Friday, 6 April 2018




TAMBAYA TA 31

Home TAMBAYA TA 31
TAMBAYA ======== 👇 Shin malam dalibi mai neman ilimi dawa ya kamata yayi abota. AMSA ===== 👇 Dole ne dalibi ya takaita abokai, duk da manzon Allah saw yace karkayi abota sai da mutum mai tsoron Allah. Sabida haka ka sami wanda yake kan irin tafarkin da kake kai, anan ne zaku karar da junanku, shi zai karu da kai, kai ma zaka karu dashi, zaka tuna masa, shima zai tuna Maka. Wanda baka gane ba zai ganarda kai, kaima wanda bai gane ba zaka ganar dashi. Amma idan kayi aboki da wanda yake shirme, to kaima zaka zama mashiririci, a haka kuma karatunka zai lalace. Allah shine masani. ✍ ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876

Share this


Author: verified_user

0 Comments: