[6/9, 10:47 PM] Ermeenartπ: π·π· *DUK ABIN DA KA SHUKA*π·π·
♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*♻
*WRITING*
By
*ERMEENART*π
©Edited by :HUMYLUVπ
*01-02*
*Bismillahir Rahmanir Rahim*
*GARGA'DI*π·
_*BAN YADDA AYI MINI AMFANI DA WANNAN LITTAFI NAWA BA,TA KOWACE IRIN HANYA KO SIGA,KO A SAKA SHI A DOCUMENT,BA TARE DA IZINI NA BA,PLEASE BEWARE.THANKS*_
*SADAUKARWA*π·
_*NA SADAUKAR DA WANNAN NOVEL 'DIN NAWA GA 'DUMBIN MASOYANA MASU KAUNAR NOVELS 'DINA INA YI MUKU FATAN ALKAIRI DA GODIYA MAI TARIN YAWA ALLAH YA BAR SO DA 'KAUNA,ALLAH KUMA YA BAR MU TARE AMEEN*_
*FATAN ALKAIRI*π·
_*INA YIWA 'DUMBIN 'YAN UWA AL'UMMAR MUSULMI BAKI 'DAYA FATAN ALKAIRI, DA KUMA FATAN ANYI SALLAH LAFIYA ALLAH KUMA YA KAR'BI IBADUN MU BAKI 'DAYA AMEEN.*_
Ruwa ne ake tsalawa kamar da Bakin kwarya ga duhu cikin tsakar dare wurin karfe uku ga iska mai'karfi ta na ta kad'awa sai 'karar rufin kwano daga saman d'akin kake ji,ga sanyi yana ta bugawa mai ratsa jiki,wadda duk rufar da ka yi sai kaji sanyin wannan yanayin yana ratsaka bare kuma baka rufa da komai ba.
Ahmad da yusuf yara ne 'yan kimanin shekaru Sha Uku da haihuwa, amman Ahmad ya bawa yusuf shekaru biyu.suna kwance suna ta sharar bacci cikin d'akin su, d'akin abude yake feshin ruwan nan na ta shigo musu cikin d'akin nasu ga sanyi yana ta ratsa d'akin wannan 'karan ruwan dana rufin d'akin da suke yi,ga kuma feshi ruwa yana shiga d'akin shi ya tayar da Ahmad daga baccin sa yana tashi ya kalli inda d'an uwansa yusuf yake kwance Yusuf ya wani takure Ahmad ya 'kura masa ido sannan ya ja wani dogon tsaki ya maka masa ashar yusuf kuwa bai san yana yi ba baccin sa yake yi hankali kwance ya d'an rufa da wani dan kyalle,
Ahmad ya mayar da kansa ya kwanta zuciyar sa na ta kimsa masa mugayan abubuwa zumbur ya tashi kamar wadda aka tsikara ya nufi wurin da yusuf yake kwance ya yaye masa mayafin da ya rufa da shi ya nufi waje ya wullar da shi cikin ruwan nan da ake yi,
Ahmad bai tsaya iya nan ba,bayan ya cillar masa zani a cikin ruwa sai ya d'auko wata roba aciki ruwan wadda innar su ta tara mu su ruwa don suyi amfani da shi, bai tsaya ko ina ba sai kan Yusuf ya she'ka masa yana she'ka masa ya yi sauri ya mayar da robar ya rufo musu 'kofar d'akin nasu dan kar Yusuf yayi 'kara su Inna su ji shi,
cikin firgici Yusuf ya tashi yana mummurza idonsa hankalinsa ya tashi yana bude ido ya ga Ahmad sai ya fashe da wani gigitaccen kuka dan ya san halin yayan nasa don ba tun yau ya fara Shan wuyarsa ba, yana kuka ya ce"yaya Ahmad dan Allah kayi hakuri"
Ahmad yace "to tsohon munafiki ka rufe mini Baki ko na tattaka ka banza har ka isa ina bacci ka ce kaima zaka yi har da wani rufa wai kai adole kana jin sanyi ko!.... an fisonka duk wata tsana ni ake sakawa toh wlh yanzu ka fara Shan wuya a wurina yaro",
yusuf yana jin sa ya zuba masa ido yana ta kuka duk ya cika da tsoro jikinsa sai rawar sanyi yake yi ga ruwa na ta d'iga daga jikinsa,
sanyi sai ratsa sa yake yi sannan yace "yaya kayi hakuri dan Allah ka barni nayi bacci "Yusuf abun tausayi ga yarinta duk da shima Ahmad d'in yaron ne amman fa ya fi Yusuf tsageranci ga sanin kan mugunta.
Ahmad ya ja tsaki sannan yace"toh shege naji saura kuma da safe naji ka fad'awa su inna abun da nayi maka kaji! ko baka ji ba!
_Yusuf yace naji! yaya bazan fad'a musu ba insha Allah da sauri ya bashi wannan amsar cikin tsoro_
Ahmad ya kuma kallonsa ya hareresa bai sake ce masa komai ba ya koma ya kwanta ya juyawa yusuf baya sannan ya ja bargonsa ya rufa yana tsaki,
ya cigaba da baccin sa cikin kwanciyar hankali yusuf kuwa yana nan a jike haka ya 'kara raku'bewa ya kwanta a 'yar katifarsa.
Domin kuwa Ahmad duk ya cika wurin kwanciyar yusuf da shirgin kaya wai ai shine babba shiyake da iko da d'akin nasu.
Duk wannan abun da ake yi inna da Abbaaa suna can suna ta sharar baccin su dama lokacin damuna bacci akwai dadi.
Asuba nayi aka fara kiran sallah sai lokacin su Inna suka tashi domin yin sallah.Abbaaa har ya fito yayi alwala inna ma haka lokacin ruwa ya d'an tsagaita sai d'an yayyafi kad'an,
Abbaaa ya nufi da'kin su yusuf dan ya tashesu,su tafi masallaci ya buga musu kofa ya ji shiru, sai ya sake bugawa,Yusuf ne ya fara tashi sai yaji Baba na ta kiran su ya amsa yace "gamu nan zuwa Abbaaa" ,Abbaaa yace" Yusuf ya amsa da na'am ka tashi kenan inji Abbaaa sai yace "Eh na tashi to ka taso yayan naka mu tafi masallaci yace to Abbaaa gamu nan sannan ya tashi da sauri ya sauya kaya dan kar su Abbaaa su gane abun da Ahmad yayi masa,
Har ya yunkura zai tashi Ahmad su fito tare sai ya tuna da kashedin da ya yi masa akan tashin sa a bacci nan cikin tsoro haka ya hakura ya 'ki tashin Ahmad don idan ya tashe shi akwai tashin hankali ya fita ya mayar da 'kofar d'akin ya rufe,
Yana fita Baba yace je kayi alwala mu tafi masallaci,har ya yunkura zai d'auki buta sai yaji Abbaaa yace "ina Ahmad din sai yusuf yace gashi nan fitowa Yusuf ya wuce ya d'auki buta ya fara alwala yana cikin yin alwalar,sai yaji Abbaaa ya kira sunan sa, sai yace masa "yana ga kamar abun rufar ka acikin ruwan nan da aka yi ,
sai yusuf ya ce laaaa hmm... Ab.. ba..aa sai yayi shiru Abbaaa ya sake ce wa "ina jinka kayi shiru sai yusuf ya cigaba da cewa "wlh na barsa kan hundo ne har aka fara ruwa ban sani ba,sai ya jike na fito da shi na shanya sai muka rufa da bargon Yaya Ahmad ina ga fadowa yayi ana iska,
Yanayin yadda yusuf yake maganar cikin in-e-ina zaka tabbatar da ba gaskiya ya fa'da ba, Abbaaa kawai jin sa yayi ya girgiza kai yayi murmushi yace to shikenan Allah ya yi muku albarka yusuf yace ameen dai-dai lokacin ya gama alwala yana ajiye butar wurin d'akinsu,
Duk wannan abun da ake Ahmad yana can kwance yana ta sharar baccin sa dama Abbaaa ya san Yusuf ka re Ahmad yayi domin kuwa ya san halin Ahmad yayi-yayi fad'an har ya gaji akan zuwa masallaci da Makaranta amman ya'ki ji idan kuwa ya matsa masa ma da ya je to kuwa yawon sa zai wuce shiyasa ya kyalesa ya bisa da addua,
Abbaaa ya kama hannun Yusuf suka wuce masallaci.
*_SU WAYE AHMAD DA YUSUF ??_*
❤
*Urs*
*ERMEENART ✍πΌ*
[6/9, 10:48 PM] Ermeenartπ: π·π· *DUK ABIN DA KA SHUKA*π·π·
♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*♻
*WRITING*
BY
*ERMEENART*π
©Edited by:HUMYLUVπ
*03-04*
*_SU WAYE AHMAD DA YUSUF??_*
Ahmad da yusuf yara ne a wajen Malam Garba wadda suke kira da (Abbaaa) dan asalin garin Bauchi ne da kuma Innar tasu Asma'u wadda suke kira da (Inna) ita kuma yar asalin garin Katsina ce.
Malam Garba yana da rufin asirin sa daidai gwagwardo suna xaune ne cikin kwanciyar hankali abun sa shi da iyalinsa.
Kafin haihuwar su yusuf da Ahmad Allah ya bawa Abbaaa da Inna zuri'a har rai goma duk mata suna rasuwa wasu ana haifar su wasu kuma har sai sun tasa sun fara wayo Allah ya karbi abun sa,bayan Inna ta haife yaran nan duk sun rasu bata sake samun wani cikin ba har sai da ta dibi shekaru ashiri har sun fidda rai da haihuwar sun fawwalawa Allah komai.
Cikin ikon Allah wata rana Inna ta tashi da rashin lafiya nan aka tabbatar da tana dauke da juna biyu lokacin har ta dan manyanta, sun yi murna sosai suka cigaba da rainon cikin nasu,
Don tun da ta same shi take Shan bakar wahala ta yau daban ta gobe ma da daban ga abu ya zo da jikin girma ana haka,har Allah ya kawo lokacin haihuwar Inna sai da ta kwashe kwanaki biyar tana nakuda sannan ta haihu ta, haifo yaron ta D'a namiji masha Allah kyakkywa kamar sa daya da Babansa,
Sati na zagayo wa yaro ya ci suna Ahmad ba wani taron suna aka yi ba domin jikin na Inna har yanzu da saura tana ta fama da rashin lafiya.sannu a hankali ana magani jikin Inna yayi sauki ta cigaba da rainon dan nata domin Allah ya bata yaro mai rigima Ahmad baya tashi rigima sai ya ga Inna ta tsiri aiki ko tsakar dare duk ya hana su bacci,
Sai da Ahmad ya shekara daya sannan ya rage rigima.Ahmad na da shekara biyu inna ta sake samun wani cikin amman bata sha wata wahala ba, ba kamar a cikin Ahmad ba haka ta raini abun ta ga wahalar Ahmad domin kuwa akwai shi da ta'adi wani lokacin sai dai Abbaaa ya fita da shi waje Don Inna ta samu ta kammala aikin da take yi ga cikin ta ya tsufa,
Wata ranar laraba da MISALIN karfe uku na rana Inna ta tashi da ciwon nakuda cikin ikon Allah ko awa biyu bata yi ba ta kara haifo wani santalelan yaron sati na zagayo yaro ya ci sunan Yusuf ansha shagalin suna sosai,tun bayan haihuwar Yusuf inna basu sake samun haihuwa ba.
Inna da Abbaaa suka cigaba da rainon yaransu har suka dan tasa aka saka su a makarantar islamiyya da ta boko amman fa Ahmad baya son makaranta Kullum sai anyi masa fada Abbaaa yayi ta masa misali da dan uwansa Yusuf,irin kyawawan halayyar sa gashi yaro wanda shi ya kamata yana babba ya rinka yi su,dan wata rana shine shugaba a gida.
nan Ahmad zai cika ya batse yayi ta zinkirin fishi yayi ta yiwa Inna jifa da kaya idan kuwa ya sami Yusuf to kuwa dukkan tsiya zai yi masa dan akwai lokacin da Ahmad ya yi masa wani mugun duka har yayi masa targade a hannun dan yace sai ya hau bishiyar mangwaro ya ciro masa Yusuf ya ki,
Ahmad baya kaunar Yusuf ko kadan muguntar yau daban ta gobe daban sai yayi abu amman haka zai dage yace Yusuf ne
ba yadda Yusuf zai yi haka zai karbi laifin da ba nasa ba idan na fada ne ayi masa idan ma na duka ne haka za a zane Yusuf, Ahmad yayi ta dariya yana jin dadin,
wata rana ya saka Abbaaa ya yi wa Yusuf wani mugun duka wai ya ganshi ya sayo wa Mai Dawa taba, Mai Dawo wani gagarumin dan daba ne a garin ya gagari kowa haka Abbaaa ya kama yusuf ya zane,cikin rashin sanin Ahmad shi yake aikatawa.
kuma Ahmad shine yake zuwa Mai Dawa yana aiken sa ya na dan bashi biyar ashirin. Sai daga baya Abbaaa ya gane duk sharrin Ahmad ne tun daga ranar Abbaaa da Inna suke ji da yusuf komai suka rarumo shi duk dan Ahmad ya gani ya gyara halin sa amman inaaaaa.....
Abbaaa sai ma gani yayi halin Dan nasu Ahmad ya cigaba da lalacewa suka bishi da addua domin kuwa muguntarsa gaba take ba baya ba,
Dan har yaran unguwa bai bari ba idan an aiki yara idan da kudi ne toh kuwa Ahmad zai kwace kudin nan sannan ya hada wa yaron da duka idan kuwa nika ne toh zai kama ya zubar da shi kuma ya kwace kudin nikan, haka zai sa Inna biya da yawon bada hakuri,
duk sanda yaje makaranta kuwa sai anyi fada da shi ga shi da shegen karfi tsiya shiyasa yara suke tsoronsa. *To wannan kenan*
***********
Bayan Abbaaa sun tafi masallaci Inna na idar da sallah ta tashi domin ta kikkintsa ta hada musu karin kummalo Don Abbaaa baya dawo wa gida sai rana ta fara fitowa,
Ta na ta aiki wurin 6:30am har ta kammala kokon da zasu sha,sannan ta ji karan bude kofa daga wurin dakin su Yusuf dama bata yi mamaki ba don tasan wa zata gani Ahmad ne ya fito yana zumbure - zumbure Baki Inna ta kalle shi bata ce masa komai ba sai Allah ya shirye ka Allah ya gyara mini kai Ahmad,
Ahmad ya kara ciki yana batsewa yace Inna sannu da aiki bata kalle sa ba tace yauwa sannan ya dauki buta Don yayi alwala ya tafi masallaci yayi sallah sai yaji butar ruwa ne amman kadan yayi tsaki ya nufi wurin da ruwan yake ya diba ya shiga bayi ya kama ruwa sanannan yayi alwala ya fita
Fitar sa ke da wuya sai Inna ta jiyo kara a soro wayyoooooo!! Allah na Inna ya kashe ni, ba shiri da sauri ta ajiye abun da take yi ta nufi soro Bakin ta dauke da innalillahi wa inna ilaihi rajun dan taga me ke faruwa.
Toh.... Ko mai Ahmad yayi kowa ya make iko sai Allahπ€ nima dai na ce Allah ya shiryi Ahmad ameen ya Rabbi
❤
*Urs*
*ERMEENART ✍πΌ*
[6/9, 10:48 PM] Ermeenartπ: π·π· *DUK ABIN DA KA SHUKA*π·π·
♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*♻
*WRITING*
BY
*ERMEENART*π
©Edited by:HUMYLUV π
*05-06*
*This page is dedicated to my lovely aunty Humaida (HUMYLUVπ) tnx for ur love Nd encourage my God bless you,u Nd ur family really proud of UπΉ❤❤*
"Inna na zuwa idon ta ya sauka akan abun da Ahmad yayi ya ma ke Zuwairiyya ta fadi ga farantin ta na talle a gefe ya fadi gasarar da take ciki duk ta zube a ca'bi,tana ta kuka tayi zaman da'baro a kasa,Ahmad kuwa da yayi aika-aika ko ta kanta bai bi ba yayi fitarsa ya nufi masallaci,
Inna ta karaso wurin da take ta d'aga ta,ta kwaso kayan tallan suka shiga gida tace sannu Zuwairiyya Ahmad ne ko ta dagawa Inna kai alamar eh tana ta shasshekar kuka dan taji faduwar,
Inna ta rarrasheta,ta wanke mata jikin sannan ta biya kudin 'barnar da Ahmad yayi.Domin kuwa Inna da bata yi niyyar saya ba don har ta gama hada musu karin da zasu ci da sauran gasararta,ta jiya. Zuwairiyya ta tashi suka yi sallama da Inna ta dauki farantinta,tafi gida tana tafe tana dan d'in gisawa.
Zuwairiyya yar makotansu Ahmad ce Yarinya yar kimanin shakaru sha uku sa'ar Yusuf ce amman ya bata wata daya da haihuwa Yarinya mai hankali da girmama manya.
_Ahmad ya tsane ta wai dan tana kawo musu tallan gasara Kullum sai ta sa an yi musu koko da safe abincin talakawa,
ita ma Zuwairiyya haka take hakuri da shi dan ko a hanya idan ta hango Ahmad to kuwa babu shiri zata canza wata hanyar dan muddin suka had'u sai ya bata rankwashi aka ko ya zageta.
Bayan fitar Zuwairiyya, Inna ta cigaba da aikin ta, tana yi wa Ahmad addu'ar shiriya dan ta fara gajiya da halinsa.
Ahmad yana fita bai tsaya ko ina ba sai masallaci yana shiga ya had'u da Abbaaa da Yusuf har sun kammala abun da suke suna shirin fitowa,kallon-kallo suka yi wa juna babu wanda ya ce wa wani 'kala ya wuce ya tayar da sallah Abbaaa ya girgiza kai ya kama hannun Yusuf suka taho gida dan lokacin bakwai tayi.
Inna ta kammala aiki ta, ta shirya musu karin kumallon nasu a cikin dakin ta kan tabarma,ta zauna tana hutawa tana saurarar rediyo, Abbaaa yayi sallama suka shiga shi da Yusuf ya kalli Inna yana murmushi yace sarkin kokari har kin gama Inna tayi dariya tace Malam kenan na gama ina ta jiran ku,
Ga ruwan zafi can na dora muku idan kun yi wanka sai ku karya ko,Abbaaa yace yauwa Allah ya yi miki albarka Inna tace Ameen ya Rabbi sannan Abbaaa yace can muka hadu da yaran nan yana ta zinkirin fishi mai aka yi masa ne,
Inna ta dan ja numfashi sannan tace hmmmm.. Yanzu Malam Ahmad har sai anyi masa,fuskarta da alamun damuwa,nan ta labartawa Abbaaa abun da ya faru tsakanin sa da Zuwairiyya.Abbaaa yayi shiru sannan daga baya ya ce Allah ya shirye sa ya ganar da shi wlh ina tsoron yaron nan ya tashi da wannan mummunan halinsa
Inna ta kalle shi ta ce babu komai kar ka damu ai addu'a zamu yi ta yi masa bashi kad'ai ba ma har sauran yara masu irin halinsa,Abbaaa ya ce hake ne to Allah ya shirya mana zuri'a Baki daya Inna Tace ameen ya rabbi Abbaaa ya tashi ya nufi ban daki don yayi wanka.
Abbaaa ya shirya ya fito Yusuf ma haka ya fito cikin uniform din su na makaranta nan suka zauna suka karya bayan sun kammala sun yi hammadala ga ubangiji,
Abbaaa ya kalli Yusuf yace tunda ka shirya kai bara na baka kudin taranka sai na ajiyeka a makarantar tun da shi wancan rigimaman bai dawo bare ya shirya na ajiye ku a makarantar tare yana fad'a ya mikawa Yusuf naira ashirin ya kar'ba cikin ladabi yace ya gode sannan Abbaaa yace wuce muje Yusuf akar kayi latti,Abbaaa ya ce wa Inna to mu zamu wuce
Inna tace toh Malam Allah ya kiyaye Allah ya tsare, Yusuf Allah ya taimaka ayi ta kokari ban da fada kaji Yusuf yace toh Inna,Abbaaa ya goya Yusuf a babur suka wuce,tafiyar su ke da wuya sai ga Ahmad yana zuwa kofar gida ya hango 'kurar tafiyar su yayi kwafa ya ja dogon tsaki ya shige gida.
❤
*Urs*
*ERMEENART ✍πΌ*
[6/9, 10:48 PM] Ermeenartπ: π·π· *DUK ABIN DA KA SHUKA*π·π·
♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*♻
*WRITING*
BY
*ERMEENART*π
©Edited by:HUMYLUV π
*07-08*
"Ahmad yana shiga gida ya wuce yayi shirin makarantarsa sannan yayi karin kummalonsa bayan ya kammala,Inna ta ba shi kudin taransa ya karba ya dauki jakarsa na nufi makaranta.
_Cikin ikon Allah Ahmad yanzu yana aji na biyar a babbar sakandare Yusuf kuma yana aji na daya tsiransu da Ahmad aji daya ne,saboda wayon Yusuf da basirarsa Yana 'karami aka saka shi makaranta da wuri_
_Yusuf shine monitan ajinsu yana da kokari sosai dan har yan ajin suna kiransa da BABBAN KAI Ba ruwansa da shiga shirgin kowa abu indai ba a saka da shi ba to kuwa ido ne nasa shiyasa malamansu,suke ji da shi hatta shugaban makarantar tasu yana jinjina hallaya irin ta Yusuf kamar ba ciki daya suka fito da Ahmad ba dan shi kusan Kullum sai an kai masa 'karar Ahmad d'in_.
Shi kuwa gogan wato Ahmad idan ban da rashin ji babu abun da yake a makarantar karatun ma badamun sa yayi ba dan sun sha haurawa su guda shi da abokansa marasa ji, a kamo su a zane gaban asambile,idan kuwa fad'a ake yi toh ko ba da shi akeyi ba zai sayi fad'an ayi da shi.
Yusuf da Ahmad duk sun fara zama samari musamman Ahmad da yake yana da tsayi kuma yana da d'an kauri wankan tarwad'a ne,bakinsa mai kyau ne kyakkyawa da shi masha Allah,sa'banin shi Yusuf da bashi da wani jiki kuma yana da dan tsayi baza dai a ce masa kajere kai tsaye ba amman shi fari ne tass kamar balarabe shekarun Ahmad yanzu sha takwas (18)Yusuf Yana da sha shida (16).
Ahmad yana nan dai sai abun da yasami ci gaba dan babu abun da ya rage daga halinsa kiyayya kuwa Kullum karuwa take tsakanin sa da dan uwansa Yusuf.
****
Ahmad yana xaune a kofar gidansu misalin karfe sha daya na safe, kamar yadda ya saba zama duk weekend (wato karshen sati) idan babu makaranta yana cin abincinsa na safe to zai fito ya zauna,
Yana zaune sai ga wasu 'yan mata nan Hanne da Larai yaran gidan mai unguwa zasu wuce daga gani su sun girmewa Ahmad ma dan shekarun su zai kai ashirin (20) Ahmad ya kalle su har sun dan gifta shi yace ku! Kuzo nan duk cikin 'yan matan nan babu wadda ta daga kai ta kallesa suka ci gaba da tafiyar su,
ya sake ce wa ku dan uwarku! Ba magana nake yi muku ba yan iska karuwai jibesu duk fuska ta 'baci da bilicin kamar wasu burarruka yan kut mar uba!
'Yan matan nan suka juyo da ba su yi niyyar kula sa ba amman da suka ji irin zagin da yayi musu kuma su basu yi mishi komai ba sai suka dawo da baya suka kara so inda yake sai Larai tace masa ba dai uwarmu ba kuma mai kama da birrai tana gida tana tu'ka tuwo ta murguda masa baki ta ja hannun Hanne tace zo mu tafi suka wuce,Ahmad ya tashi da sauri ya sha gabansu ya fizgo Larai ya wanke ta da wani gigitaccen mari har sau biyu Larai ta kwalla wani kara ta rike kuncinta ta saka kuka,
Sannan Ahmad ya nuna ta da yatsa yace banza! ballagaza! Jaka! wallahi duk sanda na kuma ganin 'kafar ki a nan layin sai na karya ki na rantse da Allah, Hanne da take tsaya itama kukan take dan duk ta cika da tsoro ta kama hannun Larai suka wuce, Ahmad ya ja wani mugun tsaki,duk abun nan da akayi akan idon Yusuf komai ya faru,lokacin ya dawo daga islamiyya wadda suke duk ranar asabar da lahadi lokacin da ba makarantar boko da safe.yusuf shi kadai ke zuwa shi kuwa Ahmad tuntuni ya yaye kansa ya dai na zuwa sai dai ta rana idan ya ga dama yana zuwa amman wani ikon Allah yana da kokari sosai shima a islamyya.
Har Yusuf zai shiga gida sai ya dan jiyo hayaniya a bayansa yana juyawa kuwa sai yaga abun da yake faruwa ya tsaya ya fasa shiga gidan.
Bayan ya ja tsaki ya gyara rigarsa sannan ya furzarwa da bayan su yawu ya juya zai koma wurin zaman sa anan ne yaga Yusuf ashe na kallon sa ya maka masa wata harara yace kai dan uwarka! mene ne zaka tsaya kana kallona ko ni sa'anka ne eheee...
Yusuf ya girgiza kai yace a'a Allah ya baka hakuri,Ahmad yace banza kawai ya tashi cikin 'bacin rai.Yusuf ya bi bayan su Larai har sun d'an yi nisa ma ya tare su,suna ta kuka nan ya basu hakuri yace musu kunga nima yayana ne amman bana jin dad'insa dan Allah kuyi hakuri nan ya rararrashe su sannan ya dawo zai wuce gida nan ma Ahmad ya bishi da harara har ya shiga gida yace banza matsoraci!
Yana shiga gida Inna tana wanke-wanke ya mata sannu da gida ya wuce daki ya ajiye littattafansa,ya fito dauko kujera ya zauna kusa da ita yafara taya ta wanke wanken yayi shiru alamun mai damuwa,Inna ta kalle shi tana fara'a tace Yusuf ya akayi ne ko baka da lafiya ne naji kayi shiru Yusuf yace a'a Inna, tace to mene ne yace wlh Inna abun da Yaya Ahmad yake yi,yayi yawa wlh abun ya fara damuna ni nafiso kome zai yi abun sa yana tsayawa a kaina,amman ya dai na yiwa mutanen waje nan Yusuf ya kwashe labarin komai ya fadawa Inna,
Inna tayi salati ta sanar da ubangiji tace Allah Nagode maka.ni kuwa wannan yaro mai yake so ya zama ne anyya..... AHMAD!
Ni yaushe zan huta ne akansa tun yana zanin goyo nake fama da shi yanzu kuma ya fara girma ma bazai barni na huta ba ta fashe da kuka,hankali Yusuf ya tashi ya matso kusa da ita,
Ya ce Inna ki dai na yi masa kuka sai ya kara lalacewa dan wannan kukan naki bakaramar masifa ba bane a gare shi nan ya rarrashe ta tayi shiru sannan Inna tace zai zo gidan ne ya sami ne wlh na gaji da wannan halin nasa!! Bara Abbaan naku ya dawo.suka cigaba da wanke-wanken su
_*toh a nan zan dan yi jan hankali ga mu matasa wanda zaka ga duk mun gagari iyayenmu musamman ma a wannan lokacin namu na yanzu zaka ga iyaye ba a mayar da su komai ba.Basu isa da yaransu ba maimakon D'a ya bi iyaye to iyaye su suke binsu wanda wannan babbar kuskure ne.mukan saka iyayenmu kuka akan irin halayyarmu ko mu haddasa musu ciwuwwuka kala-kala wanda zasu cutar da rayuwarsu wanda wannan bakaramar masifa fa bace a garemu dan Ubangiji da kansa yace muyi biyayya ga iyaye kar mu sake! Mu daga musu murya ko da uffan kar mu ce musu,kuduba ku ga 'kan'kartar UFFAN!, aka ce ko ita kar muyi yunkuri furta musu toh idan muna so mu ga dai-dai MU BI IYAYENMU idan muna so y'ay'anmu su bimu suyi mana biyyayya toh MU BI IYAYENMU!! dan Allah dan Annabi muji tsoron Allah mu biyayya agare su domin shine zamu sami rabauta duniya da lahira saboda da sai munyi haka zamu ga cigaba a rayuwarmu sannan kuma mu gama da duniya lafiya.Allah ya ganar da mu Baki daya,Allah ya shirya mu a hanya ma daidaiciya sannan kuma Allah ya jikan iyayenmu Allah saka musu da gidan aljannah ameen ya rabbi*_
Bayan sun kammala Inna ta bawa Yusuf kud'i yaje kasuwa yayi musu cefa nan abincin rana ya karba ya ce mai za a sayo tace masa kayan miya na dari da hamsin da maggi star da kuma nama na Naira dari biyu Yusuf ya ce mata toh Inna ya wuce ya saka takalminsa yace sai na dawo Inna tace masa to Yusuf Allah ya tsare a dawo lafiya yace ameen sannan ya sa kai ya fita
❤
*Urs*
*ERMEENART ✍πΌ*
[7/6, 10:03 PM] Ermeenartπ: π·π· *_DUK ABIN DA KA SHUKA_*π·π·
♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*♻
*WRITING*
By
*ERMEENART*π
©Edited by :HUMYLUVπ
*DEDICATED DIS TO UMMY B LOLO DURLING TAWAN ZAINAB VC &MZEE TA AUNTY ZAINAB (MUM HAFSAT) AND MAMAN MEENAL❤❤πππππππ»*
*09-10*
Yusuf na fita ya ci karo
da Ahmad a soro,Ahmad yace masa" zo nan dan ubanka! Yusuf ya ja da baya cikin jin tsoro yana zare idanu had'e da d'ora hannayen sa asaman kansa, "Yaya Inna ce ta aike ni ka... su.. wa faaa....Ahmad na tun karo sa Ya ce toh ni" ina ruwana yau sai na sauya maka kamanni a gidan nan,
"Dan Allah yaya kayi hakuri" shhhh shiru shege da kai kamar faskaren icce na"hana ka yin gulma ta amman ka ki ji,
"Zaka min shiru Ko sai na mazgeka.
Ashe Ahmad tun lokacin shigar Yusuf gida shima ya biyo bayan sa ya fasa zama a wajen yana shigowa soron sai ya ji Yusuf yana fad'awa Inna abun da yayi wa su Larai da Hanne,Sai ya fasa shiga gidan ya la'be a soron cikin 'bacin rai yace" yaro zaka fito ka same ni wlh sai na sumar da kai!,
Ahmad yana gama magana ya fizgo Yusuf ya wanke sa da wani wawan mari,ji kake tass! Tass!! har sau uku Yusuf ya kwalla 'kara ya sa ka kuka wayyoo Allah na Inna!!,
Inna taji kamar an kira ta tana d'aki sai ta'kara jin kuma alamun kamar ihu ana kuka saboda tana cikin 'kuyar d'akin sai tayi sauri ta fito ta nufi soron saboda daga nan take jiyo karar,
isar ta ke da wuya kuwa sai ta iske Ahmad har ya kwantar da Yusuf yana ta duka ya hau ruwan cikinsa Yusuf yana ta kuka yana ko'karin kwacewa Inna ta 'karasa da sauri tana ta salati da kyar ta kwace Yusuf a hannun Ahmad,
"Ta wankawa Ahmad mari,tana fad'in lallai deedah burinka bai wuce ka illata mini yaron nan ba kohh,toh ngd Allah ya shirya mini kai.
Yusuf sai kuka yake yi Domin kuwa ya sha duka sosai sannan Inna ta jawo Ahmad ta rufesa da duka cikin 'bacin rai tana fad'a!
"Ahmad! yaushe zaka yi hankali ne na gaji! Kai kenan Kullum baka tausayin d'an uwanka wlh ina guje maka ranar da zaka yi dana sanin wannan abun da kake yi,
"Budewar Bakin Ahmad kuwa sai yace"wlh ni babu wani dana sani da zan yi aikuwa Inna sai ta 'kara wuta a dukan da take yi masa "auuu.. Ahmad har futsarar taka ta kai nan,ina fad'e kana fad'e
Yusuf yana ta jan Inna kiyi hakuri yana kuka sannan ta ce "Allah ya shirya mini kai ta kara wa Ahmad wani dukan, sai da tayi mai isar ta sannan ta cika sa ta ce"bara Baban naku ya dawo yau - yau din nan zaka koma gidan kawu Aliyu a kano,sannan ta kara masa da rankwashi,ta kamo hanun Yusuf tace sannun kaji Yusufa kayi hakuri Allah ya jarabce ka da d'an uwa mara tausayi
Yusuf bai ce komai ba sai kuka ta kamo hannunsa zasu shiga gida sai ta ji 'karar babur din Abbaaa ya dawo ta tsaya suka fasa shiga gidan don ta san yanzu zai shigo gara ma yazo ya tarar da su ya ganewa idon sa,
Bayan Abbaaa yayi packing din babur dinsa a waje ya shigo cikin soron cikin sallama suka amsa Ahmad yana gefe yana ta haki baki duk a fashe yana ta zubar jini,
Abbaaa yace lafiya yana ganku a anan kunyi carko - carko Inna tace ina fa lafiya sai lokacin kallon Abbaaa ya kai kan Ahmad sai ya doka salati lafiya!" Ahmad me ya sameka,Inna tace ai Malam bashi zaka tambaya ba kalli abun da yayi wa d'an uwansa sai a lokacin ya lura da irin mugun dukan da ke jin Yusuf din duk jikin sa yayi rud'u - rud'u abun ka da farin mutum,Abbaaa ya 'karaso cikin sauri Yusuf! Yusuf ya taho ya rungume sa ya sake fashewa da wani kukan,
Haba! Ahmad sai ya fara masifa na rantse da Allah sai na ballaka wato ni ba aga ciwon da aka ji mini ba don kai aka fi so kai za a kula to wlh bazan yadda ba!
Inna da Abbaaa suka saki baki suna kallon sa cike da mamakin furicin sa, Inna ce tayi kokarin tace,
____________________
" Malam ka gani ko! sai a lokacin Abbaaa yayi magana yace "mu shiga cikin gidan koma mene ne sai na ji suna shiga Inna ta shinfida musu tabarma a tsakar gida suka zauna Ahmad kuwa yana can gefe a 'kasa ya zauna,
"Yanzu abun da nake so a fad'a mini mene ne ya jawo wannan fad'an in ji Abbaaa, nan Inna ta kwashe abun da duk ta sani ta fad'awa Abbaaa Yusuf ma haka ya fadawa Abbaaa duk abun da Ahmad din yayi,
Nan Abbaaa yaji duk abun da suka fada laifi na Ahmad ne sannan ya jiyo ya kai kallon sa wurin Ahmad yace yanzu kai ne ka ke aikata wannan abun sai ya sun kuyar da kai nan Abbaaa yayi musu fad'a sosai su duka biyu, sannan suka bashi hakuri da alkawarin baza su sake ba,
sannan Inna tace tana da magana Abbaaa ya ce ina jinki,
"tace Alfarma nake neman Malam yace ina jin ki Allah ya sa zan iya yi miki tace Ameen sannan ta ce Malam dama alfarmar ita ce da ka mayar da Ahmad gidan kawun su Aliyu a Kano ya cigaba da karatun sa a can, sai Abbaaa ya dan nisa ya ce toh... Zan yi tunani akan maganar ki insha Allah Inna ta ce to Nagode Malam,
"Kawu Aliyu 'kanine wurin malam Garba wato Abbaaa bashi da wasa ko kad'an babu wanda Ahmad yake tsoro irin sa domin kuwa baya yi masa ta wasa tunda ya koma Kano da aiki fitsarar Ahmad ta cigaba.
Sannan Abbaaa ya kalle su Ahmad yace "ku tashi muje kyamis a wanke muku ciwon sannan a baku magani kar zazzabi ya kwantar da ku dubi yadda duk kuka ji wa kan ku rauni dan Allah,suka ce toh, suka tashi suka fita
suna fita sai ga Larai da yayansu Musa yana masifa kununa mini gidan su yaron yau sai ya san ya ta'ba ku......
Yau saina yayyafa masa ruwan bala'i INA gidan yake...
" Laaaa yaya gashi can ma...
Affuwan cajina ya 'kareπ¬ mu hadu anjuma love you all ππ·
❤
*Urs*
*ERMEENART*✍π»
π·π· *_DUK ABIN DA KA SHUKA_*π·π·
♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*♻
*WRITING*
By
*ERMEENART*π
©Edited by :HUMYLUVπ
*11-12*
```This page is dedicated to all members of ♻exclusive writer's forum♻ Allah yabarmu tare, kuma Allah ya bar zumunci da had'in kai Allah ya kara mana basira sannan kuma ya shige mana gaba a duk al'amuranmu ameen ya Rabbiππ```
"Laaaa Yaya ga shi can ma...
"yauwa! Muje nuna minshi yau ko d'an gidan uban waye sai ya san ya ta'ba ku,kuma ya san shi 'karamin mara kunya ne"in ji Musa yayan su Hanne,,,
Tun da su Hanne suka taho Abbaaa ya hango su sai ya ga kamar su Hanne take nunowa ai kuwa yana'kara kai hagensa wurinsu sai ya ga su d'in dai take nunowa wanda suke tafe,sai ya ja tunga suka tsaya domin kuwa ya ga alama mun wurin su suka nufo kuma da dukkan alamu ba lafiya ba,Yusuf ma ya koma gefen Abbaaa ya tsaya a tsorace Ahmad kuwa ko ajikinsa yana tsaye yana ta faman muzurai.....
Suna tafe har suka 'kara so wurin da su Abbaaa suke a tsaye Hanne tace "ga shi nan Yaya wannan ne" ta nuna Ahmad da yatsa, Ahmad yayi mata wani mummunan kallo,,
..."ke! dallah can mene ne kike nuna ban ce kar na 'kara ganin 'kafarki a unguwar nan ba yana rufe baki Musa yayan su Hanne yayi kansa ya sha'ko Ahmad ya fara duka,
*Kan Uba dukan ta zaka kuma ya d'aga Ahmed sama har zai saki....
sai yaji magana daga gefen da suke ana kiran sunansa "Musa!! Yana juyawa sai ya ga ashe Malam Garba ne ya nufo su,,
.... nan take Musa ya cika Ahmad ya dur'kusa cikin ladabi yana gaishe da Abbaaa cikin jin kunya,ya amsa cikin fara'a ya ce "Musa ashe kune a tafe" ya d'an sosa kyeya ya ce
"eh wlh Malam,duk ya duririce ya kasa magana domin kuwa yana jin kunyar Abbaaa saboda aminin mahaifinsu ne yana girmama sa a matsayin uba,bai so ya ganshi yana fad'a da yaro 'karami ba,
Abbaaa daya lura da halin da Musa yake ciki sai ya ce "Musa kayi hakuri wlh duk na san abun da ya faru yanzu ina dawo wa gida abun da na tarar kenan,nan Abbaaa ya labartawa masa komai yace" yanzu ganin da kayi mana kyamis zamu a basu magani sai Allah ya kawo ku,,,
Musa ya ri'ke baki ya ce "anyi abun kunya Malam! yanzu wannan Ahmad ne? "wlh ban gane shi ba ashe 'kanina na daka dan Allah kuyi hakuri Malam lokacin ina cikin fishi ne kuma da dai ban gane Ahmad d'in ba naga ya 'kara girma,cikin jin kunya.....
Cikin fara'a ya ce "Haba! Babu komai wlh ai maganin sa kenan da bai yi ba ai baza ayi masa ba nayi fad'an Kullum har na gaji ban san wani yaro bane baya jin magana,
Musa yace" sai hakuri Malam kuma muyi ta yi musu addu'a,kasan yau wurin shekaru uku bana garin ina lagos jiya na dawo sai da ka fad'a yanzu na ga kamannin Ahmad d'in,,,
Haka kuwa aka yi domin muna maganar ka da mahaifin naka yake ce mini ka kusa dawo wa, don dana ganka ma nayi mamaki ashe jiya ka dawo "
"Eh
Nan suka had'u,Abbaaa da Musa suka yi musu fad'a had'e da nasiha suka bawa juna hakuri Musa ya ja su Larai suka tafi Abbaaa ma ya ja su Yusuf suka wuce kyamis,,,,
Bayan sun dawo daga kyamis d'in Abbaaa ya wuce ya yo musu cefanan abincin sannan Inna ta d'ora musu girkin rana,,,
....su Yusuf kuwa suna shiga gida Inna ta dafa musu ruwan zafi suka yi wanka sannan suka jira Inna ta gama abinci suka ci suka sha magani,,
*_______________*
Abbaaa na dawo wa bayan ya ci abinci yana hutawa,Inna ta zo ta zauna tace "sannun da hutawa Abbaaan Ahmad rigima da Yusuf hakuri tana dariya,, shima yayi dariya ya ce" yauwa uwar gida tayi murmushi tace Malam kenan,
Abbaaa yace "ai gaskiya ne ko akwai wata bayan ke Inna ta yi dariya tace" "hhhmmm Malam kenan sannan ya dube ta yace"to ya aka yi?
ta gyara zama ta ce"hmm..yauwa Malam dama akan maganar Ahmad ne,komawarsa wurin Kawu Aliyu kace zaka yi tunani amman naji shiru,Abbaaa ya tashi daga kwanciyar da yake ya zauna shima yace" yanzu zaman Nan da kika ga nayi wlh tunanin hakan nake yi,,,,,,, kin ga yanzu satin nan mai zuwa zasu fara jarrabawa kammala sakandare toh idan suka kammala sai mu tattara mu kai shi da kan mu..
Toh Allah ya kaimu hakan yayi,dama yau wurin shekara biyu bamu je wurinsu ba sai dai su,su zo mana har sun yi fishi ma sun d'auke mana 'kafa"in ji Inna....
Abbaaa ya ce "haka ne fa, bara zan kira shi Kawun na fad'a masa,to shikenan amman fa Malam wani hanzarin ba gudu ba anyyya Ahmad zai gyara halinsa kuwa kar yaje can ya na d'auko musu magana, Abbaaa yayi dariya yace "kar ki damu ai yasan halin Kawun nasa Inna tace "to shikenan Allah ya shige mana gaba Abbaaa" ameen ya Rabbi
*******
Alhamdulillahi yau ranar LITININ Ahmad sun fara rubuta jarrabawar su ta kammala babbar sakandare,,,,
....su Ahmad ana ta ji da kai ana tafiya ana ta'kama an dau guga yana shiga makaranta wasu yara suna ball yan jss2 ai kuwa bugawarsu daya sai a jikin Ahmad gaba daya ca'bin nan ya 'bata masa gaban rigar sa, ya nufesu cikin fishi da zuciyaππ»π¬π
❤
*Urs*
*ERMEENART*✍π»
π·π· *_DUK ABIN DA KA SHUKA_*π·π·
♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*♻
*WRITING*
By
*ERMEENART*π
©Edited by :HUMYLUVπ
*13-14*
_Am sorry plz lover's nayi mistake wurin saka page number na saka 11-12 a maimakon 13-14 amman gashi nan na gyara tnx 4ur love and correction really appreciate_
```This page is dedicated to``` *Ummu Anilaπtnx for ur corncern,πUmmie Naseer,tnx 4ur love and ❤Jikar Garba tnx i really appreciate tnx for ur encourage*ππ
Ahmad ya nufe su cikin zuciya ko tsayawa bai yi,ya duba jikin nasa ba,,,,,,
D'aya daga cikin yaran ya d'ora hannu aka daya ga Ahmad ya tunkaro su kuma ya ga fuskar nan tashi babu sauki,ya ce "Nazir ka jawo Mana mun shiga uku,gaba daya hankalinsu ya tashi
.....Ahmad yana zuwa inda suke ya sha'ko Nazir,daga cikin yaran nan ya fara duka "kai dan uwarka ni sa'anka ne yana ball da shi mari ji kake tass! Tass! jini ya fara zuba a kan yaron da Bakin sa.......
Ko ajikin Ahmad baidamu ba
Sauran yaran suna ganin haka jini na zuba jikin d'an uwansu sai tsoro ya kamasu suka saka kuka suka ruga a guje sai staff room din malamai,domin su fad'a musu abun da ke faruwa,
......suna isaa kuwa suka sami Malam shehu form master din su Ahmad shima yana shirin fita domin Malamai basa nan suna can ana ta tsare-tsaren jarrabawar da su Ahmad zasu yi,,,,
suna haki duk a tunzure sai ganin su yayi akansa yace "ku! lafiya! mene ne?"! Sai haki..... Suke yi sun kasa magana sai nuna masa waje suke yi da yatsa
..... ya sake ce wa" wai mene ne?
D'aya daga cikin yaran ya daure ya fara fad'a masa abun da yake faruwa,bai ma gama yi masa bayani ba yana jin sunan Ahmad ya tashi cikin sauri ya fito ya nufi inda abun ke faruwa suma suka biyo bayansa duk a tsorace,,
.... Suna zuwa basu tarar da Ahmad ba sai Nazir yayi kneel down yana ta kuka fuska duk ta kumbura ga jini na zuba,Malam Shehu ya na zuwa ya doka salati Nazir tashi tashi! Ya d'aga sa yace Ahmad ne ko yana ina?,
Nazir cikin kuka yace "zane ni yayi kuma yace nayi kneel down idan na sake na tashi sai yayi mini wani mugun dukan tunda na 'bata masa uniform kuma ban sani baaaa,,,,,,,,,, ya saka fashewa da wani kukan duk sai ya ba shi tausayi yace masa" tashi ka yi hakuri kaji yanzu ina Ahmad din yake sai Nazir yayi masa nuni da gefensu inda suke diban ruwa wurin famfo,
Malam yana kallon wurin sai ya ga Ahmad a wurin da abokansa su biyu shi amman shi babu riga a jikinsa suna ta hira sai ya kwalla masa kira "Ahmad Garba! Zo nan".......
Haba! Ya tashi cikin zafin nama yaga waye ne yake kiransa da rainin hankali har sunan Babansa zai kira sai ya ga ashe Malamin na su ne sai ya dan rusuna yace" yaaa Malam ina zuwa ya tsuke fuska,,,,,,
Ya kalli abokan nasa yace "kuga wannan d'an rainin hankalin koh...d'an sa ido ya'ki ya daina shiga harkata ina ga sai ranar da na taushe masa baki" suka kwashe da dariya suka ce masa "wlh kuwa shege mai riga daya ba, ai ya fiya sa ido kaje kaji mai zai ce maka inji Umar amininsa,sanannan Ahmad ya tashi ya ce " kai nifa babu inda zani indai ya gaji da tsayuwan ya tafi ko yazo ya same ni inda nake nasan dai magana ce akan wa d'an can dabbobin yaran ya,koma ya zauna
"A'a Derdah ka tafi kafa sanshi sarai" hhhhh wlh bazan bishi ba"
Malam Shehu ya ga Ahmad bashi da alamun zuwa hirarsa ma yake yi ya sake cewa" Ahmad! Wai ba kiranka nake yi ba! Dan iskanci ma maimakon kuje kuyi bitar karatun ku saura minti ashirin ku shiga jarrabawar amman kun zo nan kuna zauna kuna ta hira da jan magana ko!
...... Duk da haka Ahmad ko gezau sai da abokan suka had'a shi da Allah sannan ya tashi ya nufi wurin Malam din,
Yana zuwa Malam ya rufe shi da fad'a "yanzu abun da kayi ka kyauta! Yaro 'kanin 'kaninka dan yayi maka d'an laifi cikin rashin sani shine zaka ka masa kayi masa wannan mugun dukan haba Ahmad!......."Malam ayi hakuri Ahmad yace.....
Haka dai Kullum ayi hakuri ayi hakuri kayi a hankali fa jarrabawa za ku fara......... kar ka jawo wa kanka abun da zaka sa mu koreka,,, to yanzu ina rigar taka ma take,,,
"Gata can na wanke ne na shanya," kana nufin haka zaka yi mana yawo babu riga a schl,yayi shiru "stupid! Je ka dauko rigar ka saka ka kai yaron nan ayi masa treatment kuma na baka 10mint ka dawo idan kuma ka sake ka sake ta'basa ni da kaine",
Ahmad ya je ya d'auko rigar yana fishi ya saka ya kama hannun Nazir suka wuce.....
Sauran yaran kuwa Malam yace su koma su cigaba da wasan su,,,,
Har Malam ya juya zai tafi sai ya hango abokan Ahmad suna nan inda suke, suna dad'a gyara zama basu da niyyar tashi yace "auu baza ku tashi ku kuyi shirin jarrabawar ba wai ku wane irin yara ne....... suma suka tashi suna zumbura baki suna ta mita suka tafi, Malam ya kalle su yace Allah ya shirya mana ku,ameen ya Rabbi
Ahmad bai zame ko ina da Nazir ba sai Bakin gate suka fita.......... To ko ina zasu shida aka bawa 10mint ya dawo kuma an ce masa yaje kyamis na cikin schl π€π€ kuma gashi yana da Exam nan da 10mint again...... Ku biyo ni dan jin yadda zata kaya
❤
*Urs*
*ERMEENART*✍π»
[7/18, 3:03 PM] Ermeenartπ: π·π· *_DUK ABIN DA KA SHUKA_*π·π·
♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*♻
*WRITING*
By
*ERMEENART*π
©Edited by :HUMYLUVπ
```This page is dedicated to*ππ```
Maman Meenalππ»
Ummu Sadeeqπ·
Hajlow πΈ
Xeecul πΉ
Zahrah Gumelπ
Sadiya Aminuπ·
Salma othmanπΌ
Maryam danmalamπΊ
Shamsiyya idrisπΈ
Sameenahπ
Dr meenyπ
Ummu Anilaπ·
Xeeπ
Mamin Yasmin π
Paxeeπ
Yar dagwasππ»
Khady seefawahπ·
Bilkisu Abdul π
Ballyπ
Autar Hajiya π·
El_ladernπ
Nafee Anka π
Ummieyπ·
Sis Aishafπ
Aunty Queen π
AmnoorπΊ
Phauxy✍π»
Aunty Haliloss π·
*love you all THANKS for your encourage Nd concern*
*15-16*
```Ahmad suna fita ya kalli Nazir yace masa "kaii!Nazir ya d'ago ya kalle sa
...Akwai wani kyamis din da ka sani a nan layin danni ba area ta bace ban sani ba?"
Sai Nazir yace masa"eh na sani akwai wani a nan bayan schl din babu nisa ma,na ta'ba rako auntyn mu,aunty Humaida dake ciwon kai aka bata magani```
... "dallah can ba surutu na ce ka yi mini ba muje ka raka ni na kai can a baka maganin,danni baza ni na cikin schl d'in nan ba sun fiya saka idon masifa!"in ji Ahmad.....
Shi dai yaro yayi shiru bai ce komai ba domin kuwa tsoron sa yake yi, nan Ahmad ya kama hannun sa suka tafi.......
,,,Aji ne ciki da d'alibai masu zana jarrabawar ana ta hayaniya duk an cika da d'ouki ana ta surutu....... can kuma sai ga Malam Shehu da Malam Garbati da Malam ibrahim da wasu mutane na biye da su irin manya manya arnan masu jan ido,daga dukkan alamu sune tafe da Exams questions d'in don suna d'auke da wata babba jaka green an rufe ta da gwad'o suna tafe,,,,,,,
Har suka 'karaso cikin ajin dukkan d'aliban nan suka tashi suka gaishe su cikin ladabi sannan suka koma suka zauna mazaunin su,sannan Malam Ibrahim ya fara yi musu jawabi akan yanzu jarrabawar zata fara 'karfe tara na safen nan (9am)yayi musu fatan alkairi Allah ya bada sa a... Suka yi masa godiya
Cikin lokaci kad'an aka rarraba musu answer sheet sannan aka basu questions paper sai da aka tabbar kowa ya samu sannan aka basu lokaci aka ce su fara...
,, Ahmad ya kai Nazir anyi masa treatment sun dawo schl ya kai shi ajin su daga nan bai tsaya ko ina ba ya wuce sai d'akin jarrabawar yana shiga ya tarar da har an fara sai ya tsorata domin kuwa idan ya sake ya kawo matsala akan Exams din sa Abbaaa sai ya ci masa mutunci yana cin wannan yanayin sai ya hango Malam Shehu,
...... sai ya nufi inda Malam Shehu yake a tsayen ....... sai d'aya daga wanda suka zo da takardun jarrabawar ya ga Ahmad ya taho kai tsaye wurin Malam shehu sai
"ya daka masa tsawa" heeyy!!! are you stupid, come back! "Ahmad ya juyo ya kalle sa ya maka masa harara ya tsaya cak! Ko gezau mutum ya sake masa magana
" i say come back here antiserious,look at you fine guy But you are not serious at all,what sayed the time now!!!.... Ahmad yayi banza da shi yayi shiru yana kallonsa ido cikin ido
Am asking you, you keep eyes on me like Owe....
Sai Malam Shehu yazo wurin wannan mutumin da kyar! Ya lallashe ya bashi hakuri amman sai da ya ce wa Ahmad yabawa mutum nan hakuri sannan ya bashi da yana tsaye cak! Yana muzurai
Malam shehu ma ya 'kara basa hakuri sannan ya bar Ahmad ya zauna yayi wannan jarrabawar nan....
********
Cikin ikon Allah gobe juma'a su Ahmad zasu kammala jarrabawar su,,,
Ahmad yana zaune shi da Inna tana tsigar zogale Ahmad na taya ta suna hira a tsakar gida yana fad'a mata da gobe zasu kammala jarrabawar Yusuf ya na band'aki yana wanka,,
Inna ta kalle sa tace "toh alhamdulillahi amman naji dad'i Ahmadu na Allah ya bada sa a Allah ya sa albarka na taya ka murna Allah ya sa rabo ne" "ameen ya Rabbi" Ahmad ya ce mata yana murmushi cikin jin dad'i yana wasa da hannayen sa cikin zogalan
"ka kusa zama mutumcin Kano"Inna ta fad'a cikin fara'a tana ta tsige zogalanta
"what!! Inna wai dama da gaske kuke zan koma gida kawu,,, toh wlh Allah baza ni ba haka Kurum!"
Yusuf ya fito daga wanka ya yace "Inna sannun da aiki tace yauwa Yusuf, ya shige daki domin ya shirya....
Sannan Inna ta kalli Ahmad ri'ke da Baki ta ce "ai kuwa ko mai zaka yi sai ka je dan mun ruga da mun gama magana da Abbaaan,,,,ku jira nake ya dawo ma yanzu yana hutawa ya kira kawun ya fad'a masa nan da sati biyu muna tafe zamu kawo ka ta mayar da kanta kan abun da take yi"
Ahmad yayi wulli da zogalan hannun sa ya tashi yace "na rantse da Allah babu mai kai ni wlh bazani ba"
sai ga Abbaaa yayi sallama ya dawo, ya 'kara so yace "mene ne kuma, meke faruwa"
Inna tayi murmushi tace" babu Abbaaa shirman Ahmad ne fa,sannun da dawo wa ta nuna mai wuri tace ya zauna ya zaune yace "washh!.....na gaji wlh"inji Abbaaa Inna tayi dariya tace sannu sai kayi wanka zaka ji dad'in jikin....
.
Ahmad cikin zafin nama ya suri takalminsa yayi hanyar waje yana fad'a
"wlh baza ni ba dan an tsane ni komai ba a so na ace gidan wannan azzalumin za a kai wlh sai dai na bar gidan nan da naje wurin wannan mutumin nan " ya sa kai ya fita..... .
❤
*Urs*
*ERMEENART*✍π»
[7/19, 1:52 PM] Ermeenartπ: π·π· *_DUK ABIN DA KA SHUKA_*π·π·
♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*♻
*WRITING*
By
*ERMEENART*π
©Edited by :HUMYLUVπ
*This page is dedicated to NANA KHADIJA NOVEL GROUPπΉAND RAI DANGIN GORO NOVEL GROUPπ,THANKS FOR UR LOVE*❤
*17-20*
Ahmad yana fita Abbaaa ya kalli Inna yace mata"mai yaron nan naji ya fita yana cewa ne?"
Inna tana tattare zogalan ta data gama gyarawa da wanda Ahmad ya zubar mata,sannan ta kalli Abbaaa tace
"hmmm.. Malam kenan kasan dai halin abun ka sarai!.... Ba wani abu bane ka kwantar da hankalinka,akan maganar sa ne ta komawa gidan kawun fa, shine yake ta wannan iskanci"
"kaga fitsararran yaro shine yake ta wannan abun, toh zai dawo gidan ya same ni" in ji Abbaaa,,,,,,,,
Yusuf ya shirya cikin riga T-shirt ba'ka da jeans blue yayi matukar kyau sosai domin kuwa yanzu siffar samartaka sai bayyana take yi a jikinsa ga farinsa sai 'karuwa yake yi kamar balarabe,,,,,
Ya fito ya tarar da su inna a zaune yayi wa Abbaaa sannu da zuwa sannan ya ce wa musu "zai wuce gidan su abokinsa Fahad zasu je dubiyan wani d'an ajin su a islamiyya baya jin dadi,,,,
suka yi masa fatan alkairi da addu'a sannan na wuce ya tafi........
Inna ta mi'ke tsaye ta ce "dan Allah Malam ka bar zan can nan na Ahmad ka bari kayi wanka,ka ci abinci idan ka huta sai muyi maganar koma mene ne koh"
,,,,,,Abbaaa "yayi murmushi yace tohh uwar gida sarautar mata.... ya mi'ke tsaya sannan ya dubeta ya ce "Yau kenan zogale zamu ci yayi dariya,ya na zura takalmansa......
"Inna ma tayi dariya ta kalle sa tace"malam kenan daman nasan zaka so hakan shiyasa nace yau dai bara nayi mana kwad'onsa mu ci dan mun kwana biyu bamu saka shi a Bakin mu ba.....
"Haka ne fa,aikuwa naji dad'i sosai,Allah ya yi miki albarka" inji Abbaaa
Inna ta ce"ameen ya Rabbi"tana murmushi
sannan ya sake ce wa "asaka mini kuli-kuli yaji sosai da sukari"
Inna tayi dariya tace "to shikenan an gama za a saka maka"
Yace "yauwa! Godiya nake"
Abbaaa ya wuce band'aki domin yayi wanka,Inna ta wuce ya ajiye zogalan a madafa sannan ta zo ta jerewa Abbaaa abincin sa ta koma ta d'ora zogalan........
Ahmad ya na fita bai zame ko ina ba sai yayi gidan su abokinsa Umar wanda suke rashin jin su tare a schl....
Yana zuwa ya tarar da shi a d'akinsa yana bacci Ahmad ya d'ad'a masa duka,,,
ya tashi a firgice....... Sai ya ga ashe Ahmad yace masa"ni har ka tsorata ni dallah can Malam mene ne"
Ahmad cikin 'bacin rai dallah banza gara ina cikin wata matsala ne shine nazo ka samo mini solution"
Umar ya tashi zaune yace "to mene ne ina jinka yana gyara zamansa ya fuskanci Ahmad din,
.....nan Ahmad ya zayyana masa komai akan komawar sa Kano gidan kawunsa...
Yana gama fad'a masa Umar ya tashi tsaye zumbur!! " haba dai! Baabaa wlh wasa ne wannan kar ka sake ka yadda,wannan ai cutar tayi yawa dan an ganka mai hakuri shine za ayi ta cutar ka...... Kunji fa wai Ahmad ne mai hakuri π¬π
Toh na rantse da Allah kar ka yadda"
sannan ya dawo ya zauna,yanzu kai ka yadda zaka koma can d'in" in ji Umar
"Haba! Wuce nan ni mahaukaci ne,ya za a yi na yadda ma,kaima ka san halina" inji Ahmad sannan ya kwashe duk yadda suka yi da Inna ya fad'awa Umar.....
Umar yace "yanzu ka san me za yi" Ahmad ya ce "a'a" toh abun da nake so da kai inji Umar ka koma kaji shi mai Abbaaa zai ce idan suka dage da sai ka je sai ka dawo mu san yadda zamu yi.....
Ahmad ya tashi cikin zafin rai dallah Malam kai kaji irin matsalar ka nasan fa halin su,,, iyayena ne fa na tabbata ba zasu janye maganar nan ba,,, ni na gama yanke shawara muddin suka dage sai na je barin garin nan zan ji wlh Allah....na tafi can uwa duniya serious,,,
Umar ya kalle shi cikin mamaki yace "what! Barin mee..." Eh barin garin zan yi na ce yana saka hannu a aljihu "inji Ahmad
....... Umar kalle sa yace" toh wlh kar ma ka fara so kake ka lalatawa kan ka rayuwarka ne! Toh wlh ka rufawa kan ka asiri ka zauna kar ka je ko ina,,,
.....nan dai cikin dabara ya bashi hakuri don ce masa yayi,ya fasa ma komawa gidan shi zai wuce duniyar daga nan...... da kyar! Umar ya rarrashi ya hakura zai koma gidan yaji hukunci da Abbaaa zai yanke sannan suka yi sallama Umar ya rako shi ya wuce gida......
Abbaaa yayi wanka har ya kammala ci abincinsa yana zaune yana hutawa ga iska na kad'awa yana jin radiyo,,,,,,,,
Inna kuwa ta gama tace zogalan ta data dafa,ta ajiye ya gama tsanewa kafin ta had'a musu su ci.....
Ta dawo ta zauna Inda Abbaaa yake a zaune, tayi masa sannu da hutawa sannan tayi masa magana akan Ahmad d'in,da bayanin da yayi mata na kammala jarrabawar su....
Abbaaa yayi murna sosai sannan yace "ki rabu da shi ai muke da iko da shi ba shi ke da iko da mu ba dole ko yana so ko baya so sai ya koma,ki bar ni da shi........
Inna ta ce" yauwa Alhamdulillahi,naji dadi Sosai Allah ya sa hakan shine alkairi,,
Abbaaa yace" ameen ya Rabbi, ya dauko wayar sa yace bara na kira kawun na fad'a masa......
..... Sai ga Ahmad ya shigo ko sallama yana ta zinkirin fishi bai kalli inda suke ba ya shiga da'ki ya kwanta,
Abbaaa da Inna suka girgiza kai suka yi masa addu'ar shiriya......
sannan Abbaaa ya kira Kawu Aliyu yayi masa bayanin komai, yaji dad'i sosai sai murna yake yi suka yi wa juna godiya sannan yayi addau Allah ya bar zumunci suka yi sallama ya kashe wayan sannan ya fad'awa Inna yadda suka yi ita ma tayi murna sosai.....
Abbaaa ya kira Ahmad ya fad'a masa sati biyu masu zuwa zasu kai shi Kano sai yayi yan shirye - shiryen sa kafin lokacin,bai ce mu komai ba ya tashi ya shiga d'akin su yana ta fishi..........
Dare nayi wurin karfe daya da rabi,Ahmad ya had'a kayan sa cikin sand'a yadda babu mai jin sa ya kashe kayan sa ya bude kofa a hankali ya fita sannan ya juya ya kalli gidan yace sai dai ku kai wani ba dai ni AHMAD din ba.........
❤
*Urs*
*ERMEENART*✍π»
π·π· *_DUK ABIN DA KA SHUKA_*π·π·
♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*♻
*WRITING*
By
*ERMEENART*π
©Edited by :HUMYLUVπ
*This page is dedicated to you Beloved sister's*❤
*Ummie Naseer*πΉ
*Salma*π·
*Mom Anwar*π
*Aunty Nana*π
*Ummu Anila*π
*21-25*
Ahmad ya juya ya cigaba da tafiyarsa cikin sauri..... Can kuma yaga tafiyar baza tayi masa ba sai ya had'a da gudu...
Yana cikin gudun kuwa sai ga karnukan nan sun fara haushi alamun sun fara ji motsin mutum sun hango shi kuwa sai suka bishi da gudu suna yi masa haushi,,,,,,,
Da Ahmad ya ga alamun shi suke yiwa haushi kuma kar su cigaba da yi mutane su ji su fito domin suga meke faru ai kuwa sai ya cigaba da gudu........
ya rasa inda zai shiga sai can yana cikin gudun ya hango wata rumfar mai sayar da shayi amman babu kowa a wurin sai yayi sauri ya shiga ya buya,,,,,,,,,,haka karnukan nan suka gama haushin su suka tafi......
Can bayan wasu yan lokuta da ya ji babu haushin karnukan sai ya d'an leko ya ga babu komai a wurin sun tafi sai ya fito a guje ya nufi titi yana haki......
Ahmad bai zame ko ina ba sai gidan su Umar abokinsa yana zuwa ya fara buga musu 'kofa.....
daman d'akin Umar shine a soro Umar yana cikin bacci sai yaji kamar ana buga kofa,,,,,,
Ahmad ya sake bugawa da 'karfi sai Umar ya tashi a firgice ya d'auko touhligth ya fara haskawa ya fito cikin sand'a ya zo wurin kofar yace "wanene?"
Ahmad cikin murya 'kasa-' kasa yace "ni ne fa ka bud'e"
Umar yace "Ahmad!!" Sai yayi sauri ya bud'e kofar.......
yana bud'e Ahmad ya shigo cikin gidan a guje ya fad'a d'akin Umar,,,,,,
Umar ya mayar da kofar ya rufe sannan ya dawo d'akin ya zauna yace "Ahmad lafiya Umar cikin tashin hankali ya sake ce wa" me ya fito da kai cikin daran nan......ban ma gane ba wannan jakar mece ce nake gani a hannunka?"
Ahmad ya gyara zama ya ajiye jakakarsa sannan ya kalli Umar yace,
"abokina ya dafo kafad'ar Umar sannan ya ",wlh su inna sun ki janye maganar nan ne suna nan kan bakan su.....nan ya kwashe komai duk yadda suka yi da Abbaaa ya fad'a masa,,,,,,,,
Duk maganar nan da Ahmad yake yi Umar dai ya zuba masa ido yana jin sa bai ce masa komai ba,
sannan Ahmad ya sake ce masa" dama ai na fad'a maka baza su janye ba don haka ni yanzu,,,
"na yanke hukunci barin garin nan dama tun tuni na yanke hukunci hakan zan yi tafiya ta can inda babu wanda zai san inda nake ko an nemi ma baza a ganni ba"
Umar ya kalle sa yace "Ahmad wai mai sa kai baka ji ne ka fiya daurin kan masifa! Yanzu kasan irin tashin hankali da zaka jefa iyayanka idan ka saka 'kafa ka tafi ka bar garin nan kuwa.....?
" ni ina ruwana su suka sani,ba su suka so hakan ba "in ji Ahmad......
Umar ya ri'ke baki yace" Ahmad wlh iyaye ba abun wasa bane kana ganin wannan abun kamar wasa wlh zaka zo kana kuka kana da ka sani kuma ita dana sai kyeyace....... " ni dai na baka shawara ka koma ka bi umarnin iyayanka,,,,,
" ka ganni nan duk iskancina da rashin jina bana 'kin bin umarnin su Baba duk abun da suke so ina yi daidai abun da zan iya.......kaima ai ka sani,,,,, amman dai na san ina rashin ji dan har na fika........."
Ahmad ya kalle sa ya wani bushe da dariya yace "Umari kenan nifa ba wa'azi nazo kayi mini ba Malam Kaji!...... Zuwan nan ma fa daka ganni nayi wurin ka,don bamu gama Exams bane zuwa nayi na kwana gobe mu shiga schl ina gama abun da zan yi na wareee...... Da wlh kaima sai dai kaji ana cigiya ta,,,
" ni matsa ka bani wuri na kwanta "ya koma can bayan Umar yayi kwanciyar sa ya tayar da kansa da jakarsa,, Umar ya bisa da kallo yace" Allah ya shirye ka..... kuma Allah ya kaimu safiyar "shima ya koma ya kwanta....
" Ahmad ya tuntsire da dariya yace ameen ya Rabbi ya uztazu Umari "
....... Gari ya kaure da kiran sallah,asuba tayi har gari ya fara Shaa,,,,,
Abbaaa ya tashi ya yi alwala Inna ma haka sannan Abbaaa ya bugawa su Yusuf kofa yace shi ya wuce masallaci domin kuwa yau sun makara,
Yusuf yace" toh Abbaaa sai mun taho "Abbaaa ya ce" toh, sai ka tashi dan uwanka Yusuf ya fita yana sauri......
Yusuf dai tun da ya shi bai ga Ahmad amman bai kawo komai aransa sai yayi tunani ko yana band'aki nan yayi alwala shima ya fita ya nufi masallaci Inna ma na cikin daki tana gabatar da tata sallah.......
Bayan su Yusuf sun dawo daga masallaci misalin karfe bakwai na safe, Abbaaa yake tambayar ina Ahmad dan ya san yau suke kammala jarrabawar su ta karshe bai ganshi ba kar ya je ya makara......
Yusuf yace shima dai ya tashi bai gan shi ba....... Inna tace "tohh nima kuwa ban ga fitar sa ba ko ya shirya ya wuce makarantar ne oho, kasan halin Ahmad sai shi tun jiya fishi yake da mu ko abinci dare bai zo ya ci ba"
Abbaaa yayi dariya yace"deedah kenan ina ga kuwa dan yau zaka su kammala jarrabawar ta su ana cikin farin ciki da dauki ina ga ya wuce makarantar, toh Allah dai ya bada sa a,.........
Inna tace "ameen" amman duk jikin ta a sanyaye yake.... nan Yusuf ma yaji kan sa na ciwo yarasa mai ke masa dadi haka ya karbi magani ya sha ya koma ya kwanta...... dan babu schl yau, ance kar suje masu Exams ake bukata yau a schl din.......
Karfe takwas na safe Ahmad har sun tsufa a schl shida Umar karfe tara suka fara Exams din sai sha daya suka kammala suka fito dama paper daya ce ta rage musu, suna fitowa ya kalli umar yace "toh Allah ya sada mu da alkairi ni na wuce"
Umar ya jawo shi yace "wai kai yanzu da gaske kake! Haba Ahmad!"
Ahmad ya fizge hannun daga na Umar,,,dallah can Malam cika ni ya wuce ya zaga can bayan wani aji a dauko jakar kayan sa yace wa Umar
"ni na wuce kaga tafiya ta ka rike wa'azinka "ya wuce ya fita daga schl din ya bar Umar da Baki a saka ya bishi da kallo sannan ya shiga aji shima ya dauko littafinsa ya bi bayan Ahmad din........
Yana fita Ahmad har yayi nisa yana ta sauri har ya karsaa titi zai tsallaka sai ga wata mota nan Honda mutanan ciki suna tafiya suna hira suna ta shewa suna zura uban gudu Ahmad kuwa har yayi tsakiyar titin zai tsallaka,
basu ankara ba ji kake kuuuyyyy... Motar nan tayi ciki da Ahmad ya fad'i ko motsi baya yi kayan suka yi wulli can gefe guda,...... Akan idon Umar, Umar ya tafi a guje ya zubar da littattafan sa yana ihu ya nufi waje yana kuka mutane suka fara taruwa
❤
*Urs*
*ERMEENART*✍π»
π·π· *_DUK ABIN DA KA SHUKA_*π·π·
♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*♻
*WRITING*
By
*ERMEENART*π
©Edited by :HUMYLUVπ
*This page is dedicated to you Beloved one the ♻ _EXCLUSIVE WRITER'S FORUM_*♻ *much of love*π
*26-30*
Umar yana gudu yana kuka har ya 'karasa inda Ahmad yake a yashe a kwance,,,,,, yana zuwa ya tsaya tak! Kukan da yake yi ma ya tsaya sai hawayen dake gangarowa cikin idonsa zuwa cuncinsa.......
Domin abun da idon sa ya gane masa........... Ahmad ne a kwace jini yana ta zuba daga gefen kansa da kuma Bakin sa,mutane sun kewaye shi har da 'yan makarantar tasu wasu suna salati wasu kuwa cikin d'alibai sai Allah ya kara suke suna yi mishi mugun fata.....
*_shiyasa ako da yaushe ya uwa mu ci yawon abun alkairi domin duk abun da muka yi a rayuwa to kuwa komai daran dad'ewa indai muna raya sai ya zagayo mana kanmu ko bama raye ma to sai fa ya sami wani acikin dangin mu ko na ALKAIRI ko na SHARRI don haka mu yawai ta abun alkairi a rayuwarmu domin neman dacewa,, Allah ya bamu ikon yi.. Allah kuma yasa mu dace Ameen_*
Umar ya buge mutanan nan cikin zafin rai,ya fad'a kan Ahmad ya fashe da wani sabon kukan"wayoo Ahmad! Innalillahi wa inna ilaihi rajun, kaga irin abun da nake ta fad'a maka ko......amman Ahmad baka ji "yana maganar yana kuka" Dan Allah ka tashi kar ka mutu ka bar ni " Ahmad! Ahmad!"umar yana ta kuka kamar ransa zai fita yana ta jijjiga shi.....
Mutanan dake wurin suka d'aga Umar daga kan Ahmad da kyar! Yana ta kuka yana kiran saunan sa...... Sai Mutanan da suka kad'e Ahmad da yake 'yan albarka ne suna nan a tsaye basu gudu ba,,,,,,,,,,
...... bayan an dauke Umar daga kan Ahmad yana ta kuka suka sa mutanan nan suka taimaka musu aka saka Ahmad a motar tasu da kayan sa domin su kai shi asibiti bayan an saka Ahmad a motar Umar ma ya shiga motar dan ya bisu suka wuce asibiti cikin hanzari domin a ceto wa Ahmad rayuwarsa,,,,,,
Domin kuwa babu wanda yasan halin da yake ciki babu inda yake motsi a jikinsa....
'bangaran Yusuf kuwa yana cikin baccin sa bayan ya sha magani sa ya tashi a firgice ya saka salati yana ta had'a gumi yana ta dube - dube cikin d'akin nasu ya le'ka can ya leko can sai kuma ya tashi ya fito a firgice ya nufi d'akin Inna....
Yana shiga kamar wadda aka cillo daga sama,,,,, sai ya sameta tana zaune ta doka uban tagumi da dukkan alamu tunani take yi......
Itama cikin firgici ta dawo tunanin da take yi domin taga shigowar mutum sai ta ga ashe Yusuf ne,,,,,,
"Yusuf lafiya na ganka haka ko sallama babu,,,mene ne! Yusuf yana jin Inna ta fad'i hakan sai ya fad'a kan Inna ya saka kuka yace
"In..na.. Yaya Ahmad " yana kuka
"mene ya same shi!" Inji Inna tana d'ago Ahmad din daga jikin ta,tana tambyansa duk hankalin ta a tashe ya sake..... cewa "Inna mafarki nayi Yaya Ahmad ya mutu muna ta kuka" ya sake fashewa da wani kukan.......
Sai Inna tayi ajiyar zuciya ta ce "Yusuf kenan ai mafarki ba gaskiya bane kayi shiru kaji babu komai yanzun nan ma zaka ga ya dawo daga makaranta,,,,,,"
Yusuf ya gyara zaman sa yace "Inna wlh ban ta'ba irin wannan mafarki ba ya tsoratani" yana maganar yana goge hawayen fuskarsa
Inna tayi murmushi tace "Yusufa kenan ka kwantar sa hankalinka ka ji babu komai insha Allah,kuma Yusuf fa ma ban da abun ka ai mutuwa nan tana kan kowa duk mai rai mamaci sai muyi fatan dace da Allah ya sa mu cika da imani"
Yusuf yace "ameen ya Rabbi, duk maganar ki haka ne,amman yau da Yaya ya mutu tab! Da kuwa nima binsa zan yi"
*Allah sarki d'an uwa rabin jiki, Allah ka bar mu da namu yan uwan ka 'kara mana had'in kai ameen*
Inna tayi dariya tace "Yusuf baka da dama Allah dai ya raya mini ku"
Yusuf yace ameeeeen Innata, sai tace"yauwaaa autan Inna Allah ya nuna mini auran ku....."
Yusuf ya saka dariya yana jin kunyar maganar Inna ya tashi tsaye yana dan sosa keya yace "yanzu zan yi wanka, akwai ruwan zafi ?"
Inna tace "akwai d'an autan innarsa gashi can sai ka surka kayi wanka"........ yace"to Innata Nagode Allah ya bamu kud'i mu kai ku Makka ke da Abbaaa,,,
Inna tayi dariya tace"ameen ya Rabbi Yusufa.....tana dariya domin ta ji dadin abun da yace" Allah ya yi muku albarka Allah ya sa ku gama da duniya lafiya "
Yusuf yaji dadi shima yace" ameen ya Rabbi Hajiya Innata daga yau hajiya zan rika ce miki yana dariya...... Inna ma tayi dariya tace "Yusufa kenan '
yace "na'am Inna ta bara naje nayi wanka Inna tace" toh a fito lafiya"
"ameen hajiya" Inna sai ya fita ya koma d'akin su don yayi shirin yin wankan......
Yana shiga d'akin sai ya ga da'kin yayi masa fad'i kamar an dauke wani abu a d'akin ya tsaya ya rike mugu yana dan tunani ......
can yana tsaye yana ta tunani yana kalle-kalle kallan d'akin sai ya kalli wurin kayan Ahmad sai ya ga babu komai wayam........ya zaro idon,
.....ya sake goge idon sa sosai domin ya tabbatar da abun da yake gani din gaske ne ko kuwa idon sa ne ke nuna masa.....
ai kuwa idon sa daidai ya nuna masa gaba d'aya wurin kayan Ahmad babu komai,,,,,,ya 'kara sa wurin ya fara dube-dube amman bai ga komai ba babu jakar Ahmad ta kaya gaba sa ya fad'i yace "Innalillahi wa inna....
Sai ya fito a guje ya koma da'kin Inna,har ta dan fara bacci ta farka shigar Yusuf d'akin.... Sai ya fad'a mata abun abun ke faruwa suka fito tare cikin tashin hankali nan suka yi duban duniya babu Ahmad babu kayansa kaf!! Cikin d'akin
Inna ta fashe da kuka ta saka salati yace "Yusuf je ka kirawo mini abban ku a kasuwa...Yusuf ya rarrashe ta sannan ya saka takalminsa ya tafi ya kirawo Abbaaa.....
'bangaran Ahmad kuwa suna shiga asibitin suka nufi emergency da shi Umar ya shiga a guje ya kira Nurse's,,,,,,
sai ga Nurse's din nan a guje dauke da gadon daukar marasa lafiya suka dora Ahmad a kai aka shiga da shi thearther room,
Wadan nan mutanan da suka kad'e Ahmad suka ce a nuna musu inda Dr yake zai suyi magana sai daya Nurse din dake wurin tace "ai yana cikin dakin da aka shigar da Ahmad yana wani aiki.......... suna cikin haka sai ga Dr ya fitowa wanda suke cewa Dr.Nur sai shi wannan bawo Allah da ya fige Ahmad yayi wurin sa cikin sauri duk hankalinsa a tashe yace "Dr sannu da aiki" Dr ya amsa "yauwa" cikin fara'a,,,, sannan yace kune kuka kawo wannan fara lafiya sai yace "Eh mune sai Dr yace" toh gaskiya baza mu taba shu ba sai mun ga police haka Dokar aikin mu take,
"yace innalillahi yanzu Dr ya za'a wlh ni bako ban san ka garin nan ba shigowar mu kenan zamu gidan dan uwan mahaifin mu wannan tsautsayin ya same mu.... "
Dr ya dafa kafadar sa yace kar ka damu nan bayan mu akwai police station kana zuwa kayi musu bayani zasu baka dan sanda guda daya ku taho yare da..... izinin Allah kuna zuwa duk wani taimako zamu yi iya kokarin mu ceto ran dan uwanku da yardar Allah.....
Yace" ok Dr na gode haka kuwa aka yi basu fi minti goma da fita ba Sai gasu da da sanda guda daya sun dawo nan aka gama komai akayi duk rubuce - rubucen da za a yi......
Ba 'bata lokaci Dr ya shiga ya fara aikinsa kan Ahmad........ Su kuma suka zauna suna jiran tsakani,,,,.......
❤
*Urs*
*ERMEENART*✍π»
π·π· *_DUK ABIN DA KA SHUKA_*π·π·
♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*♻
*WRITING*
By
*ERMEENART*π
©Edited by :HUMYLUVπ
```This page is dedicated to``` *_ERMEENART NOVEL GROUPπ_* ```much of LOVE May God Bless You All```π
*31-35*
Suna zaune gaba d'aya har Umar, dukkan su basa cikin nutsuwa Umar ya daka uban tagumi ya zubawa d'akin da Ahmad yake ciki ido.....
,,sai d'aya daga cikin wad'anda suka buge Ahmad din yake yi wa daya daga cikin 'yan uwan nasa magana yace "Yaya Ajmal"
shi wanda aka kira da wannan sunan ya d'ago ya kalle shi shima ya ce" na'am Fu'ad "cikin sanyin murya don tunda abun ya afku hankalin sa ya kasa kwanciya shi dai burinsa yaji halin da Ahmad yake.......,
Sai Fu'ad ya cigaba da cewa"yaya Ajmal ya kamata ka kira daddy ka fad'a masa halin da muke ciki ko d'an uwansa nasa ne sai ya turo mana shi asibiti mu tafi tare coz kaga yamma ce take yi kuma babu wanda muka sani"
Ajmal ya dan shiru sannan ya ja numfashi yace"Eh Bro abun da nake tunanin yi yanzu kenan"yana maganar yana taba saje fuskarsa ya cigaba da cewa,
"amman abun da yasa ban kira Dad ba,so nake naji halin da yaron nan yake ciki ne",
Sai Fu'ad yace "Eh kayi gaskiya to Allah ya mu ji alkairi Allah ya bashi lafiya" dukan su suka ce "ameen ya Rabbi".
'bangaran Yusuf kuwa yana fita domin ya kirawo Abbaaa,,,,, yana fita sai suka ci karo da Abbaaan yana taho wa gida nan sai Yusuf ya tsaya har ya 'kara so......
Abbaaa yana 'karasowa yace "Malam Yusufa kai kad'an a waje,ko wurin Fahad za aje ne yana dariya ya ajiye babur dinsa....,
Yusuf yace " a'a Abbaaa"
Sai Abbaaa yace "yauwa dama yau da Labari na zo muku mai dadi yanzu muka gama waya da Kawun ku yake ce mini ya turo su mai sunan Baba su tafi da Ahmad shiyasa kaga na dawo yanzu dan na sanar da ku, shi kuma idan ya dawo sai ya kikkintsa idan sun karaso sun huta idan Allah ya kaimu gobe sai su tafi.........
Yusuf yace" toh Abbaaa Allah ya kawo su lafiya yace "ameen Yusufa sai can ya lura kamar yana cikin damuwa sai yace"saaaahh.... Yusuf ya naganka kamar a firgice mene ne,lafiya??",
Yusuf ya dan ja numfashi yace "Abbaaa lafiya amman kuma ba lafiya yanzu ganni ma da ka yi mini Inna ce tace na kirawo ka"
Abbaaa ya ce "subahannallahi! Toh wuce mu shiga gidan naji koma mene ne,sai ya kama hannun suka shiga gida......
Suna shiga cikin gidan suka tarar da Inna a zaune kan tabarma ta zuba uban ta gumi,Inna na ganin su ta tashi tsaye ta kara so inda suke ta sake fashewa da wani kukan, hankalin Abbaaa ya tashi ya ce "Asma'u lafiya mene ne kike kuka!"
Nan ta kwashe komai ta fad'a masa ba su ga Ahmad ba tun dazu sun dudduba ko ina kuma babu kayan sa ko d'aya cikin gidan suna tunanin ko guduwa yayi tana shasshekar kuka,,,,,,
Abba yayi salati kamar shima zai yi kukan,ya rarrashi Inna tayi shiru sannan yace "bara su fara zuwa Makarantar su Ahmad din su duba idan bayan nan sai suje gidan su abokinsa Umar idan nan ma basu same sa ba sai su dawo a san yadda za a yi......
Inna tace" toh Allah ya sa a dace" suka ce ameen Abbaaa ya kama hannun Yusuf har zasu fita Inna ta dakatar da su tace dan Allah su tafi da ita,ko ya zauna a gidan ma hankalin ta ba kwanciya zai yi ba" Abbaaa yace"toh" Inna ta d'auko hijab ta saka suka nufi makarantar su Ahmad........
Suna isa makarantar su Ahmad suka tarar babu kowa sai mai gadi,,,
saboda d'aliban suna gama jarrabawar duk ake kora su gida saboda suna tsayawa wasannin banza duk sanda suka kammala makaranta har ma'aikatan tsaro akan kawo wa schl din shiyasa babu wani dalibi da yake tsaya suna gama abun da suke yi kowa zai kama gaban sa.......
Suka yi wa wannan mai gadin sallama suka yi masa bayanin abun da ya kawo su sai yace
"gaskiya tun wurin karfe biyu na rana kowanne dalibi ya bar makarantar amman d'azu bayan ya fita ya dawo aka bashi Labarin an kad'e wani dalibi daga cikin d'aliban makarantar nan,
Dukkansu suka saka salati Inna ta fashe da kuka" shikenan Ahmad Allah ya jikanka"......
Yusuf najin abun da Inna tace sai ya fashe da kuka yace "Inna dama tunda na yi mafarkin nan jikina ya bani amman kika ki yadda",,,,,,
Abbaaa yace "haba dan Allah kuyi mana shiru mana wai da me zan ji ne...... sai wannan mai gadin yace " dan Allah ku kwantar da hankalin ku, amman naji ance sun dauke shi sun tafi asibiti da shi idan kun dudduba ba ku ganshi ba sai kuje kuduba can asibitin ko shine....
Abbaaa yace" toh mun gode Malam yanzu asibitin ma za mu fara zuwa mu duba, Wanne asibitin kaji ance sun tafi"?
Sai wannan mai gadin ya ce "gaskiya ban ji ance ga asibitin da duka tafi ba, amman kuje wannan babbar asibitin na gwammnati ku duba"
Abbaaa yace to mun gode sai anjuma,suka wuce suka tari adaidaita sahu suka hau suka nufi asibiti.......
'bangaran iyayen Umar ma suna can suna ta neman sa.....
*_______________*
Sai da Dr Nur yayi awa daya da rabi akan Ahmad sannan ya samu ya farfad'o suka yi masa treatment din daya kamata sannan ya fito yana fito su Ajmal da Umar duka suka yo kansa "Dr ya jikin nasa" inji Fu'ad....
Dr ya kalle su yace "alhamdulillahi da sauki" ku biyo ni da office,,, suka ce to ya wuce suka bishi a baya yana tafe suna binsa har suka karasa office din nan Dr Nur yake yi musu bayani da Ahmad ya zubar da jini sai an kara masa kuma za a yi masa gwajin kwakwallawa don a tabbatar da kan sa bai tabu ba sannan kuma sun yi masa allurar bacci nan da 2hour zai tashi insha Allah....
Sai suka ce toh alhamdulillahi yanzu zamu iya ganin sa sai Dr yace Eh amman dan Allah kar kuyi masa hayaniya coz ba a so ya tashi indai ba allurar ce ta sake sa ba suka ce toh,,,,,,, Ajmal yace "Dr muje a gwada jinina idan yayi sai a diba a kara masa".....
..... Dr yace" ok ya kira wata Nurse yace suje da Ajmal yayi mata bayani kuma ya bata group din jinin da za a duba, nan suka yi masa godiya suka fito...... Sai da suka fara zuwa ka ga jikin Ahmad sannan suka wuce zuwa wurin d'ibar jinin Umar kuwa yace bara yaje ya fad'awa iyayen Ahmad halin da ake ciki.....
Umar na fitowa su Yusuf suna tsaya a daidata sahu......
❤
*Urs*
*ERMEENART*✍π»
π·π· *_DUK ABIN DA KA SHUKA_*π·π·
♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*♻
*WRITING*
By
*ERMEENART*π
©Edited by :HUMYLUVπ
```This page is dedicated to:```π
*Hajma*π
*Bilkisu*πΉ
*Fateema Hassan*π
*Dr meeny*π
*36-40*
Suna tsayawa Abbaaa ya fara fitowa daga cikin adaidaita sahun sannan Yusuf sai Inna ma ta fito,, Abbaaa yana sallamar mai sahun sai ya ji Yusuf yace "laaaa Abbaaa! wancan kamar Umar abokin Yaya"......
Abbaaa yace"yana ina!" lokacin har ya sallami mai sahun......
"gashi can "inji Yusuf ya nuna Uwar sai Abbaaa yace" aikuwa shine"sai Abbaaa ya kwalla masa kira da yake babu wani tazara tsakanin su Umar din zai iya jin sa...,,,,
Umar yana cikin tafiya sai ya ji ana kiran sunan sa,sai ya juyo don yaga mai kiran sa sai ya ga su Abbaaa ne sai ya taho a guje wurin su ya tsugunna ya gaishe da su....
Yace "Abbaaa wlh wurin ku zan zo dama dazu ne wani tsautsayi ya sami Ahmad... Sai Inna ta d'ora hannu aka ta saka wani sabon kukan tana salati,shikenan Ahmad na rasa ka.....Umar muje ka nuna mini gawartasa,,,
Abbaaa ya kalle ta yace"wai ke Asma'u mai yasa kike yi mana haka ne,ai Abun kiyi murna ne ma,ki godewa Allah da yasa muka ji Labarin yaron nan yanzu da bamu gan shi ba fa?... Kinga dan Allah ki yi hakuri kiyi shiru"
Inna tayi shiru bata sake ce wa komai ba sai shasshekar kuka da take yi....Yusuf kuwa sai rawar jiki yake yi duk ya firgici....
Sannan Umar ya cigaba da cewa "a Babban titin bayan makarantar mu wani mai mota ya bige shi amman jikin da sauki don tun d'azu da safe ma muna nan asibiti har mutanan da suka bige shi,,,,,"toh Allah yayi maka albarka yanzu muje ka nuna mana inda yake" in ji Abbaaa sai Umar ya ja su suka wuce don ya kaisu d'akin da Ahmad din yake.......
"wow,alhamdulillahi! Amman Nurse naji dad'i Sosai da jinin nan yayi dai-dai, toh d'an Allah yanzu kiyi sauri aje a kara masa wlh ina jin tausayi halin da yake ciki"in ji Ajmal.....
Sai Nurse tayi murmushi ta ce"ai sai mun je mun ga lafiyar jinin naka mu tabbatar babu wani cuta a ciki sannan zamu saka masa,amman ka kwantar da hankali da izinin Allah yanzu za a 'kara masa,,,,,,,, badan Dokar aikin mu ne haka ai daga ganin ka ma kai lafiyayye ne tana dariya ta fad'i masa hakan"
Ajmal ya kalle ta yayi dariya yace "Nurse kenan... Toh bara ni na je na ga halin daya ke ciki yanzu sai ya mike,,,," sai Nurse din tace masa"ok,yauwaaa kaga... sai ta dakatar da shi "kaima zamu rubuta maka maganin da zaka sha da kuma abubuwan da zasu kara maka jini,
Yace" ok babu damuna thnks ni na wuce ta ce masa "toh Allah ya bashi lafiya "Ajmal yace ameen sannan ya fita......
Ajmal yana fitowa Fu'ad dama yana zaune yana jiransa yana ganin ya fito ya tashi da sauri ya ce" Yaya Ajmal an yi dace? "
Ajmal yace" an yi dace Bro wlh yayi dai-dai... yanzu zasu je su gwada jini ne suga babu wani ciwon sai suje su kara masa"
Sai Fu'ad yace "haba! Yaya wane irin ciwo kuma idan zasu je su 'kara masa kawai suje dan ni na gaji wlh yunwa nake ji,,,,,
" toh ai Dokar aikin tasu kenan! Kaifa ka cika matsala wlh,,,,,kai! baka ga wani ikon Allah ba dazu da muka je ganin patient din nan namu " inji Ajmal....
"ni ban gani ba mene ne"inji Fu'ad....sai Ajmal yace"dama ai baza ka gani ba banza...... Wlh ni gani nayi muna kama shi serious Bro"
Fu'ad ya kwashe da dariya yace "kaji ka dan Allah ni bar zancan nan, ni dai ban gani" Ajmal ya kai masa duka kai fa shasha ne"
"Eh naji babu nifa har na kira Dad na fada masa halin da muke ciki na fad'a masa sunan asibitin yace zai kira Baffan ya fad'a masa sai yazo wurin namu idan yaso muka gama abun da muke yi sai mu tafi tare da shi gidan nasa" inji Fu'ad.....
Ajmal yace masa "ok yayi kyau...toh wuce muje muga halin da yake ciki,,,,..."su yaya manya sai wani damun kanka kake yi akan wannan yaron inji Fu'ad,,,, Ajmal ko kallon inda yake bai yi ba ya wuce gaba yana tafiya Fu'ad ya saka dariya ya bi bayan sa suka nufi dakin da Ahmad yake........
Umar yana tafe su Abbaaa suna binsa har suka'karasa d'akin,Umar ya bud'e musu suka shiga,suna shiga suka ga Ahmad a kwance yana bacci kansa d'aure da bandeji da hannun sa na dama.....Inna ta tafi a guje tana kuka ta zauna gefen gadon ta bishi da kallo tana share hawaya su Abbaaa ma suka 'karaso suka zauna a wata kujera da take a gefen gadon suma suka kalle shi yana ta bacci suka masa addu'ar samun lafiya,,,,,
sannan Abbaaa ya kalli Umar yake tambyar wad'anda suka buge Ahmad a motar yana son a nuna mishi su yayi musu godiya da basu gudu sun bar shi rai a hannun Allah....
Abbaaa bai rufe baki ba sai ga su Fu'ad sun shigo suna shigowa sai wayar Abbaaa ta hau 'kara alamun ana kiransa sai Abbaaa ya d'auko wayan a cikin aljihunsa yaga waye ke kiran sa sai yaga Kawu Aliyu ne ke kiran sa ya dauka cikin sallama suka gaisa....... Suka gama magana Abbaaa ya kashe wayan,
Inna kuwa tun shigowar su ta kafesu da ido saboda kamannin da ta ga suna yi da yaranta wato Ahmad da Yusuf,... Yusuf ma haka sai kallon su yake saboda da kamannin da yaga suna yi da Ahmad......
Sai Umar kalli Abbaaa yace "Abbaaa ga mutanan ma da suka bige shi,ni wlh Abbaaa wannan ma suna yi mini kama da Ahmad din,"
yana fadin hakan sai Abbaaa ya kai kallon sa wurin su Ajmal suna had'a ido sai ya tashi cikin sauri ya yazo gaban Ajmal yace " *wa nake gani kamar mai sunan Baba!!*..........................
❤
*Urs*
*ERMEENART*✍π»
π·π· *_DUK ABIN DA KA SHUKA_*π·π·
♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*♻
*WRITING*
By
*ERMEENART*π
©Edited by :HUMYLUVπ
*41-45*
" *wa nake gani kamar mai sunan Baba!!*....."sai Ajmal ya d'an saki baki yana kallon Abbaaa yana tuna ina ya san wannan fuskar amman ya kasa tunawa.....
sai kuma yayi murmushi ya d'an tsugunna zai gaishe da Abbaaa,,,,sai Abbaaa ya d'ago sa " yace tashi,,tashi Saddiku.....Allah mai iko"........
Sai Umar ya kalli Abbaaa ya ce " Abbaaa daman ka san su? "
Sai Abbaaa yace masa"na san su Umari 'ya'yana ne "
Sai Fu'ad ya zaro ido ya maimaita abun da Abbaaa yace...."sai ya dan tabo Ajmal yace masa "Yaya kaji fa abun da wannan tsohon yake cewa ina muka zama 'ya'yasa kaji wani rainin hankali,,,,,, sai Ajmal ya bugesa yace" dallah can Malam rufe mini Baki".....
*______________________*
Sai Abbaaa ya kalli Inna yace "Asma'u yanzu ke baki gane wad'annan ba?..sai yayi mata nuni da Ahmad.........
Inna ta d'an girgiza kai tace"a'a Malam,,ban gane su ba,amman ni tun da suka shigo nake kallonsu,,,,,don yana yi mini kama da su Ahmad".....
Tabbass! Dole ki ga haka dan yan uwansu ne.... Abbaaa yayi dariya yace " toh mai sunan Baba ne SADEEQ.....d'an wajen Kawu Aliyu da d'an uwansa muhammad" Abbaaa ya fadawa Inna,,,,,,
sai Inna ta mike tsaye " innalillahi wa inna ilaihi rajun Malam! Ya aka yi ban gane shi ba.....wannan abun kunya har ina ta tallafe kuncinta na dama da hannun ta.......
Sai Fu'ad ya zabura Yace"yaya Ajmal! Kaji ya san sunayen mu ko dai shi ne baffan na mu,,,,Innalillahi... Sai Ajmal yace nima abun da nake tunani kenan dan kasan rabon mu da su yau shekara goma...tun kana d'an shekara sha biyu....... "Fu'ad yace haka ne amman idan sune zan fi kowa jin dadi., dama amman ya ce zai kirasa ya fada masa yazo muna nan....... Sai Ajmal yace to Allah ya su din ne suka kara mayar da kallon su wurin Abbaaa.....
Abbaaa ya bud'e baki zai yi magana kenan sai ga Dr Nur tare da d'aya daga cikin Nurse's din nan,tana biye da shi a baya hannun ta d'auke da jinin da za a 'karawa Ahmad don sun tabbatar da jinin lafiyayye ne babu wata cuta a cikin sa,,,,,,,,,
suna shigowa d'akin Dr Nur ya umarce su da su fita dan Allah zai duba Ahmad sannan kuma zai saka masa jinin,sannan yace "idan sun gama zai yi musu magana su dawo wurin Ahmad din don ana bu'katar wani ya zauna a tare da shi saboda ba a so ya farka babu kowa a kusa da shi.......
Suka ce masa"toh" Haka suka fita gaba d'ayansu suka koma nan harabar d'akin suka zauna daga waje.......,,,
Suna zama sai Ajmal ya kalli Abbaaa yace "Baffa dama kai ne! Wlh nima ban gane ka ba" sai Abbaaa yayi murmushi yace "tabbass baza ka gane mu ba musamman ma su Ahmad,,,,,,,,,dan baza ku san su ba dan tun basu fi shekara biyar ba rabon ku da ganin su...
Sai Ajmal yace" haka ne Abbaaa dan muna gama makaranta daddy ya kaini Dubai karatu shi kuma Fu'ad bayan na tafi da shekara daya sai aka kai shi American don nashi karatun kuma gaba daya sai karshen shekara muke dawo wa hutu ko zasu zo nan Bauchi bamu suke zuwa sai dai idan mun dawo suce kuna gaishe mu,,,,,,,,
Abbaaa ya ce "haka ne mai sunan Baba"sai Fu'ad yace ina su Ahmad din da Yusuf?..,,,,,
sai Inna ta kalli Fu'ad tace ga Yusuf nan Ahmad kuma shine wanda tsautsayi yasa kuka buge shi"
Suka ce "Allah sarki, Allah ya bashi lafiya sai Ajmal yace"Yusuf zo nan mana sai yusuf ya taso yazo wurinsu suka zauna tare yana murmushi dan yaji dadin ganin su shima.....
Sai Abbaaa yace yanzu ya karatun naku?,,,, sai Ajmal ya bashi amsa da"alhamdulillahi ni na gama yanzu shi Fu'ad saura shekara daya ya gama nasa...........
"tabbass! Duk an yi haka mai sunan Baba,,,,saboda lokacin da zaku tafi ma sai da ya nemi shawara ta toh Allah ya taimaka Allah ya sa a yi a saa.......,,
Dukan su suka ce ameen ya Rabbi,,,,,
,,,, sai Abbaaa yace amman munyi waya da shi Baban naku bai ce mini kun dawo ba,ni da yace mini ma ya turo a tafi da Ahmad nani tunanin su Musa ya turo su tafi tare........,,,
Sai Ajmal yace "Eh gaskiya kam haka akayi Baffa,don cewa yayi bazai fad'a maka ba so yake yayi maka surprise yaga zaka gane mu"
Sai Abbaaa yayi dariya yace "Allah sarki Ali,,,, gashi kuwa nina fara gane ku...... Toh ban da abun sa ma ya uba zai kasa gane yaran sa.....,,,
Wlh ma nayi tunanin su Musan ya turo,,,,yanzun nan shigowar kuma d'akin kafin mu fito nan muka gama waya da shi Baban naku yake ce mini da kun sami tsautsayi kun bige wani..... nazo nan asibitin na same ku naga me ke faruwa,,,,,
amman tun da ya fara yi mini bayanin sai jikina ya bani da kune kuka buge Ahmad amman abun da yasa ban saurin yake hukuncin bashi amsar hakan ba dan ban tabbatar ba saboda ban gan ku ba.............
Ajmal yace"haka ne Baffa,toh yanzu Baffa ka kirasa ka fad'a masa halin da muke ciki"...
Abbaaa yace" yanzun nan kuwa Saddiku"sai Abbaaa ya d'auko wayarsa cikin aljihu ya danna number ya kira Kawu Aliyu yana kira ta shiga ta fara ringing can sai ya d'aga suka gaisa da Abbaaa nan Abbaaa yayi masa bayanin komai kuma......
Kawu Aliyu bai ji dad'i ba ya jajantawa Abbaaa ya kuma ce masa insha Allah suma suna nan tafe zasu zo gobe su duba Ahmad din.... Suka yiwa juna godiya suka yi sallama.....
Abbaaa yana ajiye wayar yayi musu bayanin duk abun da suka ce sannan yace gobe Insha Allah yace ma zai zo ya duba Ahmad din........
Suka ce Allah ya kaimu kuma Allah ya kawo su lafiya "Abbaaa yace ameen ya Rabbi.....
Suna zaune suna ta dan hira jifa - jifa sai ga Nurse ta karaso inda suke tace suzo Dr yana magana kuma Ahmad ya farka,,,,,dukkan su suka tashi lokaci daya suka shiga dakin a hanzarce........ suna shiga suka tarar da Dr Nur har ya tayar da Ahmad ya gyara masa kwanciya ya d'an tallafe shi da filo daga bayan sa nan kuma hannun sa ga robar karin jinin nan an saka masa yana ta shiga jikin sa,,,,,,,
Suka karasa wurin Ahmad na ganin su ya fashe da kuka,,,,,Dr Nur ya rararrashe shi yayi shiru dan kar ya dawo musu da aiki baya.... Nan Dr duk yayi musu bayanin yadda zasu bashi magungunan sa da kuma yadda zasu kula da shi,,,, suka Inna suka yi masa godiya shima yayi wa Ahmad add'uar samun lafiya suka fice shida da Nurse din.....
Umar ya karasa wurin Ahmad yace "abokina Allah ya baka lafiya kaji" Ahmad ya dan gyada kai alamun ya amsa sannan Umar ya juyo yace wa su Abbaaa to ni zan wuce gida dan su Baba ba su san halin da muke ciki ba"sai Abbaaa yace toh shikenan amman tsaya muje na raka ka sai nayi wa iyayenaka bayanin komai sai Umar yace "toh"
Abbaaa ya kalli su Ajmal yace toh ku kula da shi kafin na dawo suka ce "toh Baffa sai kun dawo" yace" yauwa suka fice da Umar......
Yusuf kuwa murna shi da Inna ba a cewa komai sun kasa rufe baki tunda suka ga Ahmad ya farfado suna can gaban sa sun kura masa ido sai tambyar sa suke mai yake so amman yayi musu banza kamar bada shi suke magana ba......
❤
*Urs*
*ERMEENART*✍π»
π·π· *_DUK ABIN DA KA SHUKA_*π·π·
♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*♻
*WRITING*
By
*ERMEENART*π
©Edited by :HUMYLUVπ
```This page is dedicated to``` *_JIKAR GARBA π_* ```much of LOVE May God Bless You```π
*46-50*
Ahmad yayi banza da su ya rufe idon sa kamar me bacci.......Inna ta kalli Yusuf tace " ina ga ya samu bacci yi shiru kar mu tashe shi kaji Yusufa"....... Yusuf yace"toh Inna" ....
"toh Inna bara muje muyi sallah sai mu dawo don naga maghriba tayi har an fara kiran sallah"in ji Ajmal...Inna tace "toh Saddiku sai kun dawo nima bara nayi alwala sai nayi sallah don nima ban yi ba".....
Ajmal yace "Inna ayi Mana please yana murmushi"
Inna tace"insha Allah,ai Kullum a cikin yi muku ita muke tayi murmushi itama"
Ajmal yace "mun gode sosai Inna sannan ya ce wa Yusuf da Fu'ad "ku tashi mu je masallaci muyi sallah" suka ce sannan suka tashi suka bi bayan sa suka fita zuwa masallaci......
Suna fita Inna ma ta tashi,domin ta gabatar da tata sallah,,,,,,,,,...
*****
Abbaaa suna isa gidan su Umar suka tarar da mahaifin Umar yana alwala a kofar gida suka karasa inda suke suka yi masa sallama suka gaisa da Abbaaa,mahaifin Umar yana ganin Umar da Abbaaa sai yaji hankalin sa ya kwanta don yayi tunanin Umar yawon nasa da ya saba ya tafi,,,,,,,,,suna cikin gaisawa
Umar ya shiga gida ya ajiye littattafansa ya fito..... Ya samo musu ruwa nan suka yi alwalar shi da Abbaaa...... Bayan sun yi sallah sun fito Baban Umar ya shifid'a musu tabarma suka zauna a soron gidan,bayan sun zauna suka sake gaisawa shi da Abbaaa cikin girmama da mutunci........
Bayan sun gaisa Abbaaa yayi masa bayanin duk abun da ya faru da kuma kar su ga Umar bai dawo gida da wuri ba,,,mahaifin Umar ya jajanta masa sosai ya nuna damuwar sa,,,, Abbaaa yayi masa godiya.....
Sannan mahaifin Umar yace wa Abbaaa"kasan halin yaron naka nayi tunanin yawon nasa daya saba ya tafi......
don har mun fara cigiyarsa ma muka share dan mun san zai dawo gida......ashe tsautsayi ne ya sami abokin nasa,,,,,
toh Allah ya kiyaye gaba shi kuma Ahmad Allah ya bashi lafiya"
Abbaaa yace "ameen ya Rabbi" sannan mahaifin Umar yace wa Abbaaa"bara na shiga gida na kawo abinci sai mu kai musu asibitin yanzu...
Abbaaa yace"a'a ai da ka bar shi wannan ai wahala"
Baban Umar yace"a'a Malam ai idan kayi mini haka ka nuna mini Ahmad ba d'ana bane, kuma mene abun wahala a ciki"
sai Abbaaa yace" inaaaaa ai Ahmad d'an ka ne halak malak....ya fad'a yana dariya"
sai baban Umar yace
"yauwa toh dana ji bara na zo sai mu tafi"
Abbaaa yace "toh Malam sai ka fito"
Baban Umar ya kalli inda Umar yake ya ce"kai Umar shiga kayi wanka idan ka gama sai ka d'ebo wasu kayan naka ka biyo mu asibitin ka zo ku zauna tare da Yusuf kana d'an taimaka musu har Allah ya bawa abokin naka lafiya...... Ya zaro kudi ya bawa Umar yace yayi kud'in mota
Umar ya sa hannu ya karba cikin ladabi yace"toh Baba yana murna"
dan har ga Allah yaji dadi don yana tausayin halin da ya baro abokin nasa ya tashi cikin zumud'i zai tafi ya shirya sai baban nasa yayi masa magana yace "
Amm..Umar ai kun gama jarrabawar taku ko? Umar yace" Eh Baba mun gama yau"
"to Allah ya bada sa a " ameen......baban Umar ya shige cikin gida Umar ma ya wuce d'akinsa sai..
Sai Abbaaa shi kad'ai a zaune yana jan carbi yana jiran fitowar baban Umar su tafi.........
Mahaifin Umar yana shiga gida ya labartawa magaifiyar Umar abun da ya faru tace bara ta d'auko hijab itama zata bisu dan taga jikin Ahmad din,,,,,haka kuwa aka yi ta shirya abinci har da ruwan shayi sannan ta d'auko suka fito soro.........nan baban Umar ya tarar da Abbaaa inda ya bar shi a zaune yana ganin suka ya tashi tsaye suka gaisa da magaifiyar Umar sannan baban Umar ya leka yace wa Umar sun tafi sai ya taho......
Suna fitowa daga gidan sai suka yi karo da wani mai taxi nan makocin su,,, Mahaifin Umar yayi masa magana suka gaisa nan ya kwashe su gaba daya sai asibitin..
******
Bacci 'barawo ashe rufe idon nan da Ahmad yayi har yayi gaba da shi.... Inna suna xaune da su Ajmal bayan sun dawo daga masallaci sai Fu'ad ya kalli Ajmal yace "yaya wlh yunwa nake ji ga jikina yana bukatar wanka ya dan yi tsaki.."
Ajmal ya kalle shi ya ja tsaki shima "wai kai Fu'ad wane irin mutum ne wlh zan yi maka rashin wulakanci fa! Wai kai kadai ne mutum ko an fad'a maka ni duk ban jin yunwar ne"
Ajmal yana rufe baki sai ga su Abbaaa nan sun yi sallama sun shigo......nan suka had'u aka jajantawa juna da iyayen Ahmad dana Umar sannan suka tafi...
Cann jumawa saiga Umar nan ya dawo suka zauna shi da su Ajmal suka zuba abincin nan suka ci tare sannan amman Fu'ad yana ci yana yatsuna fuska Ajmal ya kalle shi ya girgiza kai
Bayan sun gama cin abincin,Umar ya raka su Ajmal suka yi wanka a wani bandaki dake nan barandar dakin bayan sun kammala su ka wuce masallaci suka yi sallah insha'i.....
*******
Gari ya waye yau ASABAR misalin karfe sha daya na safe sai ga kawu Aliyu da matarsa da kuma 'kannan su Ajmal, *Humaida*da *Bilkisu* da kuma Autar su *Amnoor*
suna iso garin Bauchi har sun shigo asibitin suna shiga asibitin kawu Aliyu yayi wa su Ajmal waya yace sun karaso nan suka zo suka taho da su har cikin d'akin lokacin Ahmad har an cire masa abun 'karin jini,,,,Umar ya wanke masa jikin nasa yana zaune a kan gadon yana Shan shayi goshin nan nasa d'aure da bandaji har yanzu da hannun sa....
Su Kawu Aliyu suka shiga cikin sallama suna shiga Humaida suka hada ido da Ahmad tace wow! Sai ta tabo Bilkisu tace "Sis innalillahi! kalle shi amman ya had'u.... i love him" ta dan yi fari da ido.......
Wayyoooooo Humaida a tawa shawarrar.. kar ma ki fara Ahmad NO EASY! .. Amman nayi shiru πkar ki ji haushi ni,ni Ermeenart nayi nanππ»♀ππ»♀ππ»♀ππ»♀
❤
*Urs*
*ERMEENART*✍π»
[8/1, 6:49 PM] Ermeenart π: π·π· *_DUK ABIN DA KA SHUKA_*π·π·
♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*♻
*WRITING*
By
*ERMEENART*π
©Edited by :HUMYLUVπ
♻ *E.W.F*♻
*51-55*
Ta dan yi fari da ido....sai Bilkisu ta kalle ta cikin mamaki tace hmmmm!"ta girgiza kai...
Daga wannan bata kara ce mata komai ba sai Humaida ta had'e rai ta zum'bura baki.....har suka 'karasa cikin d'akin... Su Abbaaa da Inna suna ganin su baki ya ki rufuwa ana ta _lale marhabun_......su Yusuf suka tashi suka bawa su Kawu Ali wurin da suke zaune suka zauna,,,,,,
Ahmad kuwa yana Shan shayi tunda suka h'ada ido da Humaida ya ga tana ta kallonsa sai ya kauda kansa yana tsaki cikin zuciyarsa kuwa cewa yake yi (ina ga wannan mayya Ce shegiyaa sai kallon mutane take yi kin yi jaka yar rainin hankali)ya ja tsaki....
*________*
suna zama suka gaiggaisa aka jajantawa juna Kawu Ali ya tashi ya je ya zauna kusa da Ahmad ya dafa kafad'arsa yace "Ahmadu abokina kuma d'ana yana dariya,,,Allah ya baka lafiya Allah ya 'kara sauki Ahmad yace bude baki a hankali yace"ameen",,
sannan Kawu ya ce "kar ka damu zaka sami sauki kaji"
Ahmad ya gyad'a kai alamun ya amsa sannan ya sunkuyar da kansa 'kasa yana kallon shayin da ke hannun sa........ Sai Kawu ya kuma cewa "yanzu ga 'yan uwanka nan zamu bar su Ajmal da Fu'ad dama hutu suke yi zasu zauna har lokacin da Allah ya sa ka sami sauki sai ku taho tare kayi zaman ka a wurin kaji"
Ahmad yayi banza da shi kansa yana nan a 'kasa ya ha'de rai a zuciyarsa kuwa cewa yake yi (babu inda zani ji 'ya' ya kamar mayu tun yanzu sai wani kallon mutum suke yi dan rainin hankali) _shi Ahmad a tunaninsa kallon da Humaida take yi masa wai na rainin hankaline bai sai kamuwa tayi baπ_
sai Abbaaa ya ce "insha Allah nan da sati biyu yana tafe da ku yana murmushi sannan ya ce muna godiya Aliyu Allah ya bar zumunci" nan suka cigaba da hirar yaushe gamo tsakanin Abbaaa da kawu....
Ahmad ya mikawa Yusuf shayin daya ke sha yace ya koshi Yusuf ya karba ya ajiye sannan ya d'auko masa maganin sa ya bashi ya sha sannan Umar ya taimaka masa ya koma ya kwanta....
Bangaran Humaida kuwa ta ishi Bilkisu da hirar Ahmad tunda suka gaisa tayi masa sannu ya amsa ta shiga farin ciki...... duk motsin da Ahmad zai yi akan idon ta kuma sai ta fada wa Bilkisu, Bilkisu data gaji tace 'wai ke Humaida mai yake damun ki ne... baki tafasa zaki kone duka duka shekarun ki nawa? 18 fa! Har kike irin wannan abun toh wlh idan kika cigaba da haka baza kiyi karatu ba nan gaba ki shiga hankalin ki"
Humaida ta dan yi tsaki fuska ta 'bata rai "haba aunty Billy yanzu dan na SO d'an uwana laifi ne"....
Bilkisu tace "noooo babu komai Sis Allah ya bada sa a" ta cigaba da danna wayar ta da take yi,,,
Bilkisu ita ce babba ta girmi Humaida,amman Ajmal da Fu'ad sun girmeta daga ita sai Humaida sai Amnoor amman daya ke Humaida nada girma jiki sai kace ita ce mai shekarun Bilkisu dan ta fita girman jiki,
Bangaran Inna suna ta hira da mahaifiyar su Ajmal Hajiya Rukayya Inna ta kalle ta tace "Hajiya yanzu su Bilkisu suka girma haka ikon Allah har Humaida ta fi Bilkisu amman tana karama tafi kowa kankanta" dukkan su suka yi dariya......
sai Hajiya Rukayya tace "Inna kenan ai kune bakwason zumunci,sune dai yayanki har sun girma sun zama 'yan mata..gashi ma har su Ajmal suka bige dan uwansu amman ba su sani ba, saboda babu zumunci"
Inna tace "ba haka bane hajiya kisan yau da gobe ga kuma jikin girma"...
Hajiya tace "haka dai kika ce amman tana dariya sannan tace ai kin fini yarinta ma" dukkan su suka saka dariya sai Abbaaa ya juyo ya kalle su suna cikin hira da kuwa sai ce tohh dariyan me ake yi haka......
Inna tace babu komai tana murmushi sai Kawu Aliyu yace " tohh yayi haka ake so Allah bar zumunci Hajiya ku shirya muna sallah zamu tafi" suka ce "toh"
nan suka tashi dukkan su suka yi sallah har Ahmad shima yayi tashi a zaune dan jikin nasa babu kwarai har yanzu.......
Bayan sun yi sallah suka zo suka yi sallama suka sake yiwa Ahmad adduar samun lafiya sannan su Ajmal suka raka su suka tafi amman Humaida hankalin ta na kan Ahmad shi kuwa bai son tana yi ba....
***********
Tun bayan tafiya su Humaida kusan Kullum sai ta kira Fu'ad a waya taji ya jikin Ahmad din..... Don sun fi shiri da shi saboda Ajmal baya yi mata wasa shiyasa ma bata fara kiran wayan a tasa ba.....
Cikin ikon Allah yau Ahmad satin sa biyu a asibiti ya sami sauki sosai yau ranar LARABA misalin karfe sha daya na safe aka sallame su daga asibitin suka koma gida washe gari da safe Abbaaa ya kira Kawu ya sanar da shi Kawu yace to Alhamdulillahi amman yana neman Alfarma da Abbaaa ya barsu su taho Kano yau din (Alhamis) Abbaaa yace to shikenan babu damuwq nan suka hada kayan su Abbaaa da Inna suka ja Ahmad daki suka yi masa fada na fitar hankali dan Inna har cewa tayi in har ya sake yayi rashin ji to bata yafe masa ba....
Nan suka yi sallama Yusuf da Umar suka yi ta kuka Inna ta basu hakuri.... *su Ahmad kuwa tafiya ta meka sai kano*
************
*Garin KANO ta Dabo Tumbi Giwa*
❤
*Urs*
*ERMEENART*✍π»
[8/6, 1:56 PM] Ermeenart π: π·π· *_DUK ABIN DA KA SHUKA_*π·π·
♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*♻
*WRITING*
By
*ERMEENART*π
©Edited by :HUMYLUVπ
```This page is dedicated to``` *_Aunty Humaida HUMYLUV_ π*```much of LOVE May God Bless You```π
*56-60*
*_Garin KANO ta Dabo Tumbi Giwa_*
Humaida ta tashi daga bacci ta yi wanka ta shirya sannan ta fito daga d'aki ta shiga falo,,,,,,,
nan ta tarar da Amnoor da Bilkisu sun gama breakfast zasu wuce makaranta....... dama ita Humaida tare suka yi candy da Ahmad wannan shekarar,,,,shiyasa sai da ta gama baccin ta sannan ta fito saboda tasan ba makaranta zata ba,kuma ba wani aiki zata yi ba saboda akwai mai taya su aiki wato Baraka mai aiki......
Bilkisu tana karatunta a BUK yanzu level 3 zata shiga,Amnoor kuwa tana jss3,ss1 zata tafi.
Bilkisu ta kalli Hajiya Rukayya mahaifiyar su wadda suke kira da (momy), tace "hmmm momy ga yar hutun ki nan sai yanzu aka tashi......."
momy ta kalli inda Humaida ke tahowa tayi dariya tace"ai halin Humaida sai ita shiyasa take 'kara hawa kamar fara shi",,,
Sai suka kwashe da dariya gaba d'ayansu momy ta sake cewa "Allah kuwa Bilkisu,nima fa ta fini girma"nan ma suka yi dariya suna kallon Humaida.......
Humaida na 'karaso wa inda suke ta samu guri ta tsaya ta had'e rai ta zumburo baki...dan tun da ta taho taga ana kallon ta ana dariya tasan maganar ta ake yi.....
Momy ta kalle ta tace "lafiya kika zo kan mu kika tsaya mene ne haka babu sallama babu gaisuwa haba Humaida"
momy na rufe baki sai ga Nasiru direba wanda yake kai su Bilkisu makaranta ya shigo yayi sallama ya gaishe da momy yace idan su Amnoor sun shirya su fito,,,,,,,momy tace masa"eh gasu nan zuwa Nasiru"
Dama Bilkisu suna ganin shi ita da Amnoor suka tashi suka shiga d'aki suka d'auko jakunku nan su na makaranta suna fitowa suka yi sallama da momy suka wuce suna fita Nasiru ya jasu a mota sai makaranta,zai fara zuwa ya ajiye Amnoor sannan ya wuce ya kai Bilkisu......
Humaida na nan tsaye tana fishi bayan momy tayi mata fad'a,,,
sannan ta dawo kusa da momy ta zauna tace "momy ina kwana"....
Momy ta ce"lafiya kalau ga breakfast din ki can kije ki karya"
Humaida tace "ok momy tnx",
sai momy ta kalle ta tace "wai ke fishin me kike yi ne haka"
nan Humaida ta d'an 'kare had'e fuska tace "momy naga su aunty Bilkisu ne ina fitowa kuka saka mini dariya" ta karasa maganar ta cikin shagwa'ba....
momy ta kalle ta tayi dariya tace "Humaida kenan"hirar su fa suke yi bada ke suke ba....... Sai ta d'an saki rai tayi fara'a
tace"ai nazata dani suke, idan suka dawo na rama kuma na had'a su da daddy,,,,,,,,,
momy tayi dariya tace "hhhhmm.... Humaida rigima kedai baki gajiya da fad'a,......ta d'an sunkuyar da kai tayi murmushi...
Sannan momy ta ce"yau dai abokin naki zasu dawo (Fu'ad) ...."
Humaida ta tashi jumbur cikin murna "dan Allah! Mommy,da gaske!"
"Da gaske mana jiya suka yi wa dady ku waya an sallame su a asbiti shine yace su dawo yau"
"Wow! Amman na ji dadi Sosai wlh,,,,,amman har da Ahmad d'in za su taho? ko,momy"
Momy ta kalleta tace"kin jiki kuma da wata irin tambaya Humaida,da shi mana zasu zo,ai Ahmad ya zama namu yanzu shi da gidansu sai dai ziyara".....
Momy ta fad'a tana dariya..... Humaida ta saka wata dariya,"
"toh Momy Allah ya kawo su lafiya"cikin jin dad'i yau dai zata kara saka Ahmad a idon ta.....
Sannan tace "momy bara nayi maza nayi breakfast din sai mu fara shirye - shiryen abincin su kafin su 'karaso",
Momy tayi dariya tace "Humaida wannan murna haka tace "Momy ai dole ne nayi,nayi missing din su broz sosai wlh"
tana fad'i ta mike tsaye Momy tace "yauwa idan kin gama break din sai ki duba kitchen duk abun da babu sai ki fad'a mini a sayo yanzu,dan kar a zo a fara aiki ace babu wani abun tace"toh Momyna" sannan ta wuce don tayi breakfast d'in........
Sai ga daddy nan ya sauko Humaida ta gaishe shi,sannan karaso wurin momy yace"hajjaju zan dan leka office amman dade zan yi ba idan kuma su Ajmal sun dawo kafin na dawo to a kira ni a waya momy ta amsa nan suka yi sallama ya wuce.
*_________________*
Ahmad tunda suka nufi hanyar Kano bai ce wa kowa 'kala ba....
Ajmal da Fu'ad kuwa suna ta d'an hira jifa - jifa amman da tafiya tayi tafiya Ajmal shiru yayi dan baya son yawan magana idan yana tuki musamman a babar hanya,,,,
Ya mayar da hankalisa gaba d'aya kan ta kinsa...haka wancan lokacin Fu'ad ne ya d'auke sa da hira har Allah ya a kawo tsutsayi ya ratsa suka bude Ahmad......
Fu'ad kuwa kayan surutu da rawar kai Bakin sa bazai iya shiru ba sai ya kalli Ahmad yace "Ahmadi ya kayi shiru ne"......
Ahmad kuwa bai san yanayi ba ya tafi duniyar tunanin, yana ta tunanin irin fad'an dasu Inna suka yi masa da maganganun da suka fad'a masa zuciyar sa cike take da Bacin ciki.....ya karkata fuskarsa yana kallon waje ta cikin wundon motar.....
Fu'ad daya ji shiru sai ya kallo Ahmad ta cikin mirrow mota wanda yake nuno mutan nan da ke bayan mota a Zaune sai ya ga alamun Ahmad din baya tare dasu.....
Sai Fu'ad ya juyo baya ya zuro hannun sa ya dan daki Ahmad ya kira sunan sa da karfi....... sai lokaci Ahmad ya dawo daga duniyar tunanin...
Sai Ahmad ya zabura ya dawo daga duniyar tunanin da yake sai ya ga Fu'ad ke yi masa magana.... "Ahmad tunanin me kake yi ne ina ta magana kayi shiru" in ji Fu'ad sai Ahmad yayi murmushi yace babu "komai" ya sun kuyar kuyar kai.... Sai Fu'ad yace "toh shikenan amman ka rage tunani kaji"
"Ahmad ya gyada kai yace toh".... haka suka cigaba da dan yin hirarrakin su shida Fu'ad,,,,
***********
Momy! Momy!! ..... Na'am! Na'am Humaida! ya ake yi ne?
momy ta tashi ta nufi kitchen din inda Humaida ke kiran ta momy na shiga Humaida tace "momy kinga babu koda babu dankali kuma babu fruit" ta fada tana shagwaba da rawar murya kamar me kuka....
"Humadaiπ€ni na zata wani abun ne ma to ba sai a sayo ba yanzu " inji momy
" Dama ina so na yiwa Ahmad farfesu dan ya ji dadin Bakin sa kinga mara lafiya ne shi toh dana ga babu shine naji babu dadi"
Momy tayi dariya tace "hhhhh Allah ya shirye ki, ni muje na baki kud'i kuje da Nasiru naga ya dawo tun dazu sai kusayo duk abun da babu....... Ta biyo bayan momy tana dariya
Suna zuwa momy ta bata kud'in,babu 'bata lokaci suka tafi da Nasiru kasuwa suka yo cefanan.... sai ga shi sun dawo da kaya niki-niki nan Humaida da Baraka mai aiki da momy aka had'u a kitchen aka fara aiki cikin lokaci kadan har komai ya kammala.....
Humaida aka jajjere komai akan dinning table sannan ta wuce tayi wanka da dau kwalliya tayi kyau sosai ta saka wata atamfa pink Nd black an yi mata dinkin doguwar riga,ta bazo gashin ta baya tayi style na dauri sannan ta fito falo ta zauna tana baza kamshi ta kunna Tv takai tashar Arewa24 tana kallo,,,,,,
Sai ga momy ma nan ta sauko cikin Wiss Atamfa orange da adon green da black ajiki tayi kyau sosai itama, tana fitowa.....
suka ji Hon din mota ai kuwa Humaida zumbur momy! Bara na gani ko sune,ta tashi ta leka ta hundo tana lakawa sai taga ashe Nasiru ne ya dauko su Amnoor daga schl........
"momy basu bane su aunty Bilkisu ne " momy tace"ok suma insha Allah yanzu za kiga sun karaso" ta zauna akan kujera suka cigaba da kallon....... Sai ga su Bilkisu sun shigo suka yiwa momy sannu da gida sannan Bilkisu ta kalli Humaida ta saka dariya tace"ke kuma wannan kwalliyan fa kamar wadda zata gasarar sarauniyar kyau hhhhh"
Humaida tayi banza da ita ta cigaba da kallonta........ Dukan su suka yi dariya da momy da Amnoor saboda irin hade ran da Humaida tayi, tai banza da Bilkisu...
Sannan momy tace Bilkisu kuma ku tashi kuje ku shirya yanzu su yayan ku zasu dawo Bilkisu tace""auuu haka ne fa wlh na sha'afa"
Nan suka tashi Suma suka je suka yi wanka suka dawo suka zauna ana ta jiran su Ajmal
saboda da akwai tafiya sosai tsakanin Kano da Bauchi shiyasa har yanzu basu kara so ba inji momy .......
Misalin karfe 5 na yamma sai ga su Ajmal nan sun shigo layin Ahmad kuwa ya saki ido da Baki yana ta kallon gine gine kala kala masu abun burgewa unguwa kamar a turai......
suna karasawa gidan suka yi Hon Baba mai gari ya bude musu gate suka shigo nan ma Ahmad ya saki baki yana kallon irin tsaruwar da gidan yayi.Ajmal kuwa yana ta hamdala ga ubangiji sun dawo gida lfy
Su Bilkisu,Amnoor, Humaida aka tafi da gudu za a tarbi su Yaya momy ta bi bayan su cike da farin ciki don suna jin Hon din Amnoor ta laka ta hango su tace musu, sune..........
❤
*Urs*
*ERMEENART*✍π»
[8/7, 8:36 PM] Ermeenart π: π·π· *_DUK ABIN DA KA SHUKA_*π·π·
♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*♻
*WRITING*
By
*ERMEENART*π
©Edited by :HUMYLUVπ
```This page is dedicated to:```
*Meenal cute*π
*Bally*π
*Asiya Adam*π·
*Habiba Usman*π
*Dotar Ubbe*π
*See See*π
*Neena Cool*π
*Aunty Haliloss*✍π»
*Amnoor*π
*Ummixeey*π
*Rahila Dauoda*π
*Ummu Khamal*π
*Sis Aishaf*πΉ
*Salma.I.G*π
*Deeejerh*π```much of LOVE May God Bless You All```π
*61-65*
"Oyoyo! oyoyo!"in ji su Amnoor.... Suna gudu har suka 'karasa inda Ajmal yayi packing motar a harabar gidan
suna 'karasawa wurin motar,har Fu'ad ya fito fuskarsa d'auke da fara'a dan yaji dad'in yadda suka fito tarbarsu....... Humaida ta tafi da gudu ta rungume Fu'ad "oyoyo Yaya,i Miss you" cikin shagwaba....
Fu'ad yayi dariya ya ce "eyyah sowie Swt sis we Miss you all,,,,
Bilkisu kuwa wurin Ajmal tayi daman ita sun fi shiri da shi dan halin su kusan iri daya ne ga hakuri da kunya,,,,
tana zuwa ta bud'e masa motar ya fito,yana fitowa Amnoor ta ruga a guje ta rungume shi,,,,,, "yaya Ajmal i Miss you,kwana 2 babu mai bani sweet Nd chocolate tun da ka tafi har momy ma bata bani,wai ina Shan za'ki da yawa,"cikin shagwaba take maganar ta.........
Amnoor na rufe baki dukkan su,suka kwashe da dariya har momy..
sai Ajmal yace "sorry Autan momy ai gani na dawo yanzu, YAU sai kin sha chocolate kin koshi,ki tuna mini anjuma muje shopping sai ki za'bi duk wadda kike so kinji"
Amnoor ta saka tsalle cikin murna tace "ok Yaya dt iz why i love youuuu tnx" tayi masa Kiss a hannu sannan ta ruga a guje tayi wurin momy tana fad'a mata Yaya zai kai ta shopping momy tayi dariya tace Allah ya kaimu Auta.....
Bilkisu tace "Yaya Ajmal sannu dazu ya hanya"
Yace" alhamdulillahi Sis"
tace "masha Allah" sannan ta sa hannu ta kar'bi yan abubuwan da ke hannun sa,su waya ne da laptop.........sannan shima yace"nagode sosai lovely Sis,ya kalle ta fuskar sa d'auke da murmushi...
*
Ahmad kuwa yana cikin motan ya saki baki yana kallon su cikin ransa kuwa cewa yake (ji dan Allah wani iskanci da abun haushi, ai wannan iskanci ne wlh bazan zauna a gidan nan ba,su iskantani)
Momy kuwa tana tsaye ta rike hannun Amnoor sai nishad'i take yi dan taji dadin ganin yadda yaran ta suka dawo cikin koshin lafiya,,,,,....
"Yaya! ina AHMAD d'in? Momy tace tare zaku taho da shi yana ina ban ganshi ba"in ji Humaida cikin shagwaba take yiwa Fu'ad wannan tambayar......
Tana d'an dube-bude ko zata hango Ahmad cikin mota, da yake motar irin mai duhu glass ne,
Tana rufe baki sai Ahmad ya bud'e motar ya fito fuskarsa dai babu yabo babu fallasa.......dan baya son Humaida ta cigaba da yin maganar sa,haushin ta yake ji haka kawai yaji bata burge shi.....
Aikuwa Ahmad na fitowa Humaida ta saki hannun Fu'ad ta yo wurin Ahmad tana ta murna har da rawar jiki sai fari take yi ita kadai "Yaya Ahmad oyoyo,na zata su Yaya basu zo da kai ba har na naji babu dad'i......
Ta bawa Ahmad haushi amman sai ya share, yayi mata d'an murmushi..... Wayyoooooo dadi Humaida ta shiga wani shau'ki Ahmad ya kulata,,,,,,,,,,, ana ta tunanin dan yadda ta lura da shi ba shi son kule kule da magana,,,,,, kuma tabbass hakan ne Ahmad yan mata basu dame shi ba.......
Momy ta 'karaso wurin tace "toh Suda sarkin surutu kyabar shi su shiga gida ya huta ko"
Humaida tayi dariya tace "yess Ma! AM sorry"
Momy ta kalli Ahmad tace "Ahmad sannu kaji ta dan dafa kafad'arsa, kun sha tafiya ko sannu" Ahmad ya sunkuyar da kai yace "yauwa"
Sannan Momy ta kalli Ajmal tace" Yayansu wato Ajmal haka take ce masa bata fadin sunan saboda shi ne D'anta na fari,...... Momy tace masa "yanzu muje kuyi wanka ku ci abinci ku huta "
Ajmal yace" toh Momy,amman ina Nasiru yazo ya shigar mana da kayan nan cikin gida"
Sai ga Nasiru nan aguje dama yana nan a tsaye a can gefen su yace "gani nan yallabai"
Ajmal yace "yauwa kayan nan zaka shigar mana da su cikin gida,"nan ya bude boot Nasiru ya fito da kayan gaba d'aya har na tsarabar da su Inna suka bayar a kawo wa su Momy.......
Sannan suka wuce gaba d'aya cikin gida Ajmal ya yi bangaran da d'akin sa yake Fu'ad kuma suka wuce da Ahmad d'akin sa su Momy da Bilkisu suka wuce cikin gida......
Ba 'bata lokaci Nasiru ya kwashe kayan nan duka ya shigar musu da shi cikin gidan........
Momy na zama ta kira Daddy tayi masa albishir da yaran sa sun dawo cikin koshin lafiya yayi murna sosai sannan yace gashin zuwa nan da minti goma dan har ya taho dama daga office din ma.......
Bayan mintina kad'an sai ga Ahmad da Fu'ad sun fito tsaf! Daga dakinsu sun yi wanka sun rama sallolinsu nan suka shigo falo suka tarar da su Momy a zaune suna ta hira,
Ahmad ya tsugunna ya gaishe da Momy ta amsa cikin fara'a sannan tace "Ahmad ka saki jikin ka kaji nan gidan ku duk wannan kannan ka ne da yayyanka kuma duk abun da kake so kar kar kayi kunya sanar da mu ka fada mana kaji",
Ahmad yaji dad'i Sosai yadda Momy ta karbesa sai yaji gaba d'aya ta burge sa ya ce" _toh Momy insha Allah,Nagode sosai_"
Momy tayi murmushi "ai babu godiya Ahmad,kai dana ne"
Sannan ta kalli Fu'ad tace ina Yayannaku? "
"yana ciki ina ga bai gama shiryawa ba" inji Fu'ad
"Amnoor tashi kije ki kira yaya Ajmal kice yazo za a ci abinci,"
FU'AD , AHMAD ,MOMY ,HUMAIDA duk ku tashi muyi dinning d food iz ready,in ji Bilkisu, sanannan ta saki dariya...
Suma suka kwashe da dariya Ahmad yayi murmushi..... Amman fa banda Humaida saboda da tun da Ahmad suka shigo Humaida tayi suman zaune ta tafi dogon tunani saboda yayi mata kyau duk da dai ya dan rame amman yayi mata mugun kyau kamar bashi ba taji son sa ya 'kara ratsa ta.....
Amnoor na zuwa taci karo da Ajmal yana fitowa shima yayi wanka yayi tsaf! Da shi yana baza kamshi yana ganin ta ya saki murmushi yace ganin muje ya kamo hannunta suka nufo falon,
suna shigowa cikin falon sai ga Daddy nan yayi sallama shima ya dawo Amnoor ta tafi da gudu ta rungume shi "oyoyo Daddy",
_Ahmad kuwa sai da ya dan yi shock saboda yana mugun tsoransa da yake sai kuma ya basar,_
nan suka yi masa sannun da zuwa suka wuce gaba dayan su dinning suka ci abinci sai da suka koshi suka yi nak! Musamman ma Fu'ad sai da ya Ci yazo wuya suka rinka yi masa dariya, Ahmad kuwa dai ba wani ci yayi sosai ba amman ya sha fruit sannan ya sha maganin sa....
bayan sun gama suka yi hammadala sannan kowa yaje yayi sallah isha'i..... ,bayan sun dawo Daddy ya had'a su gaba daya a falonsa yayi musu nasiha da su had'e kansu kuma a zauna lafiya ,bayan nan suka dan yi kallo sannan kowa ya tafi ya kwanta..
*___________________*
Asma'u! ya tagumi kuma? tunanin mene ne kika yi haka baki bacci ba,,,,
Inna ta dan yi murmushi ta kalli Abbaaa tace"hmm...Malam ina tunanin Ahmadu na ne sai ta fashe da kuka.........
❤
*Urs*
*ERMEENART*✍π»
[8/8, 6:07 PM] Ermeenart π: π·π· *_DUK ABIN DA KA SHUKA_*π·π·
♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*♻
*WRITING*
By
*ERMEENART*π
©Edited by :HUMYLUVπ
```This page is dedicated to:```
*Meelat Ahk*π
π»
*Pharteemarh*ππ»```much of LOVE TNX```π
*66-70*
"Habaa,mene ne kuma na kuka"...inji Abbaaa sannan ya d'an yi dariya
yace"dama ai na sani Asma'u baza ki iya daurewa kina da ma'kon 'ya'ya a ranki,,,,,, amman fa naga ke da kanki kika nemi alfarmar hakan a wurina da na mayar da Ahmad KANO da zama.......ko ba a yi haka ba?
Inna ta share hawayan ta sannan ta kalli Abbaaa tayi murmushi tace"Eh haka ne Malam,kukan ma daka ga ina yi na sabon ne,,,,,,,
Abbaaa yayi dariya yace"toh kin ga tun kafin abu yayi nisa bara na kira Kawun a waya na fad'a masa a dawo miki da yaron ki hhhhhh,"
Sai kuma Inna ta saka dariya tace "a'a,a'a Malam ba ayi haka ba saboda dame yaro ma zama Saurayi ni dai rashin jin sa nake gudu kar yaje yayi abun da za a na'kasa shi"
Abbaaa yayi murmushi yace "kar ki damu duk wannan mai sauki ne mu dai muyi ta yi musu addu'a,"
nan Abbaaa yayi ta rarrashe ta sannan ta koma ta kwanta har bacci ya d'auke ta,
Bangaran Yusuf kuwa duk ya kasa bacci ya zauna yayi tagumi ya zubawa makwancin Ahmad ido yana ta kallo saboda sabon da suka yi duk da baya jin dadin sa amman yana matukar son d'an uwan nasa,daya ga zaman da tunanin bazai yi masa ba sai ya tashi ya d'auro alwala ya tayar da nafila......
*_____________*
Ahmad yana kwance idonsa a rufe kamar mai bacci amman ba baccin yake yi ba zuciyar fal! Da tunani kala - kala,yanzu an raba shi da abokansa da iyayensa da duk wani jin dadin sa,ya ja wani tsaki sannan ya gyara kwanciyar sa,a haka har bacci ya d'auke sa........
********
Cikin ikon Allah yau watan Ahmad biyu a garin Kano gidan Kawu Aliyu,ya murmure ya warke sosai har ya dawo da jikin sa,fatar nan tasa sai she'ki take yi idan ka ganshi kayi tunanin wani Babban saurayi ne me kimanin shekaru ashirin da shida....baka ce d'an shekara ashirin da d'aya bane saboda ya murje yayi kyau tass!!,,,,,
Yana zaune a harabar gidan shi kad'ai misalin karfe sha d'aya na safe, yana ta kallan bishiyu kala - kala da furanin su masu kyawun launuka,dama ranar talata ne Ajmal sun fita office da Daddy,,,
Fu'ad kuwa ya koma makarantar sa dake a America tun sati biyu da suka wuce,sai wani hutun zai sake dawowa insha Allah,
Bilkisu da Amnoor ma sun tafi tasu makarantar gidan ya rage daga Ahmad sai Humaida da Momy da kuma sauran yan aikin gidan.....
"Kaiii Momy ji yadda wannan window yayi daud'a sai kura ke tashi, wlh Baraka bata goge shi, tana yi tana na karkad'e shi da hankicin da ke hannunta"Humaida ke wannan maganar,,,,,
Momy kanta na sunkuye tana danna wayar ta bama ta d'ago ta kalle ta bata amsa"tun da Baraka bata gogewa ke mene ne amfani da ba zaki goge ba,tunda kika gama makarantar nan baki da aiki sai bacci ni har so nake a fara Register JAMB din nan kije kiyi idan da rabo ki fara wata schl din kowa ya huta,"
"Kaiii Momy ni d'in"
Momy ta ce "kedin fa Humaida" tana dariya
"Toh shikenan Momy,baccin ma fa danake yi 'kara'i ne, wanda ban yi ba Da dasafe shine nake ramawa faaa"Humaida tayi maganar cikin shagwa'ba,tana yi sai ta saka hannu ta bud'e window d'in dan ta 'kara goge shi,,,,,, ai kuwa tana bud'ewa idon yayi mata arba da Ahmad shi kadai a zaune.......sai taji wani sanyi a ranta ba shiri ta jawo window ta rufe ta fasa gogewa,
"Momy ga Ahmad can bara na je,na taya shi hira dan naga shi kadai a zaune,,,,,,,bama ta tsaya taji amsar da Momy zata bata ba tayi wulli da hankicin dake hannunta ta yar dashi ta ruga waje a guje ta fita.....
Momy ta bita da kallo har ta fita sannan ta girgiza kai tayi dariya tace " Allah ya shirya mini ke Humaida" sannan ta tashi ta shiga d'aki dan ta kwanta ta 'kara hutawa dan har yanzu safiya ce, karfe sha daya da rabi....
Humaida na fita,ta d'an tsaya ta gyara dressing d'inta ta sauya tafiya aka fara takun dai - dai, har ta 'karaso inda Ahmad yake shi bai ma lura da ita ba dan daga bayan sa ta taho,tana zuwa tayi masa sallama sai ya juyo ya kai kallon sa wurin ta,sannan ya amsa ya mayar da kasan kan abun da yake kallo......
Sannan ta jawo daya kujerar ta kusa da shi ta zauna ta kalle shi ta kashe murya tace "Ahmad sannu da hutawa".... Bai ma kalle ta ba yace "yauwa sannu"
Gaba dayan su suka yi shiru d Humaida ta ji shirun yayi yawa sai ta dan yi gyaran murya tace"hmm...am...Ahmad" sai ya juyo ya kalle ta,yana kallon ta duk ta duririce da fara kame-kame tana dan sosa kyeya..... Sai Ahmad yace "na'am ina jin ki, ya aka yi?"
"dama cewa nayi baka da waya ne? "
Ahmad yace"eh bani da ita" yana bata amsa ya tashi tsaye yace mata bara na shiga ciki na d'an kwanta,bai tsaya ya ji amsar ta ba yayi tafiyar sa ya bar ta a zaune baki a sake hhhhh.....
Humaida na shiga gida ta tarar Momy har ta shiga d'aki nan ta bita cikin dakin......
tana shiga Momy har ta fara bacci tana ganni haka,har ta juya zata fita sai taji Momy ta kira ta
dan taji alamun an shigo daki dama baccin bai yi nisa kuma ta san shigowa sai Humaida,ta kirata.sai ta koma ta zauna akan kujerar da ke gefe gadon ta fasa komawan ta zauna tana kallon Momy..
sai Momy tace mata mene?" sannan Humaida tace "hmmm.. Mommy ashe Ahmad bashi da waya dan Allah ki sa dady ya saya masa kinji,Momy tace" to shikenan zan fada masa insha Allah...
Humaida tayi godiya ta tashi ta fita sannan Momy bata koma ta kwanta ba sai da ta yiwa dady waya daya sayowa Ahmad waya.....
bayan kowa ya dawo an ci abinci an yi sallah ana zazzaune ana hira sai dady ya kalli Ajmal yace "dauko mini wayar nan dana baka kasayo dazu"
Ajmal ya tashi ya d'auko ya kawo wa dady yana kawo wa sai dady yayi masa nuni da Ahmad yace "bawa kaninka"
Ajmal ya bawa Ahmad fuskarsa d'auke da murmushi,,,,,Ahmad ya kar'ba cikin murna waya ce iphone6,yayi godiya sosai,sannan ya mikawa su Momy suka gani suka sa albarka suka taya shi godiya Humaida kuwa murna da dadi kamr me......
sannan dady yayi gyaran murya yace "toh alhamdulillahi tunda result dina ku yayi kyau Ahmad kai da Humaida yanzu na biya muku kud'i zaku zana JAMB Ku wuce jama'a ranar jama'a za a yi sai ku shirya a nan MSK center zaku yi dan haka nayi wa kabiru dire bazai kai ku".....
nan suka yi godiya sosai sannan kowa ya tashi ya tafi....
Cikin ikon Allah, Ahmad da Humaida sun zana jarrabawar Jamb dukkan su sunci kuma sun sami addimision a Buk (Bayero University kano) Ahmad yana karantar injiniya,Humaida kuma medicine
Su Bilkisu kuwa har an gama karatu taje service ta dawo,an saka ranar auran ta nan da wata biyar,
Fu'ad ma ya dawo da kyakkyawan sakamako shima ya kammala karatun nasa
********
Yusuf kuwa ana ta shirye shiryen zana SSCE wannan shekarar yana ta murna......
❤
*Urs*
*ERMEENART*✍π»
[8/9, 5:57 PM] Ermeenart π: π·π· *_DUK ABIN DA KA SHUKA_*π·π·
♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*♻
*WRITING*
By
*ERMEENART*π
©Edited by :HUMYLUVπ
*71-75*
Kwanci tashi su Yusuf har sun zana jarrabawar su ta kammala sakandare,result din su ya fito yayi kyau sosai,,,,,,
Yusuf da abokansa Fahad da Jasmir sun fi kowa cin jarrabawar dan haka gwamnati ta biya musu scholarship na 'karin karatu a kasar Dubai da su je su karanci karatun likita.......
Yusuf sun yi murna sosai ranar da wannan Labari yazo musu dan haka bai tsaya ko ina ba yazo gida ya fad'awa iyayensu sun yi murna sosai,Inna da Abbaaa sun sa albarka..... sannan Abbaaa yace kira Kawu Aliyu ya sanar da shi,kuma yace suna tafe nan da sati mai zuwa, dan tun da Ahmad ya dawo Kano basu je ba, Kawu Aliyu shima yayi murna sosai,sannan yace suna zuba ido Allah ya kawo su cikin koshin lafiya
Bayan Kawu Aliyu sun gama waya da Abbaaa ya tara su Ahmad a falon sa ya sa sanar da su abun alkairin da ya sami Yusuf da kuma zuwan su Inna nan da sati mai zuwa,nan kowa ya cika da murna yayi farin ciki su Ajmal su Momy kowa dai ya ji dad'i,
amman fa ban da AHMAD! Daya ga alamun zasu gane shi sai Ya dan yi murmushi yayi murna shima amman fa ba har cikin ransa ba......
Ranar Ahmad bai iya bacci ba yana ta Bakin ciki da 'bacin rai wai yau Yusuf ne zai tafi wata 'kasa karatu ba shi ba to wlh da sake abun da bazai ta'ba yiwu ba,ya d'auko waya ya kira wani abokinsa Mahnoor yace masa dan Allah ya shigo schl da wuri akwai matsala,,,,,, Mahnoor ya amsa masa da zai shigo insha Allah...... haka Ahmad yayi ta tunani yana kai kawo bayan ya ajiye wayar har gari ya waye....
Mahnoor aminin Ahmad ne department din su d'aya babansa Babban dan kasuwa ne a kano yana da arziki sosai amman Mahnoor shima baya jin magana dan har shaye-shaye yake yi kusan kowa yasan shi a bangaran department dinsu dan baya tsoron kowa,sai dai inda yayi wa kansa gata toh yana mayar da kai yayi karatu....
Washe gari misalin karfe takwas na safe,Mahnoor har ya riga Ahmad shiga schl din,ya kira Ahmad a waya yace ya 'karaso yana bayan ajin da zasu yi lecture yana jiransa,
Ahmad ya ce toh! Shima gashi nan zuwa yana nan daidai wurin ajin...... Ba a fi miti biyar ba Ahmad suka had'u da Mahnoor,,,,
Ahmad yana zama ya zayyanewa Mahnoor komai akan tafiyar Yusuf karatu Dubai,,,,,yana gama fad'a masa,
Mahnoor yayi wata muguwar dariya ya dafa kafad'ar Ahmad yace abokina kenan....... kar ka damu! duk wannan mai sauki ne baka ce zasu zo garin nan cikin satin nan ba........
Ahmad ya gyad'a kai yace masa "Eh" sai Mahnoor yace yauwa toh zoka ji nan Mahnoor ya kamo kunnan Ahmad ya rad'a masa wata magana gaba d'ayan su,suka kwashe da wata irin dariya mara dad'in ji ta mugunta.....
Ahmad ya kalli Mahnoor yace yauwa abokina! hakan za a yi ka kawo Good idea shiyasa nake sonka wlh mutumina,ya fad'a yana dariya
Mahnoor ya busar da wata iska daga Bakin sa yace "ai kar ka damu abokina wannan 'karamar matsala ce,ko ma nace maka ba matsalar bace gaba daya ya saka dariya,,,,, taso mu wuce class kawai Ahmad... nan suka tashi suka wuce cikin ajin nasu.
*************
"Yusuf wai me kake yi ne haka miko kayan asaka a cikin motar mana".... Inji Abbaaa
"gashi Abbaaa wlh kayan ne sun yi nauyi da kyar na d'auko su".....
Abbaaa ya kar'bi kayan ya saka cikin mota yana dariya yace"ashe dai Yusufan ma raggo ne....
Yusuf yayi dariya
sannan suka shige cikin motar gaba d'ayan su dama Inna tuntuni tana cikin motar su Yusuf na shiga direban ya ja su suka wuce sai KANO,
Misalin karfe hud'u na rana su Yusuf suka shigo garin Kano unguwar Badawa layout amman fa Abbaaa ya kasa gane gidan Kawun nan ya kira shi a waya, Kawu ya yi musu kwatance ya fad'a musu sunan layin,cikin ikon Allah sai gasu a kofar gidan,
Abbaaa yayi wa Kawun waya yace sun 'karaso suna kofar gidan kamar yadda yayi musu bayani,
Kawu da kanshi ya fito ya tarbesu shida Ajmal da Fu'ad da Ahmad,nan suka shiga cikin gida aka yi ta murna aka gaggaisa suka yi sallah sannan suka ci abinci su inna ana ta tsokanar Ahmad ita da Abbaaa duk ya zama dan gayu kama bashi ba nan suka yi ta wasa da dariya.....
Momy ta ja Inna suka yi bangaran ta Amnoor ma ta tashi ta bisu....
Yusuf kuwa dama yana wurin su Ahmad suna falon 'kasa su da su Humaida da Bilkisu ana ta hira,
Abbaaa ma suna can tare da Kawu Aliyu kowa ana ta hirar yaushe gamo,,,,,,, Kawu ya kalli Abbaaa yace amman zakuyi mana kwana biyu ko dan naji dadin zuwan nan naku
sai Abbaaa yayi dariya yace sati "d'aya zamu yi insha Allah"
Kawu yace "aahhh na zata wata daya zakuyi mana"
ya fad'a yana dariya Abbaaa ma yayi dariya yace "ai saboda da kasuwa shiyasa"
"toh Allah ya kaimu mun gode sosai hakan ma yayi Allah ya bar zumunci" inji Kawu, nan suka cigaba da hirar su,
'bangaran su Ahmad kuwa suna ta hirar su Yusuf saki jikin sa sai wasa da dariya suke yi.........
sai Ahmad ya tashi ya shiga toilet ya d'auko wayar sa ya danno numbr Mahnoor ya danna kira,cikin lokacin Kad'a ta shiga Mahnoor ya d'auka yace "Aboki ya aka yi ne"
Ahmad yace " fine Bro" dama cewa nayi yaron nan ne fa sun zo d'azu s (YUSUF) yanzu haka muna tare shi ya za a yi?...... nan dai suka gama maganganunsu nima din danake la'be ban ji su ba, Ahmad ya kashe wayan ya dan lalle'ka ko wani yaji shi sai yaga babu kowa saiya fito,
yana fitowa sai yaga falon wayam babu kowa sai Humaida ita kadai tana zaune..... Ahmad ya kalle ta yace"ina su Yaya Ajmal din kuma"
ta bashi amsa da duk sun shiga zasu kwanta nima kai nake jira kazo muyi sallama,,,,
_ashe Humaida yau taci alwashin zata fadawa Ahmad abun da ke ran ta_........
ta d'an yi murmushi... Ahmad yayi mata wani mugun kallo yace "Ni kuma!...... Hmmm toh Nagode sai da safe"
Humaida tace "tnx,Allah ya kai mu" yace "ameen"
har ya juya zai tafi tace "Yaya Ahmad!" sai Ahmad ya tsaya ya juyo.......... "i hmm.. Love....
" ME KIKE CEWA!" inji Ahmad
cikin karkarwa Humaida ta mike tsaye cikin rawar murya"babu komai cewa nayi sai da safen" tayi sauri ta wuce ta tafi jiki na rawa.... Ahmad ya bita da kallo yayi dariyan mugunta ya girgiza kai yace"shegiya ai duk na gano ki nasan meke damun ki toh bada ni na wlh! "
sannan ya wuce shima dan ya kwanta zuciyar sa fal farin ciki yana Allah Allah gari ya waye ya aiwatar da 'kudirinsa kan Yusuf.......
*___________________*
"Yusuf yana kwance shi kad'ai a daki sai ga Ahmad "kai ina ga tunda kuka zo garin nan baka fita Shan iska ba idan ba fita masallaci ba shima muna sallah kake dawo wa gida,,,,,dallah taso muje ka d'an sha iska a waje kasan harabar gidan nan akwai sanyi ga tsutsaye masu kyau" inji Ahmad
"yauwa yaya Ahmad Nagode sosai ai kasan ban san kan gidan ba,har garin ma dai baki daya kaga kuwa ban ga ta yawo ba hhhhh" ya tashi ya saka takalminsa suka fito tare da Ahmad,.
Ahmad yace kai ne baka so ba idan kace kana son a fita da kai ai babu mai 'ki..... Yusuf yace haka ne Suna ta Tafiya sai Ahmad ya yi masa nuni da wani wuri da kujeru a ajiye yace masa yaje ya zauna bara ya dauko musu lemo da zasu sha.....
Yusuf yace toh Yaya, ya tafi ya zauna yana jiran Ahmad,,,,,,Ahmad yana shiga gida ya wuce d'akin su inda yayi sa a kuwa yau gidan babu kowa sai su inna da momy su kuwa suna can cikin gidan,,,,,,, Ahmad ya dauko wani drinks na exotic mai shegen sanyi sai kuma na ga ya d'auko wani abu a cikin wata drower a daure a leda ya bud'e shi ya zuba a cikin wannan drinks din ya jijjiga shi sosai sannan ya mayar inda ya d'auko.........
Sannan ya d'auko glass cup guda daya ya fito, yana fitowa ya tarar da Yusuf inda ya umarce shi da ya zauna a zaune
shima yaje ya zauna kusa da shi yana zama ya tsiyayo lemon nan ya mikawa Yusuf yace masa ya sha...... Yusuf ya kar'ba yana murna ya kafa kai ya sha sannu yace Yaya naga wani tsintsu mai kyau idan zamu tafi zaku bani shi in tafi da shi nayi kiwo......
Ahmad ya kalle shi ya wani lumshe ido dadi duk ya bi ya isheshi yayi wata dariya yace "za a baka Yusuf insha Allah" amman a ransa cewa yake yi (sai dai kayi kiwon a lahira yaro)
Yusuf kuwa yace "Nagode Yaya"lokacin har ya shanye lemon yana ajiye cup din......
"Har ka Shanye to kawo na kara maka.." inji Ahmad..... Yusuf ya mika masa ya 'kara masa har zai kai baki sai ya rike cikin sa "Yaya Ahmad! cikina washh....!
sai ya saki cup din Ahmad yayi sauri ya tare dan kar ya fadi ya fashe,,,,,, Yusuf ya fara ihu wayyoooooo cikina wayyoooooo!!! basai Yusuf ya fadi ba sai kumfa ta baki yana shure-shure ba......
Ahmad kuwa ko ajikinsa ya bushe da dariya yaro sai muga wanda zasu kai Dubai yayi karatun, sai ya dauko wayan sa ya kira Mahnoor ya sanar masa da aikin sa yayi,,,,,,,,, su ka fara hira.......
sai kuma can Ahmad ya zabura yayi maza ya kashe wayan ya hada cup din nan da ragowar drinks din nan a leda ya dauka yayi fitar sa abun sa ya bar Yusuf a nan yashe a kwance.....
❤
*Urs*
*ERMEENART*✍π»
[8/11, 1:08 PM] Ermeenart π: π·π· *_DUK ABIN DA KA SHUKA_*π·π·
♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*♻
*WRITING*
By
*ERMEENART*π
©Edited by :HUMYLUVπ
```This page is dedicated to:```
*Cerlmeerh*❤
*Mum Sadeeq*π·```much of LOVE TNX```π
*76-80*
Ahmad yana fita sai ga Baba mai gadi nan ya dawo shima,dan a lokacin aski ya tafi har Ahmad ya gama abun sa bai dawo ba,yana shiga gida ya wuce d'akin sa ya d'auko rediyonsa ya kunna yana sauraro ya zauna kan bencinsa ya cigaba da aikin sa na gadi,,,,,,,
Yana zama sai ya ji Hon ya tashi da sauri ya je ya le'ka dan yaga su waye, sai yaga su Ajmal ne suka dawo........sannan ya tafi cikin hanzari ya bud'e musu gate d'in suka shigo,,,,,,,,,,nan Ajmal yayi packing motar tasu a packing space dake cikin gidan......... Fu'ad ya fito yayi cikin gida dan agajiye suka dawo.....
Ajmal kuwa an kira shi a waya,sai naga ya d'auka amman bai wuce cikin gidan ba sai ya nufi inda Yusuf yake a yashe a kwance yana wayar,
Yana cikin wayar sai idon sa yake hango masa kamar mutum ne a kwace a kasa.........sai yayi maza ya kashe wayar ya nufi wurin gaba d'aya cikin sauri,
yana zuwa idonsa wa zai gane masa YUSUF! Ajmal ya doka salati yayi kan Yusuf ya fara jijjiga shi,ya na kiran sunan sa.......... amman inaaaaa shiru kake ji jikin nan na Yusuf duk ya saki yayi sanyi,Ajmal yana ganin haka ya sake shi yayi cikin gida aguje yana kiran Momy!,,,,,,,,,,,
Momy suna can sama cikin falon ta ita da Inna suna ta hirar su,,,,,,, Ajmal ya fad'o musu yana haki, suna ganin shi cikin wannan yanayi Inna da Momy suka mi'ke tsaye LAFIYA! AJMAL MENE? inji Momy
Ajmal duk ya rikice yace murya tana rawa dan akwai shi da tausayi yace "Momy! Yusuf!!......... "
Momy tace "Yusuf kuma! me ya same shi!" yana ina?
"Gashi can a kwance Bakin sa na fitar da kumfa" Ajmal yana gama fad'a ya fita a guje dan ya koma wurin Yusuf din.......
dukansu suka saka salati Inna da Momy,suma suka fita a guje...... Inna dai wurin sakkowa daga bene hantsulawa tayi-tayi dan uku-uku take tsallakewa tana salati tana kuka tana fad'in shikenan Yusufa na wayyoooooo Allah!
Suna fitowa suka tarar da har Ajmal ya kira Fu'ad sun d'auko Yusuf sun nufi mota da shi,,,,,,,,,,,
Inna tana ganin Yusuf a mace a hannun su Ajmal nan take ita ma ta fad'i sumammiya Momy ta saka salati ta fashe da kuka tayi kan Inna ta kwallawa Baraka mai aiki kira tazo suka taimaka aka saka Inna itama a mota sannan Ajmal ya ja mota suka wuce sai asibiti......
Ahmad kuwa yana fita gidan su Mahnooor yayi suna can suna ta sheke ayarsu suna jira su ji an kira su jana'izar Yusuf......suna ta sha'anin su hankali kwance,
*********
Suna isa asibiti suka nufi emergency ba 'bata lokaci aka kar'be su aka shige da Yusuf wani d'aki na daban,Inna ma aka yi wani d'akin can da ita,,,,,,,,,,,su Ajmal suka tatsatsaya suna jira suga ikon Allah cikin tashin hankali Momy sai kuka take yi Fu'ad yana rarrashinta yana bata hakuri......... Sannan Momy ta kalli Ajmal ta ce masa ya kira baban su ya fad'a masa nan Ajmal ya dau waya ya kira daddyn su ya fad'a masa halin da ake ciki..........shima hankalinsa yayi matukar tashi yace masa gasu nan zuwa dama suna tare da Abbaaa ba a fi minti ashirin ba sai ga Abbaaa nan da dady sun karaso,
suma suka zo suka jeru gaba d'ayansu suka yi jungum jungum ana ta jiran ikon Allah......
Suna zazzaune sai ga wata Nurse ta fito daga d'akin da aka shigar da Inna......suna ganin ta dukkan suka tashi Momy tayi wurin tace "Nurse ya ake ciki" sai Nurse din nan ta ce mata kune yan uwan mara lafiya ko?
Momy ta gyad'a mata kai tace "Eh"sai Nurse din nan tace
"yauwa mun samu ta farfad'o dama ta samu dogon suma ne sakamakon wani abu da ta gani ya firgitata yanzu zaku iya shiga ku ganta amman bacci take yi dan Mun yi ma ta allura ne coz tana bukatar hutu a halin yanzu"
Momy tace "ALHAMDULILLAHI suka yi wa Nurse godiya sannan wuce suka shiga suka duba Inna tana nan a kwance tana bacci suka yi mata adduar samun lafiya..........sannan aka bar Momy ta zauna a wurin ta dan ta kula da ita su kuma suka fita suka koma wajen dakin da Yusuf yake suna jiran tsammani.....
Suna zaune Ajmal ya d'auko waya ya kira Ahmad ya fad'a masa ga abun da yake faru kuma ga a asibiti da suke Ahmad ya nuna masa kamar bai san abun daya faru ba duk ya rikice ya nuna damuwa sosai Ajmal har yana bashi hakuri,
Bayan sun gama wayan Ahmad ya kashe sai ya kalli Mahnooor ya kwashe da dariya,Mahnooor yace masa "ya akayi ne frnd ko jana'izar ce hhhhhh"
Ahmad yace masa NO sannan ya fad'a masa duk abun da suka yi da Ajmal........Mahnoor sake yin wata dariya ta wahala sannan ya kalli Ahmad yace"kar ka damu jiran banza suke yi dan ba tashi zai yi ba,dan wannan GUBAR ba ta wasa bace hhhhhhh..... amman yanzu kasan me?
Ahmad yace "A'a",,,,,,"toh ka tashi yanzu ka shirya na kai ka asibiti dan kar suyi zargin wani abu Ahmad yace"toh"sannan suka tashi suka taho asibitin.......
Dady suna nan zauna Sai da suka sake kwashe awa d'aya a zaunen sannan wani likita ya fito daga d'akin da Yusuf yake duk ya had'a gumi,,,,,,,
Kawu ya tashi cikin sauri ya tsaya gaban Dr nan yace "Dr ya ake ciki?" Dr yace "babu komai ku kwantar da hankalinku ku su biyo ni office"
Nan suka tashi suka bishi a baya cikin sauri har suka shiga office d'in Dr suka zazzauna sannan likitan ya kalli Kawu yayi gyaran murya yace
"duk abun da ya faru ku fawwalawa Allah kar ku damu ba wani abu ne yake damun yaron ku ba sai GUBA daya ci ta dalilin wani abun ci ko abun sha"
dukkan su suka bude baki suka ce GUBA!!
Dr yace kwarai! Kuwa haka binciken mu ya nuna mana,don haka za muyi masa aiki yanzu cikin gaggawa dan hanjinsa ya sami matsala dan anyi sa'a ma ba arasa shi ba coz gubar daya ci tana da mugun karfi da ta kai 24hours ma ajikinsa sai dai ikon Allah ya hana sa mutuwa "
Gaba d'aya suka saka salati,Dr yace" kar ku damu please kuyi ta yi masa addua,
amman yanzu mu yi iya Bakin kokarin mu akansa..........."toh yanzu likita ya za a yi?inji Kawu
Dr yace gaskiya yanzu ba a so dai ya wuce 1hours ba ayi masa aikin ba dan zaku iya rasa shi yanzu kuje ku biya kudin da duk abun da ake bukata mu kuma da izinin Allah zamu yi iya kokarin mu akansa......
Nan su Abbaaa da Kawu suka yi wa Dr godiya sannan suka wuce,Kawu ya biya duk abun da ake bu'kata.....sannan aka shiga da Yusuf dakin thearther......
❤
*Urs*
*ERMEENART*✍π»
[8/13, 10:44 AM] Ermeenart π: π·π· *_DUK ABIN DA KA SHUKA_*π·π·
♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*♻
*WRITING*
By
*ERMEENART*π
©Edited by :HUMYLUVπ
*81-82*
Ana shigar da Yusuf d'akin thearther,babu 'bata lokaci Dr da sauran ma'aikatan suka fara'a aikin su akan shi tare da adduar neman sa a awurin ubangiji.....
Suna tsakiya da yin aikinsu akan Yusuf sai suka ji 'kara daga jikin na'urar da ke had'e a jikin Yusuf da take taimaka masa wurin yin numfashi tana 'kara alamun ta tsaya,numfashi ya daina kenan,
Gaba d'aya hankalin su ya tashi Dr ya kalli na'urar yaga dai tabbass! Ta tsaya din....sai yayi sauri ya duba Vital Sign sai yaji Pulse Rate din Yusuf ya tsaya babu alamun rai,
Sannan ya kalli Yusuf nan ma ya ga idon nan na shi a sama ko 'kiftawa ba yayi,ya sa hannu ya fara jijjiga Yusuf amman inaaaaa babu alamun motsi tare da shi........
Dr kamar zai yi kuka dan Yusuf ya bashi tausayi nan ya d'auko wasu kayan aikin na daban yayi iya kokarinsa akan Yusuf amman inaaaaa......Yusuf tafiya ta meka idon nan ya kakkafe ya kalli sama....,,,,
Dukkan su Nurse din nan da Dr sai da kwalla ta zubo musu,
Sannan suka fara had'e kayan aikin nasu wuri d'aya,
Sannan Dr ya koma kan Yusuf dan ya cire masa oxgen din nan da ke hanci sa,,,,,,,,,,,,ya saka hannusa kenan zai cire oxgen daga hanci Yusuf sai kawai yaji wannan na'ura ta kama kara alamun numfashin ya dawo kuma yana tafiya yadda ake so har ya fi na DA ma,IKON ALLAH kenan,,,,,,
Dr ya kalli wannan na'urar cikin farin ciki yaga komai ya dawo ya kai kallonsa wurin Yusuf ma sai ya ga idon sa ya dawo dai-dai! sai hawaye dake bi ta gefen fuskar sa Dr yayi godiya ga Allah,,,,,,,,,cikin sauri yayi wa Nurses din nan magana da su dakata su kawo kayan aikin nan Yusuf ya farfad'o suma suka cika da murna fari ciki suka dawo....... Ba 'bata lokaci aiki ya cigaba akan Yusuf....
***
'Bangaran Inna kuwa har ta farka tana ta kuka Momy ta rarrasheta ta bata hakuri,sannan Momy ta kira dady a waya ta sanar da shi Inna ta tashi cikin minti kad'an sai gasu sun bayyana acikin d'akin shi da Abbaaa...
Inna na ganin su ta sake fashewa da wani kuka nan dady ya bata hakuri shida Abbaaa.........Inna tace ita a fad'a mata halin da Ahmad yake ciki kar a boye mata komai,,,,,,su Abbaaa suka kalleta cikin tausayi
sannan suka ce mata Yusuf yana nan lafiya kar ta damu tayi masa addua kawai.......za a dan yi masa aiki ne sakamako ulcer dayake da ita,,,,,
dan basu fadawa Inna da Momy guba Yusuf ya ci ba dan zasu iya tayar da hankalinsu.. Inna ta saka salati tace "aiki kuma!"
ta saka kuka, sannan tace ita taji sauki suje taga Yusuf din suka ce mata ai har an shiga da shi dakin thearther din..........suna cikin haka dai ga Ahmad nan ya shigo duk a firgice kamar wadda aka tona daga rami kamar gaske wai shi nan yana cikin damuwa yazo yayi wa Inna sannu...
sannan Momy ta taimaka wa Inna ta tashi suka dunguma gaba d'aya wurin dakin thearther din,,,,,,nan wata baranda inda aka yi dan zaman yan uwan marasa lafiya da Aka shiga da su thearther,,,
dukkan suka zauna sun yi shiru sai addu'o'i suke yi hankali a tashe, sannan dady Ya kalli Abbaaa yace "wlh gaba daya kaina ya d'aure ina Yusuf ya sami guba ya ci? Wanene ya bashi ya ci? Oho! Cikin 'bacin rai yake maganar nan.....
Abbaaa ya kalle shi yayi murmushi yace"haba Aliyu yanzu duk ka bar wannan maganar dan yanzu ba lokacin yin ta bane mu dai muyi ta addu'a Allah ya bashi lafiya.......Dady yace "toh shikenan yaya Allah ya bashi lafiya koma mene idan Allah ya tashe shi zamu ji,amman abun nan ya d'aure mini kai"
Abbaaa yace "ameen amman kar ka damu komai ka gani a rayuwa to fa haka Allah ya tsara abun sa,kuma hakan yake son gani kuma ta Allah ita dai-dai ba tamu ba.... Dady yace " wannan haka ne "
Suka cigaba da addu'o'in su da suke yi wa Yusuf
Ahmad kuwa yana can tare da su Ajmal duk rai a bace dan Yusuf bai mutu ba......Momy kuwa suna tare da Inna duk hankalin su suma baya jikinsu,suna zaune Bilkisu ta kira Momy a waya ita da Humaida suka ce gasu nan zuwa suma dai da suka dawo Baraka take fada musu Momy tace sai sun zo ta kashe wayan......
*******
'Bangaran Dr kuwa Alhamdulillahi har sun kammala aikin su lafiya,,,,,,,,,,,,yanzu za a fito da Yusuf,
Suka kama Yusuf a hankali suka d'ora shi a gadon da za a fito da shi sannan daya daga cikin likitan ya kar'ba ya turo shi dan a fito da shi akai shi dakin jinya....
Su Abbaaa ana zazzaune sai suka ga an fito da Yusuf kamar Gawa za a wuce da shi suka tashi cikin sauri suka bi bayan su
_Amman Ahmad zuciyarsa kamar ta fito dan Bakin cikin samun lafiyar Yusuf_..
aka shiga da Yusuf aka kwantar da shi yana ta bacci hannusa d'auke da abun karin jini ana kara masa
Sannan Dr ya kira su Dady office dinsa yayi musu bayanin komai da kuma na magunguna Yusuf suka yi masa godiya, sannan suka wuce tashi suka koma d'akin da yusuf yake,
dan su Inna da Momy suna ciki wurin Yusuf din Dady suka yiwa su inna bayanin yadda Dr yayi musu kuma nan da awa biyu Yusuf zai tashi da yaddar Allah.......
❤
*Urs*
*ERMEENART*✍π»
[8/15, 10:31 PM] Ermeenart π: π·π· *_DUK ABIN DA KA SHUKA_*π·π·
♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*♻
*WRITING*
By
*ERMEENART*π
©Edited by :HUMYLUVπ
```This page is dedicated to you My Beloved Ones:```
*Ever aunty Humluvπ*
*Aunty Queen*ππ»
*Aunty Haliloss*
*Ummixeey*π
*Hafsat Yarima*❤
*Maman Salim*π
*Khadija Abk*π
π»
*Salma.I.G*π
*Sis Aishaf*π·
*Sis Amnoor*❤
*Jameelah k/mashi*πΉ
*Pharteemarh*π
*Balqess.I.g*π²
*Nabilancy luv*π·
*Seesee*π
*Billy Ladan*π
*Rahila*π
*Ummie_Xeey*π
```and all the rest members of ♻EWF♻much of LOVE TNX```π
*83-90*
Cikin ikon Allah Yusuf awa biyu na cika ya farka,yana farkawa ya fara motsi da d'an yatsansa na'kafa,
Dukkansu,suna zaune su Momy da su Abbaaa da su Ahmad amman babu wanda ya lura da hakan.....sai can daga baya yan yatsun Yusuf na hannu suka fara motsi tare da Bakin sa kamar mai son yi magana sai kuma ya bud'e idon sa yana kallon sama,
Sai a wannan lokacin suka lura gaba d'ayan su dady ya kalli Ajmal cikin sauri yace masa ya tashi yayi sauri ya kira Dr Yusuf ya farka,
Ajmal ya tashi cikin hanzari ya fita don ya kira Dr sai Ahmad ma ya tashi ya bi bayan Ajmal dan su kira Dr wai shi anan dole ya damu yadda yake nuna musu....dan har wani tausayin sa ma suke ji,
Inna kuwa da Abbaaa gaba d'aya murna ta baibaye su har su Momy,suna ta yiwa Allah godiya.
Amman fa Yusuf ya rame sosai duk ya 'kara d'ashewa yayi fari sai bin su inna yake da kallo can kuma sai kwalla daga idonsa sai ya fara zubar da hawaye yana tuna abun da d'an uwansa yayi masa.....
Ahmad yana fita bai ma kalli inda hanyar office din Dr yake ba,ya tafi can baranda ya d'auko wayarsa ya danno lambar Mahnoor ya kira shi ya fad'a masa ga halin da ake ciki Yusuf ya tashi,
Mahnoor ma ransa ya 'baci ya ga ma zage-zagesa yace kar Ahmad ya damu su zuba su da Yusuf din indai sune zasu a had'u a wani target sai ya raina kansa,ba dai yanzu ya tsallake wannan ba.....nan Ahmad ya cika da murna ya yiwa Mahnoor godiya ya kashe wayan.....
Ahmad yana kashe wayan juyawar da zai yi sai ya ga Ajmal a bayan sa,sai ya zabura Ajmal yayi dariya yace "mene ne tsoro kuma dama mun taho ne da Dr sai na hango ka kana waya ina zuwa kuma naga har ka gama,dama ce maka zan yi har na kira Dr yama wuce dan ya duba Yusuf din,sai ka taho muje muga halin da yake ciki"
sai Ahmad ya ji wani dadi ya ratsa sa daya ga alamun Ajmal bai ji wayar da yake yi ba sannan ya kalli Ajmal yace "muje mu gani wlh ina tausayin Yusuf wai me yasa me sa dan da kayi mini waya kace zuwa kuka yi kuka tarar da shi a kwance a sume"
Ajmal ya ce masa "wlh ba kai kada'i ba har mu Yusuf yana bamu tausayi,dan mu rasa ta yadda aka yi Yusuf ya sami guba ya ci,wlh Ahmad a binciken likitoci haka suka tabbatar mana GUBA Yusuf yaci shiyasa ma aka yi masa aiki"
Sai Ahmad ya zaro ido yace "GUBA kuma!"cikin tashin hankali da damuwa kamar gaske,
"Eh tabbass guba dan ko su Momy ma dady bai bari sun sani ba yanzu jira ma yake yi Allah ya bawa Yusuf lafiya ya binciki ya akai hakan ta faru dan haka ko mun shiga kar ka mayi hirar dan kar su Momy su ji dady zai yi fad'a" inji Ajmal,
Ahmad yace "toh" jiki a sanyaye wai shi dole ya damu da halin da yusuf ke ciki,sannan ya bi bayan Ajmal suka wuce dan su koma wurin Yusuf din...
Suna shiga suka yi karo da Dr har ya duba Yusuf ya ga komai normal sai dai idan bai bi dokar da aka saka mishi ba.......sannan ya fito Ajmal suka bashi wuri ya wuce sannan suka 'karasa cikin d'akin,,,,,,,,Ahmad da Yusuf sai kallon-kallo kowa da abun da ke ransa,amman ko dan Yusuf bai nuna masa abun da yayi masa ba sai dai ido ya kalle shi, shima ya kalle shi,bayan yan mintina kadan sai ga su Bilkisu da Humaida da Amnoor sun zo da abinci ni'ki-ni'ki sannan suka yi wa Yusuf ya jiki.
*******
Alhamdulillahi yau watan Yusuf d'aya a kwance a asibiti ya sami sauki sosai sai dai yan irin abubuwan da ba a rasa ba irin su rashin kwarin jiki da kuma kula da cikinsa wurin aikin na sa,,,,,,bayan likitocin sun 'kara bincikensu akan shi suka tabbatar babu wani abun sai suka bashi sallama,su ka koma gida,
Inna sun yi murna sosai sun godewa Allah,bayan sun koma gida dady ya ta da masifa ya had'a meeting sai a ranar su inna da momy suka san Ahmad guba yaci....
Akai-akai Yusuf ya fad'i mai ya faru ko wanene ya bashi abu yaci amman ya 'ki fada sai dai yace shima kanshi bai san yadda hakan ta faru ba....
Sai hakura suka yi suka kyale shi amman fa dady ya dau zafi dan sai da Abbaaa ya hada shi da Allah da Annabi sannan ya hakura ya bar zancen amman yayi sharadin duk san da hakan ya kuma faruwa sai ya dauki tsattsauran mataki daman shi mutum ne fara wasa yana da fad'a
Ahmad gabaki daya ya bi ya rikice amman sai ya basar dan kar su gano shi.
Sannan Abbaaa ya kalli Kawu Aliyu yace masa insha Allah gobe zasu wuce gida tunda Yusuf ya sami sauki,nan dady ya roke shi da suyi hakuri su zauna dama saura wata daya bikin Bilkisu idan aka yi sai su tafi,
Da kyar Abbaaa ya yadda sannan yace toh shikenan Allah ya nuna mana da rai da lafiya dukkansu suka ce ameen
Sannan kowa ya tashi zai tafi dan ya kwanta amman dady yace Yusuf ya zauna tare dasu Inna har lokacin da zai warware...
❤
*Urs*
*ERMEENART*✍π»
0 Comments: