Friday, 6 April 2018




TAMBAYA TA 3,167

Home TAMBAYA TA 3,167

*Asssalamu Alaikum*
.
.
*Tambaya ta 3,167:*
=
Game
da tambaya ta 3,161 mutanen da suke Sallar juma'a akan titi ya matsayin Sallar su?
=
=
Amsa
=
_Toh shi titi dai asalinsa ba masallaci bane wanen wucewar jama'a ne. Inkuma kukazo kuka tarewa mutane hanya dasunan kuna sallah to duk wanda ransa ya 6aci ko kuma bata masa lokaci kokuma kuka cutar dashi lallai kusani Allah zai saka mishi domin wannan ba wajen yin sallah bane wajen wucewa ne. Inkuma masallacinne bashida yalwa to yazama dole akanku ku sauya masallaci amma bazaku tarewa mutane hanyar wucewarsu da sunan kunayin sallah ba domin baku kadai kukeda hanyarba kilama akwai wadanda ba musulmaiba suma sunada iko da ita sannan kuma shi Musulinci anginashine akan wasu qa'idoji guda biyu; *LA DARRA WALA DIRARA* wato babu cuta ba cutarwa. sannan kuma *ADDARARU YUZAL* wato ita cuta kawarda ita akeyi. To sallarku da kukeyi akan titi kuna cutarda masu wucewa dan haka kenan yazama dole akanku kunemi wani waje domin a kauda wannan cutarwar da kukeyi*****_
      _Sannan kuma idan can cikin masallacin ko harabarsa bata cikaba amma kuka fito kuna sallah akan titi to bakuda sallah saboda Annabi (s.a.w) yace babu sallah ga wanda ya bangare bayan sahu dan haka dolene kukoma can cikin masallaci ku sadarda sahu duk wanda ya 6alle yabaro sahu be cikaba yadawo titi yana sallah to bashida wannan sallar batayiba inji Rasulullahi*****_
=
=
Allah Yasa mudace
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
*مجلس تعليم الكتاب والسنة*
📓📔
Watsaps
08036222795
09031200070
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook ta wannan hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
.
Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka wa atubu ilaika*Asssalamu Alaikum*
.
.
*Tambaya ta 3,168:*
=
Meye ma'anar suna Munif???
=
=
Amsa
=
_Toh Munif sunane wato Fa'iline ne Anafa, daga Anafa aka samo Munif shine Fa'il. Anafa kamar abu me tsawo ko me girma, to inkace Munif kenan me daraja ko madaukako ko me tsawo ko me kyau duk Munif yana daukar wadannan ma'anonin. Kamar dogon mutum me tsawo ko babban mutum me daraja ko Kyakkyawan mutum ana cemusu Munif a larabci. Kamar yadda kuma a hausa idan akaga mace ta cika wacce takeda tsawo da kyau da kamala se kaji ance mata Dirarra, kaji ance naga wata dirarrar mace, to sukuma laraba irin wannan suna kiranta Munifah, wato sunan munif dai a takaice kamar sunane dayake nuna kyau ko tsawo ko girma ko daraja, Allahu A'alam*****_
=
=
Allah Yasa mudace
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
*مجلس تعليم الكتاب والسنة*
📓📔
Watsaps
08036222795
09031200070
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook ta wannan hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
.
Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka wa atubu ilaika

Share this


Author: verified_user

0 Comments: