Sunday, 11 November 2018




TATTAUNAWA TSAKANIN MUHIVERT INDIA TARE DA HALIMA ABDULLAHI SHU'AIB

Home TATTAUNAWA TSAKANIN MUHIVERT INDIA TARE DA HALIMA ABDULLAHI SHU'AIB
*🥀📚ER INDIA NOVELS GRP📚✍🏻🥀*

           _Ke Gabatar Muku Da Shirin_
                                   👇🏻
  *📖DUNIYAR MAKARANTA DA MARUBUTA📝*
                             📚✍🏻📚✍🏻📚✍🏻📚
                                    📚✍🏻📚✍🏻📚
                                            📚✍🏻📚
                                                 📚



TARE DA::::::::::::::::::::_________✍🏻
*Muhievert India Er India/Er Luv*

```Kamar koda yaushe Shiri ne da yake zak'ulo muku makaranta littattafan Hausa (Hausa Novels) har ma da marubuta litattafan Hausan kansu dan jin ta bakinsu game da abinda ya shafi karatun ko kuma rubutun, A yau ma wannan gida ya zak'ulo muku wata shahararriyar marubuciya dan jin ta bakinta ga kuma yadda hirar ta kasance:```
*BAK'UWAR MU TA YAU👉🏻MARUBUCIYAR LITTAFIN AUREN JINSI*
_______________________________


         *Ya sunan Malamar?*
_ASALAMU ALAIKUM YAN UWANA BARKANKU DA WANNAN LOKACIN_
  _"to masu karatu cikkaken suna na 💥Haleemah Abdullah shu'aib💥 know as 🌟ummu Basmah in Facebook in WhatsApp am using H. @. S wannan shine sunan da aka fi sanina dashi a WhatsApp._

             *Da kyau! Masu karatu zasu so suji d'an tak'aitac-cen tarihinki*
_Dafarko ni Dai an haifini ne acikin garin jos north babban birnin Plateau state a wata anguwa da ake Kira da (anguwan rogo) nayi primary school a government school, sannan nayi secondary a private school dake shagari corner, nagama 2011 - May-25th sannan nayi diploma in computer school, da kuma diploma in Islamic education duk a garin jos, yanzu haka nasamu admission ta hanyar DE, 200 level university of jos insha Allah wannan shine Dan abunda muka taba acikin karatu Amma kuma dora daga inda muka tsaya Allah yabamu illim me albarka_

          *Masha'Allah.. Toh! Bari mu tsunduma cikin shirin gadan-gadan, Shin me ya ja hankalinki ko nace meya baki sha'awa har kika fad'a harkar rubuce-rubuce??*
_A gaskiya na kasance d'aya daga cikin mallaman makaranta, a hasashen danayi, Sai na duba Naga cewa ba inda yafi saurin isar da sako irin hanyar littafi, duba da yanzu an samu cigaba sosai Wanda Bai iya rubutu da karatu ba ma zai iya samun sauraren littafi, ta hanyar wayar hannu, shine nayi dubi da wannan hanyar nafara rubutu Wanda nafara rubutu ne ba Wai kamar novel ba_

            *Ko zaki iya fad'awa masu karatu irin gwagwarmayar da kika sha a lokacin da kika fara rubutu?*
_Sosai akwai gwagwarmaya Dan nafara rubutu a wall dina Facebook, tun ina yi ban samu masu karantawa Har nafara samun liking, nakan Dan yi short story misali "UWAR MIJI" da sauran su Ina school lokacin SS ONE Sai nafara rubuta wani littafi Wai bacewar Auwal, Sai nazama abin dariya agun classmate dina, Amma Bayan nagama nasamu wata mallamar mu nake nuna mata, Sai ta karbi rubutun ban sake Jin labarin rubutun ba Sai danaje SS two, Sai malamar ta kira ni, take tambaya na meyasa na zabi rubutu, to a wannan lokacin banda dalili, Amma ta jinjina mun bisa kokarin danayi da kuma irin errors dana samu kinji kadan kenan_

          *Da kyau! Zaki kamar shekara nawa kina rubutu?*
_Wanda na fara a online Bai Dade ba domin 1st January 2017 Kinga Bai Kai shekara ba, Amma indai tun Wanda nafara misalai dashi ne to yanzu zai Kai 5 years_

         *Hakane, wanne Littafi kika fara rubutawa?*
_BASMAH_

         *Wanne irin gwagwarmaya kika sha lokacin da kina rubuta wannan littafi ko kuwa baki sha wata wahala ba?*
_To gaskiya wahalar Dai Bata dayawa amm baza'a rasa ba ko yaya ne saboda koya ka dauko lbr zaka taba gwagwarmaya, saboda nayi shine akan yaran da ake haifan su "WITH A SILVER SPOON" Amma Alhamudillah tunda ya karbu agun masoya_

         *Masha'Allah! Naso daman na tambayeki shin me littafin yake qunshe da shi ya kuma karb'uwarsa ta kasance? toh Alhmdulillah muje ga tambayar gaba tunda kin bada amsarsu. Shin kin fuskanci wani k'alubale ga su makarantan kan shi wannan littafi?*
_Duk matsalar mu writer's iri d'aya ce tsakanin mu da readers, duk rashin hakuri ne ke sa readers ganin ba'a kyauta musu, ko suga Ana musu wulakanci to duk in mukayi hakuri Sai komi yawuce_

        *Idan na fuskance ki kina so kice kin samu 'yan wasu k'orafe-k'orafe kenan daga wajen makaranta a lokacin?*
_Sosai domin wannan ne lokacin na farko Dana fara long typing a watsapp, kuma abun akwai wuya to da zarar readers sun ji shiru zasu fara korafi_

          *Nawa ne adadin littattafan da kika rubuta?*
_Na rubuta littafi biyu yanzu Ina Kan na uku insha Allah_

          *Nasan masu karatu zasu so suji sunan su ko dan wa 'yanda basu karanta ba su nema su karanta shin ya sunayensu yake??*
_BASMAH_
 _AUREN JINSI_
    _YA'MACE_

               *Da kyau! Me Auren Jinsi yake k'unshe da shi kuma me yaja hankalinki har kika rubuta shi??*
_Duk Wanda yaji ance *AUREN JINSI* wani zai fahimta wani kuma Sai da bayani, to inda ance auren JINSI Ana nufi mace ta Auri mace ko namiji ya Auri namiji, sannan ya kunshi "lesbianism" Dan Akan shi ma yake bayani, da kuma yadda uwa ke neman Auren Yar cikin ta da kuma rikicin tsakanin ya da kanwa da kuma karshen su zai kasance kuma labarin ya tafi base on true life story ne wannan shine a taikace._

         *Lallai kice akwai chakwakiya... Bayan da kika fara rubuta shi wannan littafi na Auren Jinsi shin kin samu wani k'alubale daga wajen makaranta game da shi wannan littafi? Misali kamar abubuwan da kika rubuta ciki wasu suce hakan ba zaiyu ba ko makamantan haka??*
_Kai ai babban kalubale ma kuwa, Dan banyi Nisa da rubutun ba nafara cin Karo da matsala Wanda Ada zan ajiye rubutun ma gabadaya, saboda su yan lesbianism din su bibiyani Wanda suka dinga turo mun da sako Kala Kala ta Facebook, watsapp, Wattpad, Instagram da sauran su, Har kira na, Wanda sun nuna Hakan tonon silili a gare su, Amma dake Ina Shawara da mahaifiyata da wasu manya frnds dina su suka karfefe ni Har na idda rubutun_

               *Babbar magana... Lokacin da kika fuskanci hakan ya kika ji, kuma me ya baki tsoro har kika so ki ajjiye rubutun??*
_Gaskiya naji ba dad'i mutum Sai Allah, Sai wasu suke tunani ko Nima Yar less ce ta bakin su, so Abinda yafi bani tsoro shine Kar garin neman Gira a rasa ido, in zo suna na ya baci a banza, wannan shine abinda ya bani tsoro_

           *Wanne irin Nassarori kika samu game da shi wannan littafi na Auren Jinsi??*
_Akwai nasarori Dana samu a rubutuna na *AUREN JINSI* Wanda cikin ikon Allah littafi yasamu karbuwa agun mutane da dama, harda manya mutane kuma nasamu kyautuka da dama musamman wadanda ke cikin jaha ta wata Plateau da kuma jos, inda kuma account dina yayi nauyi Dan gaskiya baki na bazai gajiya wajen gode ma masoya, in fact Dai a taikace yanzu haka maganar Dana Miki akwai Wanda ya dauki nauyin buga wannan littafi na AUREN JINSI, a cewar sa yakamata littafi ya shiga kasuwa domin Bai kamata ace ya tsaya a iya online ba, saboda irin karantarwa da yake dauke dashi, reader's duk Wanda Bai karanta AUREN JINSI ba to ya nema, sannan a karshen littafin nasa comment na masoyana kusa three pages wannan shine a taikace_

            *Mu koma ga sabon littafin da kike rubutawa in na fad'a dai-dai shine 'Ya mace ko? Tunda naji kince littafin uku ne, shin me yake k'unshe da shi, wanne saqo kika isar a cikin littafin??*
_YA'MACE ya kunshi irin soyyaya da ehmatan zamani kewa samarin su ko nace soyyayar shan sweet, da kuma son zuciya da kuma rashin sanin me gobe zata haifar_

          *Ko akwai wata matsala da kike fuskanta lokacin rubuta wannan littafi ?*
_Har yanzu ban fuskanci matsalar komi ba tunda yanzu nafara, Sai Dai rashin comments Amma yanzu Kam littafi yafara wuta Ana comments ba laifi_

            *Masha'Allah! Toh! Ya batun kuma cikin gida ma'ana b'angaren iyayenki kan irin rubutun da kike na novels shin sun amince da hakan ko kuwa sun nuna b'acin ransu akan hakan? Kinsan wasu iyayen sukan tsanantawa yaransu kan irin wannan fanni da suka jefa kansu ciki, shin ke ya abin yake a b'angarenki?????*
_Wallahi ban fara rubutu ba Sai da shawarar mahaifiyata, Dan ni gaskiya ban iya yin komi batare da shawarar ta domin banda kamar ta a duniya, kuma yanzu duk irin Albarka ko cigaba danake samu to Albarka su ke Bina kuma Ina Jin dadi haka sosai da sosai, kuma akwai sisters dina Wanda muke the same blood dasu duk suna ganin irin rubutuna ba Abinda zan ce Alhamudillah_

            *Mu d'an dad'a komawa baya kad'an cikin littattafanki shin wanne littafi kika fi so kuma me yasa kike sonsa??*
_Duk cikin su Ina son ko wane, saboda ko wane daga cikin yana taba yau ne, Amma Basmah yafi shiga Raina saboda shine littafina na farko, kuma Ina ciki Yar shi duk Wanda ya ganshi ko yasan Wanda yake dashi ina 👏🏻 da a taimaka mun dashi Dan Allah_

        *Allah yasa toh! A ganshi, wacce marubuciya ce ko marubuci yake burgeki a salon rubutunsa kuma me yasa yake burgeki????*
_Gaskiya Haleemah k. Mashi na Burge ni, sosai saboda inda ka duba rubutun ta zaka samu duk ya shafi da ne da kuma gargajiyan ce, ko wasu al-adunmu na hausa, Sai kuma D Sulaiman, Sai online writers kuma a maman Shakur da marubuciyar Wayasan Gobe_

            *Mafi yawan marubuta sukan zamo d'aya daga cikin wata k'ungiya, Shin kema kina cikin wata k'ungiya ko kuwa har yanzu baki shiga ba???*
_Yes am in, Intelligent writers Association (onwards together)_


           *♡TAMBAYOYIN MASU KARATU♡*

*☎Sman:* ```zamu so muji wace shekara ta farq rubuta novels, kuma ya sunanasa, kuma miya ja hankalinta ko ya bata sha,awa har ta fara rubuta novels```

*📚Haleema:* _Na bada amsarta_

*☎Habeebah Pretty:* ```Tambaya ta itace tana d aure ko babu?```

*📚Haleema:* _Malama Haleemah Bata da Aure Amma ta kusa insha Allah_

                *Na samu saqonni daga wajen masu saurare da dama suna yi miki fatan alkhairi cikin wannan shiri*
_To Nima Ina musu fatan alkhairi kamar ko yaushe_

                     *Da fatan sunji, a gurguje wacce shawara ko saqo kike da shi ga su marubuta har ma da makaranta??*
_To masha Allah, shawarata ga yan uwana marubuta shine muji tsoron Allah sosai acikin dukan lamuran mu, indan Zaki yi rubutu kiyi akan abinda hankali zai iya dauka, kuma ki dinga sa Jan hankali acikin rubutun ki, kuma kar ki zama me batsa acikin littafi bawai Hakan ke sa littafi farin jini ba, shawarata ta karshe shine muy kokarin ganin mu zauna da readers lafiya batare da kin wulakanta kowa ba ko nuna girman Kai_
        _Readers kuma kuyi hakuri da marubuta domin kuwa ba'a son rai ake jingirta littafi ba, sannan mu dinga kiyyaye harshe akan kowa ma ba Wai Sai marubuta ba indan Baku readers ai ba writers Dan haka daku muke takama fans Allah yabarmu tare Amin_

              *Gaskiya ne! da fatan sunji kuma zasu fahimta, duba da lokaci nata hararar mu ko kina da wa 'yanda zaki gaisar?*
_Ni ta ko wace banda munafiki, ina gaishe da masoya duk inda suke a fadin duniya, sannan kuma Ina gashe da Ahalin wannan gidan *INTELLIGENT WRITERS ASSOCIATION IWA* onward together, especially you my editor sainah ummun meenal, sannan kuma jameesha kanwa, mumy zil Kuna da yawa. Maman Muhammad duk inda nake muna tare.Hanan Abuja ke ta daban ce ko cikin dubu. Mims queen kema ina yinki, marubuciyar kalar tawa uwar. Real me dambu kema kina Raina. Mrs mansor, ummu Maryam, mamu gee, zineet, khaleesat hydar, jeeda m Bello. Alhamudillah bazasu fadu ba amma Ina gaida ku All. My Abu Basmah am always thinking of you._

           *Me zaki ce game da shi wannan shiri na Duniyar Makaranta da Marubuta?*
_Gaskiya Alhamudillah, naji dadin wannan shirin kuma Ina Muku fatan alkhairi, musamman ke muheebat Yar India, Allah yasa ku fi haka Allah kuma yakara mana zumunci tun daga duniya Har gidan aljannah._



*_Amin, Muna godiya. Wannan ita ce k'arshen tattaunawar mu da Malama Halima H @ S duk da lokaci ya k'ure bamu gama jin ta bakinta ba, sai nace kuci gaba da kasancewa tare da ni Muhievert india Er india/Er luv/Er Mumcy/Dad/Er gata.lol duk wanda kuka kira ni da shi zan amsa.......... ku tara wani lokacin dan jin bak'uwar mu ko bak'on mu na gaba cikin dhirin.🙋🏻‍♀🙋🏻‍♀🙋🏻‍♀🙋🏻‍♀BIIIIIIIIIIIIIIIIIIIISLAM MAKARANTAAAA😘❤_*


{ 10 November 2018 }
{ 2: 43pm to 5:34pm }


*Er India Novels Grp📚✍🏻*


Share this


Author: verified_user

0 Comments: