TAMBAYA TA 22
Post By:
Hausa Novels
Tambaya Mabudin Ilimi
TAMBAYA ======== đ Asalamu alaikum mallam ya ayyuka ya sanyi ya fama da jama a ,Allah ya saka da mafificin alherinsa ,mallam yar uwatace take gidan Mijin ta take fama da mawuyacin hali mijinta yakasance yana bin mata sosai Wanda hakan yajawo ba ya iya kusantanta koh biyamata bukata kullum ba jituwa asakanin su kuma yaki yadena halinsa sabida tayi tayi ama INA ita kuma tanason zaman aurenta bataso ta fita ,yanxu yaje ya kara aure bada saninta ba kuma gashi hakan yanaso ya sanyata wani hali NA biyebiye mallamai bana sunah bah Dan Allah mallam ataimaka mana da shawara da adua akai AMSA ===== đ To xamu fahimci matsalar su ta fuskoki kamar haka. Maganar gaskiya wata matar bata gyara kanta, bata da Ni'ima, ko babu tsafta, kinga miji zai iya kauracewa mace ya kama iskanci a waje ko kuma wanna zaisa ya kara aure. Jiya Wani yake gaya min, yace da matarsa ta nemi magani, Sabida bata da Ni'ima, maimakon ta nemi magani, amma take masa hayaniya wai yafi son kishiyarta, ta dena masa magana. Wannan kadai zai iya sanyawa miji ya kauracewa matarsa. Sabida wata matar tana da karancin Ni'ima, kenan sai tana hadawa da magunguna da zasu kara mata Ni'ima, sannan kuma normally a irin wannan lokaci na sanyi Ni'ima tana daukewa mata, Sabida yanayin sanyin sa ake ciki, musamman ma wadanda suke yankin da ake yin sanyi sosai. Wata matar kuma, maganar gaskiya jahila ce a bangaren zamantakewa, da wannan ne yasa zakaga da yawa wasu Mazan, karuwa suna kwace musu mazansu na SUNNAH, Sabida Su sun iya yanga da kwalliya da da iya style a bangaren kwanciya da dai sauransu. Wata matar inba miji ne ya nemeta ba, ko kusa dashi ba zataji ba. Wata matar kuma, babu magana mai dadi sai wauta, kinga sai a hankali. Wata kuma ba kwalliya sai kazanta. Wani lokacin kuma, shi namijin ne shaidanin kansa, kowacce irin mace zai aura sai yayi iskanci, ba mamaki daman ya saba iskancinsa, kaga babu ranar denawa indai ba shiriya bace daga Allah tazo masa ba. Sabida haka ina kira da cewar ya kamata ake yawaita bincike akan namijin da za'a aura, Sabida akwai baragurbi irin wadannan. Sannan kuma ina kira da ake Kiyayewa, masu HIV sun yadu yanzu a doron duniya suna yadata yadda suka gadama. Jiyannnan ake gayamini anzo za'a daura auren wata yarinya, da akaje gwadon jini sai aka tabbatar tana da jinyar HIV, sai mahaifinta yace akwai kanwarta idan yana bukata, sai ango yace ya amince Indai ita yarinyar ta yarda, da aka gayawa kanwar tace ta yarda, sai wannan mai HIV din ta dakko kayanta tace wallahi ta shiga duniya, kuma ta dinga yada Wannan jinyar, kuma ko mutum bashi da kudi ma zata yarda ya sadu da ita Dan ma ya dauka. Kinga idan irin Wannan yarinyar taci karo da irin wannan mijin nata ae an sami matsala, itama matarsa sai abin ya shafe ta. Amma karta daga hankalin ta Dan yayi aure, inda Ace zina yakeyi anan ne xata daga hankalinta. Kawai ta dukufa wajen yimasa Addu'ah Allah ya shirya mata shi. Maganar bibiyar Malamai kuma, babu abinda zai amfana mata, babu abinda zai faru sai abinda Allah ya kaddara faruwarsa. Allah shine masani. ✍ ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876



0 Comments: