Friday, 6 April 2018




TAMBAYA TA 27

Home TAMBAYA TA 27
TAMBAYA ======== 👇 Assalamu.alaikum ina neman shawara. ina da yar mace kuma Allah yayimin wadata. amma inada wani amini malami yanada da namiji yaturo.dansa yanemi aure yar ta amma batasonsa yadace dole na auramatashi nikuma nadauke nauyi komai narayursa amma I dan na aurar DA yar ta nasata acikin kuncin .rayuwa,meye mafita .? AMSA ===== 👇 Allah ya rufa Maka asiri da baka aura mata shi ba. Sabida idan ka aura mata shi, ko dai tayi Maka biyayya, ita kuma tana cikin takura da kuncin rayuwa, ko kuma ta jiya Maka baya ta kangare Maka a matsayin ka na ubanta, idan ka gaya mata magana ma tayi fachali da ita, Sabida tasan baka mata adalci ba, ko kuma tasa Ku bata kai da amininka, bayan kuna zaman lafiya a baya, yazo baya ganinka da mutunci shi da dansa. Sabida ba mamaki zasuke tunanin ko kana daurewa yarka gindi akan fushin da takeyi na kin amincewa da rashin nuna soyayyar shi a xuciyarta wannan wanda za'a bata, ko kuma ka tausaya Mata idan kaga halin da ta shiga, karshe kaga ma cewar raba auren shine maslaha, kazo Ka raba auren, kai kuma Ku bata dasu. Sabida haka auren dole gaskiya babu Alkairi a cikinsa, magana mafi gaskiya ka hakura, shine zaifi Maka Alkairi. Ka bata wanda take so, indai kun amintu dabi'unsa da addininsa. Allah shine masani. ✍ ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876

Share this


Author: verified_user

0 Comments: