Friday, 6 April 2018




TAMBAYA TA 23

Home TAMBAYA TA 23
TAMBAYA ========= 👇 Assalamu alaikum mlm dafatan katashi lfy,mlm tambayata anan itace,menene hukuncin mutumin dayake amfani da layu da guraye a gidansa ko acikin motarsa domin kariya. AMSA ===== 👇 Shirka ne tsantsa. Nayi bayani a baya akan hakan, kuma tana daga cikin irin shirkar da idan mutum ya mutu yana yi wallahi ba abinda zai hana Allah ya sanyashi a wutar jahannama, Damin ita aka tanadarwa wadanda suka mutu suna shirka ga Allah. Dole ne mutun ya yarda da cewar Allah ne ke kashewa, shi ke rayawa, shi ke Kiyayewa, shi ke haddasa komi da komi a cikin rayuwar Dan Adam, Wanda shi Dan Adam din yake kwatanta Jin dadinta da rashin Jin dadin ta. Kenan idan Allah yaso kareka ba wanda ya isa ya cutar da kai, haka idan yaso wani abu ya sameka, babu mai kareka sai Allah din. Sabida haka ne ma Allah yace WAMAYYATAWAKKAL ALALLAH FAHUWA HASBU, wato duk wanda yayi tawakkali ga Allah, to Allah ya isar masa. Xai bashi kareshi. Allah shine masani. ✍ ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876

Share this


Author: verified_user

0 Comments: