Friday, 6 April 2018




TAMBAYA TA 32

Home TAMBAYA TA 32
TAMBAYA ========= 👇 Assalamu alaikum gafatta akwai littafin danake koyawa yan mata a makaranta,amma anzo bayani kan jinin haila da yanda ake wanka idan ya dauke nake jin kunya inyi musu bayani akai shin zan iya tsallakewa? AMSA ===== 👇 Idan ka dauke ilimin haila ga mata, kamar ka dauke musu Rabin ilimin da suke nema ne. A takaice ma dai shi ilimin haila ilimi ne na mata su kadai, tinda kaga namiji ba haila yakeyi ba, shiyasa duk hadisan da suke magana akan haila, zakaga matan manxon Allah saw ne da sauran mata suka rawaito, Sabida sune sahibul kissa a wannan fagen. Sannan duk kunyarka akaramukallahu manzon Allah saw ya fika kunya, amma dai a haka yake yiwa mata bayani, Sabida a addinin musulunci babu kunya idan Anyi tambaya ko a fagen karantarwa, domin wata bata sani ba, sai kaine zaka sanar da ita, kaga kenan ba kunya a ciki akaramukallahu. Wata mata tazo wurin manzon Allah saw tace dashi, idan mace taga irin abinda namiji ya gani, zatayi wanka? Sai manzon Allah saw yace zatayi wanka. Sabida bata sani ba, sai a lokacin ne ma ta sani. Ashe da manzon Allah saw ya barta bai bata amsa ba, zatayi ta zama ne a cikin rashin sani. Wani ma yazo wurin manzon Allah saw yace, idan namiji ya sadu da iyalinsa Akwai wanka a kansa? Sai manzon Allah saw yace dashi, Nima ina aikata haka, Ni da wannan sai kuma muyi wanka (sai manzon Allah saw ya nuna ummuna aisha). Kenan idan baka fito ka buda musu bayani ba, zaka barsu a cikin jahilci, kuma dalibanka ne, sannan bazasu taba ganewa ba. Allah shine masani. ✍ ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876

Share this


Author: verified_user

0 Comments: