,kamar bayaso yayi magana yace,kidai godewa Allah Muntari da sallau sun bude baki sai kallon princess suke,yanda take nuna kulawa ga faruk,faruk kuwa ko ajikinsa yaja hannunsu sallau da niyyar tafiya,muryar princess ya tsinka tana yaya faruk,inason magana dakai A fusace yajuyo yana waike mayyace,nagaya miki mudaku badaya bane sai faman shishige mana kike,mu talakawane,dan Allah kiyi hakuri ki rabu damu Princess maganar yadan sosa mata rai ,kasa magana tayi, Tsaki faruk yaja,yayi gaba su sallau suka bisa;suna haba aboki wannan zankadeddiyar budurwa haka,tazo tana rokanka,amma kana ja mata aji,meyasa kowama saika nunawa halinka Faruk yakalli sallau,yace sallau kai meyesa bazakayi tunani ba,ina *dan talaka* mara gata,dan daba,mai shaye shaye,zanyi soyayya dayar maikudi dan kasuwa shararre wanda yayi suna,aikaima sallau kasan bamai yuwa bane,ko karatun bako kadan nayifa,iyakacina secondry,itako na tabbata tahada masters da degree Muntari yace aboki karka ja da ikon Allah,bayan wuya sai dadi,inaga yarinyar nan zata zamo alheri agareka,kawai kadinga bata time dinka Faruk ya furzar da huci yace ya isa haka,ya isa,banson ajefani matsala nida mahaifiyata kamar yanda aka jefamu abaya,taje tanemi daidai da rayuwarta Princess ce tadoso wajen,suda suwaiba,suwaiba ta rike tulun ruwa Princess cikin rauni tace faruk kaine daidai da rayuwata,waya gaya maka so akwai ruwanshi da kyau,kudi mulki,so baruwansa da talauci,rashin gata,so acikin zuciya yake,faruk ance kaso mai sonka,ka tausayamin ni macece mai rauni, Faruk yace kinga princess kike kowa,dan Allah dan annabi ki kyalemu acikin talaucinmu,kije ki nemi dan mai kudi irinki,ni banda ra,ayin soyayya,natsani soyayya,arayuwata mutane biyu nakeso arayuwata daga ummata sai kanwata suwaiba,donhaka kije,abinki Kuka princess tasa mai tsuma zuciya tana faruk ,saboda kai na baro dangina,tushena,nataho na yarje zanfara sabawa dakai,karkamin haka faruk Faruk yakara fusata yace ya isa,banson jin kukan ya mace arayuwata,kidaina banso nace miki,karki kisa in tuno da rayuwar baya,karkisa intuna butulu Princess tashare hawayenta tana naji naji,faruk zan koma inda nafito amma kasani,kana manne acikin kogon zuciyata,zandinga zuwa akai akai,har sai randa nasami soyayyarka Princess tana gama maganar nan,ta tafi aguje,tana kuka,tana zuwa kofar gidan,tabude motarta tashiga,driver yajata Suwaiba taji ba dadi,ta kalli faruk kamar tayi kuka,karban tullin yayi yatayata,suka shiga gida, Inna tace a a suwaiba ina kika baro bakuwa zaitun Faruk yace wai inna meyasa kike hakane,haba, inna yazaki ringa shishigewa masu kudi,bayan kinsan matsayinmu, Inna tace kai tilo ,kazauna ka nutsu ,bansan yaushe zaka cire kiyayyar mutane ba,bayan basu sukama abinda haryau ka gaza mantawa dashiba,tunda khadija ta mutu,bazata sake dawowaba,kuma Allah ne ya kaddara bakaine mijintaba Kuka faruk yasa kamar karamin yaro,yana inna meyasa zaki dinga tasomin daciwon dabazan taba mantawa dashiba,inna kinaso ki tsinci gawata anan,kicigaba da maganar khadija,khadija kadai nakeso,banajin zan iya rayuwa dawata mace bayan ita,khadijace daidai da rayuwata,khadija ita tasani farinciki kuma ita tasani bakin ciki Kuka suwaiba tasa tace,yaya dan Allah dan annabi kubar zancen nan,karkusa yanzu ciwona yatashi , Kuka suke ba kaukauta,daga baya faruk yakoma llallashinsu *to wannan wani irin rayuwa sukayi abayane*? Princess tana zuwa gida ta seta nutsuwarta,afalo ta tadda alhaji da momin yara suna lissafin kudin daza,a kashe abikin su binta da maryam Alhaji yace aha wanake gani kamar yar lele yar gatan babanta Seta nutsuwarta princess tayi ta taho wajen ta dad nice,naga bazan iya jure rashin ganinka bane,shine,nadawo Murmushi alhaji yayi yana yaki taho kizauna Momin yara cikin baccin rai tace haba alhaji yaza,ayi muna lissafi kazo ka rusamana tsari, Alhaji yace mekike fada haka momin yara,indai maganar lissafine kuje kuyi da anty amarya,ko miliyan ishirin ne zan bayar Momin yara dayake taji maganar kudi tace a a abar zancen anty amarya ,mayi dasu maryam Anty amarya ta saman benanta tace inajinki munafuka,to dani za,ayi lissafin nan, Momin yara takalli saman tace keke,karki kara cemin munafuka,donni ba munafuka bace,ai ba bikin amira za,ayiba bikin yayana za,ayi Alhaji rai abace yace banson hayaniya,inbahaka ba ran kowa zai bace,ku kiramin najib da kamal,suje kamfanin motocina,kowa yadauki mota daddaya, Kamal da najib ne suka shigo suna ihun murna, Alhaji yace sa,arku daya princess ce tagayamin motarku ta tsufa a canja muku,inba hakaba wlh baxan chanja mukuba Ransu dukansu ya sosu,tawajen yarinyar akabasu mota ,lallema tazaci ubanta By Maryam yarmama [10:19am, 17/05/2017] Queen yarmama: *⚽DAN TALAKA⚽* 46-50 By Maryam yarmama *dedicated to* _salma pinky,asykhaleel,classic feedoh and anty khady_ *Always remember that,no condition is permanent* *this page is dedicated to _yarmama and hajur novel group_* Bikinsu maryam shirinshi ake ba wasa,don event shida za,ayi *get together* *mothers night* *me and you night* *arabian night* *best world couple* *walima* Amare ansha kyau,momin yara sai tsomasu take aruwan tsafi da bita zaizai,asiri kala kala ankarbo(momin yara karki manta rana chasa,in da tara ta barawo,rana daya namai kaya) Safeenace tashigo gidan ,tafaka motarta agefe,ranta abace,uncle affan ne yanufo wajen yana a a safeena yau kece agidanmu,kinji yanda ikon Allah yake ko,mun rabu da princess Tsaki safeena tayi,tace saime,ai Allah xaibata wanda yafika,mtchhh taja tsaki tabi ta kofar baya,tahaura bene,zuwa shashin princess, Princess zaune take tayi tagumi,hawaye yanabin fuskarta Safeena taji duniya tamata kunci,taji itama tafara tsiyayar da hawaye. Ahankalu princess tadago da idanunta dasuka rine dahawaye,tace saukar yaushe besty Safeena zama tayi agefen gadon tana jiya da daddare,yau za,a fara event ko?kinyi anko? Princess tace mezai hana,ai tare dakema dady yasa aka mana anko kala goma Tabe baki,safeena tayi tace ai uncle affan butulune,Allah zai kawo wani,wanda yafisa komai da komai Princess tace hmmm Ameen,bari mushiga wanka,don naga mutane ancika makil,yayana mujaheed yanzu muka gama waya dashi wai bazaisamu zuwaba Safeena tace Allah sarki,dan uwa rabin jiki,wallahi tunda naga hotansa yaburgeni sosai Princess tace kokin kyasane? Safeena tace mexai hana,dariya sukayi dukansu Anata kwasar,mutane zuwa trophical hotel,su princess saikace sune amaren,sunfito awani material dan ubansu mai shegen kyau da tsada,saikace tagwaye,domin safeena ma fulanice usil Maryam ce tashigo dakin tasha kwalya,tayi kyau don duk gidansu princess kyawawane,saidai princess tamusu zarra A yatsine ta kalli princess tace aunazata kishi zai hanaki zuwa,sainaga kin riga kowa shiryawa,to ina godiya da wannan karamcin,muhadu acan Shiru princess tamata,don batada lokacinta Safeena taga dole taramawa princess tace hmmm su amarya maryam ansha kyau tamkar dawisu,Allah yasa kamar yanda fuska yake sabo,haka ciki yake sabo dal aleda,don amaran yanzu yawancinsu kyau afuska Maryam taji zafin abinda safeena tafada,tace ke safeena badake nakeba da yar uwata nake,karki nemi ki gayamin magana yanzu Safeena tace kauna abaki amma ba,a zuciyaba,ai indai ana neman makiyar princess aka sameki angama,ke ko kunyar fadin yar uwarki bakyaji Fuuuuuu maryam tafita daga dakin har tanacin tuntube, Princess takalli safeena suka tafa tace wallahi besty kinmin daidai,irinku akeso Taro yayi taro,duk inda aka duba yayan manyane suke wajen,har sarki da governor ya hallaci bikin,da shugaban kasa Saida akafara event,princess da,safeena suka shigo,kallone yadawo kansu, Princess sai waigw waige take tana neman alhaji,hangosa tayi adinning table,suda mai girma gwammna da president,hannun safeena taja,suka nufi wajen alhaji Tana zuwa cikin shagwaba tace dad tun dazu nake ta nemanka harda zanyi kuka Dan mai girma president dake zaune a dinning suda abokansa,yanajin muryar princess yajuyo,yana godiya ga Allah,yau yasamu matar aure Alhaji yace haba yar lele,kiyi kuka kuma,bayan gani Princess ta gaishe da president da gwamna Cike dajin dadi suka amsa Nass yace friends kunga wata baby,dama alhaji aminu yana da diyar nan haka Bushewa da dariya sukayi,suna kaje ka gwada sa,arka Nass ne ya iso wajen yana dad,dan bani makullin motarka ,zandan fita,yanayi yana satar kallon princess Kallo daya princess tamai ta watsar tace dady zantafi gida ,kaina naciwo Alhaji yace to shikenan yar lele,safeena ki lurarmin da ita,inkin je kicewa mairo kokuma binto su dafa mata ruwa tayi wanka Safeena tace insha Allah dady Barin wajen sukayi suka fita,har princess sun bude motar da niyyar shiga,princess taji an riko hannunta ana baby ji mana Juyowar dazatayu tafeshe fuskarsa da mari fas Dan president nass yarike kunci cike da mamaki,yacirw glass din dayake hannunsa,yana kallonta Princeess bata damuba tacigaba,tana kai wani irin dan iskane zaka rikemin hannu Safeena cike da tsoro tace princess kinsan wakika mara kuwa dan president ne fa Princess ta dakawa safeena harara tace ina ruwana,shigewarta bayan mota,tasa keyy Safeena tace nass dan Allah kayi hakuri,kawar tawace yau ranta abace yake, Murmushi nass yayi yace niko tamugun burgeni ko zan samu kimin kokari ki yimin hanya Safeena tace aha karkaji komai,zanma hanya Nass yace gaskiya dakinsamu kyautar miliyan ashirin harda mota By Maryam yarmama [11:58am, 20/05/2017] Queen yarmama: *⚽DAN TALAKA⚽* 51-55 By Maryam yarmama *Dedicated to* _salma pinky,asykhaleel,classic feedoh and anty khady_ _wannan littafin sadaukarwane,ga masoyan, *Dan talaka*ina godiya bisa kaunar da kuke nunamin Safeena tazaro ido,tace,indai,hakane karka damu,ai tanajin maganata Canjan numban yawa sukayi, Safeena tashiga motan,princess ba abinda take binta dashi illah harara Haka aka kare biki,amarya suka tare agidajensu, Princess ta nufi kauyen nassaran kuki,inda tahadawa suwaiba da inna kayayyaki nasawa adinke Airport aka nufa da ita,tahau jirgi,zuwa gidansu umma Shigarta keda wuya,suka gaisa da umma cikin farinciki ta amsa Suwaiba tazo da gudu ta rungumeta,tana antyna,oh ny sweet anty Dariya princess tayi tace duk nikadai, Hirane ya barke a tsakaninsu Faruk yashigo gidan,rai abace,yakalli princess yace kebawai nahanaki zuwa gidannanba Princess cikin shagwaba tace aini innata nazo in gaishwr,don daga mahaifina babu wata kamarta aduniya A sanyaye faruk yafara sakkowa,don yana so arayuwa yaga anw kaunar inna da suwaiba Bai kulata,ya kalli inna,yace inna kinji hukuncin dame gari ya yanke Inna tace a a saika fada,faruk yace,wai yace indai na auri yarsa ammita,zai bani gida da gonaki,inkuma bazan auri yarsaba nu tattara mubar garin nan Inna takama salati tana wannan wani irin zaluncine,kai meka yanke Princess tadago da fararan idonta,tana kallon faruk taji wani hukunci ya yank Faruk ya kalleta,ya basar yace inna,na yanke kawai mubar garin nan Inna cikin damuwa tace inmukabar garin nan,ina zamu,nufa,muba kudiba, Princess tace,zansiya muku gida agarin kano Faruk cikin bacin rai yace waike ana maganar yan danginmu ,ina ruwanki,bama bukatar komai daga gareki, Murmushin yake tayi tace ,faruk ka tuna ance kaso mai sonka, Faruk tsaki yayi yace aduniya ,sodayane tak nadauka na bawa margayiya khadijah,don tamin hallacin da har inmutu bazan manta da itaba, Gaban princess yabada dum,arazane tatashi,bakinta na karkarwa,idonta yacila fal da hawaye,a hankali ta kalli inna datayi tagumi,tace dan Allah dan annabi ku fiddani a duhu wacece khadijah,kuma,faruk wani irin mutum ne Tsawa faruk ya daka mata yace baki da bukatar sanin koni waye,damarki ta karshe dazan baki itace banayin kowacce ya mace,bayan khadijah,khadijah samun kamarta sai an tona,bantaba son yamace arayuwataba bayan khadijah,nayi kukan rashin khadijah,bazan taba yafewa yayanta nuraba ,ya cucemu arayuwa A sanyaye princess ta kalli faruk,abin mamaki hawayene fal a kwayar idonsa, Suwaibace tafashe da kuka tana yaya danAllah dan annabi kadaina ambaton mugu azzalumi agidannan,sokake xiwona yatashi inmutu kowa yarasani Faruk ya kalleta cike da tausayawa yace suwaiba,aduniya saina rama miki abinda aka miki,nura kuwa saiya gwammace tsakuwa. Da aya Inna tace aa faruk barsu da Allah,in cutanmune sun riga sun cucemu,Allah zai mana sakayya Princess ta kalli faruk tace faruk zan zamema khadijah Faruk da mamaki fal aransa yace a a bazaki iya zama khadijah ba,don khadijah alkyarbar matace,farar fitila mai haskawa,khadijah daban take Kuka mai tsuma zuciya princess tasa ,tafita daga gidan aguje,abakin motarta ta tsaya tana kuka,duk tarin samarin dasuke sonta amma mutum daya ya tsaya yana wulakanta Bude mota,tayi da niyyar shiga,caraf taji an rike mata mayafi, Ahankali ta juyo,faruk ne yazuba mata dara daran idonsa wanda kwarjininsa,yacika mata ido fall Sunkayar dakai tayi,hawaye yana tsiyaya a idonta. A hankali faruk yayi gajeran tsaki,azuciyarsa yace yarinya sai kuka uwa jaririya,sannan yace ke!na manta sunanki,pls kiyi hakuri ba laifina bane,daga zuciyatane ,khadijah tana manne a zuciyata Kuka ta rusa mai tsuma zuciya,tashige mota,tana ni nakawo kaina,airport ta nufa,tahau jirgi Saukatayi,kiran mahaifinta tagani yana yar lele,ina kika shigane ,kiyi sauri akwai wani albishiri mai dadi Dariyar yake tayi,kamar tana gaban alhaji tace ganinan zuwa banisa nayiba,kiran driver tayi yazo yadauketa saigida Tana shiga motoci,tagani,sunfaka ,sunfi talatin Takofar baya tabi,amira tagani tsaye tana dannen waya Princess tace mister chatting baki dady yayine? Amira ta dubeta murmushi dauke akan fuskarta tace anty kin tako arziki nanda sati biyu bikinki Zaro ido princess tayi tace what,?amira banson wasa aure kuma?nidawa?innalillahi wa,innahiraihi raji,un Dagudu tahau upstair dinta tafada kan gado,tana kuka,tana wallahi ni faruk nakeso By Maryam yarmama [1:01pm, 20/05/2017] Queen yarmama: *⚽DAN TALAKA⚽* 56-60 By Maryam yarmama *FANTASTIC STARS WRITTERS* 🍀F S W🍀 *dedicated to* _salma pinky,asykhaleel,classic feedoh_ _fans i need ur prayer,to achieve my goal,may God help us,help in our life amen_ _here is a amazing page,for we *FANTASTIC STARS WRITTER*am proud to be the member of this group,i like the way we love each other like family and sisters,keep it up_ Wanka princess tashiga,tafito duk fuskarta ya kumbura sakamakon kukan dataci,fita falo,tayi dangin mahaifiyarta dake saudiyya tagani dasu alhaji,a akwatuna sunkai ishirin awajen, Gaishesu tayi bayan daya,kowa yana sam barka zaitun an girma Zama tayi,tana daddy kayan waye wannan? Washe hakori alhaji yayi yana ai dan,maigirma president nw ya ganki yace yana sonki,shine wai suka kawo kayan tambayar baki,da daddare zakuzo ma kuzanta Galala princess tayi dabaki,tana kallon uban arzikin da aka ajiye agaban,alhaji,wai kayan tambayane. Yayar mahaifiyarta da ake,kirada,umma tace ai naso mehfuza tananan taga uban arzikin data kwaso, Tabe baki princess tayi,ta kallesu bayan daya,tashi tayi tahaye samanta dagudu Dariya alhaji da sauran abokansa suk kwashe da dariya,suna su princess manya harwani kunya akeji Haka aka watse,yayinda umma da hajur,suka tashi sukayi hanyar dakin princess,don suma komawa saudiyya zasuyi Princess tana ganinsu tarushe da kuka,ta rungumi umma tana umma ki taimakeni bana sansa wallahi,ku gayawa dady yajanye,wlh bana sonsa Cikin tausayawa,umma tace hakuri zakiyi,kibi umarnin mahaifinki,yayanki mujaheed,yace mubaki gwala gwalan nan ki dinga sawa Araunane princess ta kalli ,karamin akwatin mai dauke da sarka da dankunne da zoben gwal,karba tayi,tana godiya Har bakin mota rakasu tana kuka,haka suka rabu Princess zaune take a bedroom dinta,tahada kai da gwiwa tana kuka,tun dazu alhaji yake kiranta taki picking Tsulum taga mutum yashigo,bakowa bane fyace nass,yasha manyan kaya,yayi bala,in kyau Murmushi yaketa zubawa ,yana baby nanda sati daya kinzamo mallakina Dasauri princess ta kallosa tana *who gave you and other to enter my room* Zama nass yayi,ya lumshe ido,yazauna yana haba my wife,zaki hana mijinki shigowa dakinkine Princess tace mallam ka ficemin daga dakina,Allah ya sauwake in aureka,inada wanda nakeso,kuma shizan aura Ran nura yabace kishi ya turnuke mai zuciya,besan lokacinda yakamo princess yamakureta iya makura, Abinka da yargata,ba karfi,kokarin kwacen kanta take tagaza,ihuma takasa,jitayi ya yaga mata rigar dake jikinta Tashin hankali,bayyane karara a fuskarta,tana kokarin kare kirjinta tace dan Allah kayi hakuri karka ketamin rigar mutunci,kaji tsoran Allah Dariya nass yayi yana angayamiki yau nasaba yiwa mata fyade,inbaki saniba to kisani,ina sonki,don haka kinga in namiki fyade ,bawanda zai kara kallonki da mutunci,nine nan mijinki Kuka princess tasa tana basa,hakuri Amma ina kamar kara zugashi tayi,saida yamata kaca kaca😭😭😭 Dakyar take numfashi, Gyara jikinsa yayi yana dariyar mugunta yana,wlh saini nass naci bulus,kuma innaga dama in aureki innaga dama in chanja ra,ayi Karkade rigarsa yayi ,yayi tafiyarsa, Kuka princess tasa,tana maimaita sunan Allah ,gashi takasa tashi,lallabawa tayi tadauko wayarta,ahankali ta danna number din safeena Ringing biyu yashiga,cikin kuka princess tace safeena kina ina mutuwa xanyi kitaho da likitarki,ki biyo ta kofar baya Kashe wayarta tayi tana shesshekar kuka mai tsuma zuciya Ba,afi minti talatinba,saiga safeena tashigo likitan na biye da ita,dauke da first aid box Kara safeena tasaki tana besty waya miki rashin imanin nan,innalillahi wa,innahiraihi raji,un Kuka princess tasaki dakyar tabudi baki tana safeena ubangiji Allah saiya sakamin,nass ne yashigo dakina yamin fyade ta karfi da yaji. Dafe kai safeena tayi tana kuka mai tsuma zuciya tana badai nass dan president ba? Princess tace shine?wallahi shine Safeena tacewa likitan tafara aikinta,itama likitan tayi shock tunda take bata taba ganin irin fyaden nanba,dinki har biyu tamata,sannan tamata alluran barci,kuka kam,princess tasha,har suma tayi ;ta sanadiyar alluran barcin tasamu bacci Likitan ta kalli safeena dake kuka kamar ranta zaifita tace madam,wannan anyi amfani da karfi wajen yimata fyade,wanda yasa yoyon fitsari yakamata,don haka ayi gaggawar kaita asibiti,donni nayi iyakacin kokarina Kuka safeena ta kara sawa,tana likita dan Allah kitayani daukarta ta boyayyiyar hanya,mukaita gidana dake gwaygwalada,sai inkira kwararrun likita a dubata *gaskiya koni saida na zubdawa princess hawaye* Safeena,sukadauki ,princess suka sata a mota,suka nufi gidanta dake gwaygwalada, Kwararrun likita takira,suka fara dubata,dakyar suka ,shawo kan al,amarin, Safeena dake falo sai zubda hawaye take,takalli likitocin dasuka fito tana ya akeciki Babban likitan yadanyi murmushi yace ai gaskiya ta taki sa,a yoyon fitsarin yadaina,tana bacci anjima kadan zata farka,mun mata allurar kashe duk wani radadi dake jikinta Sannan zan aiko a kawo magungunar daxata dungasha Kudi mai yawa safeena tabasu tanata godiya Dakin tashiga,tazauna tayi tagumi,ba,afi sa,o,i uku ta farkaba Dasauri darawar jiki saffeena ta tashi tanamata sannu Kuka,princess,tasa tana safeena ke kawatace tagari wacce nayarda dake,dan Allah ki binne zancen fyaden nan anan,yanzu sonake kije kauyen,nassarawan kuki,kije gidansu wannan guy din damukaje gidansu mukayi fada,ki kiramin shi,kimai kuka kihadashi da Allah da annabi kice yazo inacikin mayuwacin hali Safeena tazaro idonta tana meye hadinki dashi? Princess tace inyazo ka gani,kawai kije,zan kula dakaina Dasauki safeena tahau jirgi tanufi nassarawar kuki,tana zuwa,tagasu gidan faruk ana watso musu kaya waje By Maryam yarmama [1:56pm, 20/05/2017] Queen yarmama: *⚽DAN TALAKA⚽* 61-66 By Maryam yarmama *FANTASTIC STARS WRITTERS* 🍀F S W🍀 *dedicated to* _salma pinky,asykhaleel,classic feedoh and dohta anty khady_ Safeena ta yamutse fuska,tana kallon yanda ake cillo musu kaya waje,inna na kuka,mutane suncika ana kallon yanda maigari yake bada umarnin,a cigaba da watso musu kayan,dama bawani kayan kirki bane dasu Kallo yadawo kan safeena,safeena ta hango faruk da sallau acan karkashin bishiya,sun rikesa suna basa baki Wajen tanufa tana sannunku Muntari da sallau suka amsa,suna kallonta Cikin yanga ta kalli faruk da fuskarsa yana dauke dabacin rai tace faruk kake ko tilo Faruk ya kalleta kamar zaiyi kuka,yace karki kara cemin tilo,ki kirani da faruk dina Ido cikin ido,safeena tace an so what,kai ka kyauta abinda kawo princess,to princess tana chan tana nemanka Faruk cikin gadara yace da wanne zanji,bazanje ko inaba,har kudinsu yasata hauka,harta isa tacemin inzo Safeena cikin lallashi tace faruk dan Allah kataimaka kaje wallahi da matsala Faruk yace nace miki bazanjeba,ko ana dole arayuwa Safeena takalli,su sallau da muntari tace dan Allah kubamu waje zamuyi magana Sallau da muntari suka matsa chan nesa suna,badamuwa Kallon faruk tayi tana faruk kaiwani irin mutum ne,bakasan hakuriba Faruk daya juya mata baya yana sauraronta cikin bacin rai ya juya da niyyar wanka mata mari Kuka safeena tasaki ta durkushe awajen,tana faruk,ka agaza kaje dan Allah,princess tana wani cikin hali da tana bukatar taimakonka,fyade wani azzalumi yamata wanda yasa takamu da yoyon fitsari A razane faruk ya kalleta,fuskarsa dauke da alaman tambaya,dafe kai yayi yana tariyo baya ,bakincikin dayaji lokacin da nura yayan khadijarsa yawa suwaiba kanwarsa fyade,wanda yasa bakinciki ya kashe khadijah Kuka faruk yasa kamar karamin,yaro,yace tana ina,? Safeena itama tarushe da kuka tace tana gidana,tana jinya Faruk yace taho muje,amma harda innata zamuje da kanwata Safeena jiki asanyaye tace badamuwa Haka suka tattara,daga inna har suwaiba sukabar kauyen,a motar safeena,akasa kayansu a boot,faruk da su muntari sai kukan rabuwa suke. Airport sukaje,safeena tamusu bizza zuwa abuja, Inna sai rike safeena suke,tana yarnan bazan fadi ba kuwa Dariya safeena take,kamar zata fadi,suwaiba tana kankame da faruk Haka suka sauka,daga jirgin,driver yaxo yadaukesu,sai hadadden gidan safeena dake gwaygwalada, Kallon ikon Allah su faruk suke,faruk kuma ko ajikinsa,motan yafaka a garage din harabar gidan Safeena ce tafara shiga, Princess tana ganinta rushe da kuka tana ai nasan faruk bazaizoba,zan hakura da indangana har Allah yaciremin sonsa,yanzu naxama bazawara bawanda zai aureni Muryar faruk ta tsinka,yana waya gaya miki haka, Dasauri tadago da idonta,tana kallon dake tsaye ya manna hannu a kirjinsa yana kallonta cike da tausayawa,ya matso wajen,yace princess namiki alkawarin zan aureki ,zan kula dake,zan kwato miki yancinki,kuma ni bazan aureki don arzikinkuba kodan kyawunkiba,zan aurekina in nuna miki soyayya ta gaskiya,so baya tsufa,komin arzikinka ka auri mai sonka,don inka auri mutum don arzikinsa baya sonka,to kana tare da wahala Kuka princess tasa tana alhamdulillah;godiya ga Allah,rungumar safeena tayi tana kukan farinciki. Safeena jikinta yayi sanyi,sai yanzu ta yarda tabbas *Dan talaka* By Mimi yarmama [3:51pm, 20/05/2017] Queen yarmama: *⚽DAN TALAKA⚽* 66-70 By Maryama yarmama *FANTASTIC STARS WRITTERS* 🍀F S W🍀 *dedicated to* _Salma pinky,asykhaleel,classic feedoh and anty khady_ _This page is dedicated to *my department and hostel friends*,thank you for ur love,i love you all_ _this page is also dedicated to *professor :doctor khalid .a. musa*you are a star to me,i like the way you care about our department_ Princess tabugawa dadynta waya,tace zatayi kwana uku agidansu safeena, Soyayya mai karfi ya kulli a tsakanin princess da faruk,princess tana bala,in son faruk sosai,kullum nacewa inna take tabata labarinsu Faruk yahana yace bayanzuba,sai randa tazamo matarsa. Haka princess tayi gumm da bakinta,safeena ta iyakacin kokarinta,takardun secondry din,faruk ta karba,tanemo mai aikin security a kamfanin babanta,albashi dubu arba,in Princess tana komawa gida,suka hadu da alhaji a falo,suda momin yara da anty amarya suna hira Dariya dady yasaki,yana yar lele zonan, Jiki a sanyaye princess tazo,tazauna akujerar dake fuskantar dady,momin yara suka bita da harara Turo baki princess tayi tana dady gani Alhaji yace kije dakinsu najib ki kiraminsu da su amira Kara turo baki princess tayi tace dad kaima kasan bashiri muke dasuba ka kirasu awaya Alhaji yace haba za,ayi Ba,afi minti kalilanba,saiga su sunzo sun zauna,daga amira sai najib sai kamal sai princess sai su momin yarane,kowa yana sauraron abinda,alhaji zaice Alhaji yayi murmushi yace alhamdulillah kamar yanda namuku gargadi nace kowa yafiddo miji,dan arziki wanda gidansu anyi suna,to kuma najib haka nakeso kowa,yaje ya nemo auran *Yar babban gida*zan auramai koma wacece Kuma zan baku kamfani bibbiyu,acikin manyan kamfanonina,sannan zaku zabi garuruwa bakwai zuwa honey moon Atare suka washe ,najib da kamal suka washe baki,suna godiya ga alhaji Tunda aka fara magana princesa tayi ,gefe da kanta tana tunanin faruk Alhaji yace yar lele,saida ya kira sau uku ta amsa a firgice Alhaji yace yar lele tunanin me kikeyi Princess tace bakomai dad Alhaji yayi murmushi yace,yar lele mekika shirya game da bikinki,event nawa za,ayi,don mufara shiru kafin sati dayan yayi asha biki Araxane princess tatashi tana,no dad dan Allah karkamin haka,wallahi banason nass,katuna kamana alkawarin ba auren dole Alhaji ya kalleta cikin lallashi yace haba yarlele,meyasa kikeso ki kunyatani acikin jama,a ,saida kika bari angama komai har bizza aka muku na kasashe bakwai,nayi ordern kayanki daga dubai,yar lele mamana?ki gayamin wakikeso?kuma dan waye agarin nan Princess taji hanjin cikinta yakada,tsintsar kanta tayi da cewa dad arxiki da talauci duk daga Allah ne,badan kowa bane,wanda nakeso fyace *Dan talaka*wanda kataba kullewa saboda ya mareni a kauyen nassarawar kuki, Dariya alhaji yayi yace hmmm yar lele yau kuma raha da barkwanci kike zomin dashi Hawayene yafara tsiyaya a idonta,nan alhaji ya tabbata da gaske take,princess tace dad *Dan talaka*shine mutumin daya maye gurbin zuciya,shi nakeso,dady kayi hakuri bazan iya auran nass ba Tashin hankali fal a idon alhaji,anya wani bai juyamai kan arshiba,princess din datafi ,kowa kyamatar *talaka*yau da bakinta take fadar talaka takeso ina it can happen,tsawa yadaka mata *zaitun!* *zaitun!* *zaitun!* sau nawa nakira sunanki Princess batayi mamakin kiran sunanta da alhaji yayiba,baitaba kiranta da zaitun ba sai yau,a hankali tace sau uku daddy Alhaji ranshi yakara bacewa,yace zaitun kinyi karya ki auri talaka kina matsayin yar shararren dan kasuwa da kasa takeji dashi,akanki nadora buri mai nisa,auranki da nass ba fashi kamar anyi angama Momin yara da anty amarya biki buduri suke azuciyarsu ,tsabar murna Princess ta fashe da kuka taja da gwiwa ta rike,kafar alhaji tana dad,ka taimakawa rayuwa,so baruwansa da kudi,dad wallahi bazan iya auren nass ba,inna auri nass mutuwa zanyi Duma mata dundu alhaji yayi,yakamota yadinga fesa mata mari,har saida tayi hakko,yayi bal da ita,yana hucci yace ni zakisa inji kunya,to kije na sallamaki,kije kinemi wani uban bayan ni dazai wakilci bikinki,da tsinannan yaron nan,na cireki ajerin yayana, Arazane princess tadago da idanunta,ga jini na malala,a hancinta tace daddy? Alhaji yace karki kara kirana da daddinki,ki kirani da alhaji aminu Momin yara cikin kissa tace,alhaji a sassauta ra,ayinnan Tsawa alhaji yadakawa momin yara yace ya isa momin yara,agabanki ,ranar nan natarasu dukansu nace duk wacce ta auri talaka,saina tsine mata,na sallamata,ko na mutu battada gado,kuma dukansu sukayi signing suka amince Donhaka ta tartara tabarmin gida,intakai minti ishirin agabana saina tsine mata albarka tabi duniya, Kuka mai tsuma zuciya,princess tasa, Anty amarya azuciyarta tace bakiga komaiba amma afili tace lalle ke taurin kanki yayi tsauri,tunda kika iya jayayya da mahaifinki,to ai saiki tashi ki tafi tunda yace bayason ganinki Alhaji yace kuma kije ki dakkomin,makullan motoci guda biyardin dana mallaka miki,da gwala gwalan dana siya miki,da atm din bankinki guda hudu da fakardun gidajen dana mallaka mikisu,ki kawomin in bawa yayana masujin maganata,kar inkuskura inkara ganinki,anan gidan Xaro ido princesss tayi,amma bata karayaba,jiki yayi tsami tatashi tafashe da kuka,mai tsuma zuciya,tattara kayanta tayi ,nasawa,da gwal din da yayanta yamata,tadauki tafkeken hoton yayanta dana mahaifiyarta tasasu,a akwatinta Harta cika akwati shida da kayanta harma sun rage a drower,tayi tunanin bazata iyaba,ta dauki,abinda take bukata tajawo akatunanta biyu tafito falo,tana shesshekar kuka,ta ajiyewa dady duk kaddarorinta,tana kuka tace dady kayafemin Ko kulata baiyiba,ficewa tayi daga gidan,tana tunanin,ina zata...... Alhamdulillah *anan zan dakata,nagama part one*in Allah ya yarda bayan azumi zamuci gaba a inda muka tsaya *part 2 din dan talaka,yana dauke da abin tausayi,zalunci,soyyayya,princess tana shiga cikin wahalar da har kusan mutuwa take,zakuji labarin faruk maicike da abin mamaki da tausayi* _mai karatu wannan part one din da kuka karanta,zoman tabine;,don wahalar da princes dafaruk sukesha,saiya girgiza zuciyar mai karatu_ ★HAPPY RAMADAN KAREEM ★ *GODIYA DUBU*★ _huraira yabo(bazan manta dakeba,) _my besty salma ali wadah(kina raina) _classic feedoh(godiya) _first lady(na gode sosai) _my dohta anty khady(Ke dabance) _zuwaira madara _nabila(guduna akeyi😂) _ayusher muhd _momin shayeeda _my sayyada momin hafsat *wash wash,hannuna is tired,bazan iya lissafokuba,duk kuna raina ina alfahari daku* *INA ALFAHARI DAKU* Masoyana,inaji daku,kune yan gaban goshina,Allah yakara dankon zumunci Kalamaina yakare,yawun bakina ya kafe,numfashina yatsaya cak,harshena ya sarke,mexan ce muku,?gaskiya ina godiya sosai,saboda kaunar dakuke nunamin,masu kirana,da masuyimin text na fatan alkhairi ina godiya *SAKON GAISUWA* ♥GIFTED ONLINE WRITTER ♥FANTASTIC STARS WRITTER ♥FEEDOH NOVEL HOUSE ♥BILYN ABDUL NOVEL GROUO ♥ASYKHALEEL NOVEL WORLD ♥YARMAMA &HAJUR NOVEL GROUP ♥ZAUREN MARUBUTA HAUSA ♥ANTY KHADY LOVLY FANS ♥SALMA NOVEL GROUP ♥ENGLISH CHAT ♥MEDICALS DEPARTMENT ♥A.B.U FOR EVER ♥TIED FRIENDS WORLD ❤EIGHT UNTOP LADIES ❤SIRRINMU MATA ♥ESHER MAKE OVER ♥SKIN CARE EDDIT _am proud of you all,may God bless those groups_ AM RETURNING IN PART 2 FOR COMMENT 07030772637

Share this


Author: verified_user

0 Comments: