Friday, 8 June 2018




igiyar rayuwa 2

Home igiyar rayuwa 2

[17/06, 12:24 p.m.] H inna: IGIYAR RAYUWA. 2 Peg 1 Tunda suka Kama hanyar Lego's hawayen Shahida basu tsayaba Sai ma karuwa da sukayi tayi kuka sosai Har taji ba dadi mutum uku in ta tuna ra buwa da su har abada Sai taji wani irin bakin ciki da kunci da bacin rai kamar zai fasa mata zuciya wato jabir jafar da kuma babanta bazata iya fadin muhimmancin su kimarsu da kuma darajarsu a rayuwarta ba bata San yawan kaunar da take musu ba musamman ma dai jabir da suka yi sabo sosai da shakuwa Marar misaltuwa ta wani bangaren Tunanin asalinta da matsayinta yana kona mata zuciya ni Shahida shegiya ce Wayyo Allah na ka bani ikon jure wannan kuncin shin ina zan samu mamana ,,,,,,,ina zan samu babana,,,,,, ta ina zan soma neman su,,,,,,, ina zan dosa,,,,, ina zan fuskanta,,,,,,, ina zan shiga Tunaninta da damuwa tare da bacin rai suka hadu suka cunkushe a zuciyarta ba ta san yaushe ta soma kuka ba tun tana yi a hankali Har ta soma da karfi hakan ya ja hankalin mutanen dake cikin motar Wanda dama motar dab take da tsayawa a tasha ido ya koma kanta wasu sunyi ta tambayarta me ya sameta Ya yin da wasu ke ta kallonta kawai suna tunanin me yasa ta kuka 💅🏻Feenah baby👄 08109204012 [17/06, 12:24 p.m.] H inna: IGIYAR RAYUWA 2 Peg 2 Motar na tsayawa jama, a suka yi ta sauka Amma banda Shahida tana zaune hankalin ta tashe bata San ina zata dosa ba direban ne yashigo cikin motar zuwa inda take yace ta fita zai tafi da motar nan ta tashi ta fita da kyar ta samo kayanta a cikin kayayyakin da motar ta debo hankalin ta ta matukar tashi ganin dare yayi ga kuma cunkoson mutane ga gari ne da bata San kowa ba gari irin Lego's da ko na miji ne zai samu matsala bare mace,,,,, tsoro ya shiga Shahida sosai ta nemi waje da jakarta a hannu ta dukunkune gu daya tana ta rafzar kuka tana bakin cikin halin da ta tsinci kanta Meyasa nazo garin da ban San kowa ba wani tunani ne ya sani zuwa Lego's meya ingizani yasa ni zuwa Lego's Wai Don in yi nisa da babana da yan uwana dan in bawa mama farin ciki Mai, zai kasance dani wace masifa zan fuskanta, me zai faru da rayuwata,,,,,, jabir ina Kake Dan uwa,,,,,, ban taba fuskantar tashin hankali irin na yauba ko wani lokaci kana tare dani kana fuskantar duk wata matsala ta yau ce rana ta farko dana fuskanci rayuwa ni daya na shiga matsala da ban San ya Zanyi in fita ba tana tunani tana kuka sosai taji wasu yan iska sun matso dab da ita suna busa taba daga ganin su kasan San basa hankalin su suna surutai zuciyar Shahida ya dinga bugawa kamar zai balle tsoro da fargaba yah shigeta ya, yan hanjin cikinta Ya kada Nan da nan ta rude tafara addu, a cikin zuciyarta tana zaune kankame da kayanta kamar zata shige cikin jakarta ta dau tsawan minti biyar a haka tayi sa, a Allah ya taimake ta suka tafi jikinta na Bari ta Mike ta dau kayanta ta nufi gun wata mota data ga alamar taxi ce cikin harshen turanci tayiwa Mai taxi din magana cewa ya kaita hotel Mai kyau mafi kusa zata yi masauki *Shahida ta taki sa, a sosai* (to bari muga wani sa tataka👀) Dan taxi din bahaushene kuma mutumin kirki bata hadu da irin shedanun macutaba yace mata ta shiga ya kaita jin yayi Hausa yabata mmki dan bai mata Kama da bahausheba suka gaisa Har yake tambayarta ya akayi tazo garin da bata Sani ba ita daya,,,,,,, Ya jima yana ganinta tana zaune wajen ta me karyar cewa aiki tazo yi kuma bata San kowa ba dole Sai ta sauka a hotel kafin ta samu gidan da zata zauna ko zai taimaka mata *to an ce dama an ce in kanada kyakkyawar zuciya Allah zai taimake ka Allah ya hada Shahida da mutumin kirki sakamakon addu, a da take ta karantowa a zuciyarta sale shine sunan dan taxi din* Ya kaita hotel Mai kyau mai mutunci ya kuma mata alkawarin washe gari zai zo Ya kaita su za ga koza su samu gida a inda ya kamata ta zauna taji dadin hakan tabashi kudinsa gami da mishi Godiya Tsawon dare Shahida bata runtsa ba Tunani da kuka yayi mata yawa maimakon bacci yazo idonta a wannan lkc Sai hwy ba alamar bacci ta jima tana zaune a dakin tana ta tunani ganin ba inda zai kaita yasa ta Mike ta shiga toilet tayi wanka hade da alwala ta fito zatayi sallah ta rasa ina ne gabas din Nan ta fita tana tambaya Har ta dace ta samu wata. Mace berabiya Amma musulmace ta tambayeta Har dakin suka zo ta nuna mata tamata Godiya ta tafi ta Kwana tana sallar nafiloli hade da addu a maitsanani ta nemi taimako da tsari a gun ubangiji daya kareta daga dukkan sharrin duniya da mutane Ya tabbatar mata da alkairi Bayan ta idar ta zauna tana tunanin nasihar mahaifinta da yake yawan mata ta kuma tuna irin tarbiya da koyarwa na zamantakewar rayuwa data samu daga babanta Sai taji ta samu karfin gwiwa mahaifinta ya nunamata Mara kar ta taba karayah a rayuwa a duk halin da ta tsinci kanta ta fuskanci Shi kuka da tunani bashi zai kawo karshe matsala ba kuma muddin kana raye to kana tare da matsala mutum dole ya koyi magance matsalarsa ban da kauce hanya da kuma tsaida Gaskiya Ya kasance duk inda take ai mata shedar Gaskiya a kuma mata shaida Mai kyau 💅🏻Feenah baby👄 08109204012 [17/06, 12:24 p.m.] H inna: IGIYAR RAYUWA 2 Peg 3 Wannan tunani da Shahida tayi taji yabata karfin gwiwa ta kudiri aniyar cewa zata zauna ko a ina cikin mutunci da rufin asiri ta bude akwatin nata Ta dauko takardunta tana kallo tace baba Tunda ka ban ilimi ka min komai a rayuwa Abu na farko da zan soma yi shine neman aiki ko na gwamnati ko na kamfani Lego's gari ne da yake cike da ma, aikata Kala, Kala daban, daban ba zan rasa samun aiki ba zan nemi aiki in kuma nemi gida in zauna in yi rayuwa ta har Allah kawo min canjin rayuwa zan binne komai a zuciyarta zan cire su a Raina zan dauki kaina marainiya wacce bata da kowa a duniya zan yiwa kaina gata da ilimi da Allah ya bani zan zama uwar kaina da uban kaina yayar kaina zan zama dangin kaina zan yi dukkan kokarin inga na Kare mutuncin kaina sannan zan Ci gaba da tsare kaina da rike amanar kaina JA,AFAR. Ta kira Shi a cikin Tanya na San zaka mantani kila nima na manta ka Sai dai ba zan taba manta lkcn da nake tare da Kai ba ba zan manta irin soyayya da kauna da ka nuna min ba Alkawari ne in ban aure kaba ba zan taba auren wani ba zuciyata bazata taba son wani ba,,,, ba zan taba bawa wani damar shiga zuciyata ko mallaka ta ba,,,,,,, Da zuciyata dani kaina duk amanar ka ce koda mata nawa zaka aura na San nice mace ta farko da ka soma so a rayuwa ba zan manta wannan ba Can jabir ya fado mata a rai Dan uwa ba zan bari rashin ka yasa na karaya ba ban San ya Zanyi in manta ka ba in cire ka a Raina ba sai dai dole in koyi yadda Zanyi rayuwa ba Kai,,, dole na cire Ka a Raina in ba haka ba ba zan iya fara sabon rayuwa ba Haka ta kasance a wajen ta kulla wannan ta kunce ta saka wannan har taji kiran sallar asuba ta Kalli agogo biyar da rabi nan ta Mike ta shiga toilet ta sake alwala ta zo tayi sallah bayan ta idar ta dauko kur,,, aninta da addu, a book dinta Wanda dama ta dauko su ta jima tana krt tana addu, a ta nemi taimako da nasara gun ubangiji akan abin da tasa gaba Anan kan sallayar bacci ya kwasheta ga gajiyar hanya ga Kwana data yi ba tayi bacci ba bata tashi ba sai wajen karfe uku na yamma nan ma yunwa ne ya tasheta tayi matukar mmki dataga karfe uku nan ta Mike da sauri tayi sallar azahar sannan ta fita tayi oder din abinci Anan aka fada mata wani dan taxi yazo har sau biyu yana buga mata bata tashi ba Amma yace zai dawo A daki aka kawo mata abinci farfesun ne na kaji Sai ruwan Zafi da coffee kasa shan farfesun tayi coffee din kawai ta iya sha Tana nan zaune ita daya tunani yaso Ya matsa mata yayin da taki bari tayi Tunanin ganin haka yasa ta fita ta saye jarida da wasu magazine don su deba mata kewa kafin yamma tayi dan taxi din Ya zo Anan ko ta ga kamfani da dama suna neman MA, aikata taga kamfanin dataji yaja hankalin ta har taji tana sha, awar aiki a wajen shine kamfanin magazine din nan Mai suna *todeys world*taga abubuwa da dama daya birgeta kuma dama ta na da sha, awar aikin a kamfanin magazine ko jarida nan ta duba date din interview din da Saura Sati uku da yan kwanaki zan gwada sa, a ta Karfe biyar dai dai Dan taxi din nan ya dawo suka gaisa gami da tambayar sa sunansa yace mata sunansa danlami kuma shi bahaushene mutumin Kano nan suka yi ta zaga cikin garin Lego's inda ta ziyarci super market da kasuwa ta yi siyayyan duk abin da za ta bukata daga kayan sawa har na ci haka suka dinga yawon neman gidan haya dazata zauna Amma bata samu a inda take so ba 💅🏻feenah baby👄 📞08109204012 [17/06, 12:25 p.m.] H inna: IGIYAR RAYUWA, 2 Peg 3 Wajen karfe 10 na dare suka dawo ta mishi Godiya ta bashi kudi Mai yawa ,,,ya mata Godiya yayin da ya mata alkawarin nema mata gida a inda takeso Tsawon sati suka dauka suna neman gida bata samu ba har Shahida ta soma sabo da yan hotel din sbd alkairi da take musu kullum ta kan fito reception tayi hira dasu in ta gaji da zama ko da wasa bata bari Tunani ya dame ta Shahida ta na cikin sati na 2 a garin Lego's kuma a hotel tayi nasarar samun gida a wata anguwa Mai suna *Ebutumet*a L,S,D,P,C Estate Mai gidan yace zai bata haya Amma na shekara 2 zata biya dan basa ba da shekara 1. Kuma kowacce shekara dubu dari biyar ne dan haka miliyan daya zata biya Shiru tayi ta rasa abin fadi bata da inda zata samu wannan kudi haka in ta bari gidan ta subucemata zai yi wuya ta sake samu irinshi ba Wai kyau ko wani Abu ba wajen akwai security sosai gidan yana sama Hawa na 4. In ta zauna a gidan zata kasance cikin mutane ga makwabtanta duk musulmai ne baza dai ta samu matsala ba in tana wajen dole tabi hanyar da bata so wato ta nufi banki ta dauki cheque book dinta Wanda Tunda babanta ya bude mata account ba ta taba cire ko da sisi ba Dan haka bata San nawa ne a ciki ba ma Tana zuwa tace a nuna mata balance dinta tayi matukar mmki sosai da taga tsabar kudi Mai yawan gaske da babanta yasa mata taja dogon ajiyar zuciya tace Mai yasa baba Ya sa min kudi Mai yawa haka,, ,,Tunaninta ya bata ajiya yayi a account din ta cire kudin Amma tayi niyar dawo da miliyan dayan nan a duk lkcn da ta soma aiki zata tara ta dawo dashi Cikin sa, a Shahida ta samu gida ya shiga hannunta ta tattaro daga hotel ta dawo dakuna 3ne da falo Sai dining area da kichin da toilet gidan an Mai gyara sbd komai sabo ne kamar fenti fanka da kayan toilet dana kicin haka tiles ne a malale a kasan gidan akwai gado daya hade da katifa a daki daya sai kujeru a falo da dining table Sai lkcn ta gane dalilin dayasa gidan yayi tsada Bata bata lkc ba ta nufi kasuwa ita da danlami ta sake siyan abin da zata bukata kamar su labule tukwane plate cokula karamin gas cooker karamin fridge da T,V da dai makamantan su a Kwana 2 ta gyara gidan tsab Ta shirya komai Sai zaman kadaici da kewa Wanda yake yawan kawo mata tunani hakan yasa ta soma rubuce,rubuce hakan bai hana mata ba ta soma yawon neman aiki kafin lkcn interview din yayi nan ma bata yi nasara ba bata San kowa ba sai danlami Wanda shine yake kaita duk inda take so har ta soma sanin garin Lego's sosai Abin da yafara daga mata hankali shine kudin da ja, afar yabata Wanda ta taho da Shi Ya kusa karewa sbd ta kashe kudi sosai kuma ba taso ta sake taba kudin account dinta sbd ta san banata bane kuma in har tana so ta dogara da kanta ta manta baya to dole ta manta da kudin babanta na account dinta Wani yammaci Shahida ta dawo daga yawon neman aiki a gajiye ta zauna ba jimawa taji an buga kofa tayi mmki gami da tunanin waye ne nan dai ta tashi ta bude wata yarinyace ta gani Sannu anty ina wuni,,,,, yarinyar ta fada tana kallon ta Shahidan tayi murmushi tace lfy yan mata shigo mana Tare suka shiga falon da yarinyar Shahida tace meye sunanki yan mata Sunana humaira dama mmn mu ne tace nazo in geisheki mu makwabtan ku ne dama munje Hutu gida lkcn da kika dawo Shahida tayi murmushi tace na gode da gaisuwarki ki gaida mmn ki kice zan zo in gaisheta ina ne gidan naku Muna Hawa na 6 Shahida ta dauko chocolate Mai yawa a jakarta ta bata dama Dani, anta shan kayan zaki ba, a raba ta da Shi yarinyar ta tafi tana murna maganar da Shahida tayi da yarinyar ya mata dadi sosai sbd rabonta datayi magana da wasu irin haka ta jima haka take rayuwa ita daya wani lkcn zata zauna tayi ta magana ita daya ko ta dinga yi tana kiran jabir ko babanta ko ja,afar ta sayi waya sau da dama Sai ta kira layin jabir daga taji ya soma ringing sai tayi saurin kashewa kafin a dauka 💅🏻feenah baby👄 📞08109204012 [17/06, 12:25 p.m.] H inna: IGIYAR RAYUWA. Book2 Peg4 HAPPY RAMADAN 😘 Kwana 2 da zuwan humaira Shahida ta je gidansu ta gaida mahaifiyar humaira Wanda take kira da mmn humaira yaranta 2 humaira da Abdullahi mace ce wayayyiya ta girmewa Shahida mutanen katsina ne akwaita da kirki da kara taja Shahida a jiki tun Shahida na dari dari Har ta sake Tasha tambayar Shahida lbrn ta da dalilin dayasa take rayuwa ita daya amsa daya tabata shine aiki tazo nema ta kuma nuna mata bataso ta sake mata tambaya game da rayuwarta haka ta hakura dole ba dan taso ba sbd rayuwar Shahidan na bata mmki sosai mace Mai kamun Kai Kamila irin Shahida tana rayuwa ita daya a wani dalili.,,,,,tambayar na cinta Amma dole ta hakura A kullum shahida tayi sallah tana addu a mai tsanani Akan Allah ya bayyana mata iyayenta ya kuma bata ikon cire dan uwana jabir a ranta Ranar interview dinta yazo karfe 7 a kamfanin ta same ta kamfanin na gani na fada abubuwa da dama sun birgeta yadda tsarin kamfanin yake kwarai tana matukar son yin aiki da wannan magazine din suna da dan yawa Wa,yanda suka zo interview din suna nan zaune Har karfe 11 sannan matar ta iso Wanda ita ce C,E,O, na kamfanin kuma ita ce zata musu interview din bayan ta shiga ne aka dinga kiransu daya bayan daya Har aka zo kan Shahida ta shiga tana tsananin addu, a a ranta gami da kudirtawa a ranta zata yi iya kokarinta taga tayi nasara samun aikin nan Ta tura kofa ta shiga hannunta rike da takardun matar ta dago Kai tace mata zauna cikin harshen turanci Shahida ta zauna tana kallon matar ta mata kwarjini kuma ta birgeta da shigar datayi yasa ta kara birgeta hijab ne tun daga sama Har kasa ta lullube jikinta kyakkyawar farar mace Mai kamala Shahida taji kaunar matar Ya shigeta duk da zama da take a kudancin Nigeria ilimi da tsantsan wayewa data gani a tare da ita baisa tayada addininta da ala,adarta ba Matar ta katseta muga takardun naki nan ta mika mata tajima tana karantawa sannan ta dago Kai ta kalleta tace Shahida ko,,,,,, Shahida Al,mustapha Shahida ta girgiza mata Kai,,,,, Eh,,,,, Naga takardun ki sunyi kyau sosai Wanda ko a ina zaki iya samun aiki Sai dai Kin San bayan ilimi muna bukatar mutum Mai wayo da dabara kin San aikin kamfani kullum bama rasa abokanan gasa dana gaba duka,,,,, zan miki wasu tambayoyi idan kika amsasu to zan ga dacewar ki ko rashin sa in har kin dace da matsayin zaki samu aikin,,,,,, cikin harshen turanci take mata tambayoyin har ta gama sannan tace suna da lambar wayanta da address dinta in sun tashi zasu nemeta Nan ta Mike ta yi Godiya ta nufi hanyar fita matar tabita da kallo haka kawai taji tana son yarinyar ko meye dalili oho,,,,,,Har Shahida ta isa kofa ta juyo ta Kalli matar sannan ta Kalli kan table din nata a jikin wani karfe Mai kyan gaske ta ga ansa sunan ta *Hajiya Aisha Abubakar* Ta sake Mai da kallon ta kan matar suka hada ido Hajiyar tayi mata murmushi itama ta mata sannan ta fita Shahida ta tsinci kanta cikin farin cikin data jima bata yiba Wanda ta rasa dalilin sa gidan mmn humaira ta shige suka yi hira mmn humaira tace yau fa Shahida na Lura kina cikin farin ciki Tunda nake ganinki kullum fuskarki ba walwala amma yau naga kina cikin farin ciki meye dalili Tayi murmushi mmn humaira kenan ba kya gajiya da min tambaya bayan kin San bani da amsar ko wace tambayar ki yanxu in na ce miki ni kaina ban San me ya sani farin ciki ba bazaki yadda ba ko Shahida kenan kin zama sirri Suna wannan maganar mmn nabila ta shigo itama a Estate din take suka gaisa dasu Shahida bayan sun dan taba hira mmn nabila ta fara maganar cewa ko mmn humaira ta sama musu lesson teacher da suke nema Sbd exam Ya matso ga yaransu ba su samu Mai musu lesson ba Shahida tasa baki in bazaku damu ba zan dinga musu lesson din in har basu samu Mai musu ba Suka kalleta dukan su zaki iya kuwa kin San fitinar yara fa Tayi murmushi zan iya fitinar yara baya damuna kuma ai yara rahama ne sannan ni kadai ne in ina tare dasu zasu debe min kewa in kun yadda zan fara musu idan kunga basa fahimta sai ku canja Mmn humaira ta ce in zaki iya ai kin taimake mu damu muna samun matsalar Mai yi musu estra lesson Shahida ta soma yiwa yara lesson za a dinga biyan ta dubu hudu a wata ko wani yaro ta dage sbd neman kudi take kafin results din interview din ta da tayi ya fito Allah ya taimake ta ya sawa Sana,ar tata albarka iyaye suka dinga turo yaransu lesson gidanta sbd iyawarta da kwarewarta wajen koyawa yaran gidanta Sai da ya zama kamar wani mkrnt idan yamma tayi haka yara zasu cika a gidan suna matukar jin dadin koyarwanta ba fada ba duka cikin hikima da dabara take fahimtar dasu Haka gidan ta kullum cike yake da chocolate da biscute haka za tayi ta raba musu tana tare da su hakan ya debe mata kewa sosai haka Shahida ta Saba da sabuwar rayuwar da ta tsinci kanta har lkcn da aka dibar mata na cewa za a nemeta in har taci interview din yayi ba a nemeta ba hakan yaso daga mata hankali Amma daga baya Sai tayi tawakkali ta mika dukkan Al,amuranta ga ubangiji,,, ta kuma roke Shi zabi mafi alkairi a rayuwarta Abu guda ya tsaya mata a rai wannan mata Mai kamfanin da tayi interview Hajiya Aisha abubakar matar ta zauna a ranta ta rasa dalili ta dinga jin tana sake son ganin ta sai tayi kamar zataje gunta Sai ta fasa sbd kar tace tazo neman wani Abu ko rokonta ta bata aiki haka ta hakura taci gaba da neman wani aikin ko zata dace ********* ********* **** Hajiya Aisha zaune a office dinta tayi tagumi Tunanin yarinyar nan ya isheta haka tana jin kaunar yarinyar yana yawa a zuciyarta ta rasa wannan dalili na kaunar yarinyar da bata taba gani ba bare ta san ta Amma ta shiga zuciyarta ta zauna taso ta bata matsayin da take nema Editor ko personal sectary na danta to Amma Ya fiye taurin Kai yace Sam Shi ba zai yi aiki da mace ba sai namiji in har kuma bata bi ra,ayinsa ba ba zai bar aikinshi da yake ya dawo ya soma aiki a kamfanin ba gashi bata son takura Shi sbd son da take masa dole ta hakura da yarinyar Amma ta rasa me yasa take yawan tunata da yawan son sake ganinta Taja drower din dake gabanta ta, zaro wani takarda Mai dauke da sunanta da address dinta SHAHIDA,,,,,, takira sunan a cikin ranta me yasa na damu dake tayi wani gajeren tunani ta ce na San abin yi nan ta dauki waya ta buga mata bai jima ba kuwa ta dauka suka gaisa tace tana son ganina ta gobe da safe Da sassafe Shahida ta shirya ta nufi kamfanin zuciyarta cike da dokin sake ganin matar da kuma addu, ar Allah yabata sa,ar samun aikin *yan uwana musulmai ina mana murnar azumin RAMADAN Allah yabamu ladan wata Mai albarka yasa ibadunmu karbabbene* Ameen ya Allah 💅🏻Feenah baby👄 08109204012 [22/06, 10:38 p.m.] H inna: SA, ADATU WAZIRI GOMBE IGIYAR RAYUWA. Book 2 Peg 5 Happy sallah oll😘😘😘😘 Muslim Da sassafe Shahida ta shirya ta nufi kamfanin zuciyarta cike da dokin sake ganin matar da kuma addu ar Allah yabata sa ar samun aikin Sai da ta jira na kusan awa guda da rabi sannan matar ta iso ta zauna na minti talatin sannan akace ta shiga Kai tsaye ta nufi office din game da buga kofar tare da sallama Matar ta amsa tana murmushi zuciyarta kuma tana farin cikin ganin yarinyar bayan sun gaisa Hajiya Aisha ta kalle ta, tace dama wani bayani zan miki game da aikin ki post dinki da kike nema hard kikayi interview akai an bawa wasu daga Editor Har personal sectary sbd dana Shi zai yi aiki dasu daya zo yaga list din Wa, yanda suka yi interview din yace a cire sunan mata yace baya son aiki da mace na kyale shi sbd Shi zai yi aiki dasu Don haka baki samu wannan post din ba Amma in zaki yadda zavaki wani Sai dai matsayin karatun ki yafi nan karamin post ne Ina son aiki dake sbd kina da sakamako Mai kyau Shahidan tayi ajiyar zuciya tace ina so Hajiya ko wani irin matsayi zaki ban sbd neman aikin nake ban samuba Hajiya ta kalleta tace zan dauke ki matsayin Resecher wato Mai nemo lbr masu MA,ana da amfani Wanda zasu jawowa kamfanin mu farin jini da kasuwa Shahida tayi murmushi tace na gode Hajiya Insha Allahu Zanyi kokari inga nayi aikina fiye da yadda kike tsammani Naji dadi Shahida daga yau kina cikin reserch team na kamfanin nan ki jira nan kadan zan sa ayi typing appointment letter dinki sai in gabatar dake gun sauran ma, aikata Na gode Hajiya ba zan iya kwantanta miki farin cikin da nake na dauka ta aiki da kika yi ba Insha Allah zaki same ni Mai aiki da gaskiys da amana Shahidan ta fita Hajiyar ta bita da kallo a zuciyarta ta ce ban San me yasa nima nake murna da daukar ki aiki ba bansan Meyasa zuciyata ta dinga tunzurani dana ba ki aiki ba wannan shine lkc na farko danaji ina kaunar wata sosai da zuciya daya wacce ban taba sani ba Shahida ta soma aiki cikin nasara ta samu karbuwa sosai a gun sauran ma, aikata na kamfanin da wa, yanda suka aiki tare haka ta dawo leader team dinsu sbd yadda take kawo musu sabbin ideas da hanyar yadda za suyi su tsara labaransu wata guda tayi da fara aiki amma ta kawo musu nasarori sosai sun kara samun kasuwa haka jama, a suma suna matukar son magazine dinsu jama a da dama suna yaba mata Akan aikinta Dangantakarta da Hajiya Aisha ya karu sosai lokaci guda shakuwa da yadda ya shiga tsakaninsu duk wani aiki Mai muhimmanci in ya taso to Shahida take nema ta bawa duk da Hajiya nada Pearsonl assistan bata neman shawara ta da yawan bata aiki Mai muhimmanci kamar Shahida lokaci guda kamfani yabata mota don zuwa aiki da kuma daukan nauyin biyan gidan haya da take ciki haka ta kara mata matsayi da albashi har MA ta soma Tunanin bawa Shahida matsayin da ta ajiyewa danta Wanda yaki barin aikin shi na gwamnati har yanxu kuma yana cikin matsala da muguwar damuwa da yasa ya kasa Mai da hankali Akan aikinsa na gwamnati bare yazo ya soma na kamfanin ta bata taba Tunanin bawa kowa wannan matsayiba Sai Shahida tun tana mmkn da tambayar kanta Meyasa take matukar son yarinyar har ta daina tasa a ranta cewa Allah ne ya hada jininta da Shahida Ganin daukaka da shakuwa dake tsakanin Shahida da Hajiya yasa wasu a kamfanin suka soma jin haushin ta da kishinta sbd suna ga ta zo ta wuce su Wanda Shahida ta dauko kwazonta da yawan addu a ya kawo mata Ci gaba da daukaka a duk inda take *kamar yadda rayuwar Shahida ya canja haka komai nata ya canja kamar yadda zaka ga tana yawan dariya da kasancewa cikin farin ciki da kwanciyar hankali, a yanxu babu koda alamar murmushi a fuskarta kana ganin ta zaka San tana cikin bakin ciki da bacin rai Wanda ta danne a ranta duk wani Abu da ya shafi kwalliya ko gayu na ya mace ba za a taba ganin Shi a tare da Shahida ba hatta shigar da take yi sai da ya canja ta dawo Sai Kace wata Mai takaba duk ta kode ta canja* Sai dai duk da haka wannan kyan nata Mai daukan hankali da sanyaya rai yana nan kyanta ba ya dishewa sbd dama natural ne a takaice dai Shahida tana rayuwa ne sbd tana raye ba taba gajiyawa ba haka bata fasa yiwa Allah Godiya ba duk da halin da ta tsinci kanta Allah ya bata yadda zata yi yabata imani da karfin zuciya ya kuma Kare ta da dukkan sharrin abin ki da duniya gaba daya ko da wasa shahida bata karaya a duk halin da ta tsinci kanta Ta kan je aiki da safe ta tashi karfe 4 ta yiwa yara lesson a ko wani wata ta dauki albashi ta kan zuba rabi a account din ta tayi amfani da rabi a haka Shahida ta dau tsawon shekara 3 tana aiki bata taba Tunanin komawa gida ba bata taba Tunanin aure ko neman canjin rayuwa ba addu arta daya a kullum Allah ya hada ta da iyayenta na asali tana yawan yiwa babanta addu a da kuma burin son sake ganin Dan uwana ta jabir kafin ta mutu 💅feenah baby👄 [28/06, 12:57 p.m.] H inna: IGIYAR RAYUWA book 2 Peg 6 Jafar zaune a office din mamansa Hajiya Aisha ta kalle shi ranta bace tana fada Wai jafar Meyasa ka fiye taurin Kai kullum mgn 1 kazo ka Kama aiki a kamfanin nan Amma kaki ka dauki damuwar yarinya daba ta damu da Kai ba ka sa a ranka inda Har tana sonka bazata shiga duniya ba in banda watsewa da rashin kamewar Kai yarinya ki gudu ki bar iyayenki da yan uwan ki ki bar gidan ku ina mutunci a nan na rasa wani irin asiri ta maka da ka lika ta a zuciyarka kakasa manta ta to bari in fada maka gara tun wuri ka cire ta a ranka in har ka dauke ni mahaifiya to bazaka taba aurenta ba ko da ka sameta daga baya dama na yadda ka aure ta dan mahaifinka ne da rashin son takura maka Amma yanxun Baka isa ba yarinyar da ta gudu ta shiga duniya bazata taba zama matarka ba wani tarbiya Kake jin zata bawa yaranka in banda tsiya da rashin alkairi meye a cikin dangantakarka da yarinyar nan Wanda a dalilin ta Karasa aikin ka karasa farin cikin ka ka maida rayuwar ka Abun wasa sbd ita kullum kana cikin neman ta kamar mahaukaci kaki ka tsaya ka mai da hankalin ka kan aikinka har aka dakatar da Kai aikin soja da Kake so fiye da ranka shine ka dinga wulakanta aikin ka Akan mace to tunda yanxu an dakatar da Kai sai ka Kama aikin kamfani kafin a neme ka wannan Karon ba musu dole Kayi aikin nan ga office kuma na sama maka personal sectary mace Tunda ta soma mgn kanshi sunkuye yake sai lkcn ya dago Kai ya kalle ta yace mama please kin ce Zanyi aiki na yadda Amma mama nace miki banason aiki da mace Ta kalleshi ko zanja dalili Ba wani dalili sai ra,ayina ne banga dalilin da dole Sai mace ta zama personal sectary naba Ta kalleshi a fusace tace dalili shine yarinyar ta iya aiki ta san aiki yadda ya kamata kuma na tabbatar daza ta fi taimaka maka fiye da kowa don na San Tunanin daka sa kanka na jarabar yarinyar nan ba zai barka Kayi aiki yadda ya kamata ba dan haka zan hada ka aiki da yarinyar nan sbd ta gyara dukkan wani kuskure dazakayi kuma ba ra, ayinka nake nema ba umarni nake Baka zaka bi umarnina ko bazaka bi ba Ya sunkuyar da Kai yace duk yadda kika ce mama haka za, ayi sai dai mama ki fada mata banason Shishigi aiki kadai zai hadamu bayan shi bana son komai ya hadamu Tayi murmushi gami da fadin Allah yamasa albarka sannan Dan Allah karkaje Kayi tayiwa yar mutane masifa Dan nan ba barikin sojoji bane aiki ne na walwala da jama,a sannan wani aikin ne Kake cewa ka kawo mu buga a magazine dinmu ya mika mata wani takarda Mai dauke da sakonnin rubuce rubuce na tallan wasu kamfani da hotona Mai kamfanin yace tallan kamfaninsa zamu mishi duk da ko wani jarida da mujalla suna buga mishi nima ina son buga mishi sbd akwai mutunci Mai karfi tsakaninmu Ta kalleshi Har yanxu Baka San kasuwanci ba ba ruwan kasuwanci mu da shakuwar ku ko kusancinku abin da muka damu dashi shine nawa kamfanin mu zata samu wani riba kamfanin mu zata samu shine damuwar mu ina so ka samu yarinyar nan zan tura maka ita office dinka Sai kuyi shawara kuyi mgn taya za a bi wace irin talla zamu masa nawa kuma zamu samu inda Hali ma tayi mgn dashi Takardun ya dauka yafita Yana mmkin yadda business wato kasuwanci ya shige ta sosai bata ganin komai Sai kudi mgnr Shahida ko dole in San yadda zan bullo mata sbd rayuwata ba, zata tafi dai dai ba sai da Shahida zan yi kokari in yi duk abin da takeso sbd nima ta barni nayi abin da nakeso alkawari na yiwa mahaifinta da dan uwana ta cewa zan Nemo Shahida duk da ban San Meyasa ta bar gida ba Haka ya isa office dinsa yana Tunanin ya ajiye takardun Akan table dinsa Ya soma zagaye cikin office din yana Tunanin taya zai soma aikin da bai iya ba shi aikin daya shafi media jarida ko lbr ba iya shi yayi ba ya zaiyi aiki Akan abin da bai iya ba abin da bai karanta ba mama taki fahimta ba zai iya wannan aikin ba Lokaci guda Shahida ta fado mishi ita zatafi iya wannan aikin ta karanta kuma ra, ayinta ne kuma burintaa ne tayi aiki a kamfanin jarida ko radio television ina kike Shahida ina kika tafi rashin ki ya kuntata rayuwata komai ya daina min dadi ya lumshe ido yana tunano fuskarta yayi addu a a zuciyarsa Allah ka bayyana min Shahida Allah ka bani haske Akan inda take haka ya dafe fuska da hannunsa Yana jingine jikin window idonshi lumshe Tunaninta kawai yake sonta ko Har ya rasa inda zai yi da Shi bai San yana tsananin son Shahida da bukatar ta ba sai randa ya koma yaje gidan su ya tarar da tashin hankali da aka shiga a gidansu na rashin ta ya shiga muguwar damuwa da matsala komai na rayuwa ya tsaya mishi Amma ganin halin da Dan uwana ta jabir ya shiga matsala da rudani daya gani a tare da jabir rashin yar uwarsa ya gigita shi Sai ya daina tausayin kanshi ya koma tausayin jabir a wannan rana ya Mai alkawarin nemo Mai yar uwarsa da kyar da kyar ya iya sa Shi kula da harkokin mahaifinsa sbd bayan tafiyar Shahida komai tsayawa yayi rayuwa ta tsaya musu haka harkar kasuwanci na iyayenta ga rashin lfyr babanta Wanda sanadiyar tafiyar ta ya jawo shi tunda aka nemi Shahida aka rasa ya yanke jiki ya fadi Har yanxu bai tashi ba yana kwanci komai Sai an masa duk da yana samun kula Amma ba wani Ci gaba. 💅feenah baby 👄 [28/06, 12:57 p.m.] H inna: IGIYAR RAYUWA. Book 2 Peg7 Dole yasa jabir tsayawa Akan harkokin gidansu kasancewarsa babba yayi ta mishi misali da in Shahida na nan bazata so kamfanin iyayenta ya mutu ba bazata so rushewar farin cikin su ba dole ya kula da iyayensa da kannensa daya bashi shawarar Shahida ne,,,,, jabir din ya fashe da wani irin kuka ya rungume jafar yace Meyasa yaya Shahida ta tafi ta barmu ,,,,yaya jafar ba zan iya rayuwa ba yar uwata ba yaya jafar ina son ganin yar uwata zan je in nemo ta ban San a wani Hali take ba na San akwai dalilin dayasa ta tafi Amma koma meyene ba zata yi tunanina da baba ba,,,,,,, ta san irin kaunar da muke mata ta tafi ta barmu ina fushi da ita sosai in na ganta ba zan mata mgn ba meyasa in zata tafi bazata tafi dani ba ta san ba zan iya rayuwa ba ita ba yaya jafar ya Zanyi ina zan samu yar uwata Zaka sameta jabir kar ka karaya kar ka manta Kai da namiji ne kuma yar uwar ka ba, za ta so ganin ka a cikin wannan halin ba dole ka dau girma ka kula da baba da mama da sauran kannen ka ni na maka alkawarin nemo maka yar uwarka zan Nemo maka yayar ka kuma mata ta Kayi alkawari yaya jafar Na maka alkawari jabir Kayi ta addu a Allah ya bayyana min ita cikin sauki Karar buga kofa ne ya katse Mai Tunanin da yake shigo ya fada tare da juyawa yana kallon window Shahida ne ta shigo Kai tsaye ta nufi table din ta mai da hankalin ta kan takardun dake kan table din sannan ta daga Kai ta Kalli inda jafar yake Har ta nufi inda yake sai kuma ta tsaya cak ta juyo ta sake kallon takardun dake kan table din idanuwanta ya kaita kan Hoton zuciyarta ya wani irin bugawa da karfi sbd ganin hoton dan uwanta jabir tuni hawaye ya wanke mata fuska Dan uwa ta fada cikin muryar kuka ta kurawa Hoton ido a yadda ta Lura Sam ba alamar farin ciki ko walwala a fuskarsa na maka laifi dan uwana kayafe min nayi nisa da Kai sbd yama dole ba dan naso ba na rabu da Kai jabir a hankali idonta ya kai kan rubutun data ga anyi a kasan hoton *jabir al,mustapha the young Business tycon the youn million niear* tayi murmushi tace Dan uwa kaci gaba naji dadi sosai naji dadin yadda naga kamfanin baba yaci gaba ka kula da baba ba ban taba zata Dan uwana da nasani karamin yaro zai zama babban mutum lokaci guda jabir Kayi halin baba kana da halin girma Allah ya taimake ka Allah ya baka sa a a rayuwa ya Kare ka daga sharrin duniya kaunarsa da kaunar ganin Shi taji yana shigarta ta rasa inda zatasa kanta Nan idon ta ya hango lambar wayarsa dana kamfaninsa bata bata lokaci ba tayi saurin kira Amma batayi sa ar samun sa ba ta dau mintina tana ta kokarin nemansa kafin ta dace ta dauka muryarshi ya ratsa dodon kunnenta ya ratsa zuciyarta tuni taji wani irin kuka ya kubuce mata Wayyo dan uwa Rabin jiki Ina zan sake ganinka a yau zuciyata da idanuna suna matukar son ganin Kanina dan uwana jabir dina Ya jima yana sallama Amma ba amsa ba, ayi mgn ba yaso ya ajiye wayar Amma Sai ya fasa sbd shishikae kuka dayaji Shiru yayi dan ya fahimci meke faruwa shirun dataji yayi yasa ta zaton ko ya ajiye wayar ne ta kara fashewa da wani irin kuka Mai rudarwa da rikitarwa tace jabir dina ina zan ganka ina son ganin ka in yi hira da Kai inga murmushin ka in ga fuskarka Inji muryarka kana kiran yaya Shahida Jabir na kwance bai San lokacin da ya Mike zuciyarshi na bugawa hankalinshi tashe yace yaya Shahidana ina kike mafarki nake ko ido biyu yar uwa ina kika barni yaya Shahida dan Allah ki dawo baba ba lfy mama ta shiga halin kunci tayi dana sani su rayyan da Ahmad sun shiga damuwar rashinki gudanmu ya dawo Sai Kace gidan mutuwa a tun randa kika tafi tare da farin cikin gudanmu a maiduguri ma an shiga tashin hankali da damuwar rashin ki Yasa mata kuka cikin rudaddiyar murya yace Shahida rayuwa ta galabaita sbd rashinki yar uwa mutuwa ne kawai banyi ba ki dawo rashin ki dawo yaya Shahida ki dawo please ki dawo ko ki fada min a ina kike in zo in dawo dake in kuma bazaki iya dawowa ba ki fada min inda kike zan zo in zauna a wajenki in ba kya son gidan ni zan biyo ki kina jina yaya Shahida zan mutu da rashinki baba zai,,,,,,,,,,,,,,,,,, Tayi saurin katse wayar ta tsugunna tana ta kuka kamar zata mutu kashe wayar tayi dan kar ya sake kira tayi kuka Har taji ba dadi A falo jabir yayi ta ihu a waya yana fadin ki kunna wayar yaya Shahida Dan Allah kunna waya fada min inda kike haka ya hakura Ya rufe kanshi a daki yayi kuka har ya kasa kukan daga baya lokaci guda Zazzabi ya rufe Shi Zazzabi Mai tsanani da kyar aka iya bude kofar aka yi asibiti da shi 😭😭😭😭😭na tausayawa jabir da Shahida tooo bari muga ya jafar zaiyi Taku Mai kaunarku Nafeesa 💅feenah baby 👄 [07/07, 11:03 a.m.] H inna: IGIYAR RAYUWA book 2 . Peg 8 Mama kam wato Hajiya amne taga ikon Allah da sakayya tayi dana sani mara amfani tunda tayi sanadiyar barin Shahida gidan Tunda ta tafi ba a sake farin ciki a gidan ba sai masifa da bacin rai Kala Kala da take fuskanta GA rashin lfyr miji ga tashin hankalin dan ta jabir Jafar dake tsaye yaji murya data birkita Mai tunani jin muryarta tana kuka😭😭tana kiran jabir yasa Shi juyowa da sauri nan yaci Karo da kyakkyawar fuskarta Mai daukan hankali Sai dai tana cikin wani irin Hali na rudani da rikicin rayuwa tausayin ta ya ratsa Shi son taya dinga kwaranya a zuciyarsa farin cikin ganin ta ya cika Mai zuciya tsananin mmki ya rufe Shi na ganin ta a bayyane a gavan shi Wai itace dama mama take binshi yayi aiki da ita tun tsawon shekara uku da suka wuce yaki Wayyo rashin sani dana san da Shahidana mama ke kokarin hadani da ban je da gudu ba . Shiyasa duk abin da iyayenka suka ce Kayi in Kayi zaka ga alkairinsa mama dame zan saka miki yau kin hadani da gudan raina gimbiya Shahidana A hankali ya matsa gare ta ya tsugunna a gabanta ya tsuramata ido kuka take sosai bata hayyacinta ya kira ta cikin nutsuwa GIMBIYA Jin an kirata da sunan da ba Wanda ya santa dashi Sai dan gida yasata yi saurin dago Kai zuciyarta na bugawa suka hada ido da jafar bata San ya akayi ba sai ji tayi ta saka kuka da karfin ta taga jafar a inda bata taba zato ba bare tsammani ta kasa fada masa komai Sai kuka😭😭😭😭 Shima ba don namijin kokarin da yayi ba da ya fidda hawaye tsabar tausayin ta a tare suka Mike suna kallon juna kallo mmki kallon kauna kallon tambaya Hajiya Aisha ne ta shigo ta katse musu kallon Shahida tayi saurin share hawayen ta ganin yanayin data shiga yasa Hajiya taji hankalinta ya tashi tace Shahida meya sameki haka da kyar ta iya fadin ba komai Hajiya kawai na tuna gida ne kuma an min waya mahaifina bashi da lfy Ayya Allah yabashi lfy in ji Hajiya addu a zaki masa ba kuka ba zan baki Hutu na sati biyu kije ki duba Shi ki gaishe Shi da kyau kafin ki tafi zan gabatar dake ga G, M na kamfanin nan *general manager ja, afar Muhammad* ta kalleshi wannan itace Shahida personal sectary din ka ina ga zaku ajiye Sai hankalin ta ya kwanta ta dawo daga duba mahaifinta Ta debo kudi Mai yawa tabata ta karba ta fita tana gdy Hajiya ta Kalli jafar tace haka kawai da na ganta cikin damuwa naji ban ji dadi ba haka inaji a zuciyata ban so in yi nesa da ita yanxu haka ji nake kamar in hanata tafiya Sai dai in nayi haka ban kyauta ba ina fata in ta dawo ba za ka dinga mata halin sojoji ba Kayi mata tsawa in Kayi haka baza mu shirya ba dan ina ji da ita a kamfanin nan ta kwarai sosai wajen iya aikin jarida Sai ina ji kamar kamfanin nan a yanxu baza ta iya tafiya ba in ba tare da ita ba zuwan ta Mun samu nasara da Ci gaba sosai ya kamata ma a ce matsayinta yafi nan na bar ta a wajen ne dan ta Koya maka yadda ake aikin Dan ba iyawa Kayi ba shiyasa nake so kuyi aiki tare ina fatan bakada matsala ko kadan Mama bani da matsala mama na gode na gode sosai kin min abin daya sani tsananin farin ciki abin da ba zan taba mantawa da shiba nan gaba kome kika ce nayi ba musu da gudu Zanyi yana gama fadi ya fita da sauri tabishi da kallo tana mmk me tayi haka yake mata irin wannan gdy tayi murmushi Shidai jafar ba, a gane masa tunda yace zai yi duk abin dana sashi da gudu to lallai zai yi auren da nakeso dole ya auri surayya tunda itama kamar diyata ce diyar yayata ajidde tun tana karama take waje na na girmar da ita ta dauke ni kamar mmnta zan hada ta da jafar ayi auran gida Da sauri jafar yabi bayan Shahida ya tsaida ita yana mata mgn Amma bata kula Shi ba rudewa tayi gaba daya ta rasa Mai zatace mishi ganin taki kula Shi yasa yace mata zai yi waya gida ya fadi inda take lokacin ta dago Kai ta Kalli shi ta kasa mgn Sai hawaye Please Shahida kar ki min kuka ya bude mata kofa shigo mota muyi mgn bata musa ba ta shiga shima ya shiga yace Shahida meke faruwa a rayuwarki, meke damunki wani dalili yasa ki barin gida kin San me tafiyar ki ya jawo Bana son sani jafar bana son jin labari gida ka daina min maganar kuma bana so ka fadawa kowa inda nake please ka min wannan taimakon Shiru yayi gaba daya ta daure masa Kai wayarsa tayi kara muryar mama yaji ya gaishe ta cikin girmamawa a nan take fada masa jabir bai da lfy Yana asibiti Har suma yake Yanxu ya farfado ya dage Wai Sai yayi mgn da Kai baya jin dadi sosai Amma yaki hutawa Wai zai tafi neman Shahida ka San rigimar jabir yadda take musamman Akan abin daya shafi Shahida Kayi mgn dashi ka dakatar da Shi ko zai saurare ka Nan ta Kai Mai wayar jin jabir ya dauka ya sa ya danna speaker dan Shahida taji yaya jafar ka San yau nayi mgn da yaya Shahida naji muryar ta Takirani dataji nayi mgn Sai ta kashe yaya jafar zan tafi neman ta yar uwata tana bukata ta naji muryarta cikin rudani da tashin hankali yaya jafar na kasa hakuri ina son ganin yar uwa ka min alkawarin nemo min Shahidan Amma Har yanxu ba lbr zan tafi neman ta saurare ni jabir kar ka tafi ko ina ina ta kokarin nemanta Ba kokari nake so Kayi ba yaya jafar ka nemo ta ka kawo ta nake so ya fashe da kuka ni dai zan Nemo yar uwa Jumma mubarikina 💅feenah baby👄 [07/07, 11:04 a.m.] H inna: IGIYAR RAYUWA book 2 Peg 9 Jafar ya katse shi bazaka yi haka ba na fada maka dole ka zauna ka kwantar da hankali ka kula da baba da gidan ku gaba daya so Kake ka tafi ka bar baba bakin ciki ya kashe shi ka tuna hakkinka ne ka kula da iyayenka in ka tafi ka bar su baka kyauta ba Ka ga yadda ka dagawa mama hankali a dalilin fitinar ka in tabbatar maka duk inda Shahida take lfy ta kalau bata cikin tashin hankali Haka yayi ta lallashin shi har ya yadda ya hakura tunda suke wayar Shahida ta toshe bakinta tana kuka Mai tsuma zuciya bayan ya kashe wayar ta kalleshi tace jafar jabir dan uwana jabir dina Ya kalleta cikin tausayawa yace Shahida in har kina son kanin ki haka Mai yasa kika tafi kika barshi Ba zan iya fada maka ba wannan Sirrina NE Naji Sirrin kine Amma lokaci yayi da zaki koma gida da gatan ki da iyayenki kin zo wata duniya da baki San kowa ba kin Mai da kanki marainiya a wani dalili ko meye dalilin ki gaskiya ni bana bayan ki kin kuntata rayuwarku keda dan uwanki da iyayenki meyasa Jafar da Har zan koma gida da ban bar gida ba ka dauka cewa yanxu garin nan shine yan uwana aikina shine gatana uwa da uba na ko wace dangantaka na manta da ita jabir ma Zanyi kokari na manta da Shi da dangantaka da kowa Ya zuba mata idanu hakan yasa ta sunkuyar da Kai yace tamu dangantakar dake fa shima kin rushe shin Ta dago Kai tabbas tana jin son Shi a zuciyarta har yanxu sai dai shima zata iya rabuwa da Shi tunda ta rabu da jabir rabuwa da kowa ma ba zai mata wuya ba Tunda ta rabu da gudan ranta dan uw Tace jafar dangantakarmu a Yanxu bata da tushe ba zata yi karko ba sbd yanxu komai ya canja da kanason yarinyar da take gidansu gaban iyayenta yar gata yanxu ba haka yake ba a Yanxu bani da kowa ba dangi ba gata ni kadai ce marainiya Mai zama ita kadai a gidan ta a wani gari da zai yi wuya mace ta zauna a garin ita daya a mata kallon mutunci kai ko a wani gari aka ji mace na zaune ita daya ba za a mutunta ta ba mace Mai zaman kanta ake kiranta irinmu ko da kuwa da mutuncin mu da darajar mu ba za a mutunta mu ba mezaka cewa iyayenkaa zaka auri mace Mai zaman kanta ko wacce ta gudu daga gidan iyayenta ta shiga duniya Runtsa ido yayi ya tuno kalaman mahaifiyarsa datace ina mutuncin a macen data gudu daga gidan iyayenta sai dai wannan ba zai sa ya fasa auren Shahida ba Ya kalleta yace komai zai iya canjawa kamar yadda kika ce amma soyayyata gare ki ba zai taba canjawa na so ki a da kuma ina sonki har a Yanxu kuma zan Ci gaba da son ki Meyasa bazaka fahimta bane a Yanxu ba zancen soyayya a rayuwa ta ko na aure ka bani da farin cikin da zan iya baka Ni inada farin cikin da zan iya baki dani dake wannan ya ishe mu Wai Shahida Meyasa kika maida mana rayuwa Mai whl Jafar kaga tambayoyin ka suna daya daga cikin abin da zai fara rushe dangantakarmu idan na daina miki su fa Ta kalleshi akwai sirruka a zuciyata da ba zan iya fadawa kowa ba in muka yi aure naci gaba da boye maka Sirrina zai jawo matsala Ba zai taba jawo matsala ba Shahida na yadda ki binne Sirrin ki Ta kalleshi jafar kana son takurawa rayuwata da mgnr aure in har kana so mu shirya to dole mu rushe dangantakar da mu gina sabuwa Shahida kin taba jin inda aka taba rushe dangantakarso ta gaskiya ba zan rushe ba sai dai zan iya ajiyewa in gina sabon dangantaka dake duk randa kika ji kina so mu Karasa tsohuwar ganin Sai muci gaba yanxu zamu iya gina dangantakar abota dangantakar oga da sectary dinsa sannan zanci gaba da gina dangantakar zuciya dake har randa kika sauko kika taya ni Abu na karshe me kike so in ce da dan uwanaki Kinga dai rigimar da yake na cewa sai ya nemo ki kuma alkawari na masa cewa zan Nemo ki kuma kin San muhimmancin alkawari ya Zanyi da Shi Ta juyo ta kalleshi tace Kace masa Shahida ta mutu sbd kamar yadda in mutum ya mutu ba zai dawo ba haka na bar rayuwar gida da jabir ba zan sake komawa gare su ba na bar su har abada Kallonta kawai yake yana mmkin kalaman ta da karfin zuciya irin nata ya Lura tana bukatar lokaci dan haka ya kyale ta a wacce unguwa kike ko shima Sirrin ne Ta kalleshi ta girgiza Kai ta gane ranshi ya baci tace ba sirri bane muje in nuna maka Suna tafiya jafar yayi shuru tayi mugun daure Mai kai tasa Shi a duhu Ashe akwai mace irin Shahida mara tsoro Mai kuma karfin Hali Wai duk yawan kaunar da take ma jabir ta zabi rabuwa dashi haka kuma tana zaune a garin irin Lego's ita daya ba tsoro ba fargaba haka ta binne duk wani Abu da take so a zuciyarta lokaci guda ta canja rayuwarta Sai dai Shahida duk yanda kika Kai ga guduna ba zan bari kiyi nesa dani ba Tunda Allah ya hadamu zan dinga ga din ki zan kasance tare dake a ko wani lokaci zan fuskanci dukkan wata matsala da masifa kafin lokacin Ina da tabbacin watarana zaki sauko daga tsatsauran ra, ayinki da kika hau Ta katse Mai Tunanin da fadin Wai ina aikinka jafar me ya hada ka da kamfanin jarida Yayi murmushi yace an dakatar dani ne dalili kuwa Sirrina NE Tayi murmushi ka rama ne Allah yavaka hakuri Amma Hajiya danta take son bawa matsayinka hala yaki ne taba ka Amma zaka iya aikin jarida kuwa Yayi murmushi yace gaki zaki koyamin ko bazaki Koya min ba Bata kula Shi ba ta canja tambayar Wai a wani unguwa Kake Ina dolphin estate masu gidan ma sun ban notice yanxu ina neman wani gidan ne ko zaki nema min naga ke yar gari ce Kaci gaba da zolayata in dadi yake maka Yace Wai ni Shahida naga kin canja shiga kwata kwata kamar bake ba Ra, ayina tabashi amsa Yace ra, ayin ki ko Sirrin ki duk Wanda ka zaba Da wannan hirar suka iso estate dinsu ta Kai kwayance har gidan ta bata barshi ya shiga gidan ba sbd gudun mgn duk da ba ruwan kowa da kowa Amma makwabta da Sauran yan uwanata musulmai suna mata kyakkyawar shaida bata son rushe shaida Mai kyau da aka mata Sun jima suna hira sannan sukayi sallama a wannan rana dukkan su ba Wanda ya runtsa da sunan bacci kowa yana Tunanin me zata kasance a rayuwarshi shi dai jafar yayi alkawarin kusanci da Shahida da kuma Mai data gidan iyayenta ko taki ko taso Shahida ko tunanin gida da jabir da jafar shiya hadu ya cunkushe a zuciyarta daga karshe ta Mike ta yiwo alwala tayi sallah ta rokawa mahaifinta samun lfy gun ubangiji da kuma cire ta a zuciyar dan uwanta ta roka musu samun kwanciyar hankali a gidan su duk da bata tare da su Amma kullum tana cikin musu Addu a ********* ******* ******* Tunda suka rabu da jafar sati guda bai sake zuwa ba tayi mmki matuka ta kuma shiga damuwa da ta rasa dalilin shi bayan ita da kanta ta ce su rushe Wancan dangantaka dama baso na yake ba kenan daga cewa ya rabu dani har ya rabu dani da wuri taja dogon tsaki yaran dake zaune a gabanta tana Koya musu krt suka dago Kai suka kalleta me yah sameki Aunty Yau kin ki Koya mana krt tayi murmushi ba komai kuyi hakuri na yau Aunty kanta na ciwon kuje gida Sai gobe 💅feenah baby 👄 [07/07, 11:04 a.m.] H inna: IGIYAR RAYUWA book 2 Peg 10 nan suka fita ita kuma ta nemi dogon kujera ta kwanta tana ta mita da masifa a cikin zuciyarta me yake ji da Shi meya dau Kansa harda daina zuwa in da nake bayan yaga gidana dama ba damuwa yayi dani ba ta kasa kwanciya ta Mike office MA zan tafi ko zan samu aikin yi ta sake zama to ai madam hutun sati biyu ta bani in natafi office me zan ce mata haka ta dinga surutun zuci ita daya Sannu madam taji an gaisheta da wata gurguwar Hausa Ta juyo kalleshi yana kallonta yana dariya ta harareshi me ya kawo ka gidana kasa min ido kana dariya waye kai Sorry madam yau muka dawo Anguwar nan ga gidanmu opposite da naki nazo na karbi Aron tsintsiya ne zan share gidan zan gyarawa oga na gida Ciki ta shiga ta dauko tsintsiya ta bashi ya karba yace na gode madam Sunana tunde Ta juyo tace na tambaye ka sunanka ni kam fita ka bani waje ta rufe kofar da karfi Ya juya ya nufi inda jafar yake tsaye yace oga madam tana cikin Zafi Yayi dariya kyale ta Tunda na San dalilin zafin ta je Maza Kayi aikin ka Tunde yaron jafar ne sun jima tare jafar na gidan iyayensa baban tunde ke musu gadi lkcn da jafar ya fara aikin soja ya bar gidan ya nemi wani gida baban tunde ya dinga ya dauko masa dansa tunde ya dinga yiwa jafar aikin gida tunde mutum ne Mai ban dariya yana da dadin zama haka bashi da rashin hankali irin na yawancin matasan yanxu Lokacin da aka Mai da jafar kaduna yazo so taho da Shi sbd dadin zama dashi dayake ji to Amma a lkcn yasa tunde a mkrnt yana krt baya son raba Shi da karatunshi Dan haka ya barshi a gidansu na Lego's sbd in yazo gun iyayenshi a nan yake sauka ko in wani aiki ya kawo shi Lego's jafar baya sauka a gidansu sbd yana ga yayi girma da Kwana a gidan su duk da iyayenshi na masa fada Akan rashin zama a gida musamman mmns Ranar da jafar suka rabu da Shahida washe gari ya shiga neman gida kusa da nata ya taki sa a ko yasamu gida dab da nata suna kallon juna a cikin estate din ba kowa a wannan gidan Tunda masu gidan suka fita ko wace rana ya kanzo yaga Shahidan sai dai baya isa inda take rayuwar da take yabashi sha awa duk da tana rayuwa cikin kadaici da kuncin rashin dan uwanta bata karaya tana rayuwa Mai sauki tana kokarin samawa kanta farin ciki a wannan rayuwar da take Shahida tana mugun burgeshi da bashi sha awa musamman in ya ganta cikin yara tana Koya musu krt suna wasa da dariya ya Lura yaran na kaunar ta sosai sun fi sha awar zama tare da ita fiye da gidansu Ranar da jafar zai kauro Ya dawo kusa da gidan Shahida tare suka dawo da tunde yace mishi kaga wannan gidan kaje ka buga macen da zata bude maka kofar ta fito to itace aunty ka uwar dakin ka ita zan aura Tunde yayi tsalle Allah oga naji dadi zan je inga aunty na Jafar ya ce amma fa ta fiye fada zuciyarta a kusa take kullum tana cikin fushi kar ka je ta sauke a kan ka Ba damuwa oga zanje na San me Zanyi nan ya nufi gidan jafar na kallonshi yazo zai buga kofar yaji ta a bude hakan yasa ya tura ya shiga ya samu Shahidan Bayan tafiyar tunde jafar ya nufi gidan nata ya tura kofar gami da sallama tana zaune tayi tagumi ta daga Kai ta Kalli shi ta amsa ta kau da kai ya nemi waje ya zauna yace ba gaisuwa gimbiya Yau ka tuna ina garin ta fada ba tare data kalleshi ba Ya Zanyi Shahida kin yi katanga tsakaninmu kin Ci kinrushe dangantakar so a tsakaninmu ni kuma yawan ganin ki zai dinga kara dasa son ki a zuciyata gashi girma yazomin lokaci yayi da zan yi aure Ta juyo ta kalleshi to Kayi mana waya hanaka Kin tabbata kin amince in auri wata ba kya sona ba kya bukatata a rayuwarki Mungama mgnr nan da kai jafar tuntuni kaje ka yi ta auranka ta Mike zata yi ciki Ji mana gimbiya saurare ni naji ba kya bukatata matsayin miji Amma kina bukata ta matsayin Aboki Ta juyo ta zauna tace jafar duk mgnr daya ce Aboki saurayi miji ni a waje na ba banbanci dangantakar mace da namiji saurayi da budurwa muddin ba muharraman juna bane to ban yadda zasu hada wata dangantaka ta abota kawai ba dole akwai mgnr so Aboki saurayi duk daya ne Amma duk da haka na amince zan zama abokiyar ka sbd ina bukatar Aboki a halin yanxu sai dai ina da sharadi Ina jin ki fadi sharadinki ni Mai amincewa ne da ko wani sharadinki Ta kalleshi na farko ba tausayawa tsakaninmu bana son ka dinga yawan nuna tausayina sbd ni ba abin tausayi bace na biyu ina so ka min alkawarin bazaka taba fadawa su jabir inda nake ba bazaka sake min mgnr su ba bazaka sake min wata tambaya da bana so ba na karshe zaka manta rayuwar da muka yi Ada mu soma sabuwar rayuwa Yayi murmushi yace naji na amince kin riga da kinyi min komai da kika barni in zauna a wani bangare na rayuwarki naji dadi da kika bani matsayin Aboki Ta kalleshi tace zan tabbatar dangantakarmu ta tsaya a abota Kallonta kawai yake a, zuciyarshi yace Shahida kenan har yanxu baki da wayo Wai kin yi haka dan kar zancen soyayya ya shiga tsakaninmu baki San soyayya faruwa take ba ko anyi ta ko ba ayi ba 💅feenah baby 👄 IGIYAR RAYUWA book 2 Peg 12 Kamar yadda yake son mgnr Shahida haka itama Hajiya take jiranshi dan taji Mai ke faruwa yana shigowa gidan ko gaisuwa ba suyi ba ta soma tambayarsa jafar meke faruwa meye tsakanin ka da yarinyar nan Shahida naji ka Kama gida kusa da nata a wani dalili ya kalleta mama mu gaisa mana ya gaisheta cikin girmamawa da kyar ta amsa ya juya ya gaida mahaifinsa sai surayya dake wajen ta gaishe Shi ya amsa sannan ya Kalli mama yace please mama ki kwantar da hankali ki duk yadda kike zaro ko dauka ba haka bane Kana nufin in barka kaci gaba da Harka da wannan yarinyar da take zaman kanta ka San waye mace Mai zaman kanta mace Mai kawo Maza gida tana shake ayarta dasu tana sai da kanta suna biyanta .. Mama Ya katseta Shahida ba haka take ba Shahida macace Kamila mai mutunci bata Harka da wani namiji jama a da dama sun shaida ta duk Wanda yama shaida kazafi yace mata karuwa Allah zai saka mata SHAHIDA bata Harka da wani namiji ko mgn ban taba gani tayi da wani ba gaisuwa ko aikin office ya hada su ba ni NE kadai namijin da Shahida take Harka da Shi ba irin harkar da kike nufi ba dangantakarmu da ita Mai tsabta ce ba yadda kike tunani ba Ta kalleshi cikin bacin rai tace ba damuwa taba ce ko meye a tsakaninku inaso ka rabu da ita ka tattara ka bar inda take ina son dangantakar Taku takare Ba zai yiyu ba mama sbd son Shahida nake so nake na aure ta ...baka da hankali kanka ya kunce Wai jafar meke damun ka ne mgnr auren ka mun gama surayya zaka aura kuma ko da bazaka auri surayya ba ba zan bari ka auri wannan karuwar mara asali ba in MA kyanta ne ya rude ka bazaka aure ta ba Mama Shahida ba karuwa bace da asalinta da iyayenta in har nayi aure to Shahida ce sbd Shahida itace yarinyar dana fara so itace gimbiya wacce na muku mgnr auren ta yar kdn ban San wani dalili yasa ta barin gida ba koma meyene na San Shahida Kamila ce macace Mai mutunci da kamun Kai .ranta kam ya baci da kalamansa tace lallai na yadda so makaho ne yarinyar data gudu ta bar gida ta gama yawon tambadewa tazo Lego's tana zaune ita daya ita Kake kira Kamila mai mutuncin ka San meye mutunci kuwa to ban amince ba bazaka auri yarinyar nan ba ko yaza Kayi Ya kalleta mama in ban auri Shahida ba to ba zan auri surayya ba ma sai dai kar nayi aure Ni Kake fadawa haka Ya Mike ya fita tabishi da fada gami da fadin lallai jafar ka nuna min matsayina ka nuna min bani na haife ka ba da mahaifiyarka ta asali ne bazaka mata rashin kunya ba Jin kalamanta yasa ya tsaya ya juyo ya fasa tafiyar yace mama kema kin San ba haka bane kullum haka kike daureni Kisa nayi Abu dole in naki kice dan bake kika haife ni ba mama yau ni zan fada miki haka kin ki ki barni in auri wacce nake so sbd bake kika haife ni ba dani danki ne bazaki danne min farin cikina Akan naki ba ko wace uwa farin cikin danta na gaba da komai amma ke dan ba mahaifiyata bace kike danne dukkan wani farin cikina kituna ni maraya ne kuma amana ne a hannun ki mahaifiyata dazata rasu ta bar amanata a hannun mahaifina mahaifina ya bar amanata a hannun ki please mama kar kici amana kar ki takura rayuwata ki barni na auri macen da nake so nake buri mama Shahida itace rayuwata itace farin cikina baba please ka mata mgn Alhaji abubakar ya kalleshi ya lura baya hayyacinsa wani mgnr MA bai San yaushe yake fada ba tashi kaje jafar zaka auri macen da kakeso zan mata mgn nan ya Mike yafita .... Hajiya Aisha ranta ya mugun baci bakin ciki ya hanata mgn tsanar Shahida ya darsu a ranta yau ce rana ta farko da jafar yayi musu da ita har MA ya muzanta ta Akan Shahida Har cikin ranta tana kaunar jafar kamar danta haka kawai taji hawaye ya gangaro mata Mijinta ya matso kusa da ita yace Aisha meye abin hawaye Ta kalleshi ya ba zan yi kuka ba Ta Kalli surayya tashi ki shiga ciki nan ta Mike ta shiga ya mai da kallonshi kan aisha yace Aisha duk abin da ka koyawa yaro shi zai tashi dashi kuma shi zai maka wataran yaron nan ya rike ki matsayin uwa yana miki biyayya yana sonki sosai ke kika Koya mishi Abu kadan kika sa Shi in yaki Sai ki ce don bake kika haife shiba yau kalamanki ya mayar miki kina yawan sa jafar yin abin da bayaso ko hana shi abin da yakeso Aisha ki cire son Kai cikin Al,amarinki ki duba yadda abubuwa suke Idonta jawur ta kalleshi tace abubakar meye abin son Kai a cikin abin danayi dan nasa shi yadawo yayi aiki a kamfanin nan kamfaninsa ne fa ba nawa ba duk wata duniya da nake rike da ita nake juyawa gadonsa ne mahaifinsa ya bar masa ina aiki ba don ina so ba sai don rike amanarsa da mahaifinsa yarasu ya bar min amanar dukiyar sa dashi kanshi nayi zaman tsakani da Allah da mahaifinshi Munyi zaman amana da gaskiya har ya rasu ban taba dana sanin auren Saba Muhammad miji ne nagari tun yana da rai na rike dansa jafar da amana ban taba Mai rikon matar uba ba rikon uwa mahaifiya na masa duk da yanxu bani da da ko daya na San ciwon haihuwa na San ciwon da har yau ban manta da fuskar yar jaririyata da wauta da rashin wayo da rashin hankali yasa na bawa aminiya ta amne ba Wanda daga karshe sai lbrn rasuwarta naji haka har yau ban sake jin lbrn amne ba bare duriyarta Abubakar inason jafar kamar dan da zan haifa sbd kullum matsayin da ke gare Shi a guna ba dan riko ba dole nake aiki a kamfaninsa don in barshi yabi ra,ayinsa ya cika burinsa na son zama soja inayiwa jafar komai Dan nace jafar ya auri surayya yaki kana ga ya kyauta kana ga in na bari jafar ya auro yarinya mara mutunci mara asali ban Ci amanar mahaifinsa ba na rike Shi da amana Amma yau jafar kemin mgnr Shi marayane amana ne Abubakar ya gyara zama ya kalleta yace Aisha girma yasa kin manta komai manyanta da kika yi yasa ki tunani irin na Manya kin manta kanki kin manta lbrn rayuwar ki kin manta mgnr soyayyar mu dake da aurenmu dake yadda ya kasance tsakanina dake da iyayenki kema kina mace da mahaifinki ya hana ki aurena sbd ina inyamuri kina shuwa bani da asali aka hanani aurenki wani mataki kika dauka kin dau mataki da shine sanadiyar farkon rushewar farin cikin rayuwarki kin dau matakin daya jefa rayuwarki cikin kunci kika fuskanci tashin hankali da masifar rayuwa Mun sabi ubangiji sbd an hanamu auren juna muka kasa jurewa muyi tawakkali muka fada halaka kin San komai ba sai na tuna miki ba kina mace kenan kika kasa hakuri da abin da kike so bare jafar namiji Dan zamani Kar ki fara Aisha kullum kina sashi yayi abu dole ki hana shi ya hanu amma wannan karon ba zai yiyu ba sbd ya shafi soyayya ya shafi zuciyarsa ba zai iya hakura da abin da yake so ba kar ki fara tsai dashi auren wacce yakeso in ba haka ba zaku samu matsala kun MA fara samu daga yanxu yaron da bai taba miki musu ba yau ya rufe ido ya fada miki maganganu wannan ya nuna matsayin son da yakema yarinyar nan haka ya nuna karfin son da yake mata kar ki raba su ki barshi ya auri wacce yakeso sai a samu zaman lfy in har kina so ki tabbatar masa ke uwarsa ce to ki kyaleshi kar ki danne farin cikinsa in kuma kinki to zai gane matsayinsa kin fahimce ni Aisha Shiru tayi kamar ruwa yaci ta ta tuna rayuwarta komai amma Sam ta kasa yadda jafar ya auri Shahida ba don rashin asali ko don abin data irgo mata ba sai don tana gazata kwace jafar zai daina daukan tada muhimmanci zai bawa Shahida muhimmanci a kanta Iyaye mata kenan wasu Tunanin su kar mata ta raba ta da danta dole mu fahimci matsayin uwa daban matsayin mata daban ******** ************** Bayan Aisha tayi aure da Muhammad suna zaune lfy tare da danshi jafar Wanda ta rike matsayin da sai dai ita haihuwar ta ta tsaya mata sun dau tsawon shekara 7 da aure Amma Aisha ba lbrn ciki tun tana damuwa Har ta daina Tunda ba wai matsala ce da ita ba Allah ne bai kawo ba sai dai son da ko ya zuciyarta har ya yi yawa burinta shine taga danta ko yarta Wanda ta haifa amma hakan bai yiyu ba Watarana Aisha na zaune Mijinta Muhammad Ya shigo yace ya kawo mata wani tsohon abokinsa Wanda sun jima basu hadu ba tare sukayi mkrnt nan ta tashi ta dauko himar tasa dan taje su gaisa haka ta aika aka Kai masa abinci da sha na tarar bako Tana shiga falon taci Karo da fuskar abubakar zuciyarta ya tsinke sanadiyar ganinshi ya gara girma ya zama babban mutum da kyar suka gaisa shima abubakar din hankalinshi tashe ya bar gidan rayuwar da suka yi tare ta dinga tunawa shima ganin ta ba zata gabanshi ya dawo Mai da komai sabo Tundaga Ranar bai sake zuwa gidan ba sai dai abotarsu da Muhammad taci gaba haka suka yi kokari suka manta duk wani dangantakarsu lokaci guda Allah ya dorawa Muhammad rashin lfy wacce tayi sanadiyar tafiya da ranshi ya rasu jafar na secondary school kafin ya rasu ya danka amanar jafar a hannun Aisha yace ko bayan ransa ita yake so taci gaba da rikon jafar da duk wata dukiyar sa Haka jafar yaci gaba da rayuwa tare da Aisha ya dauke ta uwa ta daukeshi danta yawancin gadon da aka raba nasa ne bayan ta fita takaba bata koma maiduguri ba ta zauna taci gaba da kula da kamfanin jafar da mahaifinsa ya bari Yan uwansa sun so asiyar da komai su koma maiduguri Amma taki haka mahaifinta ya matsa da sauran yan uwanta Akan ta dawo Amma taki ta zama yar Lego's mace Mai kamar Maza har sai da jafar ya kusa gama mkrnt sojoji sannan abubakar ya dawo rayuwarta iyaye suka sa baki haka sai da ta nemi yaddar danta jafar sannan aka daura mata aure da mutumin data jima tana so mijin da ta fidda tsammanin da sake koda ganin Shi a rayuwa Yan uwana Kwana 2 ba lallai bane kuringa sabun post din igiyar rayuwa sbd inada biki a gabana Sai bayan bikin zakuringa samu a Kai a Kai Godiya nake masoyana 💅feenah baby 👄 [25/07, 9:33 p.m.] KHADIJA 1: IGIYAR RAYUWA book 2 Peg 13 Haka abubakar auren Aisha ya, zama kamar a mafarki sun son juna sun riki juna da amana haka ya riki jafar kamar yadda ubansa zai rike Shi tunda abubakar ya rabu da Aisha baiyi aure ba yaci gaba da aikinsa na gwamnati Aisha taso yadawo suyi aiki a kamfanin su Amma Sam yaki haka suka bar mata aiki da jafar da abubakar Sai dai suna zaune gida daya gidan abubakar Anan tabashi lbrn cikinta da haihuwar ta bayan rabuwarsu ya tausaya mata matuka na halin kunci da tashin hankali da tashiga ya mata alkawarin son ta da nuna mata kauna dasa ta farin ciki muddin suna raye burinsu a zahiri shine haihuwa Amma da alama Aisha ta gama haihuwa tun randa ta haifi Shahida sbd haihuwar ta ki ba kasar da ba suje ba haka ba irin maganin da ba suyi ba daga na asibiti Har na Gargajiya ba abin da ba suyi ba dan su samu haihuwa Amma shuru hakuri sukayi dole duk da jarabar son haihuwa da suke Wannan shine ya faru a rayuwar Aisha Shahida ta kasance diyarta Amma suna zaune tare na tsawon lkc basu gane juna ba sbd rashin sani sai dai dangantakar uwa da ya, Ya wuce komai duk da basu San juna ba suna jin kaunar juna a zuciyarsu musamman Hajiya Aisha zuciyarta na son Shahida sosai duk da yanxu tana jin ta tsane ta sbd tana ga ta shiga tsakaninta da danta jafar amma a karkashin zuciyarta kaunar na nan A Ranar da jafar suka yi fada da Hajiya Aisha Akan Shahida ta kara kullatar ta ta kara tsanar ta ta dinga Tunanin yazata yi ta raba Shahida da jafar Ta yiwa kanta alkawarin kuntata rayuwar Shahida muddin bata fita Har kar jafar ba *wannan shine rashin sani tana shirin kuntata rayuwar yarta ba ta sani ba* Jafar ya shiga damuwa da bacin rai na dalilin abin da ya yiwa mamansa ya rasa meke mishi dadi haka ya isa gida cikin damuwa Shahida taji shuru bai Leko ta ba tayi mmki Sai dai bata jeba tunde ne ya shigo ya same ta yake fada mata oga yau ya dawo Amma Ya kasa gane masa yaga kamar yana cikin damuwa Tare suka tafi da tunde tace yama sa mgn tana waje Anan yazo ya same ta ta kalleshi tace jafar lfy Ya girgiza Kai ba lfy ba Shahida nayi laifin da ban San ya Zanyi in wanke shiba Meyafaru jafar Nayi mama rashin kunya na manta kauna da rikon amana da mama ta min na rasa ina hankalina ya bata Har nayi ta mata rashin kunya duk abin ya ame ni na rasa ya Zanyi Tabbas jafar Kayi laifi mai girma da bayi da ikon yiwa uwarshi rashin kunya ko da yankan naman jikin Shi take sannan ka kara laifi da Har yanxu Baka je ka nemi ta yafe maka ba bakaje kabata hakuri ba in kana so ka fita daga cikin damuwar da ka shiga Kayi saurin zuwa ka bata hakuri in ta yafe maka zaka samu sukuni amma in baka je ba bazaka taba samun peace ba Kayi sauri kaje kabata hakuri ba kowa ke da gatan iyaye ba ba kowa keda iyaye a kaddarsa ba Ya Mike na gode Shahida Bari naje na dawo gidan ya koma yayi ta bawa maman hakuri Har ta sauko ta yafe masa ya kuma tabbatar mata ba zai sake ba Bayan ya dawo Shahida ke fada masa jafar ina son baka shawar Ina jinki gimbiya Ta yi murmushin jin wannan yadda ya kira ta a kullum ya kira ta da wannan sunan yana sata nishadi tace duk abin da ka San zai jawo rigima ko bacin rai tsakaninka da mahaifiyarka ka guje Shi ko menene sbd ba alkairi bane Ya kafa mata idanu yana kallonta a zuciyarshi yace rabuwa dake Shahida yana nufin rabuwa da rayuwata kuma ni na tabbat ke alkairi ce a gare ni mutum irin bazata taba zama Sharri ba na San mama ma zata fahimci haka wataran Haka rayuwar Shahida yake tafiya ba tare da yan uwanata ba ta Mai da kanta maraya karfi da yaji yayin da jafar ya zama shine danginta da dan uwana ta Ta bangaren jabir ma ya dau kaddara na rashin yar uwarsa Sai dai bai fasa addu ar Allah bayyana mishi yar uwar Shi ba ya dage da harkokin business na mahaifinsa Wanda rashin lfy ta nakasa jabir ya dawo babban mutum ya girma sosai ko ta ina kawo Mai yan mata ake ko zai aura Amma ina jabir yayi musu yace sai randa Allah ya dawo masa da yar uwarsa ita zata mai zabin matar da zai aura 💅feenah baby 👄 [25/07, 9:33 p.m.] KHADIJA 1: IGIYAR RAYUWA book 2 Peg 14 Hajiya amne kam bata samun farin cikin da take neman ba wanda tace ta rasa shi a dalilin shahida tafiyar shahida bai Kara mata komai ba sai Karin tashin hankali da bacin rai ga miji ya nakasa ga danta ya dawo ko murmushi wannan an daina gani a fuskarsa kullum zuciyarshi cike da kunci da kewar yar uwarsa shahida ita kanta hajiya amne bata San Tana kaunar shahida ba sai da ta tafi tabbas ba a gane muhimmanci mutum sai baya nan Tsana tsakanin shahida da hajiya Aisha yaci gaba har MA shahida ta soma tunanin barin aikin jafar ke ta kokarin bata hakuri da nuna mata kar ta damu da halin hajiya ita de tayi aikin ta haka ta kafa mata doka na lokacin da zata dinga zuwa aiki in har ta Kara ko da minti 1 NE haka zata rufe ido taci mutuncinta ta zage ta gaban kowa Dole tasa shahida ke kiyaye dokokinta Tana binsu ko wasa Bata karya dokar ta. Sai wannan rana da tsautsayi ya debeta ta biyewa jafar sukayi latti. Munji yadda takwashe tsakanin tada hajiya har takai ga korarta daga aiki itama tace ta bar aiki. Yayin da jafar ya roki mamansa ta mayar daita aikin tayarda. Saidai Bari munji ko shahidar zata yarda ta koma aiki? ** ** Tana kwance Tana tunanin rayuwarta tana kuka,taji karar buga kofane.tabbas tasan jafarne dan haka taki tashi ta bude. Shi Koyaki tafiya, ya dinga bugawa da karfi, dole ta taso tabude saboda makwabta zasu zargi wani abu. Tana budewa ya shige cikin falon,ba ta kulashiba. Yace shahida wai meke damun kine ya za ayi kiyi tunanin fada da mahaifiyata har ki iya daga hannu kice zaki mareta a tunanina zaki daraja mahaifiyata sbd ni baki duba dangantakarmu ba Ta kalleshi idonta ya kada yayi ja bakin ciki ya cika mata zuciya tace naji nayi laifi ka yafe min sai dai kamar yadda na taba fada maka ka guji duk wani Abu da zai jawo bacin rai tsakaninka da mmn ka dole ne mu rabu sbd hanyarmu bazata zo daya ba ka ji bacin rai akan abin da na yiwa mmn ka sbd mamanka ce kana sonta amma ni bakaji bacin ran dana ji ba na cin mutuncin da mahaifiyarka ta min ta kirani da karuwa wannan kalma ta min ciwo fiye da komai yau itace rana ta farko dana ji na gaji da rayuwa naji ina sha awar mutuwa yau nafi jina a marainiya haka kawai tausayin kaina ya kamani jafar ni marainiya ce bani da uwa da uba da yan uwa ni SHEGIYA ce ka San meye yarena ni inyamurace bani da asali gidan su jabir alfarma suka min suka rike ni bani da hadi dasu bani da dangantakar jini dasu jafar bani da kowa a rayuwa in nayi ciwo komai ce min sannu bani da shi yau da aka kirani karuwa bani da Mai taya ni jin ciwon abin da aka fadamin bani da Mai tayini bakin cikin wannan mummunar kalma ban San me yasa tunda muka sake haduwa da Kai a garen nan nake tsammanin akan ka sai in ga kamar zan samu canjin rayuwa ta dalilin ka sai ina ga kamar farin cikina yana tare da Kai amma a yau komai ya kare A tsakaninmu abotarmu dangantakarmu soyayyarmu wacce da muka soma gina ta yau komai ya rushe ya kare Jafar bani ba Kai mahaifiyar ka kuma aiki a kamfanin ku na gama shi ko bara zanyi amma banda aiki a kamfanin ku Dan haka yanxu bana son wani dogon mgn ka fita a gidana tun wuri kuma estate din nan in baka bar shiba ni zan barshi Tunda take mgn yake kallonta cikin shaukin so da kauna zuciyarshi taji son ta ta kuma tausaya mata ya dinga jin kamar yaje ya rungumeta ya lallasheta shin wai me zai hana na auri shahida Auren ta zai kawo duk karshen rigimar nan ya dube ta yace shahida dangantakarmu dake ba Mai karewa bace asali MA dangantakarmu yanxu ta Fara shahida ina so in aure ki in baki gatanki in zama Mai share miki hawaye zan kasance dake a lokacin farin ciki ko bakin ciki zan fuskanci dukkan wata matsalar ki zan kasance dake cikin lfy ko ciwo Shahida jafar zai miki komai ki shigo rayuwata in debe miki kewa ki debe min kewa shahida muna bukatar juna ni dake mm ba za ta zama katanga tsakanina da ke ba shahida kamar yadda baki da kowa haka nake banida kowa nima maraya ne kamar ki kamar yadda kika ce baki da dangantska da su jabir nima haka nake bani da dangsnka da hajiya kamar yadda suka rike ki suka soki haka nima hajiya da mijinta suka rike ni dangantakana da ita shine matar mahaifina ne Wanda ya rasu tun da jimawa sai dai ta rike ni tamkar dan da ta Haifa Shahida kiyi kokarin sa kanki a matsayina ki gani in kece kika ga na dau hanu zan Mari mahaifin ki ko da kuwa gaskiya NE zaki iya bari na tabbata duk yawan son da kike min bazaki kyale ni ba kila ma ki daina min mgn kila a wannan dalili rabuwar taxo Ya kalleta kanta a sunkuye yace shahida kin fahimce ni a wannan lkcn banida zabi gimbiya ina matukar sonki bana son rasaki Dan Allah gimbiya Dan kauna da so dake tsakaninmu ki dinga daraja mahaifiyata Ta dago Kai ta kalleshi idonta cike da hawaye haka kawai take jin tausayin kanta haka kuma taji ta tsinci kanta da matsananciyar son jafar tace jafar ba halina bane rashin kunya MA wasu MA bare mahaifiyarka ban San meya same ni ba a wannan lkcn na manta girman hajiya na daga hannu zan mareta nagode da ka tsai dani sai dai jafar mgnr da Kake fada ba Mai yiyuwa bace musamman MA da abin nan yafaru gimbiya ba abin da zai hana shi yiyuwa shahida zamuyi aure zaman ya isa ki sani a yanxu ba zamu taba iya rayuwa ba mutuncin ki mutuncinmu mutuncin dangantakarmu shine aure shahida mu bar rayuwar karya mu kama gaskiya gaskiyar dangantakarmu shine aure in muka yi aure zamu rufe bakin kowa zamu bar rayuwar kewa da kadaici gimbiya dole muyi aure kafin shedan ya shiga tsakaninmu *jafar zaka iya aurena a haka jafar ni shegiyace da ban San iyayena da asalina ba zaka iya aurena a haka ba zai shafi rayuwar ka da ya yan da zamu Haifa ba a ce uwarsu shegiya ce* Haba gimbiya har yanxu baki San matsayin ki a rayuwata ba kina jin akwai dalilin da zai Sa na ki auren ki shahida kece rayuwata dalilin farin cikina shahida in ke ba yar sunna bace ba laifin ki bane Wanda suka yi laifi daban bake ba ki manta wannan duk ki cire shi a ranki mu soma sabuwar rayuwa mu kafa tamu zuriyar kina jina Shiru tayi na yan mintina shi kuma yana kallonta alamar yana jiran amsa sannan ta girgiza Mai Kai tare da fadin na amince sai dai inaso ka nemi yaddar mmn ka Ya mata sassanyar murmushi Mai tattare da farin ciki da jin dadi yace mama zata yadda amincewar ki shine babba gimbiya zan ga cikar burina mafarkina zai zama gaskiya Allah zai min baiwa da Mace irin ki ngd da wannan farin ciki da kika bani Masoyana ngd 😘 💅🏻feenah baby👄 [25/07, 9:33 p.m.] KHADIJA 1: IGIYAR RAYUWA book, 2 Peg 15 Kallonsha take har yafita irin farin cikin data ga yana yi ya matukar ba mmk wai da MA jafar na kaunata sosai haka zuciyata na son jafar amma meyasa nakejin wani irin fargaba in na tuna zanyi aure,, meyasa nake tsoron aure sannan haka zanyi aure baba bai saniba dan uwana bai sani ba Anya abin da nayi na tafiya in bar jabir da baba na musu adalci sakayyar da na musu na son da suka nuna min Anya dai dai ne,,,,,,,, to amma ai umarnin mama nabi to yanxu in zanyi aure wa zai zama waliyina shin taya zan soma yin auren,,,,,,,,,,,,,, Haka ta kasance cikin sake,, saken zuci daga karshe ta tashi tayi alwala ta hau sallah dan neman zabin Allah A gidan su jafar fada ya kaure tsakaninsa da hajiya Aisha akan mgnr auren shahida daya kawo mata ya kuma ce mata Akan tayi hakuri ta kyaleshi ya auri yarinyar dayake so Mama wannan shine Abu na karshe da zan nema a wajen ki bayan shi ba zan sake cewa zanyi wani Abu da ba kya so ba zanyi duk abin da kika ce mama ba zan iya rayuwa da kowace Mace ba bayan shahida mama please ki yaddar min in auri gimbiya Na fada maka jafar ba zan taba bari ka auri wannan karuwar ba Mama please shahida ba karuwa bace shahida macace Mai mutunci macen da nake so nake buri mama karki dau hakkina ki raba ni da abin da nakeso Karkadamu jafar zaka aure ta ba dai kana sonta ba ni zan aura maka ita alhaji abubakar ne yake mgnr ya shigo cikin falon yace Mmn ka zata yadda je ka Fara shiri Tashi yayi har ya fita yana kallon fuskar Mmn ranta a bace Wanda hakan ke daga Mai hankali sai dai yadda yake jin guguwar son shahida baya jin akwai abin da zai Hana shi auren ta Abubakar ya Kalli Aisha yace wato ba kya jin mgn ko a zatona mun gama mgnr nan a wani dalili zaki Hana shi auren matar da yakeso ki tambayi kanki kinyi adalci Tace alhaji kafa San surayya tun Tana karama take son jafar kuma yaranyar nan shahida da yakeso zata iya rabamu da shi tun a waje ma yana musu dani a kanta inaga in tashigo cikin gida Na fada miki Aisha ki cire son kai a Al, amuran ki kinga son da surayya ke MA jafar amma baki ga son da jafar ke yiwa shahida ba surayya yar uwar ki ce kin fahimci ciwon ta amma baki fahimci na jafar ba in har zan fadi mgn kiji kuma na isa dake to ki bar yaron nan ya auri yarinyar da yake so nan ya fice ya barta cikin bacin rai ba Don hajiya Aisha taso ba ta yadda da auren jafar da shahida sai dai tayi alkawari ko yaushe ta samu lkc zata raba auren wannan lbr yafi komai dadi a gun jafar rawan Kai da doki ba a mgn auren shahida ya zama wani babban Al amari na daban a gare shi auren ya zo Mai da wani irin farin ciki Marar misaltuwa Ita dai shahida bata gajiya da mmkn irin yadda jafar ke dokin ta ke daukaka ta wannan baiwa ce Wanda Allah ya mata na shiga ran mutane shahida mutumce Mai shiga rai cikin kankanin lkc jafar yagama shirin komai na auren sa da shahida ya fuskanci shahida na cikin Matsala na rashin mahaifi ko yan uwa Wanda za suyi waliyancin auren ta Dan haka yayi niyar magance mata matsalar ta Wani dare shahidan tana zaune Tana tunanin rayuwarta da mgnr aurenta shin taya ya auren zai yiyu meyasa take tsoron faruwar Al amarin shin wannan aure alkairine a gare ta ko a, a dole na nemi zabin ubangiji sbd alkairi nake nema ba son zuciyata ba Karar door bell ya katse mata tunani nan ta Mike ta bude kofar jafar NE tare da wani dattijo Mai cikar halitta da kwarjini da sauri ta Loma ciki ta dauko hijabinta sannan ta musu ISO ta tarye su cikin girmamawa ta rusuna ta gai da bakon Wanda ta San shi baban jafar wato alhaji abubakar Jafar ya kalleta yace shahida na kawo miki farin cikina wato babana kin San ba abin dayafi iyaye dadi musamman ga ya Mace bani da halin baki mamana amma zan iya baki babana Jin haka yasa shahida dago Kai ta Kalle su duka tuni taji hawaye ya ciko idonta alhaji abubakar yace kar kiyi kuka shahida share hawayen ki muddin ina raye bazaki yi maraici ba jafar ya fada min komai game dake da rayuwar ki kar ki damu ki godewa Allah a ko wani Hali kika tsinci kanki ki cire komai a ranki ki barwa Allah dukkan Al, amuran ki kuma muddin ina raye zan share miki hawayen ki kamar yadda kike kukan rashin iyaye haka nake kokan rashin ya,ya Allah ya amsa addu a ta ya ban ya,ya ta hanyar ku keda jafar zan miki duk abin da uba zai yiwa yarsa zan aurar dake cikin gata da mutunci Dan haka zaki bar gidan nan a gidan ku za a aurar dake gidan baban ki Ya Mike zan tafi ki shirya koman ki gobe zan zo in Kai ki gida Shahida bude baki tayi Tana kallon shi mmk ya cika mata zuciya Ashe har yanxu akwai mutane irin alhaji abubakar ta kasa koda masa godiya Inda suka tafi suka barta a nan take har suka isa gida jafar ya mata waya ta dauka Tana sharar hawayen farin ciki yace shahida kina murna kuwa da abin dana miki ko dai na bata miki cikin rashin sani Ta amsa da cewa jafar yau farin cikin daka bani bana jin akwai Mai sake ban irinsa ka sani farin ciki da baya misaltuwa Ashe da gaske ne farin cikina yana tare da Kai ban tabbatar ba sai yau daka bani farin cikin samun uba kamar alhaji abubakar mutumin da zuciyata ke kauna sosai sbd kirkinsa da adalcinsa ban taba zata zan samu matsayin yarsa ba ka ban komai a rayuwa ina matukar maka godiya da wannan kyautatawa taka wannan alkairi naka ba zan manta ba ka shigo rayuwata ka cika ta da farin ciki ka cika zuciyata da soyayyar ka ka cire rayuwata daga cikin kewa dame zan saka maka wannan alkairin naka Shahida ban miki komai ba duk abin dana yi kaina na yiwa sbd farin cikin ki shine nawa ganin ki cikin damuwa da bacin rai yafi komai ciwo a gare ni burina ki zama uwar ya,yana soyayyar ki kasancewa tare dake yafi komai mahimmanci a wajena Zan kasance tare da Kai jafar Lumshe ido yayi farin ciki da tsananin son tana ratsa shi muryarta kawai yake ji Mai dadin sauraro da kalamai masu ratsa zuciya A wannan Rana kusan kwana sukayi suna mgn gami da shirya yadda bikinsu da yadda rayuwarsu zata kasance rabon shahida data samu farin ciki irin na wannan rana tunda ta bar gidansu Alhaji abubakar ya samu hajiya Aisha ya fada mata zai dawo da bakuwa gidan wacce ya dauke ta matsayin ya ta kalleshi waye kenan Shahida matar da jafar zai aura ni zan waliyanci auren ta Nan fa ta Mike da masifa ba zai yiyu ba yadda naki jinin yarinyar nan ba zan iya zama da ita gida daya ba ba zan juri ganin ta ba ai wannan ma cin fuska NE yarinyar da jafar zai aura ba da son raina ba shine za a kawo tagidana haka ta dinga masifa Tana zagin shahida Kallo daya ya mata yasata shiga taitayin ta yace ba dogon mgn nake son ji ba ba kuma ra ayin ki nakeson ji ba na fada miki ne in har kin dauke ni mijin ki Wanda na isa dake to baza ki tsallake doka taba zan gane matsayina da isata a gunki in har na kawo shahida kika wulakanta ta Sannan ina son fada miki ban yadda ki kuntata mata ko mata wani kallon banza ko na kaskanci ba ina so ki mutunta ta ki daraja ta kamar yadda kike yiwa surayya Bai saurare taba ya fita ya samu masu aiki yasa suka gyara mata daki aka kawata shi da duk wani abu dazata bukata 💅🏻feenah baby👄 [25/07, 9:44 p.m.] Ha Inna: IGIYAR RAYUWA book 2 Peg 16 Hajiya Aisha ta shiga halin kunci da bacin rai sosai sai dai bata yi niyar tsallake dokar mijinta ba sbd irin son da take mishi tana mugun gudun zuciyarsa sannan Tana da biyayyar aure dan haka tayi niyar bin duk abin da yace sai dai ta kullaci shahida a zuciyarta tayi kuma niyar kuntata mata ko ba jima ko ba dade Shahida ta tattaro daga gidan ta zuwa gidan alhaji abubakar da Hajiya Aisha Wanda suka kasance iyayenta na gaskiya sai dai rashin sani kawai A kullum addu arta shine Allah ya Sada ta da iyayenta na asali kafin ta mutu Allah ya amshi addu arta sai dai bata San da hakan ba shi Allah ba yadda baya ikonsa Shahida tayi matukar mmkn yadda Hajiya Aisha ta karbeta cikin mutunci duk da tsanar da ta mata yadda taga an dauke ta a gidan yabata mmk yadda Hajiya Aisha ta karbeta ba za a taba tsammanin kawai tsana a tsakaninsu ba sai surayya da kishin shahida ya shiga zuciyarta ganin irin kyau da Allah yabata shahida akwai daukan hankali dole jafar yayi ta rawar Kai a kanta duk da shima ba baya ba amma shahida macece ta isa Ta tsinci kanta cikin sabuwar RAYUWA Mai tattare da jin dadi kwanciyar hankali data samu a wannan gida har yaso yasata manta iyayenta da ta rasa haka kawai ta dinga jin wani irin sukuni da nutsuwa na shigarta Cikin kayanta ta bude ta ciro hoton jabir Tana kallo nan taji hawaye ya ciko idonta tsananin kaunar shi da son ganin dan uwanta ya shigeta jabir zan iya manta kowa zan iya manta kaunar baba da su Ahmad zan jure rashin kowa amma banda Kai Dan uwa rashin ka na kona ni ba yadda zanyi aure baka sani ba idan har kina bukatar haka zan iya gayyatar shi daurin auren ki taji muryar jafar na tsaye a gaban ta bata MA San yaushe ya shigo ba ta daga Kai ta kalleshi yana mata murmushi yayi mata kyau sosai taji soyayyarshi ya shigeta tayi saurin sunkuyar da Kai sbd irin kallon da yake mata yana shiga jikinta Ya sunkuya gabanta na sha fada miki ban son ganin ki cikin damuwa zan gayyaci jabir bikin ki Kallon tambaya ta masa ya fahimci ta kar ki damu ba zai San auren ki bane zan gayyace shi aurena NE ba dai jabir kike son gani ba ta girgiza Mai Kai alamar Eh To zaki ganshi ko da shi bai ganki ba ke zaki ganshi yadda ranki keso Nagode jafar ta fada Tana murna wannan farin ciki daka bani ya min yawa ga soyayyar ka ga gatan iyaye daka bani gashi zaka sadani da Dan uwana ta fashe da kuka zan GA jabir yaushe zan ga zuwan wannan rana ranan da zan ga Dan uwana Rabin jikina Rabin rayuwata Yayi murmushin jin dadin gsninta cikin farin ciki yace nan da sati biyu Ta zaro ido me Kake nufi Baba yasa ranar auren mu Ta kalleshi bai kusa ba ni a waje na yayi Nisa MA in ke baki damu dani ba ni na damu dana kasance tare dake Wanda ba katanga a tsakaninmu in zauna dake in gani sosai in so ki iya son raina in kwana da ke in wuni dake ba cewa komai sbd Matata nake tare da ita shahida na matsu dana mallake ki ina gaggawan ganin ranar zan jiki a kusa dani Nan da nan tayi saurin sunkuyar da Kai sbd tsananin jin kunyar abin da yake fadi Hajiya Aisha ta shirya biki sosai sbd aikin dan tan NE duk da bata son matar ta gaza yin komai hakan yayiwa alhaji abubakar dadi ganin yadda take shirye ,,shiryen bikin kuma bata taba yiwa shahida ko da kallon banza ba wannan ya nuna tabi umarnin shi Kiranta yayi dakinshi ya nuna mata farin cikin shi Aisha Nagode da mutunta magana ta da kika yi hakan ya Kara miki mahimmancin da girma a wurina haka kin Kara samun matsayi a zuciyata taji dadin haka tace zan iya yin komai sbd Kai ko da kuwa bana so sbd son da nake maka da kuma biyayyar aure zanyi duk abin da kake so muddin bai sabawa Shari a ba yace Allah ya tabbatar mana da alkairi Aisha ni na tabbatar zaki fahimta duk da na kowa ne na tabbatar in yarki ce baxaki mata haka ba ka guji wulakanta Dan wani sbd baka san ina naka zai je ba baka san wani irin Hali RAYUWA zata jefa shi ba Tace ni dai na San inda zan sami haihuwa ba zan taba yar da abin da na Haifa ba bare ya wulakantu zan kasance tare da yata ko dana tsautsayi da kaddara ya taba sawa na rabu da yata amma da zan sake samun wata damar yata zataga so da gata Wannan itace damar ki ya fada yana kallon ta ki ke yiwa ya yan wasu adalci kila Allah ya dube ki da idon rahama yabaki haihuwa da kike so kamar zaki yi ya ya duk da kina manyanta Allah ba yadda baya ikonsa Mu dai mu bar mgnr nan alhaji yarinyar dai kasa na mata duk abin da ya kamata hatta surura da kayan karau duk na sai mata taci albarkacin ka da jafar Yayi murmushi to mungode nan ta fita Tana mita An daura auren jafar da shahida ranar asabar da misalin karfe 11 na safe ************************ 💅🏻Feenah baby👄 [25/07, 9:45 p.m.] Ha Inna: IGIYAR RAYUWA book 2 Peg 17 Andaura auren jafar da shahida ranar asabar da misalin karfe 11 na safe alhaji abubakar shiya bada auren shahida yayin da Kanin mahaifin jafar na asali yayi nashi anyi dauren aure cikin farin ciki da jin dadi musamman a wajen jafar da murmushi ya kasa barin fuskarsa sai dai fa ba haka yake a gun Hajiya Aisha da surayya ba dan kuka ta dinga yi kamar ranta zai fita har MA tace zata bar gidan tunda ta rasa jafar gidansu zata tafi da kyar Hajiya Aisha ta lallabata gami da mata alkawarin sai ta raba jafar da shahida ya aure ta sannan ta hakura Suna zaune shahida tayi sallama falon ta shigo tayi kwalliya tayi kyau sosai bakin Les NE a jikinta Mai ratsin ja abinka da farar Mace ta fito sosai tamkar ba wata Mace Mai kyau da ta saura a duniya sai dai Hajiya ta kalle ta zuciyarta ya buga sbd yadda shahida ta mata kwarjini taji kaunar ta na shiga zuciyarta bata San yaushe ta mata murmushi ba shahidan ta zauna a gefen kafarta a Kasan carpet yayin da Hajiya ke zaune a saman kujera tace Hajiya nazo muku sannu da gajiya da dawainiya Allah ya Kara arziki Allah ya rufa asiri Ta amsa ameen shahida Allah ya miki albarka ita kanta bata San yaushe ta fadi haka ba har matayi mmkn kanta yarinyar da ta tsana ita take sawa albarka a wani dalili wai me yasa meki Aisha Shigowar jafar ta katse mata tunani shima gai da mama yayi sannan ya cewa shahida tazo Tana da bako nan ta Mike tabi bayan Sa suka fita Hajiyar tabi su da harara tace ya auro karuwa har ta soma nuna mana halin nata na kissa da makirci sai na nuna mata iyakarta yanxu jafar kwata kwata bashi da lokacin kowa sai nata daga Shigowar ta ya biyo ta bakin cikin su yasa ko mutanen maiduguri na kasa gayyata idan an ce min yar WA ya aura Mai zan ce musu yarinya Mai zamqn kanta yar duniya wannan Abu yana bata min rai Surayya tace amma mama Tana da kyau yarinyar kinga tunda ta shigo na kasa daga idona a kanta nima ce MA kenan inaga yaya jafar Anya zai iya rabuwa da ita Dole zan sa shi in ji Hajiya ba wai da baki ba da kanshi zai Kore ta ko ban ce mishi ba ke dai bani lkc zan nemi hanya da kuma damar rabasu A hanyar su ta fita a falon baki na waje jafar ya Kalli shahida yace wato dama duk ba kyan ki nake gani ba asalin kyanki yau ya dada bayyana a gare ni da kika yi kwalliya da shiga Mai kashe zuciya ita dai kanta a sunkuye yake Shahida please taho gare ni in jiki a jikina ko zan samu sukuni Kunys yasa ta kau da Kai tace jafar a waje fa muke gaskiya ni ba zan iya ba Ki taimake ni shahida zuciyata Tana matukar son kasancewa tare dake ya bude hannuwansa duk yace taho gani please da kyar ta iya Isa gare shi jikinta na rawa kamahin turarensu ya dinga ratsa ta ya jefa zuciyarta cikin wani yanayi Marar misaltuwa Haka ya dinga shige mata ganin yana shirin wuce gona da iri yasata saurin ja baya daga gare shi ya kalleta idon shi jawur cikin muryar shauki yace ina tsananin bukatar ki shahida ba don bakon da yazo gunki Mai mahimmanci bane ba zan iya kyale ki a yanzu ki je gunshi ki barni ba Waye? Ta tambaya Kanin ki jabir Ta kalleshi cikin doki tace shine muke tsaye tuntuni a nan baka fada min ba jabir ne fa Jabir dina zan ta tafi yayi saurin tare ta saurare ni shahida kiji yadda muka yi Ba zan iya ba jafar kayi hakuri ina tsananin son ganin dan uwana Na sani shahida jabir bai San kece Matata ba da farko dana fada masa yayi fushi yace ban cika alkawari ba na auri wata ban neme ki ba nuna masa iyayena NE suka matsa nayi aure baka dan ina so ba auren ba zai sa in fasa nemanki ba da kyar ya yadda zai zo daurin auren dan ke ba danni ba dan nace yazo ko don sbd dangantakar take tsananina da yar uwarsa wannan ne yasa yazo an daura aure dashi yana nesa kuma yayi Nisa cikin tunani bai San Waye sunan matar ba ko Waye ce ba har zai tafi na tsai da shi nace zan Kira masa Matata su gaisa A yanzu gare ki NE ko kije gabansa ko ki gansa daga nesa zabi na gare ki To babbar mgn Masu karatu tajene ko a, a nide nace,,,,,,,,,,,,,, Kufa 💅🏻FIGIYAR RAYUWA book 2 Page 18 Shiru tayi ta shiga rudani ya za ta yi can ta daure ta nufi falon ta window din falon ta lekashi nan ko ta hangoshi tuni taji zuciyarta tayi rauni ta dinga kuka sosai jabir dina Dan uwana ya zanyi in bayyana gare ka ko in ci gaba da boye kaina ?tayi murmushi jabir dina ka girma sosai ta Kare Mai kallo ya zama kato ya shiga sahun Manya ba yarinta a tare dashi sai zata shiga falon sai taji wani irin fargaba sai ta koma a wannan halin jafar yazo ya same ta ya jata yace zo mu shiga ?suka nufi falon tare da sauri taja da baya tayi ciki da gudu bazata iya bayyana a gaban dan uwanta ba haka ta dinga jin ta mishi laifi da baza ta iya fuskantar Sa ba Dole jafar ya masa karya cewa bata jin dadi sbd hidimar biki yayi masa gdy suka yi sallama Tana ji Tana gani jabir ya tafi ba tare da sun ga juna ba Haka jabir ya tafi zuciyarsa cike da tunanin ina yar uwarsa tabbas in taji lbrn auren jafar bazata ji dadi ba yaya shahidana duk Randa na same ki ba zan taba Bari ki San jafar yayi aure ba da wannan tunani ya shiga jirgi zuwa kaduna Shahida tayi kuka sosai jafar yayi ta kokarin lallashintq Wanda har yanzu ya kasa gane dalilin Tana boye kanta ya mata wannan tambayar ta amsa mishi da cewa ita kanta bata San dalili ba Alhaji abubakar yabasu gida na gani na fada a surullere shahida kam ba abin da bai mata ba na bukatar RAYUWA sai gdy tayi masa har ta gaji duk da ya nuna bai son gdy sbd Allah yayi ba dan a gode masa ba Nan yasa su gaba yayi ta musu fada da nasiha da ko wani uba na gari zai yiwa ya,yansa Hajiya MA dai ta tofa kadan duk da ba da son ranta tayi ba su jafar sun ji dadin haka wanda shi ya dauka maman ta hakura sbd ko a fuska bata nuna musu ba ************* ********** Kuyi hakuri da wannan in nasamu time zanyi typing Kutaya garinmu da addu a muna cikin tashin hankali sosai aby 👄IGIYAR RAYUWA book 2 Page 19 Rayuwar shahida da jafar ta cika da farin ciki Mara misaltuwa ko yaushe suna tare idan office NE tare suke zuwa su dawo haka tare suke aikin Wanda soyayyar da suke yafi aikin yawa sun zama abin kallo da kwatance gun sauran MA, aikata da mutane gaba daya A zahiri jafar baya ra ayin wannan aikin kwata kwata amma sbd matarsa shahida yake yi gashi an nemi daya koma aiki amma bai koma ba har yanzu bai kuma fadawa shahida ba sbd zata iya sa shi ya koma shi kuma bai son tafiya wani gari ya bar ta tare da tunde Mai aikin su suka koma Wanda shima musulmi NE yana matukar son uban dakin shi da uwar dakinshi Duk iya kokarin Hajiya bata samu hanyar raba su ba sbd ba hanyar akwai yadda da kauna a tsakaninsu babu damar shiga tsakani *watan July wata ce da shahida bazata taba mantawa dashi ba watan da ya sake juya farin cikin ta zuwa bakin ciki watan da ta dasa bakin ciki da kunci a Rayuwar ta ranar laraba shahida bata jin dadi bataje office ba jafar ne yace ta kwanta shi zai je ya dawo yanzu suje gun likita sunyi sallama cikin jin dadi da kaunar juna* Jafar yaje ya karasa wani aiki da shahidan ta Fara da wuri ya fito yana sauri a motarsa har ya hau kan titi da zai hadashi da surullere bai Ankara ba ya hango wata doguwa ta yiyo kanshi Wanda birkinta ya kubucewa direban kafin jafar MA yayi kokarin kaucewa ta hau kanshi Wanda abun bai yi kyau ba sbd hatsarin ba dadin gani Cikin kankanin lkc mutane suka je wajen ansamu an zakulo jafar da ransa sai dai duk jikinshi karaya ne ana ciro shi kuwa bai jima ba motar ta Kama da wuta jama a da dama wutar ta shafesu sbd tashi datayi bazata cikin gaggawa aka yi asibiti da jafar da sauran jama a akwai wani Wanda ya gane jafar shiyaba da address din gidansa Shahida na zaune Tana jiran shi bata ganshi ba ta Kira waya ko har ta gaji bai shiga ba har da fushin ta tana jin karar door bell ta tashi da sauri ta bude Wanda a zaton ta shine har da shirin yin masifar ta ya ki dawowa da wuri kawai sai taga police gaban ta ko ya mummunan faduwa Lfy ta tambaya bakinta na rawa Babban su ya kalleta Kiyi hakuri da abin dazamu fada dazu mijinki ya samu hatsari yana asibiti ana bukatar ki cikin gaggawa cikin harshen turanci yake mgnr Innalillahi WA, inna ilaihirraji un abin da ta dinga fadi kenan take taji cikinta ya kulle ta tsure ta dinga jin wani ruwa Mai dumi na zuba mata ta firgita ainun nan da nan ta gigice ta fita hayyacinta haka jikinta ya dinga Bari shahida ta shiga halin rudani ba ko Mai bata baki sai tunde kawai a gida ya bar abin da yake jin irin yadda take fadin Innalillahi WA, innailairraji un da karfi ya ISO wajen ya fahimci meke faruwa shima ya rude amma sai ya daure ya dinga ce mata ba sosai bane mdm karki damu oga bai ji ciwo sosai ba muje asibitin Tare suka tafi tunde NE yayi waya ya fadawa Hajiya itama a rude ta taho ita da surayya GA alhaji abubakar baya nan baya MA kasar gaba daya ya fita wani aiki waje Emergency suka nufa ganin halin da jafar yake ya Kara firgita ta da tsorota ta ta kasa isa wajen jini nes kawai ke fita a kafafunsa Wanda ba a jikinsa suke ba tsabar yadda suka kumbura suka karkace ko ta ina jini fita yake a jikinsa numfashinta taji yana shirin daukewa addu ar da take ta neme ta rasa ta ma manta me take sai jafar jafar kawai take Kira ku taimake ni jafar [05/08, 2:23 p.m.] ‪+234 808 183 2396‬: IGIYAR RAYUWA book 2‬‬ Page20 Hajiya ta gamawa jafar shirin komai na fita cikin kankanin lkc jafar na kwance ko tafiyar numfashinsa ba a gani shahida Tana zaune gabansa idontan nan sunyi ja sun kumbura kamar zasu fado tsabar kuka addu a take mishi tana tofa masa kadaici da kewarsa da tsantsan sonsa suka shigeta ta kwantar da Kai a gefensa hawaye kawai ke fita ba kakkutawa A wannan Hali Hajiya ta shigo ta same ta ta tausaya mata sai dai kun San Sharrin zuciya ta iya kitsawa mutum Abu daban daban Mai kyau da Mara kyau sai dai muyi addu ar fin karfin zuciyarmu Hajiya ta isa gare ta Sam ta kasa jure kallon ta sbd kaunarta da take ji da tausaya mata da take yi ta kau da Kai tace na gamawa jafar shirin komai zamu fita kasar India dashi amma fa banda ke Hajiya ki barni in kasance tare da mijina Dan Allah ki taimaka min Daina bata hawayenki dan ba zan saurare kiba lokaci yayi da zan raba ki da jafar matsayin yata surayya kika dauka Wanda yanzu zan kwace Shahida ta Mike gami da zurawa Hajiya ido tace me kike nufi Abin nufi a zahiri yake zan raba ki da jafar zan raba auren Ku soyayyar ku Shahida ta kalleta cikin mmk tace Hajiya a wannan lkc a wannan yanayi kike irin wannan mgnr jafar na kwance rai a hannun Allah kina mgnr raba aure mgnr son Kai da son zuciya Hajiyar ta Harare ta tace dama na samu bamu da lkc daga ni har ke har jafar zan fita dashi ne da sharadin zaki fita daga Rayuwarsu zaki yi abin da zai sa ya tsanaki soyayyar da yake miki tazo karshe idan ko kin ki jafar ba inda zai je zan barshi a wajen Kin San jafar ba dana bane zan aikata Shahida tace Allah ke RAYUWA kuma duk wannan abin da kike so ya faru zai faru ne in Allah ya rayashi Hajiya Meyasa kike haka ni in kin tsaneni ai jafar danki ne in jafar baki haifeshi ba MA na tabbata ke uwace in aka yiwa yarki haka zaki ji dadi in ni yarki ce zaki min haka Rufe min baki ki daina hadani dake ke ba ki Kai matsayin dazaki hada kanki Dani ba bamu da lkc zabi na gare ki Kin yadda ko a, a Ta kalleta ba yadda ta iya tace na yadda me kike so na miki Abin da jafar yafi tsana harka da maxa Ta zaro ido wani irin harka da maxa Ban ce kiyiba sai dai zaki yi karyar kina yi idan jafar ya farfado zan fada mishi abin da na ga dama kuma baxaki musa ba komai nace zaki yadda kinyi kinyi alkawari Tana kuka tace na yadda RAYUWAR shi da lafiyar shi tafi komai zan ta Mai addu ar alkairi da samun lfy tana ji Tana gani suka tafi da jafar fadar halin data shiga ba Mai yiwuwa bane kwata kwata tashin hankali da kunci da take ciki ba Mai yiwuwa bane Alhaji abubakar bai dawo Nigeria ba ya wuce Indian tashin hankalin rashin lfyr jafar bai Bari ya tambayi ina shahida take ba *haka rayuwar shahida ta sake canjawa bakin ciki ko da ina kewaye da ita duk halin da take ciki tunde yana sane sai dai mgnr tafi karfin shi ba yadda ya iya* Allah da ikonsa jafar ya farfado ya soma dawowa hayyacinsa tunda ya farfado yake tambayar ina shahida batada lfy yana so ya kaita asibiti 💅🏻Feenah baby 👄 IGIYAR RAYUWA book 2 Page21 Daga yafara surutan za a masa allurar bacci alhaji abubakar ya tambaye su ya basuzo da ita ba nan ta Mai karyan wai hankalin ta zai tashi in Tana ganin jafar cikin wannan Halin Shima jafar in daga baya karya da akai ta masa kenan haka Hajiya ta dage ko a waya ta hanashi mgn da shahida Wata 2 Masu kyau ya dauka yaji sauki sai dai baya tafiya sai a hankali zai koya ya fara sbd karaya da ya samu Wannan wata2 yafi shekara 2 a gun shahida Tana son jin lbrn jafar amma ba Hali Abu 1 ta iya tayi masa shine addu a Ranar da suka dawo doki a wajen jafar ba a mgn yana Allah Allah yaga shahidar sa gidansa suka wuce Kai tsaye amma sai me wayam ba shahida sai tunde ya tambaye shi ina shahida sai yayi Shiru na tsawon lkc idonshi ya kada kamar zai yi kuka tsabar jin bakin ciki da takaicin karyar da shahida tasa yayi yace bata zama. tunda ka tafi harka take da wasu maza ,,,,,,,,,,,,,,,,,, Kafin ya karasa yaji jafar ya wanke shi da wani wawan Mari sai da ya gigice ka iya bakin ka in na sake jin ka fadi mummunan kalma kan Matata zan kashe ka ka fita min daga gida kafin in sa a rufe ka A wani dalili in ji Hajiya Dan ya fadi gaskiya to Bari in fada maka tun kafin mu tafi shahida taga karayar ka tace bazata zauna da nakasashe ba haka taki binmu dole na barta daga baya ta tsiri fita Tana harkar banza da,,,,,,,,,,,, Ya isa mama ni na San shahida Tun kafin ku gaskiya Kiyi hakuri ban yadda ba Na maka karya kenan Ban ce ba amma na San akwai wani Abu shahidana ba haka take ba ban yadda ba *dole ka yadda jafar sbd wannan gaskiya ne* *ba zan iya rayuwa da gurgu ba yaji muryar shahida ya juya ya kalleta taci ado tayi kyau mmk yasa shi kasa mgn ta Kara matsowa gaban shi gaskiya jafar kayi hakuri zan iya rayuwa da kowa amma banda nakasashe zan iya hakuri da komai amma banda gurgu ina zan Kai nakasashe dan haka na fara* *kika Fara me? Harka da maxa? Ya fada cikin kunan rai* Ta juya Kai hawaye ya subuce mata girgiza Mai Kai tayi tace na riga da na San dadin namiji Kai kuma ka nakasa ya kake so nayi Ya ishe ki tsakanina dake *na sake ki saki 1* bani bake har abada ban taba sanin haka kike ba ban zaci zaki zama Mara kunya maras mutunci ba shahida ba zan yafe cutar da kika min ba da sauri ta zari gyalenta ta fita dama ta nemawa kanta wajen zama a wani gidan marayu a ikeja ta samu aiki a wajen na kula da marayu bata bata lkc ba ta nufi can da kayanta da takardunta su shahida an hadiye bakin ciki haka wataran zata zauna tayi ta ihu dan takaicin RAYUWA duk wani burin RAYUWA ya fita a ranta tana Rayuwar ce kawai Lkcn guda komai ya canja a rayuwar jafar da shahida jafar ya shiga halin tashin hankali da kunci musamman yadda shahidan ta kasa fita a ransa ya zamana kamar Kara Mai son ta ake a ransa ga ciwo da ya Hana shi tafiya sai dai yaci buri sai ya dage ya dawo da kafarshi ya koma aikinshi zai nunawa shahidan shi ba nakasashe bane zai nuna mata shi namiji ne jarumi soja ba nakasashe ba Watan su biyu da rabuwa shahida ta fahimci tana da ciki ga koshi GA kwanan yunwa ta rasa me zatayi farin ciki ko bakin cikin haka taci gaba da rainon cikin cikin tsoro da tunanin ya Rayuwar abin da zata Haifa zai kasance dama ita kam ta Saba da wahalar RAYUWA to yazatayi da abin da zata Haifa Anya ta bar shi cikin wahala Nan ta shiga neman wani aiki ba ji ba gani bata karaya tayi sa a ta samu a wani gidan radio tana daukan albashin farko ta nemi gidan haya ta koma kafin ta haihu haka rayuwarta ta ci gaba da tafiya cikin garari da kunci har ta haihu da namiji Mai Kama da ubansa tamkar jafar yayi kakin shi da kanta ta Mai huduba tana kuka tasa Mai sunan dan uwanta jabir haihuwar jabir ya sake canja Rayuwarta yaron yasa mata tsammani haka ya debe mata kewa ya kawo farin ciki ko da kadan ne Rayuwar ta ta riga da ta Saba da wannan RAYUWA haka ta raine shi da dadi da ba dadi cikin wahala da sauki har Allah ya raya shi haka Allah ya dinga buda mata ta samu daukaka a gun aikinta mutane da dama da muryarta suke karyawa da safe suna tsananin son shirinta Mai kayatarwa akan rayuwar ya mace 💅🏻Feenah baby 👄Lkcn su mama suka iso itama ta shiga halin gigita sai dai bata Kai shahida ba ita tayi saurin sa hanu aka shiga dashi theater bata San ya akayi ta tsinci kanta da lallashin shahida ba sbd a cinyarta ta dora ta tana shafar ta tana ta fada mata maganganu Masu kwantar da hankali haka tayi ta kokari har ta dawo mata da nutsuwarta dukkan su suka dukufa da addu a suna Kai Kukan su gun ubangiji da fatan samun nasarar aikin da ake masa Kukan da shahida tayi tunda uwarta ta haifeta bata ta taba irinshi ba sai da fuskarta ta kumbura sintim har ba a gane ta Hajiya tayi mmk irin kaunar da shahida kema jafar dazata tashi kadai ke haukan sonta An fito da jafar daga as aiki da aka shiga dashi sai dai kash ba nasara sbd har wannan lkcn bai farfado ba likitoci daban daban sun gan shi amma ba nasara Dan haka suka bada shawara a fita dashi kasar waje kila a dace in kuma ba ayi haka cikin gaggawa ba komai na iya faruwa Wannan lbr ya Kara rikita shahida haka duk tabi ta rame ta lalace cikin kwanaki kadan duk tashin wannan hankali ya karar da ita mijin da take jishi kadai ne gatanta suppart dinta Wanda take so kamar rai yau Rayuwarsa na cikin garari lallai wannan abin tashin hankali ne sosai Nagode masoyana naji addu arku Allah yabar zumunci 💅🏻Feenah baby 👄[05/08, 1:32 p.m.] Ha Inna: IGIYAR RAYUWA book 2 Page 22 Tafiya take tana sauri sbd tayi lattin dauko jabir daga mkrnt tana shiga mkrnt akace mata ai principal na nemanta da saurin ta ta je A nan ta tarar da tashin wai jabir yayi fada da yar gwamna har yaji mata ciwo yarinyar Tana asibiti ta same shi zaune Yana ta kuka an Zane shi har sai da yamasa Shati nan da nan ta fashe da kuka hankalin ta ya tashi da sauri yazo gun maman yana ta kuka Jabir bana Hana ka fada ba! Mai ya hada ka fada da yar gwamna ka San ta yaya nayi na hada kudin makarantar nan na biya maka dan in cika maka burinka na Hana ka yawan zuciya da fada baki Kaga Mai ka jawo mu su Waye da za mu nemi fada da yar gwamna Yace mama ita tace min wai ni shegene bani da uba ban kula ta ba shine ta turo yara suna ta min ihu shine ni kuma na musu duka Da ka kyale su yanzu ban San me zai faru ba Kaga yadda suka buge ka. Yace mama dukan zafi basu da kirki suka bigeni da karfi Kayi hakuri dan mama Kai principal din NE ya Kirata yace ana nemanta a government hause kuma danta an koreshi a mkrnt kuma duk makarantar da za suje ba za a dauke shi ba Wayyo shahida taga bala i tare da security da jabir suka nufi gidan gwamna sun zauna yafi na awa 2 ga ishi ga yunwa jabir yayi ta kuka kafin akace gwamna yace ta shiga dan yace sai yaga uban dan da yasa aka taba shalelensa da yake so kaman ransa jikinta na rawa hankalin ta tashe ta shiga har kasa ta tugunna tana bashi hakuri ko juyowa bai yi ba bare ya saurareta alamar ranshi ya baci Kayi hakuri yallabai yaro yayi kuskure haka ba zai sake faruwa ba ka yafe mana tana mgnr tana kokarin rufe fuskarta sbd gudun kada ya gane ta Dan ita kam ta san shi sai dai ta jima da cire su a ranta in akwai Wanda yake ranta mutum 2 ne jabir kaninta sai danta Ya juyo ya daka musu wani tsawa daya girgiza ta ita kanta ba jabir ba da yasaki kuka dan tsoro Dan gidan uban Waye ne da zai taba yata ita da makarantar ubanta Dan ita na bude makarantar dan kar taje a takura mata a wani waje kunyi kuskure da baza ku taba sake yi ba da kuka taba min ya Waye ubansa *ba shi da uba ta fada kanta sunkuye* *shegene kenan* Ta girgiza kai Ya daka mata tsawa ki daga Kai ki min mgn Bata San yaushe ta dago kan ba tsabar firgita ga sojoji sun kewaye su da bindigogi jabir jikinshi sai Bari yake numfashin nasa MA kamar zai suma Tana daga Kai suka yi ido 2 har yanzu wannan razanannen kyan nata na nan Wanda yasa ta kasa fita a ransa ba Daren da zai kwanta bai yi mafarkin ta ba duk da ko tsawon shekarun da suka dauka basa tare major jafar Wanda a yanzu shine gwamnan Lego's yayi aure da surayya har da yarsu daya yar kimanin shekara 3 son ta bai goge tsanar daya mata ba zura mata ido yayi yana kallon ta Shahida ya kira sunan a ransa itama ta kirashi jafar a zuciyarta duk da ta sani shine gwamna bata taba tsammanin akwai ranar da zasu sake fuskantar juna ba nan ya tsume ya bata rai ya Kalli sojoji yace ku je ku rufe su har sai nace ku bude su Shahida ta dinga rokonsa Dan Allah kayi hakuri ba dan ni ba ba dan halina ba dan Allah dan dana ka rufa mana asiri ka bar mu ka mana komai amma kar ka rufe mu *kinyi asara a yawan iskancin naki har shege kika haiho naji bakin ciki da na taba auren mata irin ki zan kyale ki sbd wannan shegen dan naki ku tashi ku fita sai dai ki sani sai na kuntata rayuwar ki* Haka suka fita A gajiye a wahalce tuni zazzabi ya rufe jabir yana kuka yana Bari ta rasa inda zata yi dashi sai ta rungume shi suna kuka tare. Suna isa gida Tasha mmk har an watsar da kayansu waje an rufe gidan order ne na gwamna cikin kankanin lkc yasa aka Mai bincike a kanta bai taba tsammanin tana garin Lego's ba bai samu lbr AKan uban yaron ba an ce masa dai da yaron aka ganta amma bata da miji hakan ya Kara Tabbatar masa da dan nata shegene Major jafar ya kuntata rayuwar shahida ya Hana danta jabir a dauke shi ko wani makaranta haka ya Kore su a gidansu haka yasa aka Kore ta a gun aiki Kai shahida ta ga bala, in RAYUWA kunci da bakin ciki sai da ya kusa haukata ta haka suka dinga kwana a gindin gada wata ran gidan marayu nan MA a Kore su duniya tayi mata kunci Duk wannan Abu da jafar ya Mata dan ya rama abin da ta mishi bai taba samun farin ciki ba duk abin da yamata sai ya dawo ya dame shi sai yayi kamar zai tausaya mata sai ya tuna cin amana da ta masa sai ya fasa ya Kara tunzura GA sonta kamar zai kasheshi Wani yammaci sun fito suna yawo ita da jabir ga yunwa ga ishi da kyar ta samawa jabir abinci ba su Ankara ba suka ji karar mota ta tsaya a gaban su da karfi sai da suka tsorata jafar ne shi kadai ba Wanda zai taba tunanin gwamna ne ya bude motar yasa kafa ya take abincin jafar ya fashe da kuka Yace ba kince kafata ta nakasa ba! To yau zan take ki da nakasashishiyar kafata sai na take rayuwarki Ta kalleshi duk ta rame ta kode tace jafar ban taba tsammanin zaka zama Mara imani haka ba Wllh sai Allah ya saka mana in wani Abu ya samu dana ba zan yafe maka ba na hada ka da Allah ya saka mana abin daka mana in abin da kake mana yana saka farin ciki kaci gaba Mgnr ki bazatasa na fasa abin da nayi niya ba alkawari nayi sai na cusa bakin ciki a Rayuwar ki kamar yadda kika cusa min na tsane ki shahida na tsane ki sai nasa kin bar garin nan da kafa 😳 Ai Kai ba Allah bane Allah Mai rahama ne a duk lkcn da kofofi suka rufe tashi a bude take shi zai San yadda zai yi damu ni da dana kuma kaima ba tabbata zakayi akan mulkin ba Kafin Kai dubu sunyi ina suke? Yau duk sun tafi ga mahaliccin su mutun daga shi sai halinshi Dan haka kayi a hankali kar giyar mulki ta rinjaye ka ka dauka Kai wani Abu ne Kai ba komai bane baka da imani jafar tunda baka kyale karamin yaro ba ban taba zata tsana zai sa ka dawo mara imani ba akwai wani lkc da ka taba yi min Allah ya isa yau zan mayar maka Allah ya isanmu sai munyi Shari a da Kai a gaban mahaliccin mu Nan ta juya ta dauki jabir Tana kuka suka barshi a wajen tafiya kawai take ita kanta ba ta san inda zata ba jafar ya juya Ya tafi jiki a sanyaye yana tunanin maganganu ta Jabir ya Kalli shahida yace mama ruwa na dukan mu ina za muje ta fashe da kuka nima ban sani ba jabir yanzu a garin nan bamu da wajen da zamu buya kar ruwa ya bige mu haka za muyi ta yawo ruwa da iska da rana ya kama sauka a kanmu Allah na nan shi zai Kare mu Yasoma mata kuka mama sanyi mama ki rufe ni a jikin wani bene ta samu ta Labe tana kuka Wayyo RAYUWA nagaji da jan IGIYAR RAYUWA na ja na gaji yanzu ta soma Jana ban San ina zata kaini ba jabir ka yafe min na kasa baka kyakkawar RAYUWA Shiru taji jabir ta daga shi ina jabir baya motsi gaba daya ya sassake ta tashi a rude kamar mahaukaciya tana gudu wai zata asibiti *tafiya take kan titi kamar kuncacciya bata Ankara ba sai mota ta ji ya doke su dukan su sun zube kan titi jabir Ta dinga kiranshi Tun tana ganin mutane sama sama har ta daina* Da sauri ya fito daga bayan motar irin car haya din nan ne Shigowanshi garin Lego's kenan akan Wani business daya kawo shi yana wani tunanin bai Ankara ba yaji direbansa ya kade wasu da sauri ya nufi inda suke kwance mutane sun kewaye su ba karamin gigicewa yayi da ganin abin da idonsa ya gane masa ya ganta a inda bai taba tsammanin ba *ya shahid* Muje zuwa shin Waye wannan mutumi 💅🏻Feenah baby 👄 [05/08, 1:32 p.m.] Ha Inna: IGIYAR RAYUWA book 2 Page 23 Ya shahida! Ya fada a razane hankalinshi yayi mummunan tashi ban taba tsammanin zan hadu dake a cikin wannan Hali haka kika dawo yar uwa jabir ya gigice sai fadin yake kusa su a mota mu Kai su asibiti Cikin minti kalilan suka isa jabir gaba daya ya fita hayyacinshi hawaye ne kawai ke fita Mai farin ciki da bakin ciki sun hadu Mai lokaci guda yar uwarsa da ya tsani yaga ko da kwarzane a jikinta ita ya gani kwance cikin jini cikin mummunan yanayi tayi muguwar rama ta kode sosai Likitan NE ya fito yace mishi maman ta farfado taji ciwo a goshin ta mun yi dressing mun sa magani mun samata drip sbd ta galabaita sai dai tunda ta farfado tana kiran sunan jabir yaron kuma yana nan cikin matsananciyar rashin lfy dama kafin hatsarin nan ciwon sanyi ya shige shi tashin shi sai sa a amma muna kokarin mu *ina yar uwata ina yayata Kai ni gunta in ganta yaya shahidana ina take* Tare suka tafi da Likitan ya same ta zaune duk ta gigice sai fadin jabir ina jabir me ya same shi jabir!!!!!!!! Cikin nutsuwa ya matsa gabanta zuciyarshi na tsinkewa bazato ba tsammani taga jabir a gabanta ta zaro ido tana kallon shi yana kallon ta basu San dalili ba sai tsintar kansu suka yi suna kuka ta kasa mgn sai kuka ya matso suka yi daf da ita ya tsuguna yaya shahidana ina kika shiga ina kika tafi kinga yadda kika dawo tasa kuka jabir mutanen duniyan nan basu da kirki ko kadan duk kowa mugune in banda mugunta jabir dana dan karamin yaro A ka,,,,,,, a, ka ta kasa mgn kuka yaci karfinta Ya isa yaya shahida Kukan ya Kare dan uwanki yazo ya share miki hawaye ko Waye ya miki haka ya Mai da ki haka ba zan kyale shiba Waye ya wulakanta min yar uwa ba zan kyale shiba Jabir dana dana jabir ban gan shiba Danki ne wancan yaron? Ta girgiza Mai Kai kin yi aure yaya shahida Sunkuyar da Kai tayi tana sharan hawaye tace lbrn da tsawo da kuma yawa ban san wanne zan soma fada maka ba a yanzu tunanina hankalina zuciyata na tare da dana Dan yaya shahida zan je in gan shi inga ya dan yar uwata yake yaya shahida ni da danki WA kika fi so Hawaye ya zubo mata baka canja ba jabir har yanzu ba ka bar kishina ba Jabir ka San a duniya in akwai Wanda shahida ke son kafin kowa to dan uwa ne jabir dina jabir duk da nayi nisa da Kai na kuma so wasu sai dai ban taba son kowa fiye da Kai ba dan uwa In kina sona haka yar uwa me yasa kika yi nisa dani kika tafi kika barmu nayi fushi dake yar uwa meyasa baki tafi Dani ba Kalleni jabir ka San abin da Allah ya kaddara zai faru sai ya faru ba makawa kuma jabir wannan gidan ba nawa bane ba nan ba ma a fadin duniyan nan gaba daya shahida batada gida ba,,,,,,,,,,, Kar kice haka yaya shahida in akwai me gida kece gidan baba da komai nashi naki ne gidan jabir naki ne komai naki ne baba mama da kannena duk nabaki Jabir ba a ba da dangantaka da baki dangantaka Allah ke hada ta duk wani dangantaka da Dan Adam zai baka karyace dangantaka da Allah ya hada shine na gaskiya kamar *dangantakarmu* da Kai duk wani Wanda na hada dangantaka dashi sai da ya bata min Kai kadai ne kawai Wanda yake min kauna ta gaskiya ya kwantar da kanshi a gefen ta farin cikinshi a wannan lkc ba Mai kwatantuwa bane Likitane ya turo kofar tare da wasu nurses suna tura gadon ta jabir karami ke kwance a Kai ya farfado yana ta rigima shine aka kawo shi tare IGIYAR RAYUWA book 2 Page 24 Kar kayi haka jabir Bana So kasa kanka cikin matsalar nan ka bar su da Allah na nan haka rayuwa zata koyawa kowa hankali Na Bari shahida sai dai zamu bar garin nan a yau Karshen wahalar ki tazo ba zan sake Bari Kiyi nisa dani ba Ta kalleshi jabir ba zan koma gida ba Naji yaya shahida bazaki koma ba akwai gidana a maiduguri zaki iya zuwa can ki zauna kafin in San abin yi kin amince Murmushi tayi mishi Nagode dan uwa yasu baba ya jikin ahi Bazaki je ki gani da kanki ba ko shima ya miki laifi kamar mama Ta kalleshi mama MA bata min laifi ba Na sani fa yar uwa ta fada mana komai daga baya ita ta Kore ki sai dai ina tabbatar miki tayi dana sani yanzu haka Tana maiduguri taje neman lbrn mahaifiyarki Ta kalleshi jabir nima da ina da burin son ganin mahaifiyata amma yanzu bana bukatar kowa bana bukatar wata dangantaka bana son wani matsala jabir Kai kadai ka isheni duk Randa kayi aure kaima shi kenan ya kamata kayi aure jabir ka zama babban mutum wani ya ganka zai dauka kaina yaya ni kanwa wai yaushe zakayi aure! Yayi murmushi dama ke nake jira tunda kin dawo zanyi aure sai dai fa ba zanyi auren da zai rabani dake ba sbd dangantakata dake tafi komai ya Kalli jabir karami yace ko abokina dani da Kai da mama ya isa ko ya Mika Mai hannu suka tafa Shahida tace banda son Kai dan uwa Jabir ya kwashi su shahida zuwa maiduguri duk wani Abu da suke bukata ya musu har makaranta yasa jabir karami sannan yace zai iya wani tafiya na kwana 2 amma zai dawo a ko wani lkc jabir ya Kalli fuskar shahida wani irin bakin ciki ke cin shi in yaga irin rama da lalacewa datayi in ya tuna wahalar data sha tsanar jafar sai ta darsu babban abin dayafi bata masa daya boye mishi shahida na tare da shi kuma ita ya aura yasa yazo har daurin auren ya Hana shi ganin yar uwarsa Dan haka ya nufi Lego's duk da yanzu jafar nada karfin mulki a hannunsa ba zai Hana shi fuskantar Sa ba hawayen yar uwarsa ba zai tafi a banza ba Tunda jafar ya rabu da shahida maganganunta ke yawo a kunnansa Anya ya mata adalci kuwa abin daya mata Anya bai kuntata mata da yawa ba son ta da kishin ta ya saya manta dukkan wani halayyar Sa na kirki ya dinga kuntata mata meyasa ya kasa kyale ta meyasa ya kasa manta ta wannan tunani sun Hana shi sakat Tunde ne ya shigo da yake har wannan lkcn suna tare ganin abin yayi yawa yasa shi yanke shawarar ya fadawa ogansa gaskiya nan ko ya zayyanewa jafar komai iya abin da ya sani abin da mamansa tayi da komai nan fa hankalinshi yatashi zufa ta dinga tsatstsafo Mai ya rasa meke Mai dadi ga mama na maiduguri taje gida *wai meyasa na kasa fahimta na kasa ganewa cewa shahida bazata yi haka ba wani batan basira ne ya same ni Wayyo nayi babban laifi na kuntatawa macan da nake so fiye da raina na yanke mata hukunci cikin fushi ya zanyi in fuskance ki shahida ban San taya zan soma neman ki yafe min ba har yanzu ina hango tsananin fushi da bacin rai a idonki* To shin wannan yaron a ina Kika samo shi aure kika sake kuma yadda bincike ya nuna an ce ba, a ga mijinki ba ko yana wani wajen Kai shahida batada aure shin ya zanyi da wannan nauyin hakkin da na yaron nan da na dauka Kanshi ya dau zafi sosai har yaji office ya kasa zama da kan shi ya dauki mota yana zagayawa ko zai gansu ba inda bai shiga ba Amma bai gansu ba wannan Ya Kara masa tashin hankali 💅🏻Feenah baby 👄 Mike da sauri suka nufi wajen shi ya rungume ta yana kuka mama allura zafi Jabir ya matso ya rungume shi yace yanzu allura zata daina zafi tunda mama da uncle suna tare da kai Mama Waye wannan Ka tuna dan uwa da nake baka lbr Yace jabir din ki! Ta girgiza Mai Kai ya kalleshi yace Kai ne jabir din mamana! Kai kam baza ka mana fada kamar wancan uncle din ba zaka bamu gida mu kwanta kar ruwa ya bige mu! Bazaka Sa a Kore mu,,,,,,,, Ya isa jabir shahidan ta fada Jabir ya kalleta mayafaru shahida Ba wani Abu ya faru ba illa kaddara Likitan ya katse su ya musu bayani akan ciwon jabir dole a kula dashi sbd sanyi ya shige shi sai a kiyaye nan ya basu maganganu ya Kara da cewa za, a iya sallamar su bayan kwana biyu ****************************** *a hankali shahida ta bawa jabir lbrn Rayuwarta kaf Tun rabuwar ta da gida har zuwa Randa suka hadu ranshi kam yayi tsananin baci jafar da mahaifiyarsa ne suka wahalar min dake yaya shahida Ba zan yafe musu ba dan yana gwamna sai meye* Kar kayi haka jabir 💅🏻Feenah baby 👄 [08/08, 8:22 p.m.] Habi ba: IGIYAR RAYUWA book 2 Page25 Baban shi ne kadai zai iya taimaka Mai kuma shima yayi fushi da shi tun Randa yaji ya Kori shahida ya daina musu mgn daga shi har maman Karin yazo ya Auri surayya wai yayi auran huce haushi duniya ta Mai zafi haka ya zauna a office dinshi ya kama Kai ya kasa yin komai ya dankawa mataimakin shi komai A wannan hali jabir ya shigo ya same shi bai samu matsala ba wajen ganin shi sbd dama sun San yana yawan zuwa wajen shi yaja kujerar gabanshi ya zauna duk kunyar jabir ta rufe shi duk da bai San ya hadu da shahida ba Jabir yace ngd yaya jafar ka iya cika alkawari ka iya rikon amana abin da kama yar uwata ba zan taba mantawa dashi ba kunci daka jefa shahida ciki Allah sai yasaka mata kuma sai nasa ka fuskanci makamancin wannan kunci ba imani ba tsoron Allah ka hana su wajen zama ka dinga gaba da yar uwa ban zaci haka daga gare ka ba zan dau fansa ko ba yanzu ba tunda yanzu kana ga kana kan karagar mulki ne sai Randa ka sauka muka yi dai dai zan nuna maka matsayin ka zan nuna maka ba, a taba min yar uwa a kwana lfy Abu na Karshe shine yaron da ka kuntatawa ka barshi da ishi da yunwa ba dan kowa bane sai naka lkcn da kuka rabu tana da ciki dan haka danka ka wulakanta jininka *jafar da ke zaune Sai daya Mike tsabar kaduwa dana,,, dana da shahida,,,,,,, jinina ne,,,,,, jabir ka min duk abin da kake so but please ka Kai ni gun shahida* *basa bukatar ka ya fada cikin daga murya shahida bata bukatar namiji irin ka ko kusa da inda take bazaka je ba duk abin da mutum zai yi a Rayuwa ya dinga tunani gashi garin zuciya da son kuntatawa wata ka cuci dan ka jininka wai ya taba maka ya, kaje ka rike yar ni zan rike jinin yar uwata zan zamewa jabir uwa da uba ko yar uwa ba zan Bari ta sake wahala akan danka ba sai dai ni zan rike shi in masa gata sbd akwai jinin yar uwata a jikinshi* Nan ya Mike ya fita ba tare da ya saurari jafar ba ya bar shi zaune kanshi a daure ya yiwa kansa wannan kadai ya ishe shi bakin ciki ya rufe ido ya tuno abin da yama shahida da yaron wani irin bakin ciki ya turnike ya rasa inda zai sa kanshi dan bakin ciki mama meyasa kika min haka meyasa kika wargaza min RAYUWA kin rabani da Matata da dana kin sa nayi ta aikata ba dai dai ba nayi ta cutar yar mutane kin tabbatar min Da cewa ni ba danki bane sai dai nima zan tabbatar miki ke ba mamana bane ************************ Hajiya Aisha zaune cikin gidan su a bangaren mahaifiyarta taji wata murya ta mata sallama Wacce taji kamar ta sani ta Kalli matar da kyau gabanta ya yanke amne,,,, tana daga zaune bata San yaushe ta Mike ba tace amne Dama,,,,,,,,,, kina,,,,,,,,,, nan Ina nan Aisha na jima ina son neman ki amma zuciyata ta kasa sbd shakkar haduwa dake Aisha tace zauna mana abin daya wuce ya wuce Amne ta girgiza kai bai wuce ba Aisha na miki laifi babba yarki dana karba nace miki ta rasu ta girgiza kai bata rasu ba Tana nan da rai Me kike ce amne yata na da rai Aisha ta fada cikin zaro ido kina nufin karya kika min ina take wayece meye sunanta ya kammanin ta yake nuna min ita ina son ganin ta ta fada cikin doki da hawaye meyasa kika min haka meyasa kika rabani da farin cikina haba amne kin San yadda naso yar nan kamar zan mutu kuma har yau Allah bai sake ban haihuwa ba ina masifar jarabar son ya, ya, kamar zan mutu na nema har na gaji na hakura ban sani ba Ashe ina da ya, zan yiwa abubakar albishir yarmu na raye Muma muna da ya, ba za a ce mana bama haihuwa ba ina take,,,,,,, Hajiya amne ta rude ganin yadda Aisha ta haukace da jin lbrn yarta ta haukace da farin ciki in tace ta bata me zai biyo baya sai dai ko yaya ne zan fada mata ta Kalli Aishan data zura mata ido tana son jin lbrn yarta tace ki yafe min yarki ta bata Ta Mike ta cakwamo rigarta baki isa ba amne karmaki Fara zaki nemo yata ki bani in ba haka ba yau komai na iya faruwa Ko yazaki yi ba zan iya baki yarki ba nima neman ta nake na miki laifi naci amanar ki nina Kore ta da kaina nace ta bar gida ta tafi sai bayan tafiyar ta na gani kuskure na na gane cewa ba jabir da mahaifinsa kadai ke son taba nima ina son ta ina kaunar ta. Aisha ta fashe da kuka zan nemo yata duk inda ta shiga zan nemo ta a fadin duniyar nan Amne tace abin da ya kawo ni kenan mu hadu mu neme ta in baki yarki in baki amanar ki na San ba zan baki shahida ba a yanzu amma ga hotonta ta zaro a jaka Aisha tasa hannu ta karba cikin doki ta Kai idonta da sauri kan hoton don ganin gudan jininta ta sake baki da hanci tana sauke numfashi da sauri da sauri kamar Wacce tayi tsere tsabar bugawa da zuciyarta keyi ta matukar kaduwa da ginin hoton shahida bakinta na Bari ta Kalli amne tace kina nufin shahida yata ce. Ta girgiza mata Kai kwarai kuwa a ina kika San ta Jikin ta ya hau rawa shahida yata shahida yata kika ce Wacce na Haifa Innalillahi WA innailairraji un ta fada tare da rufe ido tana tuno irin mugunta da sharri da makirci tsana da ta dinga mata Wayyo Allah na,,,,,, ta fashe da kuka son yarta da kaunar ya dabaibaye mata zuciya tsananin dana sani ya shigeta ta yi mugun gigicewa hawaye kamar an balle fanfo sai maimaitawa take shahida yata Wayyo Allah na *wannan shi ake kira dara taci gida* ******* ********* ******* 💅🏻Feenah baby 👄 [09/08, 3:40 p.m.] Habi ba: IGIYAR RAYUWA book 2 Page26 Shahida da jabir karami suna homework jabir yayi sallama ya shigo hannunshi cike da kayan wasa dana kwadayi da gudu jabir karami ya isa ya karba kayan yana tsalle suka baza jabir yana ta nuna mishi yana ta waina mishi mota su jirgin sama dan ya siyo masa na wasa Shahida zaune Tana kallonsu sai da ya gama ya taso ya iso gare ta tace baka gajiya Jabir kayan wasa sun masa yawa Yace kyale shi ni da dana ba batun gajiya kin San kaunar da nake ma mamansa ya shafe shi Tayi murmushi Dan uwa baka gajiya da sona I believe a duniya ba zan taba samun Mai sona da kaunata irin ka ba jabir a yanzu in akwai Wanda na yadda da shi bana shakkun kaunarsa to Kai ne dan uwa na tabbatar in ina tare da kai ba zan taba bakin ciki ba duk da an ce RAYUWA na tafiya tare da bakin ciki da farin ciki to ni dai na San ba zan yi bakin ciki tare da kai ba Ya kafa mata idanu yace kin yadda da haka yar uwa Kwarai In fadi wani Abu Ina jin ka Ya kalleta sosai yace yar uwa Mai zai Hana mu canja dangantakarmu Ban fahimce ka ba Sai da ya danyi Shiru sannan yace ina nufin mu bar dangantakar yaya da kani Tayi murmushi kana nufin Kai ka dawo yaya ni in zama kanwa? Dan kawai ka ga ka zama kato kafi ni tsayi da girman jiki kar ka manta shekara bakwai nake baka Ya zura mata ido yace ba haka nake nufi ba yar uwa mu canja dangantakarmu mu bar wancan nada mu zama abokai ko ya ya To ai dama mu abokai ne me Kake fada jabir ni ban gane kan maganganun ka Saurare ni yar uwa ya juya mata baya ina so dangantakarmu ta koma na aure ina son ki yar uwa ina son auren ki ni kadai ne namijin da zai iya saki farin ciki zan nesanta ki da duk wani bacin rai na RAYUWA za mu rayu cikin farin ciki ni dake da jabir karami yar uwa a tun Randa na fahimci ba abin da ya hadamu Tun a wannan ranar (feelings) dina gare ki ya canja soyayya kauna ta gare ki komai ya canja na kasa son ko wace Mace a rayuwata sai yar uwata yaya shahidana ya juyo yana fadin yar uwa ki au,,,,,,,,, Ya kasa karasawa sbd tsabar kaduwa firgita rudani da tsantsan tashin hankali da ya shiga sanadiyar ganin halin da yar uwarsa ta shiga sbd kalaman da ya furta mata a yanzu *alhamdulillah* Muje ga littafi na karshe dan jin yadda zata kasance ina sauraron ra, ayin ku da shswarwarin ku shin laifi ne in jabir ya auri yar uwarsa shahida dan ta girme masa da shekara kusan 7 A wani Hali jafar zai kasance shin zai yi nasarar dawo da matar sa da dansa Ya dangantakar shahida da dan uwanta jabir zai kasance shin zata yadda da auren Sa ko a, a Yaya haduwar shahida da mahaifiyarta Hajiya Aisha zai kasance Wani mataki zata dauka akan danganta kawaye da ita na iyayenta na asali da iyayen da kuma dangantakar ta tsakanina jafar da jabir *duk amsoshin suna IGIYAR RAYUWA na karshe* Ina sauraron ra ayin ku 💅🏻Feenah baby 👄 08109204012

Share this


Author: verified_user

0 Comments: