[24/05 9:21 PM] Mizz Ayuush: [3/18, 12:56] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
Da sunan Allah me rahama me jinkai, INA matukar farin ciki da Allah ya bani ikon fara rubuta wanan novel me suna gaskiya tafi kwabo, yanda na fara rubutawa lpya Allah ya bani ikon gamashi lpya,
1⃣➖5⃣
The youngest multi billionaire nan ne Ahamad sa'eed Ahamad sardauna, Wanda akewa lakabi da (ASAS) zaune cikin akwatin television na NTA suna hira dashi akan hanyoyin da zaa bi wajen kara bunkasa harkar kasuwanci a 9ja. Duk gdn daka duba sun nutsu suna sauraron program din, sbda tsanani son da jama'a suke mishi, wasu bama program din suke saurara ba, shi din kawai suke kallo sbda sbda tsananin temakonsa da son talakawa ne yasa duk jamaar arewacin 9ja suke sonshi.
Waye Ahamad (Asas)?
Ahamad sa'eed Ahamad sardauna(Asas) kyakkyawan matashi ne da shekarunsa ba zasu wuce 29yrs ba, kyakkyawa ne ajin farko, yanada sakin fuska kuma yana kaunar talaka, ya gaji dukiyarsa ne a wajen mahaifinsa marigayi sa'eed Ahamad sardauna. Shi kade ne a wajen iyayensa, civil engineering ya karnta a kasar Holland, mahaifin tsohon Dan kwangila ne da aka Dade ana bugawa dashi, ya Tara kudi masu yawan gaske yanada kamfanonin da ni kaina bansan yawan su ba, tun kafin mahaifinshi ya rasu ya Dora shi akan harkar business tun yanaki harya saba, sbda haka bayan dad dinsa ya rasu besha wahala wajen cigaba da kula da dukiyar da aka bar mishi ba. Yanada tsananin kyauta da tausayi, duk watan duniya akwai millions of naira dayake warewa sbda ya temaki talakawan da basu kudi, sanan akwai asibiti daya bude ya zuba maaikata ake kula da talakawa free of charges, sanan akwai makarantar daya bude a garin Birnin kudu jgwa state, ningi a bauchi state, da faskari a KTN state, da kuma kano. Sunan makarantar gifted and talented, yana sawa ya Debi 'yayan talakawan da suka gama primary, ayi musu exams duk Wanda yaci zaa bashi admission a daya daga cikin makarantun shi, duk yaron da Allah ya bawa SAA yana daukar nauyin kartunsa har zuwa university, ko college of nursing and midwifery, sanan idan sun gama yayi musu hanyar samun aiki. Dad dinsa ne ya bude makarantun, bayan ya rasu sai asas ya Dora akai. Zuwa yanzu sun yaye dalibai sunfi dubu a makarantita
Shekarar dad dinshi biyar kenan da rasuwa, tunda ya rasu mum dinsa take binshi akan yayi aure amma yaki, kullum sai yace mata be sami irin matar dayake so ba dataga bashi da niya saita yanke hukunci hada shi da yar aminin dad dinshi Sadiya, be taba jin yana sonta ba amma sbda tsananin biyayya dayake wa mum dinshi ya amince akayi auran, a farkon auran ba irin wulakancin da Sadiya bata gani ba, domin kuwa dakyar ya yarda suka hada shimfida da ita, kuma cikin ikon Allah daga wanan so dayan ta sami ciki. Tunda ya fuskanci tana dauke da gudan jinin shi ya dauki caring din duniya ya Dora mata, yanda kikasan kwai haka yake kula da ita, abin har mamaki yake bata. Yanzu haka cikin ta yakai wata Tara.
🏓🏓🏓🏓🏓🏓🏓
Cigaban labari
1 hour suka dauka suna tattaunawa dashi, bayan angama yayi musu sallama ya fito yana zuwa yaga body guards dinshi suka mike, da suri suka bude mishi kofa ya shiga mota, sanan suka tafi. Yaso biyawa ta gdn mum dinshi amma dake ya gaji kawai saiya wuce gdanshi dake UDB road.
Direct bed room dinshi ya wuce, INA zuwa yaga Sadiya tana kokarin shimfida sabon zanin gado da tulelen cikinta, da sauri ya ajiye jakar hannunsa yace me nake gani haka? Bana hanaki aiki ba? Cikin shagwaba tace wanan ai ba aiki bane, Dr fa yace na ringa motsa jikina, ki ringayi strolling amma ba aiki ba, karki karayin aikin komai a gdn kinji? Tace to, cire suit din jikin shi yayi ya karbi bed sheet din ya shimfida, kallonta yayi yace oya zoki kwanta tana kwanciya ya shiga toilet yayi wanka, phone dinsa ya dauka ya kira mum dinshi hlo mum barka da dare, barka Ahamad ya aiki? Alhamdulilla kiyi hakuri banzo nayi miki saida safe ba, wallahi yau agajiye nake ne shiyasa, ba komai Allah yayi maka albarka ya karemin kai, amin mum, saida safe Allah yalaimu ka gaishe da Sadiya OK zataji. Kallonta yayi yace mum tana gaishe ki, tace INA amsawa. Dining din falonshi yaje yaci abinci, yana gamawa yazo ya kwanta dake dama yayi sallar isha'i
Maman Aysha
[3/18, 14:30] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
5⃣➖1⃣0⃣
Wajen 4:30pm Asas na zaune a office yana signing a wasu files, kawai saiyaji kira a phone dinsa, sadiyace yana dauka yaji tana magana dakyar, da sauri ya fita ya tafi gda secretly ba Wanda yaga fitarshi, yana zuwa ya dauketa suka tafi standard Hosp na Dr galadanchi, cikin few minutes ta haifo kyakkyawan danta namiji, murna wajen Ahamad baa magana mum dinsa ya fara kira yayiwa albishir sanan ya kira iyayen Sadiya ma ya fada musu, don murna mum din sadiya harda rawa. Dake kalau ta haihu ana gama gyara su aka sallamesu zuwa gda.
Abinka da yan dangi kafin kace me mutane sun gama cika gdn anzo kallon jariri, da ranar suna ta zagayo aka rada mishi suna sa'eed amma ana kiranshi da sultan.
Tunda aka haifi sultan Ahamad ya tattare duk wani caring da so ya Dora akan shi, indai yana gda shiyake renon abinsa, sun shaku sosai da yaron aiki ma a dole yake tafiya ya bashi.
6month later
Mum din Sadiya ce ta kawo mata ziyara suna zaune a bed room dinta suna hira, mum tace ni meyake damunki ne kwana biyu? Naga duk daular nan da kike ciki kinki murmurewa? Ina zan murmure bayan hnklina ba a kwance yake ba, Yaya Ahamad baya sona ko kadan, Sbd ya nuna min kiyayya a fili, saida na fara amfani da maganin da kika karbomin a wajen boka ne ma ya fara saurarata, yanzun ma yana nunawa yana sona, amma na karya ne nasan duk ranar daya samu type dinshi zai juyamin baya, kuma wallahi duk ranar daya juyamin baya na shiga uku Sbd INA masifar sonshi. Shiru sukayi na Dan lkci sanan mum tace aikuwa daki shiga uku gara shi ya shiga, bangane ba? Ina nufin muyi saurin daukar mataki akanshi, ta yaya zamu dauki mataki akan shi? Shifa yanzu asiri ba kamashi yake ba, toba saimu kashe shi ba, Sadiya na zaune saida ta mike kisa fa kikace mum? Idan ya mutu ai nima na tashi aiki, kamata tayi tace zauna inaso ki nutsu ki saurare ni, mijin ki yanada kudin da harya mutu bazai taulaci ba indai ba wata kaddara ce tahau kan dukiyar ba, kuma kinga danki namiji ne, idan muka kashe shi duk dukiyarsa wajen danki zata dawo, sanan kema zaki samu tuminin takaba, kinga shikenan mun gama samun duniya, idan yaso saimu tafi kasar India ki samu wani kyakkyawan kmr mijinki ki aura tunda nasan shi dinma kyaun sa ne yake rudarki, idan kika aureshi dukiyar ki ce ba Wanda zaiyi miki wulakanci.
Dariya Sadiya tayi tace gud idea, saidai kashe Asas Abu ne me wahala domin kuwa duk Wanda zaa hada kai dasu ayi kisan yaransa ne, suna sonshi sbda kyauta ta musu dayake yi, suna jin dadin aiki a karkashin sa, banajin zasu amince da bukatar mu, kuma idan nayi poison dinsa a abinci da wuri zaa gane mu, sbda shi ba karamin mutun bane dole a tsananta bincike. To mezai hana ki hada baki da bakaniken daya amince dashi, eh to zan sami shi muyi mgna duk yanda ake ciki zan kiraki, tace to shikenan, sanan tayi mata sallama ta tafi
Maman Aysha
[3/18, 17:02] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
1⃣0⃣➖1⃣5⃣
Mum na tfya Sadiya ta kira ubale bakanike, bayan sun gaisa ta fada mishi dalilin kiransa da abinda takeso yayi Mata, cikin tsananin fargaba yace bazai iyaba. Ta tsorata amma saita dake zuciyata tace inaso ka sani duk duniya idan ka dauke mahaifiyar Ahamad nafi kowa kusanci dashi, kuma Kasan shi yanada saurin yadda mutun sanan duk a bakanikensa ba Wanda ya yarda dashi kmr kai, sbda haka dole kayimin aikin nan, idan kagama zan baka 5million idan kuma kaki zan nemo wani yayimin, kuma zan mayar da case din kanka. Sanan idan kana tunanin sanar dashi abinda nake kullawa to karka fara domin kuwa Kasan halin shi ya yarda dani 100%, bazai taba yarda dakai ba, Ahamad ko yaransa akace sunyi mishi Abu baya yadda ballantana ni matarsa kuma uwar danshi dayafi so a duniya. Sbda haka ya rage naka kaje kayi tunani, idan ka gama yanke decision ka kirani around 5pm sbda Kasan 6pm yake shigowa gda. Kuma yau nakeso ka kirani
Gumi sosai ubale ya hada, lalle mata basu da amana don rashin imani da son duniya kashe shi ma takeso ayi? Idan na amince mata ai na zama butulu, mutumin da yayi min hanyar arziki shi zanci amana? Miliyan biyar din banza, yana kashe waya ya nufi nagarta Nigerian company limited, yace ayi mishi magana da Asas, pa dinshi ne ya fito yace saidai ya dawo gobe sbda bashi a scheduled din yau, rokarshi yayi tayi har saida yaje ya fada mishi yace abarshi ya shiga. Bayan sun gaisa yayi mishi bayanin abinda ya kawo shi wajensa, cikin tsananin fushi yace how dare you zakazomin da wanan mgnar? Uban waye ya baka damar da zaka tareni da mgnar nan? A iya sanina matata ko kiyashi bazata iya kashe wa ba ballantana mutun, mutum din kuma ni! Kai bazai yiyyu ba. Wallahi yallabai da gaske nake, idan kuma baka yarda ba na kunna maka saida kaji, wacce saida ce? Recording da yayi lkcn duna waya ya kunna mishi, saida ya gama ji yace ban yarda ba, Sbd ba abinda computer bazata iya hadawa ba, ka fadamin me wife dina ta tsare maka da zakayi mata irin wanan sharrin? Ko kuma watace ta biyaka acikin masu sona? Talk to me mallam ubale, wallahi yallabai ba Wanda ya tro ni, duk abinda na fada maka gskya ne, amma idan baka yarda ba yau ka koma gda wajen 15 to 5pm, karka bari kowa yasan ka shiga gdn, ka labe a bayan dakinta zan kirata a waya zakaji komai a kunneka, idan aka sami akasin haka ka yarda na dauki mataki akanka? Cikin fargaba yace na Amince.
5:12pm
Yana labe a bayan dakinta yaji tana kora bayani kamr haka" yauwa mallam ubale ka amince ko? To kayiwa kanka gata abinda nakeso kayi shine zaiyi tafiya zuwa katagun daurin aure jibi , kuma Kasan a rule dinshi ko motor Kalau take yana sawa a kara Checking dinta idan zaiyi tafiya da ita, sbda haka nasan gobe dole zaisa a kawo maka motar, akwai poison din da nakeso na baka ka zuba acikin A/c din motar, Suna shaka zasu mutu dagashi har Mutanen cikin motar, idan driver ya mutu nasan kan mota zai kwace suyi accident, kaga shikenan kowa zaiyi tunanin accident sukayi suka mutu. Zan baka poison din idan kazo daukar motar gobe, sanan ka tromin da account no ka zan tro maka 2million yanzu, idan aiki ya kammala zan tro maka sauran.
Ji yayi kanshi ya fara sarawa, ya nemi yawun bakin shi ya rasa, besan lokcn daya zame ya zauna a kasa ba, mikewa yayi ya fice daga gdn ba tare da kowa ya ganshi ba.
Office ya koma ya kwanta yace duk Wanda yazo ace mishi bayanan, ubale ya kira yace naji komai ubale, inaso ka tura mata Acc no ba din, kuma idan ta baka poison din ka karba, godiya ga Allah ubale yayi yace to yallabai.
Maman Aysha
[3/19, 11:54] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
1⃣5⃣➖2⃣0⃣
Gabadaya kansa ya kulle, ya rasa abinda yake mishi dadi kansa banda ciwo ba abinda yake, duk tsanani baya taba wuce 6pm a office, amma yau har akayi sallar isha'i be tafi gda ba, kuma tun 6pm ya sallami maaikatan shi har pa yace ya tafi. Bayan yayi sallar isha'i saida yayi nafila raka'a hudu sanan yayi shafa'i da wutri yayi addua sosai, tunani ya shigayi akan wane irin laifi yayiwa Sadiya takeson halakashi, daya zuciyar ce tace tunda kanada kudi ai basai kayi lefi ba dukiyar ka takeso, wasu zafafan hawaye ne suka fara zuba a idonsa Allah sarki sultan bakayi dacen Uwa ba, Allah ka tsarkake min zuciyar sultan ka rabashi da sharrin zamani kuka sosai yake, phone dinsa ce ta fara kara yana dubawa yaga Maman sultan is calling.... Ji yayi gabanshi ya fadi, saida ya saita kansa sanan ya dauki wayar ta naji yayi picking tace hlo swit heart ya office din? Yace lpya kalau, tun 6pm muke zuba idonka nida yarona amma sainaji shiru, duk ya dameni da rigima kuma nasan kai yake nema, I hope you're fine? Yah am fine, I will be back very soon INA karasa wani aiki ne, tell my son dat I really miss him, OK I will.
Yana kashe wayar ya kara kifa kanshi akan table yaci gaba da kuka ya salm Sadiya wa yabaki shawarar ki kasheni don Allah? Meyasa kika biyewa son zuciya da rudin duniya? Toilet ya shiga ya wanke fuskarsa, sanan ya kama hanyar gda jiki ba kwari.
Lkcn daya koma sultan har yayi bacci zuba mishi ido yayi yana kallonsa zuciyarsa sai sake sake take, ita ta katse shi da cewa ya naga yau kmr you're not in d mood? Aiki nayi nagaji a office, wani irin bacci nakeji, ko takan abinci be bi ba ya tafi dakinsa yasa key ya kwanta sbda yanzu gabadaya tsoron ta yake.
Washe gari bayan ya gama shiryawa zai fita saida ta rakoshi har bakin mota, harya shiga mota ya fito ya mika mata key din motar da zaiyi tafiya da ita yace ubale zaizo ya dauki wanan motar da Allah, kinsan gobe ne daurin auren mas'ud, dariyar farin ciki tayi tace tafiyar tana nan kenan? Binta yayi da kallon mamaki yace insha Allah babu fashi, sanan yayi mata sallama ya nufi office.
Tunda yaje office be iya rike koda Biro ba, haka ya wuni cikin tunani da fargaba kafin lkcn tashinsa yayi ya nufi gdn mum dinsa. Sunyi waya da ubale ya tabbatar mishi da tura mishi kudin, sanan yayi recording din last maganar su data tambaye shi ko yayi abinda tasa shi. Yace to shikenan kaje ka ajiye motar zan neme ka anjima yace to. Kiran ta yayi yace tazo gdn mum, cikin fargaba tace lpy dai ko? Yace lpya bata jin dadi ne, subahanalla ganin zuwa. Dama dad din Sadiya ya fara Kira, sady taje befi da 10 minutes ba saiga su dad dinta a falon mum dinshi suka zauna bayan an gaisa ya kalli dad din sady da runannun idanuwansa yace addy dama sadiyace take son kasheni shiyasa na taraku anan sbda ta fadamin me natsare mata a rayuwa? Ya karasa mgnar yana kuka, Fatt fatt zuciyar Sadiya data mum dinta ta fara bugawa cikin gigicewa sady tace kisa kuma? Waya fada maka wanan maganar? Wallahi daddy sharri ake son kullamin, so ake a rabani dashi wallahi, dama akwai wata budurwar.......bata karasa ba Ahamad ya daka mata tsawa karki bata mana lkci dalla, inada cikakkiyar saida data tabbatar min da haka, wallahi daddy da kunnena naji ta, sanan ya basu lbarn yanda akayi, kuma a take ya kira ubale yazo ya nuna musu alert din da tayi mishi na mobile transfer na 2million din datayi mishi, bayan sun gama bada saida Asas ya karasa har inda take ya dauki dansa daga kan cinyarta, sanan ya bata takarda yace na sakeki saki uku, sanan ya kalli dad yace kasancewarta yarka shiyasa nabar case din a tsakanin mu, Amma wallahi badan haka ba da saina sa anyi mata daurin life in prison. Part dinsa na gdn ya shiga da danshi, kasa motsi dad da mum din Ahamad sukayi ita kuwa Sadiya zubewa tayi a kasa sumammiya.
Mum dinta ce tayi karfin halin zuba mata ruwa tana farfadowa ta fara kuka tana fadin mum kin cuceni, kin jefani a bala'i na shiga uku da haka suka tattara suka nufi gda.
A gda dad ya tsatsare ta tace mum ce ta bata shawara, nan take shima yayi mata saki uku. Haka suka koma kmr mahaukata washe gari sukayi asubancin tafiya wajen boka a birnin gwari akan hanya sukayi accident suka mutu. Inna lillahi wa inna ilaihir rajuun shine abinda Ahamad yake ta fadi a lkcn dayaji lbrn mutuwar su, sultan ya ringa tausayi shikenan ya zama maraya ba karamin kuka yayi ba. Tun daga ranar be koma gdnsa ba, kawai saiyaci gba da zama a gdn mum dinshi yake kula da sultan da kanshi.
Akwai wata yar yayar mum din Asas babansu daya, sunanta Surayya kyakkyawa ce ta Dade tana son Ahamad Amma shi besan tanayi ba shekarunta zasu kai 24yrs, ta gama degre a Abu zariya tana gda jiran result, lkcn da lbrn abinda ya sameshi yaje mata ba karamin tausaya mishi tayi ba, sai kawai ta yanke hukunci komawa gdnsu domin ta kula mishi da sultan, data fadawa mamanta ba karamin farin ciki tayi ba.
Surayya yarinya ce me kirki da son yara, tana da shiga rai sosai ita take kula da sultan idan kaga yanda take mishi saikace ita tahaife shi tun Ahamad yana basarwa har yazo ya fara appreciating
3months later
Ahamad ne zaune shida mum dinshi saiga sultan ya shigo da gudu dake yanzu ya fara tfya, Surayya ce ta biyo bayanshi tace au nan ka gudo, dariya tayi tace wanka fa nayi mishi kafin na dauko kayan shine ya fito dariya suka sa gabadaya su, Ahamad ne ya dauke shi yace sultan ka daina bawa aunty ka wahala kaji, mika mata shi yayi yace idan kin gama shirya shi kema ki shirya muje yawo, murmushi tayi tace to.
Haka rayuwa taci gaba Ahamad ba karamin jin dadin yadda Surayya take kula mishi da yaro yake ba, kudi yake kashe mata kmr banza duk lkcn da suka fita shopping
Yauma kmr kullum Asas suna cikin hira da mum tace ni kuwa Ahamad mezai hana ka auri yarinyar nan Surayya tunda tana son danka, kuma shima yaron ya shaku da ita, na tabbata zata rike maka shi amana. Shiru yayi na Dan wani lkci sanan yace problem din bata cikin kalar matar da nakeso, saidai na aureta sbda sultan, din, shan kunu mum tayi tace wai kai meyasa ka fiye tsurfa ne? Yarinya kyakkyawa amma kace batayi maka ba, dariya yayi yace ai ba iya Kyau kawai ake nema ba mum, akwai wasu qualities din. Yarinya daya ce take burgeni Husna yar gdn mallam bala me wankin hula, kinsan tanada addinin kullum acikin hijabi zaki ganta, wallahi yarinyar tana burgeni. Nidai idan zakaji shawarata Surayya nakeso ka aura, murmushi yayi yace to shikenan mum Allah yasa haka shi yafi alkairi yace amin
[3/19, 14:55] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
2⃣0⃣➖2⃣5⃣
2days later 9pm
Yana zaune yana aiki da laptop dinsa gefen sa sultan ne yake bacci Surayya tayi sallama ta shiga saidata Dan rusuna ta gaishe shi, sanan tace pampers zansa mishi, lallausan murmushin dayake kashe yamma ta dashi yayi mata yace bismilla a hnkli ya salm tace a zuciyar ta, wanan guy din na Neman kasheni da raina. Bayan ta gama samishi ta mike tace saida safe harta fara tafiya yace Surayya da husky voice dinshi tsayawa tayi cak tsigar jikinta banda tashi ba abinda take, mikewa yayi ya tari gabanta yace nagode da kulawar da kike nunawa yarona kin taimakeni a daidai lkcn da nake bukatar temako, nagode Allah ya saka da alkairi. Murmushin jin dadi tati tace karka damu yaya, ai nima sultan Dana ne murmushi ya karayi kmar daga sama taji yace Surayya zaki aureni? Ji tayi kmr yayi mata albishir da gdn aljanna, cikin farin cikin data kasa buyeshi tace why not? Banajin a duniya akwai matar da zata ki auranka, kai allura ne cikin ruwa dasai me tsananin rabone zai samu. Dariya yayi da har saida fararen hkornsa suka bayyana, sanan yace shikenan zanyiwa baba audu kanin mahaifina mgna, dagowa tayi ta kalleshi tace gud nyt, yace OK nyt. A Daren ranar Surayya batayi baccin kirki ba sbda murna, jin abin take kmr a mafarki.
Su baba abdu sunje Neman aure gdn su Surayya, kuma babanta ya amince, ansaka ranar biki nan da 1month, kuma tun daga ranar ta tattara ta koma gdnsu sbda a fara shirin biki.
1month later
Rana bata karya saidai uwar diya taji kunya, a yaune aka daura auran Surayya da Ahamad akan sa daki naira dubu Dari, a bangaran gdnsu ango bayan reception ba abinda akayi, gdnsu amarya ne ma suka sha bidir. A ranar da aka daura aure da daddare amarya ta tare ba yanda batayi ba abata sultan ta tare dashi a ranar amma mum taki tace idan sun gama amarci akai mata shi.
Saida ta cika sati guda da tarewa aka kai mata sultan murna a wajenta baa magana sbda dama Yaya Ahamad ya koma office sai ita da masu aiki a gdn, tunda sultan ya dawo saiya sata agaba yayi tamata surutu dake yanzu bakin shi ya bude sosai.
Rayuwa suke cikin jin dadi da kaunar juna Ahamad yana iya kokarin sa yaga ya kyauta ta mata duk da har yanzu beji yana sonta ba, amma bazaa taba ganewa ba. Lkcn da sultan ya cika 2yrs sai Ahamad yasa shi a sch wata day care ce mekyau kullum sha biyu yake zuwa dauko shi da kansa.
A kwana a tashi ba wuya a wajen Allah, sultan 3months kenan yana zuwa sch, tfya ce ta kama Ahamad ta sati daya zuwa kasar England lkcn da Surayya ta rakoshi zai tafi yace mata don Allah ki kula da dauko sultan daga sch lkci yanayi kisa a dauko shi, smiling tayi tace zan kiyaye insha Allah.
1 WK later
Yau ne ake saka ran dawowar Ahamad daga London, da wuri Surayya ta fara shirin tarar megida, tasa an gyara gda tayi girki saidai tunda driver daya tafi kai sultan makarnta har yanzu be dawo ba, kuma ta aikeshi ya sayo mata irin manyan mango din nan zata hada mango juice. Harta dauki waya zata kirashi saita ga 11:30, murmushi tayi tace may b jiran sultan ya zauna yi sbda warning din da nake wayan yi mishi, tunda sha biyun takusa bari na jirashi kawai. Har kusan 1:30pm ba musa ba sultan nan take ta rikice sbda yau Ahamad zai dawo, phone dinta taji ta fara kara tana dauka taji ance musa driver ne ranki ya Dade, musa ina sultan,? Kin ganni a asibiti yanzu na farfado wasu mutane sun dauke sultan akan hanyar mu ta tafiya makaranta, ni kuma sun harbeni a hannu, amma yan sanda sunga lkcn da abin ya faru su suka kawoni asibiti ma, cikin tsananin tashin hnkli tace yan sandan sun kamasu? Gaskya dakyar ne sbda akwai makamai a hannunsu, kuma motarsu tanada gudu sbuwa ce. Inna lillahi wa inna ilaihir rajuun kawai take fada, Nura pa ta kira tace yaje yayi reporting a station, zama tayi banda ihun kuka ba abinda take, batasan ta yaya zata tunkari Ahamad da wanan maganar ba. Phone dinta ce tayi kara tana dubawa taga Ahamad, hlo my dear kizo ki daukeni a air port yanzu na kira Nura pa wajen 10 missed call be dauka ba gunjin kukan ta yaji, my dear meya faru kk wanan kukan? Bashi lbrn abinda ya faru tayi nan take yaji yawun bakin shi ya Bushe, to kinga kiyi zaman ki kawai bari na kira imran abokina yazo ya daukeni. Yana kashe wayar kira ya shigo bakuwar no ce, yana dauka yaji ance yallabai commissioner of police ne, mun sami nasarar cafke wasu mutane tare da danka around 10am nayau, bayan azabtarwa da suka fuskanta a wajenmu, sun tabbatar mana cewa wife dinka da pa dinka ne suka sasu aikin, so muna jiranka yanzu a babbar head quarter. Mitsuka idonshi ya farayi kai gaskiya karyane how can dis happened? Ban yarda ba, Nura da Surayya bazasu taba cin amanata ba... daidai nan imran yazo yana zuwa suka wuce police station
Maman Aysha
[3/21, 17:27] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
2⃣5⃣➖3⃣0⃣
Wit respect commissioner of police ya tare su ko gaisa wa basuyi ba Ahamad yace Mr commissioner don Allah kacemin maganar daka fara fadamin dazu karyane, don Allah ka fadamin haka, taya zaayi Mutanen da suke kusanci dani suyimin haka? A hannunsu fa nabar amanar sultan, Nura pa na ne Dana amince dashi, Surayya kuma wife dina ce da take tsananin son sultan ta yaya za ayi suyi betraying dina? Ku kara tambayar Mutanen sosai, may b sharri ake son kulla musu. Commissioner ne yace take it easy Mr Ahamad, akan aikin mu meke, kuma bama yanke hukunci sai mun samu kwakkwaran shedu Amma by now your wife Surayya and Nura are d suspect but zamuci gaba da bincike, turawa yayi akazo da gidigo yace gidigo dama kai tsohon criminal ne, da gaske kake Nura da Surayya ne suka sakaka? Fuska duk a kumbure yace eh ranka ya dade idan baka yarda ba kuma inada saida sbda duk mutumin dazan yiwa aiki inasawa camera a wani waje sainace su sameni muyi magana a wajen sbda irin wanan ranar, domin kuwa akwai lkcn da wata mata ta taba sani aiki da aka kamani sai tace bata sanni ba ma, sabda haka nake saka camera. Yanzu kana nufin ka dauki video mgnar da kukayi dasu ranar da suka baka aikin? Asas ya tambaye shi, eh INA dashi, to ka fadi inda yake a dauko.
Police ne wajen guda ashirin suka tusa keyarsa sukaje suka dauko, aka kunna sukaga komai, Mr Ahamad kam be karasa gani ba ya sume a wajen sbda tsabar firgita. Saida aka yayyafa mishi ruwa sanan ya farfado, police guda hudu aka tura suka kamo Nura da Surayya, suna zuwa Surayya ta fara kukan makirci tana rantsuwa sharri akayi mata, wata mahaukaciyar tsawa ya daka mata sanan yace bayan mahaifiya ta b Mutanen Dana aminta dasu kmar Ku, Amma irin sakkayar da zaku min kenan ko? Surayya na sakeki saki biyu, kai kuma Nura daga yau karka kara nuna kasanni, sanan ya dauki sultan yace imran muje ko, yayiwa police din wajen kyautar kudi masu yawa ya tafi.
.
[3/29, 19:55] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
3⃣0⃣➖3⃣5⃣
Yana zuwa gda direct daki ya wuce, bacin rai ne fall zuciyar sa Mutanen dana amince dasu fiye da kowa sune sukaci amanata, anya zan kara amince wa da wani kuwa? Kanshi yaji ya fara juyawa kawai saiya dauki pills din bacci ya watsa ya kwanta ya fara bacci kmr macecce. Saida akayi kiran sallar magrib ya tashi bayan ya dawo daga masallaci ya sami mum da sultan zaune a falo shima zama yayi, mum tace ai tun dazu nake dubaka naga baccin baka yayi nisa. A INA aka samu sultan? Kuma ina Surayya? A nutse ya bata lbrn duk abinda ya faru, ba karamin girgirzata lbrn yayi ba, sanan tace Allah ya kara rufa asiri ya kara karewa yace amin. Amma don Allah inaso gobe kaje kayi belin su kuma inaso kayi hakuri ka manta da abinda sukayi ma, ka mika al amuranka a wajen ubangiji shi zaici gaba da kareka, a hnkli yace to shikenan mum. Tanajin dadin yadda yake mata biyayya, baya taba yimata musu.
Washe gari yaje police station yayi belin su, saidai be bari sun hadu ba yana bada kudi tafiya yayi sbda ko fuskarsu baya sha'awar gani. Surayya na fitowa gdsu kawatta Mardiya ta wuce ta bata lbrn duk abinda ya faru, Mardiya aminiyar Surayya ce, kuma ita ta bata shawarar suyi kidnapping din sultan. wata yar iskar dariya Mardiya tayi tace alhamdulilla burina ya cika inaso ki sani sbda na rabaku da Asas dama na baki muguwar shawara, kinfi kowa sanin irin sonda nake mishi, ko kin manta cewa gdnku naje ki bani shawarar yadda zanyi na mallake shi, amma sai kika zame kika aureshi sbda butulci irin naki. Tun daga lkcn nayi alkawari saina dauki fansa, shiyasa na nuna miki ban damu da abinda kikayi min ba, kuma na nuna miki ina sonki 100%. Kuka sosai Surayya take, tace Allah ya isa ban yafe miki ba.
A bangaran Asas kuwa tunda ya rabu da Surayya ya dauki kyamar duniya ya dorwa yan mata, shi yanzu ba wata budurwa da take burgeshi business dinshi kawai yasa a gaba, yan mata iri iri sai kawo Kansu suke kozai auresu, amma fur yaki bada fuska.
1 years later
Yana daki a kwance mum ta shiga ta zauna a bakin tafkeken lafiyayyen gadonsa tace Ahamad zuwa nayi muyi magana dakai, mikewa yayi ya zauna yace inajin ki mum, so nake ka kawomin matar da zaka aura, aure kuma mum? Ni ai nacire maganar aure da soyayya a tsarin rayuwata, Sbd duk yan matan da nake haduwa dasu har yanzu banga irin matar da nakeso ba, inada test mum ba kowacce mace bace take burgeni, kinyi min zabin a baya kuma nayi miki biyayya na aura, kuma dukansu ba wacce akayi Saar ta, sbda haka don Allah mum ki temaki ni ki daina yimin zancen aure, wallahi mata yanzu tsoro suke bani, nayi miki alkawari zanci gaba da tsare kaina harna mutu,,,,,,idan kayi haka that means kana jayayya da hukuncin Ubangiji, inaso ka sani Allah yana jaraba bawanshi domin yaga ya karfin imaninsa yake, duk abinda ya faru a baya jarabawa ce, sbda haka inaso kayi kokarin cinye wanan jarabawar, kuma Allah da manzonsa sunce kuyi aure domin Ku hayayyafa, sbda haka kayi hakuri kayi addua Allah yasa wanan karan a dace, shiru yayi for some minutes, sanan yace to aini bansan ma wa zan aura ba, murmushi mum tayi tace duk buhun yan matan da sukemin zarya a gdn nan ba wacce tayi maka? Idan baka da ita ni na samo maka, a hnkli yace wace ce? Husna yar gdn mallam bala me wankin hula, sbda da bakinka ka taba fadamin tana birgeka, ada kenan mum, ni yanzu ba macen da dake burgeni, ke kadai nayi trusting a duk matan duniya, rayuwa yanzu ta zama abin tsoro mum, Amma tunda kince haka shikenan zan aureta a bisa umarnin ki, Amma saidai kije da kanki ki nemomin auranta, cikin farin ciki tace zanje insha Allah, Allah yayi maka albarka yace amin.
Mum taje gdnsu Husna, kuma ba tare da bata lkci ba sun amince an saka date din biki nan da 3wks, saidai shi Asas yace bazaiyi gayyata ba.
Maman Aysha
[3/29, 22:51] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
3⃣5⃣➖4⃣0⃣
Mum din Asa's na fita daga gdn UMMA ladi tayi wata guda tace ahayye nanaye haihuwa me rana, Rabo na minnallahi tsuntsu daga sama gashashe. Mallam kakarmu ta yanke saka mukan bana aikin hajji ai damu zaayi, aikin hajji kawai ladingo? Ai mun zama miloniya, idan Husna ta auri wanan yaro ai muma saidai azo maula wajen mu, kinga shikenan wankin hula ya zama tarihi, wata gudar ladingo ta karayi, Husna ce ta shigo gdn ta dawo daga islamiyya umma gudar me naji kinayi tun daga waje ana jiyoki? Kama hannun ta tayi tace zauna yar albarka, yarinya kinyi goshi yanzu nan mahaifiyar Ahamad ta fita daga gdn nan tazo nema mishi auranki, wane Ahamad UMMA? Yaro dai daya dauki nauyin kartunki, wai kina nufin Asa's? Kwarai kuwa, wayyo dadi mafarki nake amma ko? Idan mafarki ne umma don Allah karki tasheni, barni naga koda daurin aurenmu ne saina farka, gudar da UMMA ta kara rangadawa ce ya tabbatar mata da ba mafarki take ba, cikin tsananin farin ciki tace UMMA shifa Asa's a yayyan masu kudi ma ba kowa yake kulawa ba, Amma ya akayi ya amince zai aureni? Washe baki ladingo tayi tace rabo mana 'yan nan, ai rabonka baya bace maka, sujadda Husna tayi tace Allah na gode maka. Tun daga ranar aka fara shirin biki, mum din su Asa's tace karsu saiwa Husna kayan daki su zasuyi mata komai, sanan miliyan goma aka basu suyi abincin biki, wayyo Allah zo kaga murna wajen ladingo da mallam bala.
3wks later
A yau ne aka daura auren Husna da asas, shi ango ko wajen daurin aure beje ba, kuma dama beyi wani gayyata ba iya yan uwane da kuma shakikan abokan shi suka hallata, da daddare kuma aka kai amarya dakin mijinta.
Ba karamin kyauyanci yan uwan amarya suka zuba ba, sbda tunda suke basu taba shiga irin wanan gdn ba, waifa gdn mum ma kenan to da sunga gdn Asa's kuma bansan ya zasu yi ba.
Saida kowa ya watse sanan ya shiga part dinsa inda aka kai amarya, a bakin gado ya zauna saida ya dauki lkci me tsawo sanan cikin husky voice dinshi yace INA yi miki barka da zuwa gdana, nasan zakiyi mamaki tunda akayi mgnar auranmu ban taba zuwa wajenki ba, to Amma ba abin damuwa bane iam like dat, kuma habkalinki da nutsuwarki ce tasa na amince na aureki, sbda haka don Allah inaso ki kasance me gaskiya da rikon amana. Mika mata ledar kajin hannunsa yayi sanan yace idan kin gama ci saiki kwanta, Allah ya tashemu lpy, a hnkli tace amin.
Yana fita ta yaye lullubin kanta, to wanan guy din me yake nufi dani dazai barni na kwana ni kadai? Shi besan cewa ishuruwar sonshi ta Dade tana addabar zuciyata ba? Mikewa tayi taci naman kadan sanan ta koma ta kwanta.
A WK later
Yau satin Husna guda kenan a gdn Asa's, amma ba wani Abu daya shiga tsananin su, sbda ko kadan mata basa gabanshi yanzu, duk irin kwalliyar da take tayi ta giftawa tagabanshi be taba jin wani Abu ba, ya koma sai kace dutse ko kadan bayajin sha'awar kowa.
9:15pm
Zaune yake yanata aiki a laptop dinshi Husna ta fito sanye cikin wata 'yar ficiciyar rigar bacci kallo daya yayi mata ya dauke kai, Sbd ko kadan batayi mishi ba, ba tare da ya kalleta ba yace kawomin ruwan zafi nasha Lipton kuma ki soyamin kwai kwaya uku don Allah, tace to.
Cikin hanzari taje ta fara, tun tana suyar taji zuciyar ta ta fara tashi, a tray ta jera ta nufi inda yake, tashin zuciyar taji ya karu nan take jiri ya kwasheta batasan lkcn da tayi wurgi da tray din ta fadi ba, karar tary dince ta ankarar dashi, da sauri ya tafi ya daga ta yakaita mota, cikin few minutes sukaje asibiti, investigation sosai likita yayi bayan kmr 30 mints yazo wit respect yace ranka ya Dade alhamdulilla she is pregnant, nan take fara'ar data ke fuskarsa ta dauke, wani irin mummunan faduwar gaba yaji, Amma dake he is very smart baa gane ba, murmushi ya kakalo yace anya likita ka dubata sosai kuwa? Kwarai kuwa yallabai, wata nawa ne? Ba zaa gane ba sai anyi scanning, OK to don Allah taimaka kayi mata, yace to. Ji yayi ya jike jagab da gumi, inna lillahi wa inna ilaihir rajuun, ni kuma irin tawa kaddarar kenan?meya hada husna da ciki? Anya likitan nan yasan abinda yake kuwa? Karfa ace duk nutsuwar ta tana bin maza? Kodai fyade akayi mata suka buyemin? Yanzu idan cikin nan befi sati biyu da shiga ba ni zaa likawa shi kenan? Kwarai kuwa idan kuma baka amsa ba duniya ta zageka ba, zuciyarsa ta bashi amsa. Oh my god, ya Allah ka kawomin dauki
Maman Aysha
[4/2, 07:44] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
4⃣0⃣➖4⃣5⃣
Harda shi aka shiga scanning room din, bayan likita ya gama kafin yayi magana Asa's yace Husna jeki kan benci ki jirani INA zuwa, tace to. Tana fita yace likita wata nawa ne? Yace 3 months ne yallabai, ka tabbata abinda ka fadamin gskya ne? Mika mishi takardar yayi yace karbi kaga, jiri ne ya debeshi ya tafi luuuu zai fadi, da sauri likita ya rikeshi ya kontar dashi akan koch din da ake scanning, ya gwada bp dinshi 150/100, da sauri ya nufi hanyar fita zuwa pharmacy, cikin dakkekiyar murya yace ina zaka doctor? Magani zan samo maka sbda bp ka yahau, basshi kawai doctor a yanayin yanda nake jina yanzu ko nasha mgani bazai sauka ba, sakkowa yayi daga kan koch din yace bari naje gida kawai. Mum ya kira a waya yace ta tura a kira mata mallam bala da matar shi yanaso zaiyi wata magana dasu, sanan suka shiga mota suka tafi.
Mallam bala ne da ladingo zaune sun baje nama sunaci sbda ba karamin kudi Asa's yake basu ba, tunda ya auri Husna su ladingo suka daina cin tuwon dare saidai aci nama ko doya da kwai. Wayar malam bala ce ta fara ruri yana dauka yaji muryar mum, harda durkusawa kmr tana ganinshi, bayan sun gaisa ta fada mishi dalilin kiran, washe baki yayi yace to shikenan zamuzo yanzu ma kuwa. Kallon ladingo yayi yace INA ganin yaron nan Ahamad makka zai biya mana, sbda Neman mu yake da daddaren nan, mikewa ladingo tayi ta fara rera waka tana rawa, cikin few minutes ta dauko gyalenta suka nufi gdn mum.
A zaune suka samesu, bayan an gama gaisa wa Asa's ya kalli Mum din sa yace mum dama Husna ce bata da lpya, shine na kaita asibiti, bayan duk wani gwaje gwaje da akayi mata likita ya tabbatar min tanada ciki, shiyasa na kira iyayenta tayi bayani agaban su, kallon ta yayi da jajayen idanuwansa yace Husna wa yayi miki ciki? Ladingo ce tayi karaf tace ya wa yayi mata ciki ba dadin ji? Yaufa kwanan yarinyar nan takwas a gdn ka, bakasan cewa ranar da mutun ya tare ma yana iya daukar ciki ba? Na sani UMMA, saidai cikin da Husna take dauke dashi wata uku ne. Mum tana zaune saida ta mike, a tare sukace wata uku? Ya akayi haka ta faru my son? Shiyasa na taraku tayi muku bayani. Kuka ladingo ta soma, Walla sharri ake son yiwa yarinyar nan sbda anga muna dangwalar arziki, karka yarda da zancen don Allah yallabai Amadu, wallahi sharrin makiya ne yan bakin ciki ne kawai suka shirya maganar.....kiyi mana shiru ladi mum ta katse ta, ki kyale yarinya tayi magana da bakinta, ke Husna karki bata mana lkci kiyi mana bayani wa yayi miki ciki? Tana shesshekar kuka tace mujahid ne, salati sukayi a tare sanan ladingo ta fashe da kuka garin yaya wanan al amari ya faru? Yanzu duk irin tsaron da ake baki, da nuna mana ke uztaziya ce da kike dama karya ne Husna? Nashiga uku wanan abin kunya dame yayi kama, amma wanan yarinya kin cucemu wallahi...... Asa's ne ya katse ta da cewa ya isa, kunsan komai dama, ba yanda zaayi ace bakisan yarki tanada ciki ba, zalunci da son zuciya ne yasa kuka aura min ita a haka, sbda haka Ku dauki yarku Ku fice mana daga gda na tsaneta, na tsani duk wata mace a duniya, na fuskanci duk matan duniyar nan macuta ne, maha'inta ne, azzalumai ne kuma mayaudara ne. Mum inaso kisani daga yau bazan kara aure ba, zanci gaba da rayuwata ba tare da mace ba harna mutu, matan zamanin nan basu da amana mum, jirine ya debeshi nan take ya fadi sumamme a wajen. Cikin tsananin tashin hnkli mum ta kira family doctor su, sanan ta kori su ladingo daga gdn.
Likita yazo ya gwada bp shi 200/110, cikin sauri yayi mishi hydralazine inj, sanan yace wa mum abarshi yayi bacci sosai kuma ta ringa yawan yi mishi nasiha da addua sbda be kamata ace Bp dinshi yana hawa haka ba, bcos he is just 32 yrs yanzu, sanan ya bata wasu maganin ya nuna mata yanda zata bashi, yace kuma idan da wata matsala komai dare ta kirashi, sanan yayi sallama ya tafi.
Kuka sosai mum take, dataga kukan bazai kaita ba sai tayi alwala ta fara jera salla bayan ta idar ta zauna ta fara lazumi tana addua batasan lkcn da bacci ya dauketa ba
Maman Aysha
[4/2, 09:51] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
4⃣5⃣➖5⃣0⃣
Satin Asa's uku be fita ko ina ba, sabda likita ya bashi bed rest yan dubiya ma ba kowa ne yake samun ganin shi ba, Saida likita ya tabbatar komai ya dawo normal sanan yace zai iya komawa normal activities dinsa.
Alhamdulilla ya koma day to day activities dinsa, kuma ya rage yawan tunani ya cire komai a ranshi saidai Abin daya kwallafa a ranshi shine ba ruwan shi da kowacce mace inba mahaifiyar sa ba, kullum acikin shan kunu yake matan da suke aiki a kamfanin sa ba karamin wahalar dasu yake ba Dan lefi kadan idan sukayi mishi saiya hausu da fada, yanzu ba karamin tsoron shi sukeji ba abin har mamaki yake basu sbda da ba haka yake musu ba.
Waec din da akayi Wanan shekarar students din makarantar Asa's na gifted and talented sune overall sbda haka duk gdn television da radio daka kunna zancen suke, wanan dalilin yasa gdn television na arewa 24 sukaje office din Asa's domin suyi hira dashi akan irin wanan cigaban daya samu, da kuma irin farin cikin dayake ji duba da yadda ya Debi 'yayan talakawa ya basu ilimin da ba kowanne Dan me kudi ne zai samu irinshi ba.
Anisa Sharif itace yarinyar data je tayi mishi interview din, a nutse take mishi tambayoyi yana bata amsa bayan sun gama ta kalli camera man din da suke aiki tare tace su jirata a waje. Suna fita ta kalli Asa's tace kmr yadda nayi maka introducing kaina da farko, sunana Anisa Sharif, na Dade INA sonka amma na rasa hanyar dazan ganka na fada maka, wanan dalilin ne yasa na nemi aiki da arewa 24 sbda kiran zuwan irin wanan ranar, ba karamin farin ciki nayi ba da aka zabeni a matsayin wacce zanyi maka interview, durkuswa tayi agaban shi don Allah Mr Asa's ka amince da soyayya ta, wallahi zuciyata ta Dade tana wahala a sonka.......shut up yace da karfi, karki kuskura ki kara cewa komai, fice min daga office. Zatayi magana ya kara daka mata tsawa I said walk out, jikinta har rawa yake ta mike ta fita, a corridor din office dinshi ta tsaya saida tayi kuka sosai sanan ta goge hawayen ta saita kanta, sanan ta fita wajen abokan aikin ta suka tafi.
Anisa na fita phone dinsa ta fara ruri, bakuwar no ce yana dauka yaji ance assalam Mr Asa's sunana Najwa na Dade INA Neman no ka sai yau Allah ya bani SAA na samu, na dauki lkci me tsaho INA fama da ciwon sonka........ya isa! Idan kika sake kika kara kirana saina wulakanta ki, stupid kawai. Yana katse wayar yaji kanshi ya fara ciwo idan da abinda ya tsana a duniya yanzu mata ne, amma meyasa suke bibiyarsa? Ji yayi yana bukatar ya tafi wajen dazai huta koda 1 WK ne ba tare da kowa ya dameshi ba, hotel din Lamido game reserve dake garin mambela ne ya fado mishi arai, haddaden hotel ne da ko a kasahen turai da wahala ka samu irinsa, wajen shakatawa ne dako service din waya mekyau babu sbda kar ayi disturbing din mutu. Mostly turawa da masu fada aji a 9ja ne sulafi yawan zuwa hotel din sbda yanada bala'in tsada, kuma akwai security a wajen sosai. Phone dinsa ya dauka ya fice daga office din, yana fita body guards dinshi suka Mara mishi baya ya tafi gda
Maman Aysha
[24/05 9:21 PM] Mizz Ayuush: [4/3, 19:28] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
5⃣0⃣➖5⃣5⃣
A falo ya samu mum ita da sultan, sauran yan aikin gdn kuma sai kaiwa da komowa suke mum ce tace lpy naga ka dawo yanzu? Wallahi lpya kalau mum, INA Neman wata alfarma ne awajen ki, tame fa? So nake kiyimin izini na tafi mambila sbda INA bukatar Hutu, kuma anan bana samun Hutu sosai, shiru mum tayi na Dan wani lkci sanan tace bawai zan hanaka tafiya bane my son, banaso ne kaje kayita tunani har jininka yahau, Insha Allah ba zanyi ba mum, kuma sati daya kawai zanyi garin bashi da network mekyau sbda haka idan na isa zan kiraki na fada miki, sauran kwana kin nedai be zama dole ki sameni ba. A shiryawa sultan kayansa mutafi tare tace to karfe nawa zaku tafi? Zan danyi bacci idan na tashi sai mu tafi, to amma a body guards dinka da suwa zaka tafi? Ni kadai zan tafi mum, sbda dukansu sunada aure zan tauye musu hakkinsu, da ace befi 3 days bane bama amma kinga sati guda zanyi.
Sai wajen 1:30 ya farka daga barci a gurguje yayi wanka yayi salla ko abinci beci ba ya fito range Rover dinshi ya shiga dama yasa an wanke ta Tass, 2pm suka kama hanya mum da guards dinshi saida suka rakashi har bakin mota saida motar ta kule sanan suka watse. haka kawai mum taji gabanta yana faduwa, ba ason ranta ya tafi ba dandai batason takura mishi ne, saboda yanzu tausayi yake bata. Haka ta koma cikin gda jiki a sanyaye.
Sai wajen 7pm suka shiga taraba state, yana dab da shiga garin mum ta kirashi yace nan da 15min insha Allah zamu shiga cikin garin, tace alhamdulilla Allah ya karasa daku lpya yace amin.
Suna gama waya wata babbar mota ta iyo Kansu, agarin kaucewa kan motar ya kwace sbda a speed yake tfya ga duhu ya fara, zuwa yayi ya daki wata bishiya kansa ne ya bugu da sitayari, nan take jini ya balle ya fara zuba mutane ne suka nufo wajen da gudu domin basu agajin gaggawa, ana fita dasu motar ta kama da wuta direct kamal specialist hospital suka wuce dasu batare da Ahamad yasan inda kanshi yake ba, shi kuwa sultan Dan sokewa yayi a hannunsa da glass
Suna zuwa aka shiga dasu emergency, likitoci sukayi rubdugu akanshi domin ceto rayuwarsa
Maman Aysha
[4/4, 09:34] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
5⃣5⃣➖6⃣0⃣
Saida likitoci sukayi wajen 1hour a kansa kafin ya dawo stable, saidai har yanzu he is unconscious, acikin emergency unit din akayi admitting dinsa, shi kuma sultan yana emergency paediatric unit.
Aysha kabeer maitama itace staff nurse din da take night duty a EPU, cikin dressing dinta na uniform din nursing ta shigo, wato me karatu na Dade INA ganin nurses suna burgeni acikin uniform dinsu, amma ban taba ganin wacce uniform yayiwa kyau ba kmr Aysha, tana shiga ta cire after dress din jikinta tazo suka fara handing over da staff din data gama evening shift, bed by bed suke bi, sultan shine na karshe duk gadon da suka wuce zakaga uwar yaron da bashida lpy a zaune a kusa dashi, amma sai taga sultan zaune shi kade yana wuri wuri da ido kallon sister mero tayi tace wanan fine boy dinfa? Ina Maman shi? Wallahi bansani ba, dazu doctor suraj ya kawoshi wai accident sukayi da Baban shi, kuma Baban nashi he is unconscious, ya salm Aysha tace, matsawa jikin gadon tayi ta rike hannunsa cikin tausayawa tace meye sunanka? Yace chultan, dariya tayi da har saida kumatunta suka lotsa sanan tace sultan kachi abinci? Jijjiga kai yayi alamar aa. Saida sukayi sallama da sister mero sanan ta dauki sultan ta rungume shi a jikinta ta shiga nurses room din dakin dashi, zaunar dashi tayi a bakin katifa ta bude soyayyen naman kazar data zo dashi a karamin food flask daga gda ta fara yagar mishi naman yanaci, sanan ta dauko yoghurt a Jakarta ta bude mishi ya karba ya fara sha. Saida ta tabbatar ya koshi sanan suka fito nurses station ta dorashi a kujera itama ta zauna a dayar ta dauko phone dinta suka fara chartn da Dr kamal, soyayya suke zubawa dashi ta chartn, sai smiling take ita kadai, Dr suraj ne ya shigo dakin yace Aysha sarkin yara kinsan tunda na kalli gadon da akayi admitting yaron nan naga ban ganshi ba nasan yana wajenki, wallahi aysha i like all your style naso ace nizan aureki dan dai Dr kamal yayi min shigar sauri ne. Kujera ya samu ya zauna sanan yace meya faru lkcn dana shigo naga kina smiling ke kadai? Dariya tayi tace nida abokinka ne, Kasan ya fiye rigima, dariya suraj yayi yace ni kuwa nasan haka sbda da yana gari da ban isa na zauna muyi hira dake ba, sbda yana tsananin kishin ki, smiling tayi tace ya jikin daddyn sultan? Da sauki, he is stable now, naji sister mero tace he is unconscious, mene ne problem din? Munyi mishi brain CT scan, ba matsalar komai, kuma Kuma munyi checking nerves impulses dinshi ma suna functioning yanda ya kamata, so INA ganin any time zai iya farkawa. Aysha tace Allah ya bashi lpya yace amin. To amma likita naga asibitin nan private ne, so ya zakuyi dashi kenan? Tunda bakusan family shi ba ko? Eh, dama abinda mukayi deciding dasu Dr Abdul shine zamuyi referring dinshi to general Hosp, kinga su acan zasu dauki pics dinshi dana yaron asa a media ko Allah zaisa 'yan uwanshi zasu gani, amma likita sainaga kmar yin hakan tonon silili ne, tunda kace ba matsala a brain dinsa, ni INA ganin kubarshi anan harya dawo normal consciousness dinshi, kaga saiya fadi garin su da kansa akaisu. Dariya Dr suraj yayi yace kuma wazai biya mishi kudin? Kinsan Dr kamal bazai dauki asara ba, indai maganar kudi ne karka damu, ni na amince zan dauki responsibility dinshi Dana sultan harya farfado sbda Allah. smiling Dr suraj yayi yace shiyasa nake son komai naki aysha kinada tausayi, kinada son yara, kinada kyauta kuma baki da son zuciya, Wallahi halinki yayi min sosai, amma idan kamal yaji labrn nan fa ransa zai baci, sbda yanada kishi kar yayi zargin wani Abu, sbda gskya baban yaron yanada kyau, he is very handsome kar yayi tunanin sonshi kike shiyasa kk temake shi, murmushi Aysha tayi tace kai haba, ai banajin zuciyata zataso wani mutun bayan kamal, Wallahi yaron nake tausayi tunda na ganshi naji INA sonshi, sbda sultan zan temaka mishi ji nake kmar ni na haifeshi shine kawai amma Wallahi ba wata manufa a zuciyata. Yanzu temakon da zakayi min likita don Allah kasa amaidashi amenity ward zanje na biya, saika sami wani ya kwana dashi yau, idan yaso gobe saina cigaba da kula dashi tunda daga yau na gama night, yace to ba matsala bari na tafi saida safe tace Allah ya kaimu
Maman Aysha
[4/4, 14:28] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
6⃣0⃣➖6⃣5⃣
Washe gari Aysha na bawa masu morning dakin tasa likita yayi discharge din sultan sanan ta kama hannunsa suka tafi amminity ward inda tasa aka mayar da Ahamad wajen nurses din ta fara zuwa, tana zuwa dakin ta tarar an Tara mata tarkardun bill na wajen 50k Sbd kudin aminity ward kadai 5000k ne per day, bayan ta biya ta kawo musu resit din sanan suka shiga dakin dayake yana kwance kmr me bacci da NG tube a hancin sa, kallo daya tayi mishi taji gabanta ya fadi, mutumin daya kwana dashi ta kalla tace yamai jiki? Yace da sauki, tace mungode Allah saka da alkairi, don Allah idan ba takura kaci gaba da zama dashi zanje na shirya idan na dawo saika tafi, yace ba matsala.
Tana rike da hannun sultan suka fito, tana dosowa nurses cubicle din taji suna gulmarta daya daga cikin su me suna Sakina ce tace 'yar me shisshigin tsiya ko meye hadinta dashi? Ance fa baasan yan uwansa ba, amma kinga ta kafa ta tsare awajensa, fiddausi kuma tace kyale shegiya ai saina fadawa Dr kamal, dama INA Neman hanyar da zan hadasu fada, kinsan yana kishin ta sosai, Sakina tace idan kin hadasu ma zasu shirya, kinsan Allah ya bata wani irin shu'umin kyau, Dr kamal bazai iya rayuwa ba ita ba, kuma nasan bazai baki fuskar da zaki fada mishi bama,,,,,,suna ganinta suka zama shock, amma saita basar kamar bataji me suke fada ba, smiling din dayake kara mata kyau tayi tace zanje gda na dawo, cikin guilty conscious sukace to sai kin dawo.
Tana shiga gda ta sami inna hansatu tanajin labaran karfe takwas a radio bayan ta gaisheta tace Ina kika sami kyakkyawan yaro haka zama tayi ta bata lbarn duk abinda ya faru har daukar nauyin Baban sultan da tace zatayi, tace ba komai ai temako yanada dadi Allah yayi miki albarka ya biyaki da gdn aljanna tace amin, dakinta ta shiga ta cire uniform tasa wata Riga sanan ta shiga kitchen ta soya Irish da plantain sanan ta damawa Ahamad kunun gyada na nikekkiyar shinkafa, ta wankewa Ahamad hannu ta zuba mishi abinci, sanan tayi wanka ta shirya cikin wata blue gown tayi rolling da mayafin rigar sanan ta fita. Wani boutique taje ta sayawa Ahamad hadaddun jallabiya guda biyar different colors da shot nikers sanan ta sayawa sultan ma guda uku English wear's guda biyu masu kyau, tasayi jaka medium da zaa zuba kayan, sanan taje cosmetic shop ta sayi sabulun wanka, lotions, da kuma designers perfume, brush da Maclean sanan ta dawo gda tayiwa sultan wanka tasa mishi wata ash doguwar jallabiya da gajeren wando rigar tayi mishi kyau sosai, sanan ta samo me keke napep suka koma asibiti.
In charge din dakin tayiwa mgna dake namiji ne yayi mishi bed bath da oral toilet, sanan ta dauki jallabiya daya da shot niker ta mika aka saka mishi, ta dauko turare aka fesa mishi sanan ta hada kunun gyada a cup da madara da sugar kadan ta dura mishi ta NG tube, sadai tabashi daidai level din da akeso yasha sanan ta wanke cup din ta ajiye, ta bawa mutumin daya kwana dashi nashi abincin kuma ta bashi 200k kyauta. Da rana inna hansatu ta dafo musu abinci ta kawo, kuma ta duba Baban sultan
Maman Aysha
[4/4, 19:21] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
6⃣5⃣➖7⃣0⃣
Haka aysha taci gaba da kula da Ahamad kullum ita take kwana a wajensa sanan da safe inna hafsatu taje ta zauna dashi ita kuma ta koma gda tayi wanka ta hado abincin break sanan ta kara komawa dake yanzu night off take. Wata irin shakuwa ce ta shiga tsakanin su da sultan kmr a bakinsa aka rada aunty Aysha idan ka gansu sakace kaninta ne Wanda suke d same parent dashi, dake gayu ya ratsa aysha ko yaya tayi dressing saikaga kmr yar shugaban kasa, sultan ma ba karamin daukar wanka yake ba sbda ta sayo mishi hadaddun kaya da takalma tana saka mishi, idan sunyi datti takai musu wajen wankin. Asibiti kuwa duk inda ka zaga gulmar aysha suke wai duk irin sonda MD kamal yake mata bata gani ba tana can tana son wani balarabe da batasan asalinsa bama. Idan da sabo harta saba tun ranar da MD din asibitin wato Dr kamal yace yana sonta abokan aikin ta yan mata suka dauki karan tsana suka Dora mata.
Yau kwanan Ahamad biyar kenan a asibiti, amma har yanzu be dawo conscious dinsa ba, yauma kamar kullum Aysha na zaune akan 2 seater din room da suke sanye take cikin wata hadaddiyar gown maroon color wajen 15k tasayi rigar, dake aysha yar gayu ce rigar tayi mata kyau sultan na gefenta ta bashi baby Nokia dinta yanata game din snake har bacci ya daukeshi,saita kwantar dashi akan kujera, ita kuma tanata chartn
da android dinta, kawai saitaga kmr Ahamad yana motsi, bakin gadon taje ta tsaya saitaji yana cewa don Allah jama'a Ku dauke min sultan daga cikin motar nan, Allah ka tserar min da sultan innalillahi wa inna ilaihir rajuun, la ila ha illalla muhammadu rasulullahi salallahu alaihi wa sallam, kawai saiya mike a razane, rike shi tayi da sauri ta komar dashi ya kwanta, a hnkli ya fara bude idonsa, yana budewa karaf suka hada ido wa innahu sulaimanu wa innahu bismillahir rahamanir rahim ya fada, tunda yake a duniya be taba ganin kyakkyawar hallita irin wanan yarinyar ba, duk yanda akayi aljana ce, na shiga uku! A masu son cutar dani kenan harda aljanu? Ayatul kursiyyu ya fara karntawa yana jiran ta bace amma yaga shiru, kawai saiyayi yunkurin tashi yana cewa ke wacece? Ina kika kawoni? Mena miki kike kokarin cutar dani? Don Allah ke mutun ce ko Alajana? Ina Dana sultan? Relax Mr no name, nutsuwarka muke bukata yanzu, don Allah karka sawa brain dinka charging da batayi niya ba, brain dinka Hutu take bukata yanzu. Ta yaya zaayi na samu nutsuwa bayan na farka naga abinda nafi tsana a duniya zaune kusa dani, kuma bansan inda nake ba, taya zaayi nasan cewa ba kin dakkoni nan ne domin ki cutar dani ba? Meye abinda kafi tsana a duniya? Kece, ni kuma? Meyasa ka tsaneni bayan baka taba ganina ba? Bawai ke na tsana ba, duk wata mace da take duniyar nan na tsana, mum dina kawai nayi trusting, sbda haka ki fadamin a Ina nake? A a taraba state kake, kuma nan cikin asibiti ne, kayi accident ne kaida yaronka sultan, kuma yau kwanan ka biyar unconscious sai yau Allah ya baka ikon tashi. Maganar cutar dakai da kuma tsanar mata da kayi inaso ka sani kai musulmi ne, ka yarda da Allah da manzonsa, ka yarda cewa Allah shine me kare mutun a duk inda yake ba wayonshi ko dabarararsa ba, inaso kasa a ranka cewa ba wani mutun daya isa ya cutar dakai sai Allah ya bashi iko ......yimin shiru da Allah, duk haka kuke fadin Allah a baki kmr gaske, bayan zuciyarku a bushe take. Dr suraj ne ya shigo dakin cikin farin ciki yace masha Allah patient din mu ya tashi, murmushin yake aysha tayi tace eh Wallahi ya farka, zuwa yayi ya kara dudduba shi, sanan yace akwai abinda yake maka ciwo? Yace aa, oral drugs ya rubuta ya bawa aysha taje ta sayo, sanan ya cire mishi naso gastric tube din, sultan yana farkawa daga bacci yaje ya rungume shi, matseshi yayi ajikinsa yana hamdala ga Allah daya tserar dasu.
Kafin ta dawo daga sayen mgni suraj ya fita, tana shiga dakin ta ajiye ledar akan drowa, da gudu Ahamad yaje ya rungume ta yana mata Oyo yo, wani kallon tsana Ahamad ya bita dashi sanan yace wai ke wace ce? Ta lura da kallon tsanar da yake mata, amma saita basar tace zaka sani very soon. Toilet ta shiga ta hada mishi ruwan wanka tana fitowa batare da ta kalleshi ba tace shiga toilet kayi wanka ko zakaji karfin jikinka, sakkowa yayi daga kan gadon ba tare da yayi mata mgna ba, jirini ya debeshi zai fadi ta tafi da sauri ta rike shi ya fada jikinta, zaunar dashi tayi akan kujera ta dauko maltina me sanyi ta bude mishi yasha, yana kwankwadewa ta bude mishi wata nan take ya shanye, saida ta bari ta tsirga mishi sanan ta kama hannunsa suka shiga toilet tace zaka iya wankan da kanka ko na kira wani yazo ya taimaka maka? Kai kawai ya daga mata alamar zai iya
Maman Aysha
[24/05 9:21 PM] Mizz Ayuush: [4/6, 18:20] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
7⃣0⃣➖7⃣5⃣
Akwatin kayan su ta dakko ta dauko mishi wata farar jallabiya da short niker, lotion da turare ta Dora akan gadon, sanan taje bakin toilet din tace ka kulle kofar da key idan zaka shirya, ni INA waje. Hannun sultan ta kama suka fita waje suka zauna Dr suraj ne yazo ya samesu yace yana ganku a waje? Mun bashi waje ya shirya ne, OK, iam totally confused akan patient din nan naki Aysha, meyasa kace haka? Sbda yana yimin kama da youngest multi billionaire nan Asa's, tun ranar Dana fara ganinshi naga suna mugun kama, to amma sainaga ba abinda zai kawo Asa's nan sbda idan zaiyi tfya me nisa indai within 9ja ne da helicopter yake, idan da motane kuma convey yake da body guards dinshi, kuma baya tuki da kansa shi kuma wanan naji ance daga shi sai danshi sukayi accident shiyasa nayi tunanin ba Asa's bane, amma kuma Dana kara ganinshi ido biyu dazu sainaga kamar shine kinsan har gida na koma na dauko jaridar daily trust wacce sukayi hira dashi last 2wks akan nasarar da sch dinshi gifted and talented ta samu, dan na tabbatar, kuma wallahi shine karbi ki gani, karba tayi ta duba ba wani tantama Asa's ne, dagowa tayi tace gaskiya shine fa, to amma meya kawo shi garin nan, kuma ya akayi babban mutun kmr Asa's ya bata har kwana biyar amma ko a labarai baayi cikiyarsa ba? Dr suraj yace nima abinda yake bani mamaki kenan, amma zanje muyi hira dashi idan shine ma zan gane, bari naje na duba ko ya fito daga wankan, tace to.
Yana nocking yazo ya bude mishi, bayan sun gaisa yace ya jikin? Yace da sauki, Aysha da sultan ne suka shigo ta kalleshi jallabiya tayi mishi kyau sosai kmr bakin balarabe, a hnkli tace jikinka ya kara karfi dakayi wanka ko? Basarwa yayi kmr beji abinda tace ba, kallon Dr suraj tayi tace likita idan baka da aiki don Allah ka tayashi hira ni zanje na dafa mishi abinci me Dan nauyi Kasan yau 5 days kenan yanacin liquid food, smiling Dr suraj yayi yace ba matsala sai kin dawo, tace to. Hannun sultan ta kama zasu tafi kawai saitaji Ahamad yace sultan karka bita, kallon sa tayi da manyan fararen idanuwanta tace meyasa? Be mata mgna sai wata muguwar harara daya bita dashi, kawai saita lallaba sultan tace ya zauna taje ta dawo.
Tana fita Ahamad ya cewa Dr suraj don Allah likita na tambaye ka? Smiling yayi yace go ahead INA jinka, don Allah wacece wanan Aysha? Kuma a ina take? Meyasa takemin shishhigi? Kuma meyasa naji kuna kirana da patient din ta?
Aysha staff nurse ce anan asibitin, ranar da kukayi accident ita take aiki a EPU, tun da taga danka sultan taji tana tausayin shi,,,,,,,,nan dai ya bashi lbrn komai daya faru. Shiru Asa's yayi for some minutes sanan yace yanzu kana nufin duk wani bills da kukayi Aysha ta biya? Eh, kuma ita tasa akawoka amenity, sanan duk abinda ka gani a dakin nan ita tasaya ta kawo muku. Tunani me zurfi Asa's ya shiga dole akwai abinda aysha take nema a wajensa, sbda bazai yiyyu ta a wanan zamanin ta ringa kashe mishi kudi a banza ba, saidai koma me take so bazata taba yin nasara ba Sbd yanzu ya daina yarda da mutane, more especially ma mata murmushin mugunta yayi yace zanyi maganinta, amma a fili sai yace amma tayi kokari ngde sosai
Maman Aysha
[4/7, 18:01] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
7⃣5⃣➖8⃣0⃣
Shaf shaf ta gama girkin ta zuba a hadaddun food wormers, ta jerasu a basket, sanan suka fito ita da inna hansatu suka tari me keke napep suka tafi asibiti.
Asas na zaune suna hira da Dr suraj Aysha sukayi sallama suka shiga, Aysha ce ta kalli Asa's tace ga innata tazo dubaka, durkusa wa yayi ya gaisheta, tace mishi ya jiki? Yace da sauki, sanan INA tayi musu sallama ta tafi. Saida Aysha ta rakata har wajen me napep ta biyashi kudinsa sanan ta dawo dakin, katuwar darduma ta dauko ta shimfida sanan ta fito da food wormers din, fried rice tayi da coslow, sai paper chicken da hadadden zobo dayaji kankana da cocomber, tana budewa kamshi ya cika dakin, sultan ta fara zubawa sanan ta zubawa Asa's, kallonshi tayi tace bismilla sakko kasa kaci, cikin shan mur yace yayi min yawa rage, itama shan kunu tayi tace yau 5 days kenan bakaci abinci me nauyi ba, so saika cinye wit full confidence tace oya sauko kaci, ba musu ya zauna ya fara ci, kallon Dr suraj yayi yace doctor zo muci mana, aa alhamdulilla ngde, don Allah kazo muci Dr idan ba haka ba nima bazan Ciba ya karasa mgnar yana yiwa aysha kallon rashin yadda, ta gane abinda yake nufi sai kawai tace abincin yanada yawa don Allah ka zauna kuci likita. Dama tunda aka bude abincin Dr suraj yake hadiyar yawu, yanaji aysha tayi magna yaje ya zauna suka fara ci. Asa's dayake cewa bazaici da yawa ba sau uku suna kari, zobo kuwa yasha yakai cup hudu Aysha na gefe tana kallonsu, tana bawa sultan nama yanaci. Phone din Aysha ce ta fara kara, kamal ne bayan sun gaisa yace Aysha bakya nemana ko? Cikin shagwaba tace INA Neman ka mana, to yanzu a Ina kike? Ina gda mana, me kike yi to? Kai yaya kamal ka fiye tambaya, aiki nakewa inna, dariya yayi yace danna tambayi matata abinda take lefi ne? Itama dariya tayi tace ba lefi bane caring ne, nayi missing dinka da yawa yaushe zaka dawo? Very soon, wacce rana kenan? Aa kema kin fiye tambaya, dariya tayi da har saida fararen hakoranta suka fito, sanan cikin Jan hanklin me sauraro tace iam sorry sun Dade suna hira sanan ya kashe. Asa's da Dr suraj zuba mata ido sukayi suna kallonta, saida Dr suraj ya gama cika kudunsa sanan yayi musu sallama ya tafi.
Wai wacece Aysha ne?
Yace ga marigayi alhaji kabeer maitama, alhaji kabeer Dan asalin Bauchi state ne a wata unguwa me suna jahun, su hudu ne a wajen babansu amma kuma shi kadai mahaifiyar sa ta Haifa, su kuma mutun ukun dakin su daya. Alhaji kabeer tun yana karami mutun ne me zuciyar Neman na kanshi shiyasa Allah ya buda mishi duk cikin yan uwan ya fisu arziki.
Tun da suka ga haka suka dauki tsana suka Dora mishi amma duk da haka be daina kyatata musu ba, Architecture ya karanta gashi dai diploma yayi amma sai Allah ya daukakashi akeji dashi a garin Bauchi a wancan lkcn, da haka ya hadu da uban gdnsa daya ringa buda mishi ya samu kudi masu yawa, ana cikin haka ya hadu da matarsa me suna Kadija sukayi aure, ita kuma yar asalin taraba state ce aikine yakai babanta Bauchi. Bayan sunyi aure da shekara 2 Kadija ta haifi yarta kyakkyawa aka sa mata suna aysha, lkcn da aysha ta cika shekara uku Kadija ta kara haihuwar danta namiji aka samasa suna Mohd Auwal.
Aysha tana da shekara goma a duniya arzikin alhaji kabeer ya kara bunkasa dake yana samun aiki sosai, a lkcn ne ya sayawa yan uwanshi gidaje safe content kowa guda daya harda matarsa, sanan ya biya musu aikin hajji hadda surukarsa inna hansatu dake lkcn mijinta ya mutu.
Kyautar gda da kuma biyawa inna hansatu makka da alhaji kabeer yayi shi ya jawo yan uwansa suka kara tsanarshi wai ya daidaita su da da uwar matarsa, amma duk da haka be dena yi musu alheri ba, ganin haka sai Kadija tacewa innata su sayar da gdn ta koma jalingo ta sayi wani sabda surutun da yan uwan mijin ta suke musu yayi yawa, haka kuwa akayi rana daya sukaji lbri inna hansatu tabar garin.
Bayan inna hansatu tabar garin da wajen shekara kwasam sai aka aikowa da Kadija bata da lpya, shine suka shirya gabadayansu suka nufi jalingo dubiya akan hanyar su ne sukayi accident dukkansu suka rasu aysha ce kawai ta rayu a motar.
Bayan anyi sadakar arba'in aka fara shawarar acikin yan uwan alhaji kabeer wa zaici gaba da rikon aysha, sai dukansu sukace ba zasu rike ta ba sbda lkcn yanada rai yan uwan matarsa ya bautawa, sai kawai inna hansatu tace ita zataci gaba da riketa.
Bata samu gadon babanta duka ba kasancewarta ya mace, Dan abinda data samu aka hada aka saya mata gidaje drive in masu kyau aka zuba yan haya, da wanan kudin aka dauki responsibility din kartunta harta tayi sch of nursing. Shi kuma Dr kamal Dan unguwarsu ne anan jalingo mahaifin shi me kudi ne sosai, a kasar Egypt yayi krtu tunda ya Dora idonsa akan aysha yaji duk duniya ba wacce yakeso sai ita duk da mum dinshi ta nuna bataso, hakan besa ya hakura ba. Dad din sa ne ya bude mishi kamal special Hosp sbda baya sha'awar aikin gomnati, kuma asibitin ya samu karbuwa sosai sba yana daya daga cikin Wanda akeji dashi a jalingo. Lkcn da aysha tayi qualifying da nursing council sai
kamal ya bata offer a asibitin shi, yanzu haka iyaye sun San da mgnar soyayyarsu kuma zaa saka ranar biki very soon.
A yanzu haka shekarar aysha 18, kyakkyawa ce ajin farko tanada class, tana da confidence, she is very gentle kuma tanada I don't care attitude, sanan ko tayi fushi baka ganewa a fuskarta, tanada hakuri sosai kuma kallo daya zakayi mata ka gane gayu ya ratsata
Cigaban labri
Maman Aysha
[4/7, 20:23] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
8⃣0⃣➖8⃣5⃣
Cigaban labari
Da lokacin sallar la'asr yayi Asa's ya mike ya gabatar, bayan ya ida yayi addua yace bani Aron phone dinki, tace to, cire password din tayi ta mika mishi no mum dinshi yasa ya fara kira bugu biyu ta dauka tanajin muryar shi taji wani farin ciki ya kamata, Ahamad wanan wane irin gari kaje haka? Kullum sainayi trying no ka amma saita ki shiga, sbda kace min garin ba network mekyau shiyasa ban damu sosai ba, amma fa duk da haka gabana ba karamin faduwa yake ba. Ina wayar ka naga ka kira da wani layin? Tana nan faduwa tayi saita dauke, dole saina sayi wata, number suleman PA dina don Allah zaki tromin, tace to, tana tro masa ya kirashi bayan sun gaisa yace ya fadawa driver sa na helicopter suzo su dauke shi a jalingo gbe da safe kuma idan kun shigo da wanan layin zaku sameni, yace to shikenan yallabai Allah ya kaimu, yanaso ya tambayeshi amma yana tsoron shi. Bayan ya gama ya mika mata wayar ko gdya babu, abin ya daurewa aysha kai, to shi wanan me yake nufi be? Ko gani yake sbda kudin shi nake mishi duk abinda nake? Humm lalle besan halina ba, amma wataran zai gane ko ni wacece. Kallon shi tayi tace zanje gida na dawo, batare daya kalleta ba yace indai girki zakiyi mana nagode kibarshi kawai, kar tsanar da kake min tasa kaki karbar abinda zanyi maka, kana kan strong anti biotic kuma likita yace ka ringa cin abinci sosai, kuma indai kai bakaci ba sultan zaici, ko my boy? Yaron ya daga kai alamar eh smiling tayi tace light food kawai zanyi maku tunda dare, bata jira amsar shi ba ta fice daga dakin.
Shawarma tayi musu ta dama coker oats, sanan ta gasa musu kifi ragon ruwa ta dibawa inna hansatu nata ta shiga toilet tayi wanka ta shirya cikin wani cotton material red and green, fitted gown ce tayi mata kyau sanan ta yafa gyale tayi wanka da turare ta koma asibitin. Suna idar da sallar magrib ta shiga dakin, dake da alwarta kawai saita tada salla bayan ta idar tayi addua, sanan ta nade sallaya ta samu waje ta zauna sultan ne yazo ya kwanta akan cinyarta sai surutu yake mata, ita kuma ta biyeshi sai dariya take. Sunata hirar su da sultan ta zuba mishi abincin yana gamaci yayi bacci, kawai saita kwantar dashi akan kujera, har aka kira sallar isha'i ta mike tayi, shima Asa's ya tashi yayi bayan ya idar ta zuba mishi abincin tace yaci, shawarma uku tasaka mishi sai gashi duk ya tashi dasu, shi kanshi abin ya bashi mamaki sbda ya dade beci shawarma me dadin wacce aysha ta kawo mishi ba.
Suna zaune shiru kmr kurame har wajen 9:15pm, sai kawai ta mike ta kade musu kan gadon ta dauko wani bedsheet din ta canja, Dr kamal ne ya shigo dakin da sallama shi, sbda tsabar firgita kasa amsa mishi sallama tayi, cikin guilty conscious tace dama yau zaka dawo amma dazu da mukayi waya baka fadamin ba? Cikin basarwa yace yap, so nake nayi surprising dinki, murmushin karfin hali tayi tace welcome back yace tanx, amma me kike acikin asibiti yanzu kuma in mofty? Cikin faduwar gaba tace broda na nazo dubawa, kallon Asa's tayi tace wanan shine Dr kamal, medical director na asibitin nan, kuma my husband to be insha Allah, ji yayi gabanshi ya fadi kuma besan dalilin hakan ba, a lkci guda kuma dadi ne ya kama Dr kamal, sabda koba komai yasan ba soyayya a tsakanin su. Amma a fili sai yayi smiling yace au dama Mr Asa's brother ki ne bansani ba? Mikawa Asa's hannu yayi yace salamu alaikum Mr Asa's ya jiki? A hnkli yace da sauki, Allah ya kara sauki yace amin, ai INA ganin gobe ma zamu sallame ka sbda naga jikin da sauki, smiling Asa's yayi yace Allah ya kaimu, sanan ya kalli aysha yace idan kin gama kizo na mayar dake gda tace to.
Yana fita tace na gyra maka shimfidar kaje ka kwanta, sanan ta dauki sultan zasu fita yace ina zakije min da Da? Zamuje dashi gdnmu ya kwana, aa ajiye shi, meyasa? Sbda ban amince ba, to shikenan gud nyt be amsa mata ba kawai ta Debi food flasks dinta ta fice
Maman Aysha
[24/05 9:21 PM] Mizz Ayuush: [4/8, 21:06] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
8⃣5⃣➖9⃣0⃣
A bakin mota ta sami Dr kamal, ya bude mata kofa ta shiga suka tafi. Saida yakaita har kofar gda tana kokarin bude kofar taji yasa lock, juyawa tayi ta kalleshi kawai sai taga yasha mur, Bakiyi mamakin dawowa ta yau ba? Aysha fushi fa nake dake, meye hadinki da Asa's? Ya akayi Asa's ya zama brother ki? Gabanta taji ya fadi, cikin kuskunda tace magana ta gasky bani da wani hadi dashi, to meyasa kika dauki responsibility din shi tro out his admission? Wallahi danshi sultan nakeso, sbda shi nayi mishi duk abinda nayi, kin tabbata bason Asa's a zuciyar ki? Wallahi babu yaya kamal, OK to shikenan, tun INA India mutane suke tura min text message cewa kinyi sabon saurayi patient kuma ke kike zama a wajen shi, raina ba karamin baci yayi ba shiyasa na taho yau batare da nagama abinda naje yi ba, inada mugun kishi banason kowa ya rabeki, Asa's yanada kudi, yanada kyau, he is very smart and handsome, ina tsoron kar zuciyar ki ta fara sonshi, domin kuwa Asa's maza ma yana burgesu ballantana mata, don Allah Aysha karki juyamin baya, karka damu yaya kamal, ni kudi ko kyau basa gabana, insha Allah bazaka samu problem ta bangarena ba, I promise you, murmushi yayi yace to saida safe ki gaishe da inna, OK zatayi
Washe gari da wuri aysha ta hada break fast takai musu, saida taje tayiwa sultan sanan ta zuba mishi abinci yaci, soyayyen Irish ne da kwai, sai lafiyayyen kunun gyada da paper soup din kayan ciki, tana gamawa da sultan tayi serving Asa's ma ya zama yayi yaci ya koshi, sana ta zauna sultan yanata mata shirme, phone dinta taji ta fara kara, tana dauka kafin tayi magana taji ance yallabai mun shigo a ina zamu sameka? Mamaki ne ya kamata tace yallabai kuma? Ina ganin wrong no ne fa, fisge wayar Asa's yayi daga hannunta yace Sulaiman Ku tambayi kamal specialist privt hosp, yace to yallabai. Cikin10 minutes suka karaso kusa da amenity ward akwai wani katon fili a wajen suka sauka da helicopter dinsu, sanan Sulaiman ya kara kira ta layin aysha yace sun shigo, Asa's yace to su tambayi amenity ward, kallon aysha yayi yace jeki taho dasu, tace to tana fita ta gansu, a tare suka shiga dakin, wit respect dukansu suka gaishe shi, sanan Sulaiman ya bashi Sabin kaya daya taho mishi dasu, kuma ya bashi cheque book dinshi dayace ya taho mishi dashi, sanan suka fita don su bashi waje ya shirya.
Wani danyan boyel ne ash color da kudinshi zai kai 150k akayi mishi aiki da light pink zare, sanan ya dauki hula zanna bukar me adon ash da pink ya Dora, yana cikin fesa turare Dr kamal da Dr suraj suka shigo dakin bayan sun gaisa suka rubuta mishi magani, Dr kamal banda kallon shi ba abinda yake sbda yau ne ya fito a ainihin Asa's dinshi, ba karamin kyau yayi ba, wani kishi ne ya kama Dr kamal, q yanzu idan aysha ta ganshi ya zataji? Karfa wanan shu'umin kyan nashi ya rudeta ta canja ra'ayi akaina, oh my god anya kuwa zan yarda aysha ta ganshi acikin dressing din nan? Asa's ne ya katse shi da cewa don Allah doctor aramin pen din ka, yace to, cheque ya rubuta musu na 2, 2 million shida suraj kowa ya mika mishi nasa, sanan yayi musu godiya sosai, sakar baki suraj yayi sabda tsabar farin ciki, shi kuwa kamal ya rasa me zaiyi murna ko kishi? Suma godiya sukayi mishi sosai Asa's yayi smiling irin na masu kudin da suka amsa sunansu yace a haba ba komai.
Aysha ce ta shigo dakin ita da sultan suna hada ido da Asa's taji gabanta yayi mummunan faduwa Amma dake she is very smart saita basar, Dr kamal ta kalla tace gud morning sir, morning how are you? Iam fine, yaushe ka shigo? Kuna waje mukazo muka wuce baki kula ba, smiling tayi tace OK, Asa's ne ya kalli Dr kamal fuskarshi dauke da murmushi yace Dr kamal don Allah kayi min izini nayi magana da fiancé dinka, murmushin karfin hali kamal yayi yace ba matsala, fita sukayi gabadayansu har sultan, Aysha da Asa's kawai aka bari a dakin, shiru dakin yayi for some minutes, sanan yace Aysha congrats, gaskiya kin iya business saida INA me baki shawara ki canja salon business din naki, domin kuwa idan yanzu kinci riba wataran zaki iya faduwa. Dr suraj ya fadamin kin kashe min kudi yakai 100k ko? To shiyasa ni kuma nayi miki doubling dinshi, wanan cheque ne na 200k, Ina fata ribar Dana baki batayi miki kadan ba?
Maman Aysha
[4/9, 09:21] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
9⃣0⃣➖9⃣5⃣
Maganar Asa's ba karamin zafi tayi mata ba, idan da abinda Aysha ta tsana a duniya shine kace tanada son zuciya. Idonta ne ya kada yayi ja sabda bacin rai, kallon kwayar idonshi tayi tace idan kana tunanin sbda INA Neman wani Abu a wajenka na temaka maka, to ka tafka babban kuskure, idan ka manta bari na tuna maka lkcn da aka kawoka asibitin nan you're unconscious, su Kansu doctors din da suke kanka basu da hope din zaka tashi ko bazaka tashi ba, Idan har business zanyi dakai ta yaya zanyi business da mutumin da besan inda kanshi yake ba? Kuma inaso ka sani a lkcn dana dauki niyar temakon ka bansan a wane daki kake ba, sai bayan nace zan temaka maka ne aka rakani dakin da akayi admitting dinka, kuma harna temaka maka bansan kai ko waye ba, so inaso ka sani sbda Allah da kuma danka sultan na temake ka, dukiyar mutun ko mulki ko kyau basa gabana kuma basu taba burgeni ba. Sbda haka kaima INA me baka shawara ko nan gaba ka ringa yiwa mutun kyakkyawan zato, na barka lpya. Basket din data zuba food wormers dinta ta dauka ta fice daga dakin, tana fita yabi bayanta a tare suka fita waje, da sauri body guards dinshi sukazo suka tare shi dama yasa a bawa duk wani mutun da yake morning duty a ranar kyatar dubu biyar har sub staff din asibitin, aikuwa mutane suka cika bakin wajen suna mishi gdya, sanan suka rankaya zasu rakashi inda helicopter yake,
Ita kuwa aysha mikewa tayi ta nufi hanyar gate, sultan yana ganin bata bisu ba ya tafi da gudu ya rungume kafarta yace aunty aysha ni a wajen ki zan zauna, durkusa wa tayi agaban shi nan take hawayen da take kokarin rikewa suka fara zuba, hugging din sultan tayi tace kayi hakuri my boy, zanzo har gda na dauke ka kaji? Kuka ya fara yana cewa ni bazan tafi ba, Asa's ta kalla cikin shan mur tace zo ka rarrashi shi. Karasowa wajen yayi jiki ba kwari yace tashi mu tafi sultan zuwa zamuyi mu debo kayan ka sai a dawo dakai wajenta kaji? Dagowa yaron yayi yace daddy har motana da keke na zaa dauko min? Yace eh mana kaga saika ringa wasa a wajen aunty aysha ko? Dariya yaron yayi ya mike yace idan aka dauko kayan wasana dake zamu ringayi ko aunty aysha? Smiling tayi tace eh mana, zanje gda na jiraka saika dawo kaji my boy. Kama hannunsa Asa's yayi suka tafi, sultan sai jiyowa yake yana daga mata hannu, ita kuma ta dauki kayanta ta nufi bakin gate.
Kamal ne ya dauki motarsa yabi bayan ta, har ta tsayar da me keke napep yace ya tafi, sanan ya bude mata mota ta shiga. Dubanta yayi yace naga yau gabadaya Kin damu meke faruwa ne? Wallahi nayi missing din sultan, INA son yaron sosai, hamm Allah yasa ba har Baban yaron akayi missing ba? Haba doctor don Allah, sau nawa zan fada maka cewa Asa's baya gabana? Wallahi ban taba jin koda digon sonshi a zuciyata ba, kai kadai nake so kuma insha Allah kai zan aura, murmushin jin dadi yayi yace Allah ya tabbatar mana, idan kin shiga gda ki fadawa inna hansatu next WK su daddy na zasu zo maganar saka ranar bikin mu, kuma idan zai yiyyu banaso ya wuce 1month, smiling tayi tace ka fada mata da kanka ko ka tro wani Kasan tsofi da fitina saitace nayi rashin kunya, shima dariya yayi yace to zan aiko a fada mata, sanan sukayi sallama ya tafi. Tana shiga gda ta kwanta akan cinyar inna tace inna Dana ya tafi ya barni, inna ta tausaya mata sosai sbda tasan yadda takeson sultan tace kiyi hakuri aysha dole nasan wataran zasu nemeki, dariya aysha tayi tace uhm bari na dagaki keda ba ishasshiyar lpya ce dake ba, daki ta koma ta kwanta sbda tunda aka kwantar da Asa's bata samu tayi bacci sosai ba.
Mum ba karamin farin ciki tayi ba da dawowar su Asa's, same da yayi wanka yaci abinci ya huta sanan ya bata lbrn duk abinda ya faru, har kulawar da aysha tayi musu, saidai ya boye rashin mutuncin da yayi mata. Mum tai ta ciwa aysha albarka.
Tun ranar da suka koma kullum sultan sai yayi kuka a mayar dashi wajen aysha, idan dare yayi da kyar yake kwanciya, Amma duk da haka Asa's yaki, sbda shi yanzu baya kaunar abinda zai kara hada su da aysha duk da kuwa shima yana tunata yakai sau bakwai a rana, more especially girkinta me dadi domin kuwa yanzu a dole yake cin abinci, yayi missing din girkinta sosai
Maman Aysha
[4/9, 12:43] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
9⃣5⃣➖1⃣0⃣0⃣
Soyayya me karbi aysha da Dr kamal suke bugawa, ita tama manta da wani Asa's amma time to time tana tunanin sultan, wani lkcn saitaji kamar ta kira no mum din Asa's ta hadata da sultan dake tun lkcn da ya kira mum da wayarta tayi saving, amma kuma saita fasa sbda tsoron rashin mutuncin sa. Tun ranar da kamal yace zai tro iyayensa gdnsu aysha kullum tana zuba ido taji yayiwa inna magana amma shiru, itama kawai saita hakura ta kyale shi.
1 month later
Yauma kmar kullum aysha suna zaune suna hira da inna dake off take, saiga Dr kamal ya shigo gdn bayan sun gaisa da inna yace mata Baban shi yace a fada musu acikin satin nan zasu zo maganar sa rana, inna ba karamin murna tayi ba tace Allah ya kaimu, Amma ka fada mishi ba nan garin zasu ba Bauchi zasu je wajen dangin mahaifinta sbda haka idan sun fadi ranar da zasu saika fadawa Aysha muyi musu waya, yace to shikenan. Tashi inna tayi ta basu waje sukaci gaba da hirar su. Washegari kamal ya fadawa aysha cewa ranar Saturday su abbanshi zasu Bauchi, tace to. Inna ta fadawa, ita kuma tace ta kirasu da kanta ta fada musu sbda ita bata shiga harkarsu. Phone dinta ta dauko ta fara dialing no babban yayan su mahaifinta alhaji Auwal, bayan sun gaisa ta fada mishi ranar Saturday zaa zo Neman auranta wajensu, hawanta yayi da fada Saturday jibi fa kenan? Kuma Dan iskanci baki fada min da wuri ba sai yau? Toni banida kudin dazan tare su, hawaye ne suka fara zuba a idonta tarasa kiyayyar da 'yan uwan babanta suke nuna mata, daurewa tayi tace zanyi maka mobile transfer na 50k yanzu, sai kuyi amfani da ita, ba kunya yace to Allah ya kaimu tace amin. Bayan sun gama wayar ta zauna tayi ta kuka inna tana rarrashinta
2days later
Yaune familyn su kamal zasu je Bauchi Neman auran aysha, tunda safe wajen 9am inna tace kira kamalu kiji ko su dad din shi sun tafi Bauchi, tace to. Tana kira taji switch off, tace wayar shi a kashe take, inna tace to bari kya kara kira anjima tace to.
Shiru kamal be kira ba, kuma idan ta kira har yanzu switch off, wajen 3:00pm baffanta ya kira yace ke bakin nan naki zasu zo kuwa? Karfa su bata mana lkci mu basu barmu mun fita harkokin gabanmu ba, su basu zoba. Cikin sanyin jiki tace insha Allah zasu zo baffa, INA ganin basu fito da wuri bane, to Allah yasa, wa yasani ma kosaida kuka gama yawon barikinku sanan zaayi mgnar auren. Ki kirashi ki kara tambayar sa idan ba zasu zo ba kowa ya watse ya tafi harkar gabanshi, tace to da murya a sanyaye.
Har bayan sallar isha'i no kamal a rufe take, baffanta ya kirata yayi mata zagin rashin mutunci yace karta kuskura ta kara sasu acikin shirmen maganar aurenta. Yana kashe wa kiran kamal ya shigo wayarta tana dauka yace ta fito yana kofar gdn su, a zuciyata tace yau kuma a waje ya tsaya? Hijabinta tasa ta fita, tana zuwa ta tarar ya kifa kanshi a ajikin mota. Ji tayi gabanta yana faduwa a hankali tace doctor meke faruwa ne? Juyowa yayi yace komai ma ya faru aysha, mum dina taki amince min na aureki, ta Dade tana nuna tsana da kyama a gareki, Amma ban dauki abin serious ba sai yau da tace idan na sake na aureki saita tsine min, kuma ta hana su dad suje Bauchi yana kuka yace bansan meye abinyi ba aysha, INA cikin wani hali Wallahi yanzu menene mafita? Ji tayi kanta ya Sara cikin dauriya tace mafita daya ce ka hakura da aurena, ka auri zabin mahaifiyar ka indai kanason gamawa da duniya lpya, batajira yace komai ba ta koma gda da gudu, tana zuwa ta fada jikin inna, shikenan na rasa kamal inna, mum dinshi tace bata yafe mishi ba idan ya aureni, meyasa rayuwa take juyamin ne inna? Keda kamal ne kawai kuke sona, meyasa kowa ya tsaneni? Ban taba ji ajikina cewa bazan auri kamal ba, na gama yarda cewa kamal ne mijina, ban taba son wani a duniya ba kamr yadda nakeso kamal, banida wani buri da wuce na auri kamal meyasa saida burina ya kusa cika komai ya wargaje? Tari inna ta fara cikin hanzari aysha ta dago kai, inna tari kike? Ya salm kiyi hakuri inna kar ciwon zuciyar ki ya tashi, indai nice na hakura, na mika dukkan al amari na a wajen Allah, damuwar da nake ciki yanzu is minor akan ace ciwon zuciyar ki ya tashi, zuwa tayi ta dauko mata magani tasha, bayan tarin ya tsirga inna tace kiyi hakuri Aysha gobe in Allah ya kaimu zanje na roki Maman kamalu tayi hakuri ta barshi ya aureki, aa karki je inna, indai nice Wallahi na hakura, don Allah karki je sai taga kmr ma Ku dinsu muke so, inna tace to shikenan.
Saida inna tayi bacci sanan ta tafi dakin ta, kwana tayi batayi baccin kirki ba, da asuba bayan ta idar da salla ta fara kwararo addua tana kuka. shesshekar kukan aysha inna ta jiyo ba karamin tausayi ta bata ba, tasan yadda aysha takeson kamal dama zata sha wahala kafin ta cireshi a ranta, ta kudiri niyar gari yanayin haske zataje gdnsu kamal
Maman Aysha
[4/9, 23:55] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
1⃣0⃣0⃣➖1⃣0⃣5⃣
Aysha na cikin yin addua ta fara gyangyadi, sai kawai ta kwanta nan take bacci me nauyi ya dauketa sbda dama batayi bacci da daddare ba. Inna na ganin haka ta dauki hijabinta ta fice, bata zarce ko ina ba sai gdn su Dr kamal, masu aikin gdn tayiwa mgna tace su kira mata Hajiya, da takama da komai tazo bayan sun gaisa tace lpy? Inna tace lpya kalau, karkar aysha wacce danki kamal yake nema, eh naganeki ai, meya faru,? Dama zuwa nayi na rokeki don Allah kiyi hakuri ki amince da auran yaran nan, sbda Wallahi suna son junansu kuma bakisan abinda Allah ya shirya ba,,,,,,yimin shiru da Allah, wanan dalilin ne yasa kika bugo sammako Kika zomin gda? To bari kiji ni bana son talaka, kuma bana kaunar abinda zai hadani da talaka, in banda zulama da son zuciya ai kinsan Dana ba saan auren jkar ki bane, me kuke dashi? Ita Ayshan cefa take nemo muku abinda zaku ci, kuma ita dinma a karkashin kamal take aiki, kinga kenan idan ya aureta ba wani improvement daya samu, sbda haka indai ina raye kamal bazai auri jikar ki ba gara tunda wuri ki fadawa jikarki ta fita daga harkar shi domin kuwa na samo mishi matar dazai aura, nan da wata daya zaa daura auren. Mikewa inna tayi ta fita tana fara tfya taji dyspnea nan take ta fara jin palpitation, taje daidai gate taji kirjinta ya rike bazata iya cigaba da tafiya ba, kawai saita zube ta kwanta a kasa flat.
Fitowarsa kenan zai shiga mota kawai saiyaga mutun a bakin gate a kwance, da gudu ya tafi kanta yana zuwa yace ya salm inna, da sauri ya dauketa yasata a mota direct asibitin shi ya wuce yana zuwa ya dauketa ya shiga emergency da ita, resuscitating dinta yayi wajen doctors hudu ne akanta Da kyar suka samu numfashinta ya dawo, Dr suraj ne ya kira wayar aysha tana cikin baccin ta me dadi taji phone dinta tana ruri, tana dubawa taga Dr suraj, hello likita ka tashi lpya? Lpy kalau Aysha, kizo asibiti yanzu don Allah, meya faru? Inna ce na lpy, inna kuma? How comes muna gda daya bansani ba? Eh ta fita unguwa ne, abin ya sameta a hanya, ji tayi gabanta ya fadi kardai gdnsu kamal inna taje? Hijabinta ta dauka ta fita da sauri ta tari me keke napep.
Lkcn data shiga IUC ba lefi tana numfashi da kanta, da gudu aysha taje ta rike hannun ta tace oh my god, inna meya sameki? A hankali ta bude idonta, tana magana dakyar tace aysha kinzo? Tace eh. Yawwa aysha dama inaso na ganki kafin lkci yayi. Naje gdnsu kamalu munyi magna da babarshi, amma a yanda nake gani aurenki dashi bame yiyyuwa bane, INA ganin dama Allah be kaddara kamal a matsayin mijinki ba, nasan zaki fuskanci kalubale a rayuwar ki nan gaba, Amma duk yanda kika tsinci kanki kiyi hakuri ki mika al amuranki ga Allah, ki zamo me hakuri da kuma yarda da kaddara mekyau ko marar kyau......tari ne yaci karfin ta nan take ta fara gasping da sauri aysha ta fara kiran likita, a sukwane suka zo da sauri aka mayar da ita cardiac position, sanan aka sa mata oxygen, hannun tasa ta rike na aysha sai kuma ta fara salati a hnkli, tun kafin takai karshe harshenta ya karye, sai kuma sukaji dif, doctor yasa Statescope yaji bata numfashi, ya taba pulse dinta ma yaji babu, kawai saiya nemi kujera ya zauna sbda wani mahaukacin jiri dayake Neman daukar shi.
Cikin tsananin tashin hnkli da fargaba aysha tace likita meya faru? Don Allah kar kace min Inna ta rasu kaji? Likita ka fadamin cewa inna tana nan da ranta don Allah, kawai saita fada kan gawar tana wani irin kuka me ban tausayi, inna don Allah karki tafi ki barni a lkcn da nake tsananin bukatar ki, jijjiga ta take tana cewa inna don Allah kiyi min magana mana, kinsan fa kece gatana, kece uwata kece ubana, meyasa zaki tafi ki barni? Wayyo ni Allah na,,,,,,,kawai saita sulale ta fadi a wajen, da sauri Dr kamal ya dauketa ya Dora akan gado, aka dauko ruwa me sanyi aka yayyafa mata, nan take ta bude ido a zabure ta mike tana cewa don Allah ku cemin mafarki nake, don Allah kucemin abinda yake faruwa yanzu ba gaske bane, Dr suraj ne yace haba aysha kefa musulma ce, kuma kinada addini, amma ya kike son yin Abu kamar bakida ilimi? Kisani cewa mutuwar nan duk ita muke jira, kuma burin duk wani musulmi shine ya cika da Kalmar shahda a bakin shi, kinga inna ta cika da ita, wanan shiya tabbatar mana cewa insha Allah zata samu rahamar Allah. Don Allah kiyi hakuri ki daina kuka inna tafi bukatar addaar ki akan komai yanzu, kallon kwayar idonshi tayi tace kenan da gaske inna ta mutu ko? Inna lillahi wa inna ilaihir rajuun, sai kuma ta kara fashewa da wani irin kuka. Duk Mutanen da suke wajen ba Wanda beyi kuka ba. Allahu Akbar kabira Allah yasa mu cika da imani kuma muyi kyakkyawan karshe😭 😭
Maman Aysha
[4/10, 20:26] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
1⃣0⃣5⃣➖1⃣1⃣0⃣
Dr kamal ne ya kira driver ambulance din asibitin aka tafi da gawar, sanan Dr suraj ya tafi da aysha a motarsa. Tun kafin a tafi da gawar akayiwa 'yan uwan inna waya, kafin su karasa mutane sun cika kofar gadn, mata kuma sun cika cikin gdn. Maryam Nasir amiyar aysha ita ta kama hannunta suka shiga cikin gdn. Har akayiwa inna wanka aysha bata cikin hayyacinta, bayan an gama hadata aka ummarceta da tazo tayi mata addua. Wata nutsuwa yace ta zoma aysha ta zauna tanata kwararo addua ita da yan uwan inna Wanda suke ciki daya da ita, bayan sun gama wasu kannen inna maza guda biyu sukazo zasu dauki gawar, wayyo Allah zo kaga tashin hnkli a wajen aysha, rike makarar tayi tace bazaa tafi da ita ba wani irin kuka take da duk rashin imanin mutun saiya zubar mata da hawaye, dakyar aka bambareta daga jikin gawar aka fita da ita, Ana fita da gawar ta zube a kasa sumammiya. Haka tayita suma tana farfadowa, saida wani malami ya zaunar da ita yai mata nasiha me ratsa jiki sanan ta sami nutsuwa.
2days later
Yau kwanan inna biyu kenan da rasuwa, gobe zaayi sadakar uku. Ba lefi Aysha ta ware sosai saidai har yanzu taki cin abinci, ruwa me sanyi kawai take sha idan anyi mata fada taci abinci saita fashe da kuka. Da rana ta mike zatayi alwalar sallar azhar kenan jiri ya kwasheta ta fadi, da sauri aka kira Dr kamal da suraj Sbd dasu ake zaman makoki a waje, daukar ta sukayi aka tafi asibiti tare da aminiyarta Maryam. Hypoglycemia ne yake damunta sbda rashin cin abinci, dextrose saline aka daura mata, sanan sukayi mata wasu allurai. Bacci ne me karfi ya dauketa,
Maryam da suraj ne a wajenta, a amenity room 4 akai admitting dinta, nan take Dr suraj ya tuno da yallabai Asa's, nemo no shi yayi acikin wayarsa sabda dama yanada ita, ya taba kiranshi sau biyu sai PA dinshi ya dauka yace baya kusa ya kira later, dayaga haka kawai saiya hakra. Saida yayi addua ya fara dialing no, har ta kusa tsinkewa sai kawai yaji an dauka, yallabai Asa's ne da kansa bayan sun gaisa yace Dr suraj na asibitin kamal specialist jalingo, da faraarsa yace eyya doctor ya garin kwana biyu? Wallahi kuwa, dama kira nayi na fada maka Allah yayiwa inna kakar aysha rasuwa, inna lillahi wa inna ilaihir rajuun, yaushe ta rasu? Yau kwana biyu, to INA Aysha? Gata a asibiti on admission, ya salm, Allah ya jikan inna da rahama, INA nan zuwa nanda 2hours insha Allah, to shikenan yallabai saika karaso, sanan sukayi sallama ya kashe wayar.
Mutuwar inna ba karamin taba Asa's tayi ba, tunota ya ringayi ranar da taje duba shi tanata tsokanar shi, jiki ba kwari ya koma gda, kallo daya mum tayi mishi ta gane akwai abinda yake damunshi, cikin zumudi tace my son What's wrong? Wallahi kakar yarinyar nan da nace ta temaka min a jalingo ce ta rasu, cikin damuwa mum tace kakar aysha zakace min, ai harna rike sunanta sbda sonda sultan yake mata, ban taba ganin ta ba, Amma har naji inason yarinyar a zuciyata. Allahu Akbar kabira yaushe ta rasu? Yau kwana biyu, yanzu wanka zanyi mu tafi dasu Sulaiman, tunda gobe ne sadakar uku zamu kwana idan anyi addua da safe sai mu taho, aikuwa nima zanso naje nayi mata gaisuwa, to shikenan ranar sadakar bakwai ma koma dake, to shikenan Allah ya kaimu yace amin.
Daki ya shiga ya cire suit din jikin shi, sana yayi wanka ya shirya cikin wani filtex Skye blue, kudin shi zaikai 200k, sanan ya dauki wata farar gezna dazai saka gobe, yayi wanka da turare, sanan ya dauki duk abinda yasan zai bukata ya zuba a jaka.
Sallama yayiwa mum sanan ya shiga helicopter dinshi suka dauki hanyar jalingo shida su Sulaiman
Maman Aysha
[24/05 9:21 PM] Mizz Ayuush: [4/11, 21:25] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
1⃣1⃣0⃣➖1⃣1⃣5⃣
A inda suka sauka lkcn da sukazo daukar Asa's suka tsaya, sanan suka karaso bakin dakin. Dialing no suraj yayi yana dauka yace gamu a bakin amenity ward, da sauri Dr suraj ya fito ya taresu suka shiga ciki, har lkcn Aysha bacci take, kujera ya ajiye a bakin gadon ya zauna ya zuba mata ido yana kallonta gani yayi duk ta rame saiyaji tausayin ta ya kamashi. PA ya kalla yace kuje sami muddibo ya rakaku Ku kama mana daki guda biyar a hotel din dayafi kowanne kyau a garin nan, sai kawai Ku zauna kuci abinci Ku huta ni saida daddare zan taho, yace to shikenan.
Sai bayan sallar magrib aysha ta farka, tana bude ido taga Asa's a gefenta a zaune da farko tayi zaton mafarkin da ta saba yi ne, shiya katseta da cewa sannu Aysha ya jikin? Mikewa tayi a hnkli ta zauna, sanan tace da sauki, ya hakurin inna? Tace alhamdulilla, Allah ya jikanta tace amin. Mamaki take tayi ko waye ya fada mishi, katse ta yayi da cewa ance bakya cin abinci, inaso yanzu ki fadamin me kike so kici? A hnkli tace ni bana sha'awar komai, uhm uhm Aysha, don Allah kiyi hakuri kici wani abin kinji? Ya kamata kiyi hakuri kuka ko kin cin abinci bashi zai dawo miki da inna ba, Inna has gone, she Will never come back again Sbd haka ki saki ranki kici gaba da walwala yanda kika saba, Sbd wanan kukan da kike is like kmr kina jayayya ne da ikon Allah ne, so kiyi hakuri ki zamo me tawakkali kinji? Kai ta daga mishi, cikin sanyin murya tace ngde.
Ice cream da gashasshiyar kaza yasa aka kawo mata, saida ya matsa mata sosai sanan taci, bayan ta gama Dr suraj ya debesu a motarsa yakai aysha gda, sanan ya wuce da Asa's hotel din daya sauka
Washe gari aka Tara mutane masu yawa akayi addua, bayan an ragu Asa's ya tura PA dinshi sukaje kasuwa suka sayo duk wani Abu da yasan zaa bukata, tunda ga kan buhuhunan shinkafa, taliya, kayan tea irin manyan gwangwanin nan, sabulai, man turkey etc, yasa aka shiga dasu ciki, sanan ya shiga har cikin gdn yayiwa 'yan uwan inna mata gaisuwa mutane banda kallonshi ba abinda suke, da yayi musu magana mamaki suka ringayi su duk a zatonsu be iya Hausa ba. Har dakin da Aysha take ya shiga, tana zaune da kawayenta suna ganin Asa's sukayi mutuwar zaune, dukansu ba wacce batayi falling ba, hakuri ya kara bawa aysha sanan yace zai dawo ranar sadakar bakwai. Godiya tayi mishi sosai, tace ya gaishe mata da sultan. Har kofar gdn su aysha su Sulaiman sukazo suka daukeshi suka tafi
Maman Aysha
[4/12, 18:26] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
1⃣1⃣5⃣➖1⃣2⃣0⃣
Ranar da akayi sadakar uku kowa ya watse sai 'yan uwan inna na jikinta ne suka zauna sai anyi sadakar bakwai zasu tafi. Abinda yake daurewa aysha ai shine har yanzu a 'yan uwan mahaifin ta ba Wanda yazo mata gaisuwa, kuma tun washe garin ranar da akayi rasuwar ta kirasu ta fada, ta rasa irin kiyayyar da suke nuna mata.
A bangaren kamal kuwa tunda akayi sadakar uku be kara komawa gdnsu Aysha ba, sbda yanzu kunyar hada ido da ita yake, duk lkcn daya tuna cewa mum dinshi ce sanadiyar mutuwar inna saiyaji ya rasa inda zai sa kanshi sbda bacin rai, ya tsani halin mahaifiyar shi dandai ba yadda zaiyi da ita ne. Hankalinsa be kara tashi ba saida yaji lbrn Maryam nasir kawar aysha mum take son aura mishi, yayi kuka kmar ransa zai fita har zuwa yayi ya durkusa agaban ta yana hadata da Allah akan tayi hakuri ta barshi ya auri Aysha, amma fur taki tace idan ya auri Aysha saidai bayan ranta, sbda wai yan gari duna zargin Aysha ba yar halak bace shiyasa dangin ubanta suke kinta. Tunda daga ranar ya rufe kanshi a daki baya zuwa ko ina, gashi kuma dad dinshi tsoron mum yake duk abinda ta fada dashi yake amfani.
Yau akayi sadakar 7 bayan anyi addua kowa ya watse iya kannen inna kawai aka bari su biyu zasu zauna da aysha. Da daddare bayan anyi sallar isha'i kamal ya shigo cikin gdn har daki ya shiga ya sami Aysha bayan sun gaisa yace aysha zuwa nayi na baki hakuri akan abinda mum dina tayi miki, don Allah kiyi hakuri, Wallahi bakiga yanda nake bakin cikin kasancewa danta ba, ina tsananin sonki aysha, banajin zan iya bin umarnin mahaifiyata alfarma daya nake nema awajenki ki amince min na aureki a tabiyu bayan na auri wacce mum takeso na aura. Cikin muryar kuka tace bazai yiyyu ba kamal, tun ranar da inna ta rasu na fitar da ran zamuyi aure dakai, mum dinka bata sona, auranka ba abinda zai karamin face wahala da tsananin tashin hnkli, nasan INA sonka amma bazan iya auranka ba sbda kullum zan ringa ganin ka a matsayin mutumin da mahaifiyar shi tayi sanadiyar mutuwar kakata da tafi sona a duniya, mu hakura da juna shine kwanciyar hnklinmu, sabda haka don Allah kamal ka cire ni a zuciyar ka, ka manta dani a rayuwarka, ka zama me bin umarnin mahaifiyar ka sbda aljannar ka tana karkashin kafarta, kuma ka ringayi mata addua Allah ya shiryeta, inayi maka fatan alkairi dakai da wacce zaka aura.
Durkushewa yayi yana wani irin kuka me tsuma zuciya, shikenan aysha na hakura, amma inaso kisani bazan taba son wata a duniya kmr yadda nake sonki ba, kuma bazan taba mantawa dake a rayuwata ba, Allah ya baki mijin daya fini. Mikewa yayi ba tare da yayi mata sallama ba ya fice daga gdn, yana fita kuka me karfi yaci karfin ta koda wasa bata taba tunanin ba kamal zata aura ba, amma yau gashi tashi daya kaddara ta rabasu, Allah me iko kuma me yadda yaso, Allah yasa haka shiyafi alkairi.
Asa's ya kira suraj dake yanzu sun zama abokai yace mishi wata tafiya ce ta taso mishi zuwa London shiyasa bezo sadakar 7 ba, amma yabawa aysha hakuri insha Allah yana nan zuwa next WK.
Maman Aysha
[4/14, 09:52] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
1⃣2⃣0⃣➖1⃣2⃣5⃣
Washe garin ranar da akayi sadakar 7 su Aysha suka Debi kayan su suka koma gdn baba habiba kanwar inna, gda ne me kyau safe content yayan ta ne suka gina mata kuma suka saka mata duk wani Abu na jin dadin rayuwa, kuma tayi alkawari ita zataci gaba da rike aysha har zuwa ranar da zaayi auranta.
3days later
Wajen 12pm Aysha na zaune tana kallo a laptop dinta, dake baba habiba ta fita unguwa, saiga friend dinta Maryam Nasir ta wuntsilo a gigice, kana ganin ta Kasan tana cikin tashin hnkli, hannunta aysha ta kama ta zaunar da ita akan kafet tace kawata meya faru? Tana kuka tace komai ma ya faru, dazu mum dina ta kirani take fadamin wai ni zasu aurawa kamal, abin yayi matukar bani mamaki, kuma ya daure min kai, aysha bansan da yaya zaki karbi mgnar ba, amma Wallahi bansan komai ba sai yau data fadamin. Ke kawatace danake tsananin so aysha sbda haka bazan taba yadda naci amanar ki ba, mum tanayi min barazanar zata tsine min idan ban amince ba, amma Wallahi saidai ta tsine min din sbda bazan iya cin amanarki ba aysha,,,,,,karki kara fadar irin wanan maganar Maryam, ai Uwa uwace ya zama dole kibi umarnin ta, kuma da gaske zata iya tsine miki din ko kin manta mum dinki da mum din kamal aminaine? Naji dadi kuma nayi farin ciki da ya zama kece matar da kamal zai aura, sbda dama ta dalilin ki na hadu da kamal, kuma dama akwai shakuwa me karfi a tsakanin Ku, kinga kenan soyayya bazatyi wahalar shiga tsakaninku ba. Ko kadan banga lefinki ba Maryam sabda na yadda da irin son da kike min, sbda ba yadda mum dinki batayi ba don ta rabamu sbda ni ba yar masu kudi bace, amma kika ki. Kinada kirki maryam, kinada hankali kinada tarbiya kina da hakuri na tabbata kamal ba zaiyi Dana sanin aurenki ba nan gaba, sbda haka indai sbda ni kike daga hnklinki don Allah ki daina, Wallahi na fahimce ki. Rungume aysha Maryam tayi tace nagode da kika fahimceni inayi miki addua Allah ya hadaki da mijin dayafi kamal komai da komai, Allah yayi miki jagaora a rayuwar ki aysha, tace amin, to amma ya kamal, kun hadu ne bayan ansaka muku rana? Ah ah bamu hadu ba, phone dinta aysha ta dakko ta fara dialing no kamal yana dauka tace idan kanada time kazo gdn baba habiba yanzu ka sameni, da rawar jiki yace to.
Cikin few minutes yazo kofar gdn, saidai yana ganin motar Maryam yaji gabanshi ya fadi, amma saiya daure ya karasa cikin gdn aysha tayi mishi umarni daya shiga falo, a zaune ya sami Maryam tana gaishe shi yayi kmr beji ba, aysha ce ta kalleshi tace Maryam tayi min bayanin duk abinda yake faruwa, shine na kiraka na nemi alfarma a wajenka, inaso ka sani Dan Adam baya taba wuce kaddara sa, kuma mijin wani baya taba auran matar wani, Maryam kawatce Dana yarda da ita 100%, sabda haka indai da gaske Ku masoyana ne na hakika inaso don Allah albarka cin sonsa kuke min kimin alkawari cewa idan Allah ya tabbatar da auranku zaku rungumi kaddara Ku zauna cikin aminci da kaunar juna, don Allah kuyimin alkawari zakuyi zama cikin farin ciki irin Wanda kowanne ma'auratan da suke son junansu suke, don Allah kuyimin wanan alkawarin ta karasa magana tana kuka, dakoda kamal yayi ya goge mata hawaye zuciyarsa banda zafi ba abinda take, goge mata hawayen yayi yace indai hakan zai saki farin ciki nayi miki alkawari aysha, Allah yasa haka shine mafi alkairi tace amin. Mum din Maryam ce ta kirata a waya tace tayi maza ta tafi gda tanason ganin ta. Da sauri ta mike tayi musu sallama ta tafi.
Bayan tafiyarta aysha ta Dade tana yiwa kamal nasiha, sanan daga karshe yayi mata sallama zai tafi saida ta rakoshi har bakin mota sanan ta juya ta tafi gda
Mum din kamal ce tazo wucewa ta kusada kofar gdn inna habiba kawai saita hango motar kamal aysha tana daga mishi hannu, cewa driver ta tayi yayi kwana zuwa kofar gdn.
Aysha na shiga gda ta kwanta akan gadonta ta fara kuka me tsuma zuciya, Allah sarki ni, shikenan mun rabu da kamal, shikenan soyayya ta da kml ta zama tarihi. Hayaniya ta jiyo a sakar gda tana fita taga mum din kamal ce, kallonta tayi tace wai ke wacce irin jarababbiyar yarinya ce? Wane irin asiri kuka yiwa Dana? Nace ban amince da auranku ba meyasa bazaki hakura ba? Na rokeki da girman Allah ki rabu da dana kona sami kwanciyar hnkli a rayuwata.......tun ranar da inna ta mutu na cire son danki a zuciyata, tun ranar da inna ta mutu na kudiri niyar bazan auri danki ba, sbda haka ki kwantar da hnklinki nayiwa kaina alkawari bazan taba auran danki ba koda kuwa shi kadai ne namiji a duniya..bata karasa maganar ba taji an rungemeta, tana dubawa taga sultan cikin tsananin farin ciki tace sultan yaushe kukazo? Wata kyakkyawar kamilar mata ce tace tun dazu muka shigo munga kuna mgna da wanan bewar Allah ne shiyasa muka tsaya, eyya Allah sarki sannunku da zuwa, Ku shigo ciki, ganin haka mum din kamal ta juya ta fice daga gdn. Fridge aysha ta bude ta debo musu faro da lemo ta ajiye, sanan taje ta kawo cups saida ta durkusa har kasa ta gaida mum, ta amsa da faraarta sanan tayi mata gaisuwa. Shiru wajen yayi for some minutes, sanan mum tace aysha naji duk maganar da kukayi dakeda matar da tafita yanzu, idan bazaki damu ba don Allah na tambayeki? Tana goge hawayen fuskata tace eh, don Allah inaso nasan lbrnki, kuma matar da fita wacece ita? Zama aysha tayi ta bata lbrn rayuwata gbdaya da Wanda ta sani, da kuma Wanda inna ce ta fada mata, mum ta tausaya mata sosai a zuciyar ta tace Allah sarki ashema marainiya ce, nasiha tayi mata sosai tace kowa a duniya yanada irin tashi jarabawar, tayi hakuri Allah yana tare da ita, sanan tace Ahamad da sultan sun bani lbrn irin dawainiyar da kikayi dasu mungode Allah ya saka miki da alkairi, tace amin. Mikewa aysha tayi zata Dora musu abinci, amma sai mum ta hanata tace suraj da Ahamad sun tafi suyi musu order abinci.
Maman Aysha
[4/14, 15:37] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
1⃣2⃣5⃣➖1⃣3⃣0⃣
Waya aysha ta dauka ta kira baba habiba da sauran yan uwan inna tace suzo anyi baki, kafin kace me sun cika gdn mazansu da mata. Bayan sun gama gaisawa mum tayi musu introducing kanta da cewa suna na Haj zainab sa'eed Ahamad sardauna, nice matar marigayi alhaji sa'eed sardauna, kuma Maman Asa's, kallon kallon suka farayi sbda yanda suke da dunbin dukiya amma ko kadan bata da girman kai.... ci gaba tayi dace musu don Allah idan ba damuwa inaso kubani Aysha taci gaba da zama dani, sbda tayiwa Dana abin alkairi da bazan taba mantawa dashi ba, kuma dama ban taba haifar 'ya mace ba, nayi muku alkawari zan rike aysha tamkar 'yar Dana Haifa acikina, don Allah kuyi min wanan temakon? Shiru kowa na wajen yayi, sanan babban yayan su inna yayi gyaran murya yace duk da bamu muke da iko da ita ba, dangin mahaifinta ne, su kuma sun sallama ta sbda wani dalili marar tushe, mun amince ki dauketa sbda duk Wanda yace yanason naka ya gama maka komai a rayuwa, Allah ya baki ikon riketa, cikin tsananin farin ciki mum tace amin nagode Allah yasaka da alkairi, idan kun amince zan dawo next WK na dauketa, saiku hadamu da wasu muje dasu suka gdna ko? Shikenan Allah ya kaimu tace amin, aysha ke kuma saiki shirya kayan ki zuwa next WK din ko? To HAJIYA nagode. Baba habiba ce tace ke Aysha ya har wajen karfe biyu baki Dora musu abinci ba? Mum ce tace ah Nina hanat, zaa kawo mana abinci yanzu, wato baxaku ci abincin gdnmu ba ko? Ba haka bane Wallahi, gani nayi bakusan da zuwanmu ba, kuma abokin Ahamad suraj ne yace zai kawo mana,,,,,,bata karasa rufe baki ba suka shigo hannunsu dauke da take away iri iri, bayan sunci abinci sun koshi Ahamad da suraj suka fita waje zasu yi salla, suka cewa mum ma tayi salla idan sun dawo zasu tafi.
Kafin suyi alwala Ahamad ya kalli suraj yace tunda nake zuwa garin nan, har yau banga Dr kamal ba? Meyake faruwa ne? Ya mgnar auren su da aysha? Cikin tausayawa suraj yace ai maganar auran nan babu ita? Meyasa? Sbda mum dinshi tace idan ya aureta saita tsine mishi, yanzu haka ma kawar Aysha zai aura, akwai matsala kenan a familyn Aysha ko? Ba wani matsala Kasan 'yan uwan Baban aysha basa kulata ko kadan, ba ruwan su da ita shine mum din kamal take zarkgi wai ko aysha ba yar halak bace shiyasa suke gudun ta, tofa! Meyasa kace zargi suke? Tunda kaji ta fada ai may ba tayi bincike, Wallahi zargi ne Mr Asa's, sbda inada lbrn aysha da komai nata, uhhm Allah ya rufa asiri suraj yace amin.
Masallaci sukaje sukayi salla, sanan suka dawo sukayi musu sallama suka tafi,ko wata cikekkiyar gaisuwa Ahamad da Aysha basuyi ba suka tafi, dakyar aka bambare sultan daga jikinta.
Suna komawa gda wanka kawai yayi ya kwanta, maganar da sukayi da suraj dazu ce ta dawo mishi, iam very sure Maman kamal tanada gskya, haka kawai bazata ki aurawa danta abinda ransa yake so ba, yanzu haka ma akwai abinda suraj ya boye min, sbda yanason aysha bazai fadamin gskya ba, wato dai mata duk haka suke, duk wacce ka taba akwai irin tata matsalar mittws Allah ya kyauta.
Washe gari suna zaune da mum suna hira tace mishi next WK zaka bamu Aron helicopter dinka zamuje jalingo mu taho da Aysha, bangane ba mum? Eh na roki iyayenta su barmin ita sbda naga sultan ya shaku da yarinyar, kuma gashi marainiya ce...nan dai ta bashi lbrn yadda sukayi dasu inna habiba, cikin bacin rai Asa's yace haba mum don Allah, ke kowa saiki rakito mana gda, yanzu duk abinda ya faru baki horu ba? Sbda kawai tana son sultan? Ai zuciyar mutun sai Allah mum, kuma personality of an individual cannot be judge, sbda haka baki da tabbacin tanada kirki ko bata dashi, don Allah mum kice musu kin fasa karki je ki dauko mana annoba muna zaman mu.....tun kafin naga yarinyar naji inason ta, Dana ganta sainaji zuciyata ta aminta da ita, sbda haka daukota ba fashi idan bazaka iya zama gda daya da ita ba to ka dauki danka Ku koma gnka, ni saina zauna da ita sbda halinta ya babanta dana sauran, kuma inaso kasani ba cewa nayi ka aureta ba, cewa nayi zan dakkota na riketa har Allah ya bata miji na aurar da ita. Cikin fushi Asa's yace shikenan Allah kaimu, tace amin
A weak later
Mum ta tura an dauko aysha, kuma su baba habiba sunzo sunga gdn kwanan su uku aka mayar dasu, hadaddan daki mum tawarewa aysha ta zuba matan kayan jin dadi a dakin irin Wanda ko iyayen da suka haifeta iyakacin abinda zasuyi mata kenan.
Maman Aysha
[24/05 9:21 PM] Mizz Ayuush: [4/15, 10:28] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
1⃣3⃣0⃣➖1⃣3⃣5⃣
Tunda aysha tazo basu hadu da Asa's ba, sbda idan sun hadu yana yawan jin gabanshi yana faduwa, kuma ya fuskanci aysha na da wata baiwa da acikin lkci kadan zakaji ta shiga ranka, ga Uwa uba kyau, shiyasa yake tsoro kar fitinannan kyaunta ya rinjayi zuciyarsa akan kudirin daya dauka na bazai kara aure ba. Kullum kafin ta fito da safe ya tafi office dake bata tashi da wuri, idan ya dawo da yamma kuma part dinsa yake wucewa, daddare saiya tabbatar aysha ta kwanta yake zuwa suyi hira da mum, wani lkcn ma idan yanada aiki da yawa ko fitowa bayayi saidai akai mishi abincin sa can.
Yauma kmr kullum aysha da mum suna zaune suna hira, sai aysha tace yawwa mum inaso muyi wata mgna, OK inajin ki aysha, cewa nayi da zaman nan da nake bana aikin komai meze hana na ringayi mana girki, sbda banajin dadin zaman haka, dariya mum tayi tace ni kuma nafiso 'yata ta kwanta ta huta, itama Aysha dariyar tayi tace ai dake ban saba hutun ba harna gaji Wallahi, to shikenan aysha indai kin fison hakan ai saiki fara, Amma fa bazaki iya girkin gdn nan gabadaya ba, saidai zansa a zuba kayan abinci a kitchen din part dina saiki ringa yimana abincin iya mu, sauran Mutanen gdn kuma sai kuku yaci gaba dayi musu a main kitchen, yaushe zaki fara kenan? smiling aysha tayi tace ko gebe da safe ma ko? To anjima da yamma saikuje kasuwar turai ta 'yan kaba ki sayo duk wasu vegetables da zaki bukata, sauran kayan abincin kuma suna babban store, kije ki duba idan da akwai abinda kk bukata kuma babu saiki fadamin asayo ko? To shikenan mum, Allah yayi miki albarka tace amin. Sanan mum ta kira kukunsu ta fada mishi daga yau karya karayin abinci dasu
Washe gari da wuri aysha ta shiga kitchen ta soya Irish da plantain, tayi paper soup din danyen kifi ragon ruwa dayaji spices da kayan kanshi, sanan ta dama kunun gyada na nikekkiyar shinkafa irin wanda ake zuba mishi madara, sanan ta dafa ruwan tea ta soya kwai, sanan tayi toasting din bread ta jera komai a dining, sanan ta haura sama ta shirya sultan itama tayi wanka tasa wata English gown Skye blue ta sami wani siririn mayafi ta yafa, tayi wanka da turare sanan ta kamo hannun sultan suka sakko kasa.
Tunda ta fara sakkowa daga bene gaban Asa's yake faduwa harta karaso, Amma dake namijin duniya ne ba Wanda ya gane. Shida mum ne a zaune, har kasa aysha ta durkusa tagaida mum sanan ta kalli Asa's tace ina kwana? Basarwa yayi kmr ba dashi take ba, ta kara gaishe shi for d second time still ya basar, mum ce tace bakaji ne ana gaisheka? Oh wai dani take? Batayi identifying ba so kinga bazan gane dani take ba, Aysha najin haka ta gane wulakanci ne kawai saita rabu dashi ta fara zubawa sultan abinci, bayan ta gama ta zubawa Asa's ma, tambayar shi tayi kunu zaisha ko tea? Shiru yayi kmar badashi take ba, kawai saita zuba mishi kunun ta juye mishi peak milk kusan rabi aciki, sanan tace ka zuba sugar da kanka. Juyawa tayitacewa mum na zuba miki yanzu? Ah sai anjima, hannun sultan ta kama suka zauna akan carpet tana bashi abinci a baki sbda karya bata uniform dinshi, har saida yace ya koshi, sanan ta dauko lunch box dinshi ta zuba mishi abincin dazai tafi dashi saida ta rakashi har mota sanan ta dawo.
A bangaran Asa's kuwa, daya yagi tsokar kifi yakai bakin shi saida ya lumshe ido sbda dadi, kunu kuwa kafin kace me ya tashi da cup daya harda kari, Irish din nema beci sosai ba shi kansa yasan yayi missing kirkin aysha, rabonsa da abincin ta tun yana asibiti, idan hakane mum ta temakeshi koba komai zai ringa cin abincin ta me dadi. Spoon yasa yana diban romon kifi yanasha, har saida ya shanye Wanda ta zuba mishi Tass, sanan yasa tissue ya goge bakin shi yayi wa mum sallama ya tafi.
Da rana ma haka aysha ta shirya musu hadaddiyar sakwara miyar egusi, sanan tayi paper chicken, ta hada lafiyayyen zobo da yaji kankana da cocomber, sanan tayi meat pie da cake zuwa 1:30 ta hada komai, ta zuba a wani haddaden basket ta bawa driver yakai wa Asa's office, sanan ta shiga daki tayi wanka tayi salla ta kwanta bacci.
Yana zaune a office yunwa ta fara damunshi kawai saiga driver ya shigo da abinci ya ajiye, ba wani bata lkci ya sakko ya fara diban girki, saida yaci ya koshi ya kora da ruwan zobo me sanyi, sanan ya kira driver daya kawo yace yaci saurian, saidai ya dauke guntun zobon yasa a fridge. Gyangyadi yaji ya fara, kawai saiya cewa Sakatare shi zai kwanta karya bar kowa ya shigo saiya tashi, mikewa yayi akan 3seater din office damag sanyin A/c tuni bacci ya dauke shi
Maman Aysha
[4/15, 12:20] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
1⃣3⃣5⃣➖1⃣4⃣0⃣
Sai la'asr ya tashi yayi alwala ya tafi masallacin kamfanin yayi salla, sanan ya dawo ya dauki guntun zubonsa yasha yaci gaba da aiki. A gajiye ya koma gda yana zuwa yayi wanka ya shirya cikin wata shirt me karamin hanu red color, da blue jeans, ya fesa turare ya fita golf clubes inda suke wasan golfs da friends dinsa. saida ya idar da sallar isha'i sanan ya taho gda, a falo ya sami mum ita kadai, aysha kuma suna daki itada sultan. Kallon mum yayi yace ke kadai? Ina sultan? Ai inajin yayi bacci ma, sbda tun dazu aysha tayi mishi wanka, OK, ni yunwa ma nakeji kwanan INA yawan cin abinci Allah yasa dai lpya dariya mum tayi tace idan rashin lpy ne ai bazaka iya ci ba, phone dinta ta dakko ta kira aysha tace tazo ta basu abinci. yau aysha tuwon semo tayi mata miyar danyen kubewa shi kuma sbda tasan baya son cin abinci da daddare saita yi mishi shawarma me dadin gaske tayi tsiren tukunya sanan ta hada kunun aya me kwakwa da madara tasa mishi a fridge. Fitowarta daga wanka kenan taga kiran mum, shaf shaf ta shirya cikin wata gown ta fesa turare ta sakko kasa, dake ita dakinta a sama yake. Tana zuwa tace ai abincin yana kan dining table tun dazu na jera, ko akasa zaki ci? Eh zuba ki kawomin nan na gaji da zaman dining chair din, dariya aysha tayi tace to. Malmala biyu ta zuba mata da miyar, sanan ta dakko tsiren da kunun aya da cups ta ajiye, tabe baki Asa's yayi yace wai tuwo ne abincin? Kallon shi aysha tayi race sorry bari na dakko maka naka, bayan ta ajiye ya bude ya fara ci saida yaci sosai sanan ya kora da kunun aya aysha na gefe tana kallon sa. Saida ya tabbatar ya koshi sanan yace mum da ina tunanin zan samo sabon kuku dazai ringa yimin abinci, amma naga wanan yarinyar itama ta iya so na dauketa a matsayin sabuwar kuku na, zan ringa biyanta 200k a wata, juyawa yayi ya kalli aysha yace nasan ko kin koma aikin ki na nursing ba zaki karbi 200k ba, so idan yayi kadan ma ki fada na kara miki Amma fa banason delay da shisshigi kuma ba yawo indai ba da wani dalili me karfi ba. Be jira abinda mum ko aysha zasu ce ba ya mike ya tabi.
Kunya ce ta kama mum, ji tayi kmr ta nutse a wajen, yaushe Ahamad ya koyi rashin mutunci? Wanan ai cin fuska ne, tana iya kokarinta don ta faranta mana shi kuma zai bita da irin wanan kalaman. Amma zanyi maganin shi.
Aysha kuwa wani irin bacin rai ne ya darsu a zuciyata, lalle Asa's din nan Dan renin hnkli ne, an fada mishi sbda Ku dinshi nake zaune a gdnsu? Tsananin mutunci mahaifiyar shi ne yasa nake zaune, kuma komai nayi sbda ita nake, Amma wit time zai San koni wacece.
Mum ce ta kama hannunta tace kiyi hakuri don Allah Aysha, insha nasan sbda ni kk yin komai so karki kula harkar shi kinji? Ni nasan abinda yasa yake haka.
Maman Aysha
[4/15, 13:56] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
1⃣4⃣0⃣➖1⃣4⃣5⃣
Haka rayuwa taci gaba kullum da kalar rashin mutunci da Asa's yake wa aysha, Amma tana jurewa ko kadan bata kula harkar shi, akwai wata cousin sis din shi murja yar wan babanshi ce tana nan ta dawo gdn da zama, irin masu iyayen nan ne, zatayi 24yrs tun tana karama jinisu ya hadu da Asa's, shiya biya mata kudi taje Malaysia tayi krtu, so bata Dade da dawowa ba tana zuwa gdn dataga aysha sai hnklinta ya tashi, ta Dade tana son Asa's amma bata taba nuna mishi ba, shiyasa be gane ba shi duk a zaton shi caring din da take nuna mishi na yan uwan taka ne kawai. A ranar da taje taga aysha a gdn kawai saita koma gda ta hado kayanta itama ta dawo gdn da zama. Dakinta daban aka ware mata idan Asa's ya dawo daga aiki sai yazo falo ya zauna suyi ta hira suna dariya, saidai har yanzu bataga wata alama da zata nuna mata cewa Asa's yana sonta ba.
Wani lkcn har saurayin ta take kira a waya ta hadasu su gaisa da Asa's, saita ringa gani ko mood dinshi zai canja, Amma Ina sai taga shi ko ajikinsa. Shine abin ya fara damunta tanaso ta fada mishi tana sonsa kuma tana tsoron kar yace baya sonta kuma tasan daga ranar ko farin hkrnsa bazata kara gani ba, shiyasa tabar abin a zuciyarta, amma fa ba karamin tabata yake ba.
A aladar gdnsu Asa's duk litinin da alhamis suna azimi, so yauma kmr kullum suna azumi tun karfe 2pm Aysha ta shiga kitchen ta Dora girki, saida tayi varieties na abinci yafi kala goma, drinks ma kala hudu tayi banda artificial juice, 6pm ta gama hada komai, drinks din data hada ne da kuma fruit salad tasa a fridge. A gajiye ta fito daga kitchen, gashi itama tana azumi, dakinta ta shiga tayi wanka ta shirya cikin wasu shegun Riga da siket pink color, sanan ta saka wata hula me kyau akanta, flat shoe tasa shima pink, a nutse ta sakko falon kasa, ta samesu gabadaya a zaune suna jiran a kira salla, ita kuwa murja dake bata azumin zuwa tayi ta zubu abinda ranta yakeso ta faraci ita da sultan, Asa's ne yacewa aysha ke debo mana drinks din nan ai sunyi sanyi yanzu, ni su nake so na fara sha, murja ce tace bari na karasa na dakko maka, ke aysha bari zan kawo mishi. Phone din Aysha ce ta fara kara, tana dubawa taga Dr suraj da faraarta ta dauka ta tafi can karkashin step tana amsa wayar, bayan sun gaisa yace wato kinyi kudi ko nemana bakya yi ko? Sorry Dan Uwana Wallahi INA Neman ka, ya mutan gda? Lpya kalau, ya yaya kamal anyi bikin kuwa? Eh anyi last WK, ji tayi gabanta ya fadi Amma saita daure tace eyya Allah ya sanya alkairi yace amin. Ina sonki da yawa aysha Amma kuma kinfi karfina, sbda ke yanzu matar manya yace, naga kmar uban gidana yana ciki, waye uban gdnka? Asa's mana, dariya tayi tace problem dina dakai kenan ka fiye tsokana, iam serious Aysha, don Allah kabar wanan maganar, cikin muryar shagwaba tace ni ka kyaleni da abinda yake damuna azumi nayi ko ruwa bansha ba ka samin ciwon kai, ciwon kai name? Maganar auren kamal daka fadamin, Kasan fa dauriya kawai nake, dariya yayi sosai yace aikuwa saidai kiyi hakuri, itama dariyar tayi kmr yana ganin ta tace hakuri ya zama dole yaya suraj, ya na iya da samarin kakata ta karashe mgnar tana dariya sanan tace kaga ankusa.......
Tunda ta fara wayar hnklin Asa's ya koma kanta, yana ganin ta fara dariya yaji hnklin sa yayi mugun tashi, badai yarinyar nan tayi new catch ba? To waye shi, kuma a ina suka hadu? Yana ganin dariyar data ke tayi yawa kawai saiya nufi wajenta bata karasa mgnar da take ba ya fusge phone din yayi wurgi da ita, nan take ta tarwatse a wajen cikin tsananin kishi da bacin rai yace ba cewa nayi kije ki dauko min drinks a fridge ba? Shine zaki tsaya kina wayar iskanci, idan banda iskanci ma waye zai kiraki da magrif? Kuma kinaji ana kiran salla bazaki ce ya katse ba? Karasowa wajen mum tayi tace wai kai wane irin hali ka koya kwanan? Dole sai ita zata dauko maka? Kasa murja ta dakko maka mana, kuma in banda kanason takura mata ina ruwan ka da wayar da take? Don Allah mum ki dena shiga tsakanina da yarinyar nan, kudi masu yawa nake biyanta so ya zama dole tayi min abinda nakeso, OK gadarar ka kenan? To daga yau bazata kara karbar kudin ka ba, dama ni na matsa mata ta karba, idan yaso kaje ka samo me maka girki ta ringayi ma, sbda bakwai ka kawota gdn ba.
Ita kuwa MURJA mutuwar tsaye tayi, mamaki da bakin ciki ne suka rufeta meyasa Asa's ya damu don yaga aysha na waya da wani? Kardai sonta yake? Ai kuwa idan hakane ya zama dole na kulla makircin da zata bar gdn nan.
A bangaran aysha kuwa gabadaya kanta ya kulle, ta rasa irin tsanar da Asa's yake mata, ya zama dole nabar gdn nan sbda abinda yake min yayi yawa, wasu siraran hawaye ne suka fara fita daga idonta, Amma saita basar, ta naji anfara kiran salla ta nufi fridge ta debo drinks din ta zubawa kowa har Asa's din ta mika musu, itama tasha sanan kowa ya watse aka tafi yin sallar magrib
Bayan sunyi salla aka dawo cin abinci, Asa's ya baje sai duri yake, kowa ya sake yana cin abinci amma banda aysha da tunani yayi mata yawa, dakyar ta iya shan cup daya na kunu, sai zobo kadan data sha, mikewa tayi zata tafi mum ta riko hannunta tace kiyi hakuri kici abinci Aysha, ko kinason bacin raina ne? Smiling ta kakaro A hnkli tace aa, to zauna kici, tace to. Duk da haka ba dayawa taci ba Amma ta ware sbda dama ita bata iya fushi ba.
Daki Asa's ya koma ya rasa abinda yake damunsa, meyasa yaji ranshi ya baci don yaga tana waya da wani? Meyasa ya kasa control din temper dinshi? Kona fara sonta ne? Kai gskya baso bane gani nayi zata renamin hnkli, kuma gashi mum tace zata yanata yimin girki, aikuwa ya zama dole naje na bata hakuri sbda yanzu idan ba girkinta naci ba bana iya cin kowanne girki, to kuma idan tayi aure fa? Ya jefowa kansa tambaya, mikewa kawai yayi ya fice sbda bashi da amsa.
Dakin mum yaje ya marairaice ya bata hakuri abinka da da da mahaifi saita hakura, Amma da sharadin zaije ya bawa aysha hakuri, zai sayo mata sabuwar waya, sanan zai dena yimata abinda yake. Duk yace ya yarda
Maman Aysha
[24/05 9:21 PM] Mizz Ayuush: [4/16, 20:19] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
1⃣4⃣5⃣➖1⃣5⃣0⃣
Aysha kuwa tunda ta shika daki sai juyi take ta kasa bacci, banda tunani ba abinda take, ji tayi ana nocking kofar ta tana budewa taga Asa's a tsaye, zuwa nayi na baki hkiri akan abinda ya faru dazu don Allah kiyi hakuri kuma zan kawo miki sabuwar waya gobe, a hnkli tace ba komai ya wuce.
IPhone 6+ ya saya ya kawowa aysha da sabon sim card, ba lefi ya daina hantararta saidai duk lkcn da yasan abokanshi zasu zo gdn saiya hanata fitowa, ko drinks zaa kai musu saidai ya kira murja, ita kuwa aysha ko ajikinta, sbda dama she is very gentle bata fiye son shiga harkar maza ba.
Yauma kmr kullum mum suna zaune da aysha suna hira sai tace Aysha me zaki mana a dinner ne yau? Smiling Aysha tayi tace duk abinda kike so mum, dariya tayi tace ni yau yambols nake sha'awa, to Bari naje na fire doya na fara da wuri, mum tace kin soya samosa da spring roll din da kika kwaba dazu kuwa? Dariya Aysha tayi tace na manta Wallahi yana fridge, bari na fara soyasu.
Aiki take sosai a kitchen tana gama soya su samosa ta fara suyar yambol, tana chura wa tana suya, sultan ne yazo ya zauna a gabanta yana zuba mata surutu, saiya faki ido ya wargaza mata Wanda ta chura, idan tayi mishi fada saiya tashi da gudu, saiya bari ta manata saiya kara dawowa
Su Asa's ne suka shigo shida friends dinsa Muktar da kalid, bayan sun durkusa sun gaida mum suka zauna sunata hira sai tsokanar Asa's suke wai kwanan yana yawan yin tagumi idan sun tambaye shi kuma yace ba komai, hira sosai suke a falon.
Saida ta chura wajen wajen guda ashirin kawai sultan yazo ruguza mata wajen guda goma, haushi ne ya kamata kawai saita kashe gas din ta bishi da gudu har gaban mum cikin muryar shagwaba da ta riga ta zauna mata ajiki sbda goyon kakace wani lkcn batasan ma tana shagwabar ba, tace Wallahi mum yaron nan so yake na Zane shi da bulala, tun dazu nake chura yambol yana wargaje min ta karasa mgnar hawaye na zuba a idonta, ya salm gabadaya sakar baki da ido sukayi suna kallonta, har shi uban gayyar, dariya sosai mum tayi tace Amma baka kyauta ba sultan, saidai matsalar baa shiga tsakanin Ku, gashi dai dakanki kika kawo min kara amma INA shiga cikin fadan Ku kunya zanji, dariya aysha tayi da take kara mata kyau sanan tace, don Allah karki basshi ya kara komawa. Tana shirin juyawa mum tace baki gaishe da baki ba, sai lkcn ta kula akwai mutane a zaune a wajen cikin golden voice dinta tace ina wuninku? Sai lkcn suka dawo hayyacinsu, a daburce sukace lpy kalau ina gajiya? Tace ba gajiya, mum ce tace idan kin fara soyawa kawo musu, tace to.
Tana tafiya Asa's yabi bayanta a sukwane ya sameta a kitchen, ke wacce irin banza ce? Ba nahanaki fitowa idan da friends dina a falo ba? Oh my god ai bansan kuna nan ba ko? Yakamata kayi min uzuri, to daga yau hijabi zaki ringa yawo dashi a cikin gdn nan, don naga alama so kike ki mayar mana da gda na mararsa tarbiya, don ma zanyi musu bayani ke 'yar aiki ce, and so what? An fada maka zan damu don ka kirani yar aiki? Duk abinda kaga dama kaje ka fada musu I don't care, zumbura baki tayi tace kuma Wallahi bazan saka hijabi acikin gda kmr wata matan liman ba, plate ta dauko ta zuba yambols masu yawa, dayan kuma ta zuba spring roll da samosa, ta dauka zata tafi kenan yace Dan iskanci inayi miki magana karki kara fita kuma kina shirin fita? Toba mum ce tace nakai musu ba, kawo na kai musu, kuma karki sake ki fito sai sun tafi. Mika mishi tray din drinks din tayi sanan tace idan ka kai musu saika dawo ka dauki yambols din. Yana fita Muktar ya kwashe da wata yar iskar dariya, mikewa yayi da sauri yace let me assist you Mr Asa's, lalle yau zaayi mana ruwa da kankara, mutumin da zuba lemo a cup ma wahala yake mishi yau shi ya dakko mana d whole tray din ya kawo? Dariya sukayi gabadaya, mum tace nima nayi mamaki bakai ba muktar, shan kunu Asa's yayi kmr be taba dariya ba, yana ajiyewa ya juya zai dakko sauran, cikin sigar tsokana Muktar yace ko nazo na tayaka ne yallabai? Share shi yayi kmr beji abinda yace ba, bayan ya shiga ya dakko sauran aysha tace yanzu kana nufin haka zanyi ta zama a ciki zafi har sai kun gama ci kun tafi sanan zan fita? Kaga fa harna fara hada gumi ta karashe mgnar cikin shagwaba, ji yayi gabadaya tsikar jikin shi ta tashi, Amma saiya basar ya fice batare da yayi responding ba.
Yana ajiyewa yace bismilla kuzo kuci, sanan ya haura sama dakin aysha ya shiga, komai very neets banda kamshi ba abinda yake, waige waige ya farayi a dakin dakyar ya gano inda hijabin sallata yake yana dakkowa yaji wani hadadaden kamshi ya daki hancinsa, direct kitchen ya nufa yana zuwa ya mika mata, tana karba ya fice.
Mamaki ne ya cika aysha to wai wanan mutumin me yake nufi dani ne? Kodai yanada tabin hnkli ne? Ina ruwan shi Dan na fita ba hijabi mitss idan yaci gaba da takura min Wallahi gdn zan bari. Tana fita ko kallon su batayi ba ta haura sama dakinta. Muktar da Kalid kuwa tunda suka ga aysha gabadaya su sukayi falling, amma tsoron yallabai Asa's ya hanasu mgna, sbda fur yaki basu fuska
Maman Aysha
[4/17, 10:08] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
1⃣5⃣0⃣➖1⃣5⃣5⃣
Bayan sun gama cin abincin sun Dade suna hira kafin suce zasu tafi, dake basu zo da mota ba Asa's ne ya tafi kaisu gda. A hanya Muktar ya daure yace my friend ni wanan aysha ko itace amaryar tamu ne? Cikin shan mur yace matsalata dakai kenan munafurci, dariya Muktar da Kalid sukayi sosai, sanan Muktar yace meye abin munafurci don na tambayi best friend dina matar dazai aura? Kara shan kunu yayi yace to ba ita bace, karaf Muktar yayi yace to ni INA sonta don Allah ka taimaka ka bani aurent. Mitsww kai banza ne fa wani lkcn, kuma kayi yaya da Fareeda? Ai kaji matsalar, ranar da kaga wacce tafi aysha kuma itama kace ka fasa ko? A haba, ai samun irin su aysha sai an Tara mata dubu, idan na auri wanan yarinyar ai na rufe kofa, saidai kawai na ajiye ta a gda inayi mata abinda take so.
Bakin ciki ne ya hana Asa's mgna, Kalid dayaga shirun yayi yawa yace to idan bazaka bashi ba ni INA kamu,,,,,,,shit up Asa's yace, kar Wanda ya kara yimin mgnar wata aysha daga yau, juyawa Muktar yayi suka hada ido da Kalid sukayi dariya, sbda sun gane cewa Asa's yanason aysha Amma yaki gaskanta hakan sbda be taba yin soyayya ba, zuciyarsa bata taba son wata ba, be taba dandana ya soyayya take ba shiyasa yanzu yake ganin abin wani iri.
Saida ya sauke kowa a gdanshi sanan ya taho gda.
Next WK sultan zai cika 4yrs da haihuwa, sbda haka Asa's ya shirya mishi hadadden birthday party zaayi, har IV cards ya buga yake rabawa mutane. Shiri suke sosai kayan da yaron zaisa ma daga america aka kawo su,
Ana gobe zaayi bikin da yamma mum ta shirya zata tafi rose flower sweet and bakery sabda a can zasu bada kwangilar duk wani Abu da zaaci a wajen. Daga nan kuma zata biya ta gdn aminiyarta haj hajara (maman muktar) shi kuma Asa's ya cewa murja ta shirya suje suyi order fruits din da zaa aci kuma su kira masu decoration. Da mum tare zasu tafi da aysha, amma dataji Asa's da murja zasu fita tare sai tace itama ta bisu. Mum ce ta fara tafya itada sultan,
ta fadawa Asa's su jira aysha zata bisu yace to.
Suna jingene ajikin mota shida murja suna jiran aysha, saiga ta ta fito cikin wasu shegun Riga da siket filtex lace Skye blue da touch din silver ajiki, silver mayafi tasa da takalmi da jaka, ba karamin kyau tayi ba kallo daya zakayi mata ka gane cewa gayu ya ratsata.
Tunda ta fito Asa's ya kafeta da mayun idonshi, suna hada ido kowa yaji gabanshi ya fadi sbda shima Asa's ba karamin kyau yayi ba, murja kuwa mutuwar tsaye tayi anya aysha mutun ce kuwa? Wanan kyaun ai yayi yawa, shegiya ga iya daukar wanka, inaji da guntun kyauna Amma Dana jera da ita saina ganni kmr jaka, anya zan bisu kuwa?
Maganar da Asa's yayiwa aysha ce ta dawo da MURJA daga tunanin data Lula,,,,,ke kuma INA zaki? Mum ce tace na shirya mu fita tare, zuwa ina? Inda zaku mana, kuma zan biya na karbo dinkina. Koma gda ba inda zaki, bangane ba? Eh dama bazaki gane ba ai, ina nufin ba inda zani dake, ai dama ban shirya tafiya dake ba, kuma ni mum batace min zan tafi dake ba, idan kuma kina so ki bini to ki koma gda ki sako hijabi da nikaf domin kuwa bazan tafi dake a haka kina taramin 'yan iskan samari ba, bayan inada mutunci da kima a garin nan, idan kuma bazaki sakaba to ki koma gda. Juyawa tayi zata shiga gda kawai sai yayi wani shu'umin murmushi yace idan mum ta dawo karki sake kice ni naki tfya dake, kice mata ke kika fasa da kanki. Murja shiga mota mutafi.
Haushi da bakin ciki ne ya addabi MURJA, wato Asa's kishin aysha yake ko? Da danaga ko baki yayi ni yake kira nayi musu hidima nayi zaton so ne, Ashe bayaso su ganta ne sbda yana kishinta? Ko dayake da sonta yake ai bazai ringa yawan disgata ba, yanzu haka tsoron sharrin fitinannan kyaunta yake domin kuwa irin kyawawan matan nan abin tsoro ne, kyaun su yana sasu su kauce hanya.
Aysha kuwa komawa gda tayi tasha kukanta ta koshi, da lkcn sallar magrib yayi ta tashi ta gabatar, bayan ta idar ta zauna tayi kartun kurani sai bayan sallar isha'i mum ta dawo, tace aysha baki bisu ba? Eh, kaina naji yana ciwo shiyasa na fasa idan yaso na fita gobe da safe, to Allah ya kaimu tace amin.
Sai wajen 8:40 suka shigo gdn hannusu dauke da ledoji suna zuwa suka baje abubuwan da suka sayo aka fara ci, amma aysha fur taki ci, yanda mum batayi da ita ba amma tace ta koshi, daga karshe ma mikewa tayi tayi musu saida safe. Tunda Aysha ta tafi yaji zuciyarsa ba dadi, ji yake kmr ya bita dakinta ya bata hakuri, ai kuma idan nayi haka na zubar da class dina, kuma Rena ni zatayi. Shima tashi yayi yamusu saida safe ya nufi part dinshi zuciyarsa fall tunani
Maman Aysha
[4/17, 16:32] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
1⃣5⃣5⃣➖1⃣6⃣0⃣
Washe gari bayan Aysha ta gama duk aikin da zatayi saita je tayi wanka ta shirya cikin Arabian gown, wajen 11:30am tacewa mum zataje karbo dinkin ta, kuma daga can zata wuce country mall. Mum tace bari na baki key din anaconda ta kije da ita, dake dama kamal ya koya mata driving, Amma auto ta iya. Tace to mum nagode. Hamm me karatu zo kaga yanda motar tayiwa aysha kyau, wajen me dinki ta fara zuwa sanan ta wuce country mall tayiwa sultan sayayyar birthday gift, wata yar karamar mota ce ta yara 50k ta saya, sanan ta saimi shi perfumes, ball da kuma wasu disigners kaya set biyu. Acikin mall din ta bayar akayi raping din kayan, sanan ta dawo gda.
A compound din gdn mum zaayi event din dake katon gda ne, gashi anyi mishi wasu decoration da zaisa ka kasa gane wajen. Ba karamin gayya mum da Asa's sukayi ba, idan kaga yanda aka zuba kujeru aka kawata wajen saika rantse bikin aure ne, nan kuwa birthday ne na yaro karami.
Wajen 5pm gda ya cika da jama'a, friends Asa's kowa sunzo da matansu da 'yayan su, haka yan familynsu tun daga kan yan mata zuwa kan matan aure kai har tsofaffi ma baa barsu a baya ba. Yan matan familyn sun dau wanka banda iyayi ba abinda suke, ita kuwa MURJA tafi kowa zakewa sbda Asa's yana yawan kiranta yana sata aiki.
Aysha ce ta shirya Ahamad cikin wasu shegun designer kaya, yaron ba karamin kyau yayi ba, sauri aysha tayi ta shirya cikin hadaddiyar gown dinta, material din da aka dinka mata 80k ta sayeshi background dinshi white ne, akayi mishi ado da orange kuma dinkin irin gown din da akewa amare aka mata, saidai ita gown dinta bata Jan kasa, kuma ba mayafi kawai zama tayi tai dauri mekyau da seka rantse head ta Dora, sanan ta dauko wasu shegun sarka da dankunne orange color tasa, batasha wahalar yin make up ba dake dama tayi training na 3months shiyasa duk irin kwalliyar da kk so idan kika sami aysha zata miki, wani orange cover shoe ta dakko me shegen tsini tasa, ta fesa turare, mum ce tayi mata waya tace tayi sauri ta fito da sultan kar time ya kure.
Suna fitowa idon jama'ar wajen gabadaya ya iyo Kansu, diri ri cewa Aysha tayi da kyar take tafiya sbda kallo, sai kuma tafiyar ta kara mata kyau, daga maza har matan wajen ba Wanda kyaun aysha be birgeshi ba, ita kuwa mum banda murmushin jin dadi ba abinda take, ganin duk jamaar gurin sun zubawa aysha ido ne ya dagawa Asa's hnkli, zuwa yayi ya daka mata wata irin tsawa data dawo da hnklin kowa na wajen, Dan iskanci sai yanzu zaki fito dashi tun dazu mutane suna jira, kuma kin tashi kin fito ko mayafi babu sbda rashin tarbiya. Ji tayi kmr ta nutse a wajen, wani irin bacin rai ne ya kamata, cikin bacin ran da be taba gani a fuskarta ba tace aikuwa duk yan matan da suke wajen nan basu da tarbiya, domin kuwa banga wacce ta yafa mayafi ba. Sakin hannun sultan tayi ta tafi can gefe ta sami kujera ta zauna, juyawa mutane baya tayi, wasu siraran hawaye suka fara zuba a idonta.
Har bakin wajen da aka ajiye birthday cake din Ahamad yakai sultan, bayan an gabatar da wakar happy birthday to you,,,,,,,Ahamad yasa wuka ya yankaa cake din ya bawa sultan a baki, nan take waje ya hau ihu, rada yayiwa sultan a kunne yace nima bani, aiko ya yanki kato ya samishi a baki, sanan ya yanki wani ya sawa mum ma a baki, wani kato ya kara gutsira ya rike a hannu yana waige waige, sai kuma suka ga ya tafi da gudu, kowa na wajen binsa yayi da kallo yaga INA zashi? Kawai sai su kaga ya nufi wajen da aysha take a zaune, batayi auni ba taji ya chusa mata katon cake a baki, batasan lkcn data saki murmushin dayake kara mata kyau ba, a hnkli tace happy birthday my boy dariya yayi yace thank you, tafi Mutanen wajen suka fara sunata dariya, kama hannun Aysha sultan yayi yace suje high table, suna zuwa aka fara daukar hotuna, sultan ne ya kamo hannun daddy nshi ya kawo shi inda aysha take tsaye yace ayi musu hoto su uku, zama sukayi akan step din wajen da high table yake shi kuma sultan yayi hugging dinsu ta baya dukansu sun juya suna kallon fuskarsa, pics wajen kala goma akayi musu, duk wajen ba Wanda beji sun burgeshi ba, kana ganin su Kasan sunyi matching, 'yan matan wajen ne kawai sukaji sun tsani aysha, suna kuma sbda kishi ne.
Haka akayi ta Hutuna, mum ma sunyi hotuna da aysha sosai, sanan masu abinci suka fara rabawa, bayan kowa yaci ya koshi mutane suka fara presenting gift dinsu duk Wanda ya bayar sai anyi musu photo, Aysha ma taje ta mika nata, dake bazai iya karba ba saita ajiye a kasa ya dafa aka dauke su. Sanan aka rabawa kowa senovias taro ya watse.
Har aka tshi daga wajen zuciyar aysha a dagule take, bata taba jin bacin rai ba irin yau, bata taba jin ta tsani Asa's ba sai yau, shi wanne irin butulo ne Wanda besan alkairi ba? Farkon haduwata dashi temakonsa nayi, amma meyasa ni ya butulce min? meyasa har yanzu ya kasa ganewa kudinshi baya gabana? Meye dalilin sa na disgani acikin daruruwan mutane? Yayi min wulakanci iri iri nayi hakuri Amma Wallahi wanan karan yayi na karshe, gdnsu zan bari a yau din nan Wallahi. Zama tayi tanata kuka a daki, mum tana dubawa taga bata ganta jikinta ya bata tana can tana kuka, sbda itama abinda Asa's yayi ba karamin bata mata rai yayi ba
Tana shiga dakin ta sameta tana kuka, zama tayi a kusa da ita tace nasan dole zaki yi kuka aysha, danma kinada dauriya ne, amma abinda Ahamad yayi be kyauta ba. Ni nasan abinda yasa yake miki haka sbda haka zanyi maganin shi, dagowa aysha tayi tace don Allah mum ki temaka kiyi min alfarma gobe na koma gda, don Allah kiyi hakuri bazan iya cigaba da zama a gdn nan ba, zaki tafi gda aysha amma ba gdnku ba, tun dazu na gama hada plan din komai, akwai kanwata da muke Uwa daya uba daya da ita, a Abja take da zama munyi mgna da ita zaki tafi gobe, nasa tun yau ayi miki booking din jirgi, sati daya kacal zaki ki dawo, iam very sure acikin sati dayan nan Ahamad zai gano amfaninki a gdn nan, kuma zai gane kuskuransa irin Wanda bazai kara sha'awar yi miki rashin mutunci ba, kiyi hakuri Aysha inajin ki tamkar 'yar Dana Haifa shiyasa banaso na rabu dake.
Washe gari aysha jirgin 6am tabi zuwa Abja
Maman Aysha
[24/05 9:21 PM] Mizz Ayuush: [4/18, 21:23] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
1⃣6⃣0⃣➖1⃣6⃣5⃣
Washe gari basu tashi da wuri ba sai wajen 9am, suna fitowa aka fara kallon hutuna harda wasu yan mata yan uwansu asas dake a gdn suka kwana. tun jiya aka wanke, hutunan ba karamin kyau sukayi ba Asa's kuwa pics din da sukayi da Aysha da sultan ya zubawa ido yake ta kallo, gskya yarinyar nan ba karamar kyakkyawa bace, sai lkcn ma ya tuna be ganta ba, mum ce tace Ku tashi muje mu karya tun dazu an gama abinci, dake dama ta fadawa kuku yayi abinci dasu aysha bata nan. A tare suka mike suka hau dinning, doya da kwai ne sai paper soup din kayan ciki da ruwan tea.
Ana bude paper soup din yaji kamshin ya babanta da girkin aysha, kowa ya zuba yanaci comfortably amma Asa's 2 spoon yayi, da harya tanadi chokali na shan romo Amma saiya kasa, mamaki ne ya kamashi ko ina aysha take? Tunani yayi kodai bata tashi daga bacci bane? Shi fara mikewa daga kan dining din ya nufi dakinsa, Ita kuwa mum tunda ya zuba abincin take lura dashi.
Yana komawa daki wanka yayi ya shirya cikin wata shegiyar gezna coffee color ya fesa turare, lkcn daya fito su murja ne da suran cousins dinshi su biyar a falon, yana fitowa suka bishi da kallo kowacce akwai abinda take ayyanawa a ranta, ko kallon su beyi ba ya wuce dakin mum yace mata zaije daurin auren friend dinsa tace to saika dawo. Zuwa yayi ya kara wuce su ba tare da ya kalli inda suke ba, cikin girmamawa sukace adawo lpya a tare, cikin kasaita yace Allah yasa, dariyar yake MURJA tayi tace yau 'yan mulkin suna kusa kenan, aneesa ce tace ba wani nan shi dama kullum acikin mulki yake, mutumin da muna yan uwanshi na jini Amma saiya ga dama yake mana mgna, kallon murja tayi tace naga kwana nan kina masa shisshigi to Wallahi kibi a hnkli sbda duk dinmu ba wacce batayi mishi kuma ta soshi ba, amma don dole mun hakura sbda wulakancin sa, Wallahi duk lkcn da kika sake ya gane kina sonshi saiya wulakanta ki, gara ki rifawa kanki asiri. Shan kunu murja tayi tace kudai kuce bakin ciki kuke dani, sbda kunga jinin mu ya hadu dashi, ai idan kun kula yanda yake treating dina daban ne, dariya sukayi gabadaya sanan sukace indai Mr Asa's ne zai koya miki hnkli yarinya.
Aysha tana sauka a abj ta kira mum a waya tace ta sauka lpy, sanan ta kira aunty Jidda tace ta karaso, tace to na tro driver na ya daukeki, bata kashe wayar ba driver ya kira ta ta fada mishi inda take ya karaso, kayan ta ya dauka suka nufi wajen mota.
Da faraarta ta tare ta, me aikin ta ce ta Dauki Jakarta ta kai mata daki, sanan aka akawo mata abinci taci. Cikin kankanin lkci aysha da aunty Jidda suka saba dake dukansu they are wise enough. Kuma aysha ta saywa yaranta tsarabar chocolate masu yawa.
Asa's bai dawo gda ba sai late evening, da yunwa ya shigo gdn sbda kin cin abincin reception yayi yanasa ran zaizo ya sami girkin aysha me dadi. Mum ya tambaya me akayi a gdn? Tace White rice and stew wit salad, MURJA ya kira tazo tayi serving dinshi, akan carpet ta ajiye mishi sbda yau baya sha'awar zaman dining.
Bajewa yayi ya fara ci, saidai dakyar ya samu yayi 4 spoon, ji yayi bazai iya cigaba da ci ba, hamm me krtu idan kukaga abincin very delicious, kuma a baki ma yayi dadi sbda na testa naji😀, abinda na fahimta shine girkin aysha is special, akwai wasu spices da maggi da take amfani dasu da ba kowa ne yasan su ba, shi kuma Asa's ya riga ya zama addicted da irin abincin ta.
Coke me sanyi kawai ya kora, tambayoyi ya fara jerawa kanshi meya faru yau tru out aysha bata shiga kitchen ba, ko fitowa batayi ba? Kodai bata da lpya ne? Ganin bashi da me bashi amsa yasa ya mike ya tafi room dinshi
Maman Aysha
[4/19, 17:04] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
1⃣6⃣5⃣➖1⃣7⃣0⃣
Da daddare tura daya daga cikin yaranshi yayi yaje yahuza suya ya sayo mishi lafiyayyun kaji da snacks, a falon shi suka baje da friend din shi su Muktar manyan lediji uku yasa akayi daya nasu daya nasu mum, dayan kuma ya bawa yaranshi. Zama sukayi sunata hira da friends dinshi suna tattauna yanda zaa shirya events din bikin muktar, bayan sun gama suka fara chapter ana dariya, amma asas dauriya kawai yake sboda acikin damuwa yake. Sai wajen 10pm suka tafi, suna tfya ya shigo cikin gda.
A falo ya sami su murja sunata hira, cikin shan mur yace Ina mum? A tare sukace tana daki, wucewa yayi mum tana shirin kwanciya kenan taga ya shigo, sai kawai ta zauna a bakin gado. Zama yayi a kasa yace ko kwanciya zakiyi? Tace eh Wallahi, dama gani nayi yau tru out banga yarinyar nan aysha ba, shine nace ko bata da lpya ne? Ah ah kalau take, to ina ta tafi? Ta koma garin su, bangane ba mum? Dama bazaka gane ba ai, ina nufin tabar zaman gdn nan ta koma jalingo, wane lefi akayi mata ta koma gda? Tambaya ma kake Ahamad? Kana nufin disgi da wulakanci da kayi mata jiya ba lefi bane? Tunda yarinyar nan tazo gidan nan kake hantarar ta kana mata rashin mutunci tana daurewa, amma ranta be taba baci ba irin jiya, kuma inaso ka sani nima banji dadin abinda kayi mata ba, sbda acikin daruruwan mutane ka disgata, naje na sameta a daki tana kuka shine ta rokeni alfarma nayi hakuri ta koma gaban iyayen ta da zama, kuma na amince, tun karfe shida na safe ta tafi, inna lillahi wa inna ilaihi rajuun yace a zuciyarsa, ji yayi zuciyarsa tana bugawa da sauri Amma a fili sai yace oh sabda nayi mata fada shine tayi fushi ta tafi? Shikenan ai tayi ta tfya na samo Sabon kuku. Ko sallama bewa mum ba ya mike yayi tafiyarsa.
Tunda ya shiga daki yake tunani shikenan yanzu Aysha tabar gdn nan forever? Ka bazai yiyyu ba, ya zama dole naje na dawo da ita, yini guda kawai nayi ban ganta ba amma na shiga damuwa, kenan haka zanci gaba da zama acikin irin wanan yanayin? To waini meyasa ma na damu ne? Idan ta tafi sai me? Inada kudin da zan biya ko na wane a dafamin abinci so Dan wata aysha ta tafi be kmta na damu ba, kuma ka tabbata iya abincin ta kawai kayi missing? Daya zuciyarsa ta jefo mishi question, tabbas ba iya abincin Aysha kawai yake missing ba har aysha yayi missing dinta, to amma meye hadina da ita zanyi missing dinta? Zuciyarsa yaji ta fara zafi, pics din da suka dauka ya dakko ya kafeta da ido da haka bacci ya dauke shi
Maman Aysha
[4/19, 20:05] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
1⃣7⃣0⃣➖1⃣7⃣5⃣
Yau kwanan aysha uku kenan da tafiya Abja, kallo daya zakayi wa Asa's ka gane yana cikin matseneciyar damuwa irin wadda shi kanshi bazai iya fassara ta ba,be taba tunanin Aysha tana da matsayi a zuciyarsa ba sai yanzu, be taba zaton ya shaku da ita ba sai yanzu, ya kasa tuna time din da aysha ta shiga zuciyarsa da har yake jin bazai iya wuni daya batare da ita ba, ji yayi kansa ya chushe brain dinsa banda caji ba abinda take karfa ace na fata son aysha? Kai ina wanan ba so bane na saba da ita ne kawai, kuma ba dadi ace sbda ni ta tafi shine kawai, bayan shi ba wani Abu. Koda wasa bazan taba barin zuciyata ta kamu da sonta ba, har abada insha Allah
Haka ya zauna yana tunani kmr mahaukaci, kasa daukar tunanin shi brain dinsa tayi kawai sai kanshi ya fara wani irin zafi, anya yarinyar nan bata yimin asiri ba kuwa? Allah yasa girkin data ke min ba wani shirin take zubawa aciki ba. part din mum ya tafi a sukwane,
Ita da baki ya samesu a zaune yana zuwa ko kallon bakin beyi ba ya kama hannunta ya jata zuwa daki, a bakin gado ya zaunar da ita sanan ya durkusa agaban ta ya dafa gwiwarta yace anya aysha bata asirce ni ba kuwa mum? Asiri kmr yaya Ahamad? Tunda ta tafi na kasa samun nutsuwa, banda tunanin ta ba abinda nake zuciya ta banda zugi da radadi ba abinda take ni kaina bansan me yake damuna ba mum, ya karashe mgnar yana kuka, cikin tausayawa mum tace abinda yake damunka shine ka fara son aysha batare da kasani ba, kai ina! Bazan taba son aysha ba har abada, sbda me? Sbda itama mayaudariya ce, ta shigo rayuwa tane sbda ta cuce ni, ya akayi Kasan cutar ka zatayi? Gashi kuwa ta asircemu dagani har ke, shiyasa tun farko ni dama baa son raina kika jajibo mana ita gdn nan ba, tunda farko jikina ya bani caring din da take nuna mana na yaudara ne, kirkin ta da caring din ta na karya ne mum, idan kin manta bari na tuna miki Sadiy ba irin sonda bata nuna min ba, amma daga karshe meya faru? Idan kuma kina considering sonda Aysha take nunawa sultan ne wanne irin sone Surayya bata nunawa sultan ba, amma daga karshe meya faru? Idan kuma kamun Kaine Husna da hijabi har kasa take yawo a garin nan, amma da ciki ta tare min a gda, matan zamanin nan duk kusan halinsu daya gabadayansu mayaudara ne ke kadai na yarda dake mum, amma ke kin kasa ganewa ya karasa mgnar yana kuka me tsuma zuciya.
ko kadan ba sharri a tattare da aysha Ahamad, domin kuwa ni na yarda da ita 100%, idan ka duba hallayar aysha da nutsuwarta ya Babanta data sauran matanka, kuma idan zaka iya tunawa lkcn da aysha ta temaka maka batasan ko kai waye ba, bata ma je dakin da kake ba, kuma a lkcn bata da tabbacin zaka rayu ko bazaka rayu ba amma ta fitar da makudan kudi ta temaka maka, kuma sanan taci gaba da dawainiya dakai harka dawo hayyacinka, inaso ka sani ba kowanne mutun ne zaka samu yayi maka abinda aysha tayi maka ba, kuma inaso ka sani ko ka yarda ko karka yarda aysha is different acikin mutane, halinta na daban ne kuma Wallahi kaji na rantse maka ko dukiyar ka bata gabanta, ya kamata ka lura da yanda take takunta ko kadan babu son zuciya aciki, Amma inaso kaje ka kara tunani akai.
Mikewa yayi ya fice daga dakin ko sallama be mata ba, dakin shi ya koma yayi wanka ya kwanta, Amma Sam bacci yaki zuwa magan ganun mum ne suke mishi yawo a zuciyarsa, he is totally confused akan al amarin, dakyar wahalallen bacci ya dauke shi
A bangaran mum kuwa ba karamin tausayi Ahamad yake bata ba, yana fita ta mike ta shiga toile tayi alwala tazo ta gabatar da nafila rakaa biyu, tayi mishi addua akan Allah yasa aysha alkairi ce agaresu, kuma Allah yasa itace zata magance matsalar da take damun Ahamad
Maman Aysha
[24/05 9:21 PM] Mizz Ayuush: [4/20, 20:20] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
1⃣7⃣0⃣➖1⃣7⃣5⃣
2 days later, 5:15pm
Hadaddun motocin Asa's suka shigo cikin gdnsu, da gudu body guards dinshi suka zo suka bude mishi kofa, cikin tafiyarsa ta takama ya karasa cikin gdn, mum ce zaune a katon falon dasu murja su aneesa dake har yanzu suna gdn basu tafi ba, yana shigowa kowacce ta shiga taitaiyinta sbda masifar kwarjinin shi, wata mata ya gani gefe suna zaune ita da yarta, saida ya durkusa ya gaida mum, yana shirin tfya part dinsa mum tace wanan matar fa kai take jira, cikin kulawa ya kalli matar yace meya faru? Wallahi mijina ne a kwance a asibiti bashi da lpya, aiki zaayi mishi kuma sunce sai mun biya 400k sanan zasu tabashi, kuma wallahi bamu da halin biyan kudin shine mukazo ka temaka mana, wane asibiti ne? Kadija memorial Hosp, takardar da aka rubuta kudin ya karba ya dauki no me asibitin, cikin few seconds ya fara dialing yana dauka yace kana magna da Mr Asa's, don Allah ko akwai wani patient magaji musa a asibitin ka? Eh akwai yallabai, meye condition dinshi? Typhoid perforation ne, nawa ne kudin aikin da zakuyi mishi? 400k ne yallabai, alright Ku shiga dashi kuyi mishi aikin yanzu, ka tro min Acc no dinka, zanyi maka mobile transfer na kudin yanzu insha Allah, to shikenan yallabai. Juyawa yayi ya bawa matar 50k yace kuje munyi magna da me asibitin, zaayi mishi aikin, Allah ya bashi lpy. Kwantawa matar tayi tana mishi godiya irin wacce batasan ma me zatace ba, haka ta ringa ci mishi albarka shi kuwa tuni ya tafi ya barta a wajen. Mum ce ta daga matar tace Allah zaki godewa bamu ba, mikewa matar tayi cikin tsananin farin ciki harta fita daga gdn tana musu addua.
Asa's kuwa daki ya shiga yayi wanka, yana fitowa yasa wata shirt yellow me karamin hannu da black jeans, kayan ba karamin kyau sukayi mishi ba.
Falo ya koma wajen su mum ya salm su aneesa suna ganinshi ya fama musu gyambon sonshi daya Dade yana damunsu, Zuba mishi ido sukayi suna kallon shi, a lkci guda kuma sonshi yana yawo acikin jinin kowacce acikin su. Cikin shan mur yace Ku bamu waje inaso muyi magana da mum, sum sum suka fice suka koma daya falon.
Kallon mum yayi yace wata alfarma nake nema awajenki, INA jinka my son, so nake ki shirya muje mu dawo da aysha, meyasa kake so a dawo da ita? Bakiga sultan ya shiga damuwa ba? Kullum fa sai yayi kuka kafin yayi bacci, indai Sbd sultan ne karka damu zaizo ya saba, idan ya Dade be ganta ba zai manta da ita. To ai nima nayi missing din abincita, tunda ta tafi banci abinci na koshi ba, sbda na riga na saba da irin nata, duk Wanda naci sainaji bemin ba. Aikuwa gara ka fitar da son cin abincin aysha a zuciyarka, Sbd koda aysha ta dawo bazata tabbata a gdn nan ba, idan ta sami miji aurenta zanyi, kaga kuwa bazai yiyyu tana gdn wani ta ringa yi maka girki ba ko? Shiru yayi for some minutes, sanan yace to muje mu dawo da ita, idan tayi auren ai nasan zan hakura nima. Kaga Ahamad karka maidani wata karamar yarinya, tunda ta nuna min batason zaman gdn nan bazan takura mata ba, sbda haka daga yau karka kara yimin zancen aysha. Mikewa yayi cikin bacin rai ya tafi wajen friends dinshi.
A bangaran Aysha kuwa, ta saba sosai da zaman Abja, suna yawan yin waya dasu inna habiba, saidai bata fada musu tana Abja ba. Mum kuwa a rana saita kira aysha yakai sau bakwai, ita kanta aunty Jidda tana mamakin irin son da mum takewa aysha.
Kanin mijin aunty Jidda ne yazo gdn dake a abja yake aiki, sai kawai tace ya temaka yakai su shope rite zasuyi shopping, yace to ba matsala. Tare suka shirya har Aysha, da yaranta guda biyu, tunda aysha ta fito yake kallonta, aunty Jidda da yara a back seat, aysha kuma a gaba ta zauna. Tunda suka fara tfya hnklin shi akan aysha yake saidai tsananin kwarjininta da kamala sun hanashi yayi mata magana.
A tare suka she ga ciki Jidda ta wuce tana daukar abinda basu dashi a gdn, ita kuwa Aysha side din chocolate ta tafi ta ringa jida, dake dama da kudinta a jaka, daga nan kuma taje ta Lodi ice cream, ta Debi wasu manyan apple masu kyau. Zagayewa tayi ta tafi wajen biyan kudi sbda kar Jidda tace zata biya mata, tana zuwa akace kudinta 10k, bag dinta ta zuge ta fara kirgo kudin kawai saita ga uncle mahamud ya biya, zatayi mgna yace,,,shittts, kayan ya karba yace let's go, a tare suka jera har bakin mota aunty Jidda na tsaye tana jiransu, kallonta aysha tayi tace aunty har kin rigamu fitowa? Dariya tayi tace eh Wallahi aysha, sanan uncle mahamud ya bude musu kofa suka shiga suka tafi.
A can gefe kuma, senator Sadik dawaki ne zaune cikin makekiyar range Rover dinshi, shopping yaje yi shida guards dinshi, zasu tafi kenan ya hangi aysha tana fitowa daga motor, kallo daya yayi mata yaji yayi falling, shine ya fasa tafya har saida suka gama shopping di suka fito, sanan yacewa wasu daga cikin guards dinshi su bisu a baya su samo mishi address din su aysha da no gdn da take, sanan yace wa driver shi su tafi.
Kamar yadda ya umarcesu haka sukayi, sunbi su ayshan ba tare da uncle mahamud yasan suna binshi ba, kuma sun samo mishi komai sun fada mishi
Maman Aysha
[4/21, 20:03] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
1⃣7⃣5⃣➖1⃣8⃣0⃣
Washe gari
Mum ce zaune ta tafka uban tagumi abin duniya ya dameta banda tunani ba abinda take, yau kwanan aysha shida kenan a abuja, gobe ne ranar dawowarta, duk wata dabara da zanyi akan Ahamad yaso yarinyar nan aysha nayi, kuma da alama ya fara sonta, Amma sbda taurin kai irin nashi har yanzu yaki ya furta. Allah ka sani banida wani burin daya wuce Ahamad ya auri Aysha, idan da alkairi Allah ka cika min burina. Yanzu ya zama dole na dawo da aysha gobe, Allah yasa idan ta dawo Ahamad ya furta mata yana sonta da bakin shi, wai da kuwa naji dadi,,,,,Asa's ne ya katse mata tunani da cewa mum ya naga kinyi shiru? Ina fata ba abinda yake damunki? Ba abinda yake damuna Ahamad, kawai dai INA tunanin yanda aysha zata dawo ne, Wallahi nima INA son yarinyar, INA ganin zanyi musu waya ince ta dawo yau, murmushin jin dadi Ahamad yayi yace da kuwa kin temaka min mum, kinga gobe zanyi hadadden break fast kenan, hararar shi mum tayi tace wato kai ta abinci kake ko? Ah ah, ba iya abinci ba ai she is lovable dukkanmu munyi missing dinta, to Amma idan zata dawo yau din a me zata daho? Ko na tura su Nura su dakko ta? Ah ah ka kyaleta kawai zan tsara yanda zaayi, smiling yayi yace na fita office, duk yanda ake ciki kya fadamin. Cikin tafiyarsa ta kasaita ya nufi waje, yana zuwa body guards dinshi suka Mara mishi baya, da rawar jiki suka bude mishi mota ya shiga sanan suka shiga nasu suka fita. Motoci uku ne agaban sa, uku a bayan shi, wacce yake ciki kuma tana tsakiya.
Asa's na fita mum ta kira aunty Jidda tace tanaso aysha ta dawo gda yau, sai aunty Jidda tace aikuwa dama akwai kanin Baban su Ihsan zai taho kano yanzu da motarsa, kawai saisu taho tare ko? To shikenan Allah ya kawo su lpya, tace amin.
Sai wajen 4pm su aysha suka baro abuja daga ita sai uncle a motar, banda shara gudu ba abinda yake, shiru motar ba Wanda yake mgna, can dai uncle ya daure yace aysha tun ranar Dana fara ganin ki naji na kamu da sonki, amma kwarjininki ya hanani nayi miki magana, don Allah zaki iya sona? Why not? Kanada qualities din da zaa sonka, problem din kawai shine akwai Wanda zuciyata take so, kuma tanayi mishi so me tsanani. Wanan wane me SAA ne aysha? Koda na fada maka sunan shi bazaka sanshi ba, to shikenan Allah yasa haka shi yafi alkairi, tace amin. Basu shiga kano ba sai wajen 9pm. Tun a hanya suke waya da mum, har cikin gda ya rakata bayan sun gaisa da mum yayi mata sallama ya tafi, dake dama wife dinshi a kno take da zama.
Su murja suna zaune suna hira ta gaishe su amma ba Wanda ya kalleta, ballantana ya amsa mata Sbd dukansu haushinta suke ji. Dakinta ta wuce tayi wanka tasa wata lallausar gown green color ta yafa wani karamin gyale, ta fesa turare sanan ta sakko kasa, abincin ma kadan taci taji ta koshi. Hira su MURJA, aneesa, Najwa da karima da kuma Sa'adatu suke suna shewa, idan aysha tasa baki sai kowa ya share ta, dataga shariyar tayi yawa kawai saita shiga dakin mum sultan yana kwance akan gado yana ta bacci, zama tayi a kusa dashi tana shafa kanshi suna hira da mum tana bata labrn aunty Jidda tana da kirki sosai, dariya mum tayi tace shiyasa nace kije gdnta, nasan bata da matsala. Hirarsu suke sosai aysha na ta bata lbri har zuwa shops rite din da sukayi, dake yanzu jin mum take kmr ita ta haifeta.
Asa's ne ya shigo gdn cikin tfyarsa ta goggagun matsu kudi da suka amsa sunan su, a falo ya wuce su murja suna kallon film, suna gaishe ya amsa a ciki, dakin mum ya nufa, tun daga bakin kofa yake jin dariyar su, mamaki yayi yace mum kuma yau wa ta samu suke zuba hira haka? Yana shiga dakin suka hada ido, ya slm zuciyarsu ce ta fara harbawa da sauri, cikin unique voice dinsa yace mum Ashe keda 'yarki ne shiyasa najiKi acikin farin ciki, dariya mum tayi tace Wallahi kuwa, kallon aysha yayi yace ya gajiyar hanya? Wayyo Allah shikenan na dawo yanzu zai fara kashe ni da voice dinsa, a hnkli tace alhamdulilla, sannu da dawowa, tace yauwa. Zama yayi suke hira da mum, time to time kuma yana kallon Aysha, gani yayi tana gyangyadi yace aysha ai gara kije ki kwanta naga kmr bacci kk ji ko? Smiling din dayake kara mata kyau tayi tace eh, mikewa tayi tace saida safe, shima mikewa yayi yace ai nima tfya zanyi mum saida safe, cikin tsananin farin ciki mum tace Allah ya tashe mu lpya.
A tare suka fito falo su MURJA da tun shigar Asa's dakin mum suka shiga damuwa, suna ganin fitowarsu suka bisu da kallo, hanyar steps aysha ta nufa, kawai saita ji yace mata gud nyt, a sanyaye ta jiyo tace OK nyt, sanan ya juya ya tafi fuskarsa dauke da smiling din da shi kansa besan dalilin yinshi ba
Maman Aysha
[4/21, 22:50] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
1⃣8⃣0⃣➖1⃣8⃣5⃣
Abuja, 7:30pm
Convey din motocin senator Sadik dawaki ne suka tsaya a kofar gdn aunty Jidda, daya daga cikin security dinshi ne ya fita ya cewa megadi ya fadawa megidan senator dawaki yana sallama, aikuwa yana zuwa yana fada mishi sai gashi da saurinsa kmr an jefoshi, durkusa wa yayi yace yallabai gani, cikin isa da takama yace wata yarinya na gani a gdnka nakeso, wa kenan? Bansan sunanta ba, Amma taje shope rite jiya da yamma, no Jidda ya fara kira tana dauka yace jiya tare da aysha kukaje shope rite ne? Eh, katse wayar yayi yace yallabai aysha ce, kanwar wife dina ce, saidai Wallahi an samu akasi ta koma kano yau din nan, ranshi yaji yayi mugun baci sbda ba abinda idonshi yake son gani kmr aysha, cikin damuwa yace bani address din ta na kanon? Yana rawar jiki ya rubuta mishi, sanan yace ya bashi no sa sbda idan yaje zasuyi communicating, yace to. Yana bashi sukaja motocinsu suka tafi.
A daddafe senator dawaki yayi bacci, washe gari karfe 10am suka dauki hanyar kano shida securities dinshi.
Da wuri aysha ta shiga kitchen ta shirya mishi lafiyayyen break fast, mum ce tace tayi mishi nashi shi kadai sbda yanzu sun Dan kara yawa a gdn aiki zai mata yawa. Cikin zubudi ya fito bayan sun gaisa da ya gaishe da mum yace akai mishi abincin part dinsa, aikuwa murja tayi caraf tace bari nakai maka, ta dauka tana wani karairaya saura kadan ta fadi, da sauri ya karbe tray din a hannunsa yace da kin sake kin zubar min da saina balla miki kafa, turo baki tayi tace ni dinma? Yap sbda kin fiye iyayi da yawa, kujera ta samu ta zauna ta kafeshi da ido, kallonta yayi yace zaki iya tfya tanx, haka ta fito daga dakin ba tare da taso hakan ba. Rabonsa da yaci abinci me yawan nayau ya dade, saida yaci ya koshi sanan yayi wa mum sallama ya tafi.
Sai wajen 2pm Senator Sadik dawaki suka shiga kano, direct gdnshi dake kwanar ganduje ya shiga yana zuwa yayi wanka ya kwanta sai bayan la'asr sanan ya tashi yayi salla yaci abinci, wanka ya karayi ya shirya cikin shiga ta alfarma, sanan ya hada securities dinshi suka dauki hanyar gdnsu Asa's. Amma kafin ya tafi saida ya kira mijin aunty Jidda ya fada mishi, shi kuma ya kira mum ya fada mata cewa zaizo gdn dake dama already yayi mata bayani
Tun a bakin gate din farko securities din asas suka hanasu shiga, sbd ya fada musu duk mukamin mutun karsu barshi ya shiga mishi gda saida izininsa, argument ake tayi a tsakanin securities din Asa's dana senator, daya daga cikin securities din Asa's ne ya dauki waya ya kirashi, ya fada mishi abinda yake faruwa, shi kuma ya kira mum ya tambaye ta, tace eh nasan da zuwanshi zance yazo yi wajen aysha, ji yayi gabanshi yayi mugun faduwa, Amma saiya daure yace OK bari nace su bude mishi gate ya shigo to.
Kiran su yayi yace su bude mishi, sanan sukayi mishi jagora zuwa wani hadadden falo da fadin kyaun shi ma bata lkci ne, Cikin shiga ta alfarma Aysha ta shirya, kafin taje ancika mishi gabanshi da kayan motsa baki. Cikin nutsuwa tayi sallama ta shiga falon, saida ta durkusa ta gaishe shi binta yayi da wani mayataccen kallo sanan ya amsa cikin isa da kasaita, kallo daya tayi mishi taji be mata ba, kuma ita dama kudi baya gabanta. Saida ya kora lemo sanan yace ranar da kukaje shope rite na ganki, kuma tun daga ranar banida nutsuwa, kuma banajin zan samu nutsuwa har saina aureki, wanan shine dalilin zuwana kuma a shirye nake Dana kashe ko nawa ne akanki......
Zaune yake a office tunani ya addabi zuciyarsa, senator Sadik yazo zance wajen Aysha, to a ina ya Santa? Wato har senators sun fara zuwa wajen aysha kenan? Wani irin kishi ne ya kamashi, kawai saiya Debi phones dinshi ya fita body guards dinshi na ganinshi suka taho da gudu suka Mara mishi baya.
Suna shiga gdn suka fito da gudu suka bude mishi kofa, police din da sukazo da senator ne a cike a gdn banda muzurai ba abinda suke, Asa's na fitowa suka gaishe shi wit respect, dakatar da guards dinshi yayi ya nufi falon dasu aysha suke, yana zuwa bakin kofa yaji aysha tana cewa nagode kwarai da sonda kake min, tabbas duk mutumin dayace yana sonka ya gama maka komai a rayuwa, Amma don Allah kayi hakuri, an riga anyi min miji, kuma INA sonshi bazan iya rabuwa dashi ba.......idan ke bazaki iya rabuwa dashi ba, shi zai rabu dake sbda ba abinda kudi bazai yi ba, zan kashe ko billion nawa ne naga na mallake ki, sbda haka zansa a nemo min yaron dayake sonki zanyi amfani da dukiya da kuma mulki da nake dashi, na kwaceki daga wajen shi. Waima na tambayeki waye shi? Kuma Dan gdn waye? Ji sukayi ance nine nake sonta, kuma har yanzu baka Tara kudin da zaka iya bani ba, juyawa sukayi cikin fargaba senator dawaki yace Mr Asa's how comes? Akace kanwar ka ce? Eh kanwata ce, kuma my wife to be insha Allah, shiru senator Sadik yayi sbda ko yasha giyar wake yasan be isa ya hada kanshi da Mr Asa's ba, mutumin daya juyawa 50trillions baya, INA wanan ogana ne ban isa inja dashi ba, mulkin da nake kai kawai zan nuna mishi amma ba kudi ba, kuma mulkin ma ban isa na nuna mishi ba sbda federal government har Aron kudi suke a wajensa. Mikewa yayi yace iam sorry bansan kai zaka aureta ba, Allah ya tabbatar da alkairi, smiling Asa's yayi yace amin. Hanyar fita senator Sadik ya nufa, shi kuma Asa's ya rakashi har sunje bakin mota senator yace yawwa dama Wallahi ina son ganinka, so nake hada jirgin ruwa, shine akace min duk 9ja ba Wanda yasan sirrin yanda ake sai kai, sbda kana dasu dayawa, shine nakeso don Allah ka bani haske, smiling Asa's yayi yace to ka samu time kazo sai nayi maka bayani, yace to shikenan nagode, musabaha sukayi yayi mishi sallama ya tafi
Maman Aysha
[4/22, 09:37] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
1⃣8⃣5⃣➖1⃣9⃣0⃣
Kafin ya koma har aysha ta shiga cikin gda, da fargaba mum ta tare ta, cikin yanayin damuwa tace aysha yaya kun daidaita kanku ne? Cikin sanyin jiki aysha tace ni gaskiya bemin ba mum, na bashi hakuri nace mishi inada mijin da zan aura, washe baki mum tayi tace to ai shikenan aysha, Allah ya hadaki da mafi alkairi tace amin, to amma Aysha zai yiyyu kuwa, kowa saiki ce bakya so? Ya kamata ki sami wani ki tsayar sbda kinga bazakiyi ta zama haka ba, dole zakiyi aure, ni naga kanin mijin Jidda ma kmr yana sonki, ko shine Wanda kike so din? Tayi tmbyr cikin fargaba, eh shima yace yana sona, Amma na bashi hakuri, ni Wallahi mazan nema tsoron su nake, dariyar jin dadi mum tayi tace yaro man kaza Aysha har yanzu ke yarinya yace, Sbd har yanzu shekarunki basufi 18 ba, shiyasa amma ai aure dole ne kiyi, kedai ki nutsu kiyi tunani idan kin sami Wanda ya dace saiki fadamin kinji? Kai kawai aysha ta daga mata, amma a zuciyata cewa tayi ai indai INA tare da shu'umin danki to ba namijin dazai taba burgeni harna soshi, Asa's na daban ne, halinsa ya babanta dana sauran maza, komai nashi is unique and special, I like all his style inama da gaske yake shi zai aureni, da nayi SAA a rayuwata, daya wanke min bakin cikin mum Din kamal a zuciyata, daya zuciyar ce tace kinga ki rufawa kanki asiri Mr Asa's yafi karfinki, kina gani senators ma respecting dinshi suke,,,,,mum ce ta katseta da cewa aysha ya kikayi shiru ne? Smiling tayi tace ba komai mum. Su kuwa su murja suna gefe sai wani gadara sukewa aysha waisu yan gida, ita kuma sundauketa kmr yar aiki, sai suyi ta aikenta ta dakko musu Abu, iya kuwa ko kadan bata damuwa
Asa's ne ya shigo falon yana waya da Salisu Zango me gabatarda shirin inda ranka, bayan sun gaisa yace na tro PA dina da 5million, ka dauki 1million ka bawa mutumin dayake Neman taimakon 3million din nan, million daya kuma ka rabawa wanan mutane ukun, kafin Salisu yayi gdya Asa's ya kashe wayar, wajen da suke zaune ya karaso, ya gaishe da mum, sanan ya koma part dinsa yayi wanka ya shirya cikin orange shirt da black jeans ba karamin kyau yayi ba, ya dauko designer turarensa yasa, sanan ya dawo falon da suke zaune, binshi da wani mayataccen kallo su murja sukayi, ita kuma mum tayi baki suna babban falonta, aysha ya kalla yace INA abincina? Tace yana kan dining table, debo ki kawo min part dina, murja ce tayi saurin cewa bari na kawo maka, kafeta yayi da mayaudaran idanuwanshi yace ke kika girka? Tace ah ah, to banason shisshigi. Juyawa yayi ya koma part dinsa tsuka murja tayi tace marar M kawai, shifa duk mutuncin da kake dashi idan yaga dama saiya gurza maka, su karima da aneesa sukace shiyasa muke fada miki kibi a hnkli, nifa gda ma zamu tafi don banajin a rashin mutuncin sa zai iya aurar daya daga cikin mu, ya zama dole mu hakura dashi ko munaso ko bama so. Najwa ce ta kalli side din da aysha take zaune tace kema karki zake don kinga yana kulaki, muma da muke yan uwanshi na jini ya gurza mana ballantana ke tsintacciyar mage, bushewa sukayi da dariya murja tace yau akwai wadda yake wulakanta wa ma kmr ta, ita besata a layin mutane bama ai, suka kara kwashewa da dariya.
Duk da abinda sukayi mata ya bata mata rai amma saita basar ta nufi wajen dinning din ta fara diban food wormers na abincin, saida takai mishi komai sanan taje fridge ta dakko hadadden kunun ayar datayi mishi takai, tana shirin fitowa yace ba zakiyi serving dina ba? Komawa tayi ta zuba mishi duk abinda yake bukata, ba tare daya kalleta ba yace ga kujera nan zauna, ba tare da taso hakan ba ta zauna saida ya gama cin abincin sanan yace a ina kuka hadu da senator Sadik? Cikin sanyin murya tace nima ban sani ba, to waye mutumin da kikaace mishi kinaso? Ni ba wani wanda nakeso na fada mishi ne kawai sbda ya rabu dani, OK to meyasa kika koreshi bayan yanada kudi, kuma yayi miki alkawarin billions of naira, ai be kamata ki koreshi ba, sbda dama kudi kike so, kuma kudin ya biyoki har gida amma kika ki? Ko kina hangen Wanda yafi senator kudi ne? Nida zaki ji shawara ta da kin aureshi kawai ya karashe mgnar yana kallon kwayar idonta.
Cikin bacin rai tace kai kake min ganin me son abin duniya sbda bakasan halina ba, kudi mulki ko kyau basu taba burgeni ba, halin mutun kawai nakeso, kuma a iya zamana dakai ban taba rokonka ba, kaga kenan baka da damar da zaka kirani meson zuciya, kuma mgnar auren senator bakai zaka sani na aureshi ko karna aureshi ba, ni nake da raayin kaina, sbda haka ba damuwarka bace, na fuskanci har yanzu kallon me son zuciya kake min sbda kawai na temake ka?danasan cewa kai butulu ne da ba abinda zaisa na rabe ka, temakon da nayi maka ba abinda ya haifar min sai bacin rai, nayi dana sanin temakon danayi maka Wallahi, kuma insha Allah yau zanbar gidan nan sbda nagaji da zargin da kake min, kuma idan kana tunanin sonka nake ka daina, sbda ko kadan bana sonka, in fact na tsani halinka sbda kai butulu ne ta karashe mgnar tana kuka Mikewa tayi zata tafi kawai saitaji ya fusgota ta fado jikin shi, hugging dinta yayi sosai karki tsaneni aysha, don Allah karki tsaneni Wallahi ni ba butulu bane akwai abinda yasa nake miki haka, amma yanzu na fahimce ki aysha, na gane ke ko wace ce, kiyi hakuri namiki bayani pliss. Bana bukatar jin komai a bakin ka Asa's, ni kawai ka sakeni na tafi, fisgewa tayi daga jikin shi ta fice da gudu tana kuka
Maman Aysha
[24/05 9:21 PM] Mizz Ayuush: [4/23, 11:13] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
1⃣9⃣0⃣➖1⃣9⃣5⃣
Tunda aysha ta shiga side din Asa's hanklin su murja ya tashi, misali ma da sukaga bata fito da wuri ba, kowa acikin su ta tsure jira suke suga awanne yanayi aysha zata fito, na farin ciki ko bakin ciki? Kawai sai sukaga tazo ta wuce da gudu ta haura sama tana kuka, bushewa sukayi da dariya, murja tace ya gurza Mata, hahaha Mr Asa's ba M walla, shiyasa nake ji ajikina kmr he is in Luv wit me, Sbd ni da wahala yayi min rashin mutunci, yana mugun daga min kafa, saidai kawai wani lkcn idan na gaishe shi yana kin amsawa, shima kuma sai miskilancin ya motsa. Aneesa ce tace to ai ni gara ya aureki ma daya auri Aysha, shegiya sai danbanzan kyau kmr aljana, Wallahi na tsaneta, karima ce tace ai bake kade ba nima na tsaneta, murja tace ballantana kuma ni......shigowar Asa's falon ce tasa sukayi shiru, batare da ya kalli inda suke ba ya haura sama da gudu, binshi sukayi da kallon mamaki.
A bangaran Aysha kuwa tana shiga daki ta kwanta flat a kasa tana kuka, idan tace batason Asa's to tayi karya, sbda ba macen da zata kalleshi bataji tana sonshi ba, sbda kota ina ya hadu to d core, Ita kanta batasan lkcn data fara sonshi ba, ada tana ganin bazata taba yiwa wani sonda tayiwa kamal ba, Amma a yanzu saita gane Ashe da ba soyayya take ba domin kuwa sonda takewa kamal ada, ko quarter Wanda takewa Asa's bekai ba. Kuka ne me karfi yaci karfin ta, problem din Asa's bashi da mutunci, butulu ne shi me manta alkairi, ya zama dole zuciyata ta hakura dashi, dama ban taba nuna mishi INA sonshi ba mikewa tayi ta fara debo kayanta daga wardrobe tana zubawa a akwatinta,,,,,cikin hanzari ya wuntsilo dakin, karaswa inda take tsaye yayi cikin unique voice dinsa yace haba aysha don Allah kiyi hakuri mana, don Allah karki tafi ki barni a lkcn da nafi kowanne lkci bukatar zama dake, Wallahi aysha ni ba butulu bane, kuma nasan alkairi, akwai abinda yasa nayi ignoring dinki for d first time, amma yanzu na gane gaskiya, nasan ko ke wace ce Aysha, na gane cewa you're innocent kuma halin ki is different akan na yan matan zamanin nan, don Allah ki rufa min asiri karki bari mum tasan abinda yake faruwa Sbd nayi mata alkawari bazan kara bata miki rai ba, don Allah kiyi hakuri ki nutsu muyi mgna dake ba tare da kowa ya sani ba.
Ni ba wata magana da zaka fadamin na yarda dakai a yanzu, zargina fa kake, na tabbata yanzu da ace zaka zo gdn nan da kudi, kuma asamu akasi ka neme su ka rasa ni zakace na satar maka, sbda duk lkcn daka kalleni gani kake ni me kwadayin abin duniyace, duk alheri da kyautatawar da zanyi maka gani kake sbda inaso na cuceka nayi badon Allah ba in fact gani kake na shigo rayuwar ka ne domin na cuceka so kaga zamana a gdn Ku bashi da wani amfani kenan, sbda ba fata nake ba idan wani Abu ya sameka zaka iya cewa da hadin bakina, Sbd haka ya zama dole yau nabar gdn nan,,,,,,mum ce ta shigo cikin bacin rai tace Ahamad me kayi mata? Dama duk alkawarin da kayimin na karya ne? Ba abinda nayi mata mum, sbda kawai nace INA sonta zan aureta shine tace wai barin gdn zatayi ya karasa mgnar yana kallon kwayar idon Aysha, wani irin farin ciki ne marar misaltuwa ya kama mum, kallon Asa's tayi tace fita inason mgna da 'yata. Karaswa gabn aysha Ahamad yayi ya rike hannunta sanan ya tsareta da sexy eyes dinshi yace INA tsananin sonki Aysha, INA miki sonda bazan iya rayuwa batare dake ba, don Allah INA rokonki ki temaka ki soni, mum zatafi kowa farin ciki idan kika aureni, Amma duk sonda takewa abin idan bskyaso nasan ba zatayi miki dole ba, don Allah aysha ki temaka ki amshi soyayya ta badon halina ba pliss🙏🏻 kallon mamaki aysha ta bishi dashi, dama acikin maza ma akwai makirai? Dama Asa's makiri ne haka? Cikin kankanin lkci ya zame ya dora min lefi, mum ce tace Ahamad nace ka fita, ko bakaji ne? Sakin hannun aysha yayi yace to zan fita mum, amma don Allah ki tayani rokonta ta amince ta aureni, sbda Wallahi idan bata aureni ba komai zai iya faruwa dani, cikin tausayawa mum tace to naji fita.
Yana fita mum ta kama hannun aysha ta zaunar a bakin gado, aysha na Dade INA jiran wanan ranar, na Dade INA hana idona bacci INA rokon Allah ya nuna min wanan ranar da raina da lpyata, idan nace zan fada miki irin sonda nakewa Ahamad bata lkci ne, sbda shi kadai ne Dan dana mallaka, tun ranar dana fara ganinki naji ina sha'awar ki zama surukata, sbda na yarda da tarbiyarki 100% tun ranar nake addua Allah yasa Ahamad yace yana sonki, Amma be fada ba sai yau, don Allah aysha ki temake ni badan halina ba kuma badan halin shi ba ki auri Ahamad, wani irin kuka aysha ta fashe dashi, shikenan anzo wajen, makircin Asa's yayi tasiri, to meyasa yamin haka? Karya yake baya sona,,,,,,mum ce ta katseta da cewa aysha idan sabda na rokeki ki auri Ahamad ne ya saki kuka, to inaso ki dena, ni kmr Uwa nake a wajen ki, kuma bazan takura ki akan abinda nakeso ba, idan bakya son Ahamad ki fadamin, nayi alkawari zan aura miki duk Wanda kike so
Maman Aysha
[4/23, 16:16] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
1⃣9⃣5⃣➖2⃣0⃣0⃣
Gogewa aysha hawaye tayi tace kidena kuka kinji.....ko kadan ba sbda haka nake kuka ba mum, ina kuka ne sbda tsananin mutuncin ki da kamalarki, Maman kamal tasan asalina amma sbda bamu da kudi tace Santa bazai aureni ba, amma ke mum ba wani asalina kika sani sosai ba, danki kawai na temakawa kuma idan zaa fitar da masu kudi guda uku akasar nan, zaa saka da danki, amma sbda dattako da kirki irin naki har kike rokona na auri danki bayan ni ba kowa bace. Koda ace ni wata ce Asa's yanada qualities din da zaa soshi koda bece yana so ba, ni yakamata na rokeku mum, sbda Ahamad yafi karfina, nagode kwari da karamci da kuma dattakon da kika nunamin Allah ya biyaki da gdn aljanna cikin tsananin farin ciki mum tace amin ya rabbi, bari naje nayi alwala naji anfara kiran salla, aysha tace to mum. Mum na fita aysha taci gaba da kukanta, oh ni kuma haka Allah ya shirya min rayuwata? Kamal yana tsananin sona amma mum dinshi taki yarda na aureshi, Asa's ya tsaneni baya sona ita kuma mum dinshi tanaso na aureshi, Toni yanzu wacce irin rayuwa zanyi agdnshi kenan? Meyasa yacewa mum dinshi yana sona bayan kuma nasan karya yake? Meyasa Asa's yake so ya aureni? Sbda ya zama addicted da abincin ki zuciyata ta bani amsa, kenan zai aureni ne sbda na zama kukun shi, amfanina a gdn kawai nayi mishi girki yaci, daga baya ya auri wacce yakeso 'yar gata me galihu yar masu kudi kmr shi. Haka ta zauna tayi ta kuka dataga kukan bazai kaita ba kawai saita mike ta shiga toilet yin alwalar sallar magrib.
Asas kuwa hnklinshi a kwance ya koma side din shi, sbda yasan mum zatayi convincing aysha ta soshi, karasa aikin da yake a computer yayi dayaji kiran salla kuma ya tafi masallaci, bayan an idar da salla ya fito ya shiga gda, gabadaya su suna falo har mum, phone dinsa ceta fara kara yana dubawa yaga Muktar ne ya kirashi yana picking yace yallabai zamuzo anjima mu karasa meeting dinmu, is alright sai kunzo, Amma don Allah kasa aysha tayi mana shawarma ta me dadi sbda Wallahi nayi missing din ta da yawa, kuma naje bakery wajen 12 amma ban sami me dadin ta aysha ba, oh sbda kwadayin shawarma ne kuka kirkiri meeting? To Wallahi karma kusa ran zakuci, sbda bata da lpya, kuma ko kalau take ma bazatyi ba sbda ba bewar ku bace, ah bewar mu ce mana tunda kukun ka ce, a gdn uban wa nace maka kukuna ce? Idan kuka nemi Ku renamin hnkli Wallahi zansa securities din bakin gate su hanaku shigowa, kafi kowa sanin halina. Dariya sosai Muktar yayi yace iam sorry yallabai Asa's, Wallahi tsokanar ka nake, don Allah ka temaka mu hadu Wallahi abinda zamu tattauna yanada matukar muhimmanci, dariya Asa's yayi yace banza harka sare? Irin wanan kora bayani haka? Shima dariya yayi yace ai dole na sare, nasan rashin mutuncin ka zaka iya sawa su rufe mana gate din, dariya sosai Asa's yake, sanan yace tunda ka bani hakuri INA jiranku, saikun zo Muktar yace to shikenan.
Harya kashe wayar yana dariyar sa mejan hnklin duk Wanda yake kallonshi, mum ce tace waye ya kiraka? Wallahi Muktar ne, wai Dan renin hnkli so yake Aysha tayi mishi shawarma, wai duk wacce yake saya batakai tata dadi ba dariya mum tayi tace ai yar tawa expart ce, Muktar ai amininka ne da dare beyiba don tayi mishi aiba lefi bane, ai naga kmr yau a gajiye take ne, Hutu take bukata yanzu ko Aysha? Ya karashe mgnar yana wani mayaudarin murmushi, sunkuyar dakai aysha tayi da sauri domin kuwa idan taci gaba da kallonshi to xuciyarta zata buga, wayyo Allah mutumin nan so yake ya kasheni da sonsa, wai shi wanne irin shu'umin mutun ne? Kai gaskya Allah yayi mishi bewa,,,,,,katse mata tunani yayi da cewa aysha ya kikayi shiru? Dagowa tayi cikin golden voice dinta tace ai baayi sallar isha'i ba, kuma akwai ingredients din so ba problem bari naje nayi, dariyar farin ciki yayi yace ke kadai? Bari nazo na tayaki, mamaki ne ya kama su aneesa, cikin kissa murja tace kai haba yallabai Mr Asa's, muna gdn ka shiga kitchen? Bari naje na tayata.
Dukansu yan matan suka mike suka shiga kitchen, waje kawai suka samu suka zauna suna kallonta tana ta faman aiki, karima cema ta fere mata Irish, kuma ta yanka mata cabbage Amma su banda bakar magana da habaice ba abinda suke, dake akwai soyayyun kaji har paper chicken tayi musu, ta hada musu zobo me kankana da cocomber aciki. Bayan ta gama ta zuba musu, ta dibawa mum nata sanan ta mikawa su murja sauran tace su raba.
Su MURJA sun fita sai ita kadai a kitchen din, tanaso ta fita kuma tana tsoron ko bakin suna falon mum, karta fita Asa's yayi mata rashin M, Dora kanta tayi a drowa kitchen tace mittss kuma gashi bani da no shi bare na kirashi, batasan a fili ta fada ba kawai saitaji yace aikuwa is unfair ace mata bata no mijinta, Gabanta yazo yana wani shu' umin smiling yace ya akayi baki da no na? Shiru tayi ta kasa mgna, karbar phone dinta yayi yace nayi miki saving no tun ranar Dana kawo miki wanan wayar, Sbd baki damu dani ba shiyasa bakisan tana ciki ba, dubo no yayi ya nuna mata yace kingani? Kasa mgna tayi, matsowa kusa da ita yayi sosai yace aysha meyasa baki damu dani ba? Meyasa kike nuna min halin ko inkula? Sbda kaima baka damu dani ba, wa ya fada miki ban damu dake ba? Duk duniya INA ganin ba Wanda yakai ni damuwa dake, sbda na damu dake shiyasa nake tsananin kishinki aysha, ke kuma kike ganin kmr na takura miki, karya ne, kana sona amma kake zargina? Ai duk mutumin da ake so baa zargin shi,,,,,,,,,,,shittts, Dan yatsanshi yasa akan pink lips din ta, cikin unique voice dinsa yace is OK Aysha, nasan yanzu bazaki yarda dani ba, amma wit time zaki fahimce ni, kin gama hada komai tace eh, Debi wasu muje ko, tace to.
A tare suka jera suka nufi side din shi, suna zuwa bakin falo yace jirani anan banaso friends dina su kalle min ke, na hannunsa ya fara kaiwa sanan ya dawo karbar na hannunta, Muktar ne ya biyo bayan shi ba tare da ya sani ba yana zuwa yace dama jikina ya bani tare kuke, Dan renin hnkli kai ka iya zuwa kuyi hira da yan matan mu, amma kai bakaso a kalli taka, duban Aysha yayi yace muna godiya da shawarma me dadi, mungode sosai smiling tayi tace ba wani abu, mika mishi tray din Asa's yayi yace jarababbe tunda ka ganta ai saika tafi ko, yana dariya ya karba ya tafi
Yana tafiya yace iam crazy about your luv Aysha, kinga friends dina har tsokanata suke, don Allah aysha ki temaka ki soni, wata kasala taji ta saukar mata, kawai saita juya zata tafi, hannunta ya rike yace zaki tafi baki ban amsa ba, kukan shagwaba ta fara, kawai sai yayi wani smiling dashi kadai ne yasan maanarshi, sanan yace shikenan jeki nagode saida safe tace Allah ya kaimu.
Sai wajen 11pm su Muktar suka tafi, shi kuwa Asa's dakyar tunanin aysha yabar shi yayi bacci
Maman Aysha[24/05 9:21 PM] Mizz Ayuush: Gaskiya tafi kwabo💵💵
2⃣0⃣0⃣➖2⃣0⃣5⃣
Washe gari da wuri aysha ta tashi ta hada break fast, Amma da kyar ta karasa sbda yau zazzabi take ji, tana gamawa ta koma daki tayi wanka tayiwa sultan ma sbda zai tafi islamiyar safe dake wk end ne, wata skye blue din gown tasa me kwala, dake tayi retouching saita taje gashin ta shafa mai ya kwanta a bayanta, Dan karamin dankwalin rigar ta dauro ta Kasan gashinta, sanan ta fesa turare jitayi bakinta ba apatite, kawai saitace sultan ka sauka kasa kaci abinci ni bacci zanyi, make kafada yayi yace nima zanyi baccin, sultan bakaci komai ba fa, kuma kaga makaranta zaka tafi.
Dukansu sukazo suka hau dining har mum, murja ce tayi serving din kowa zasu fara ci kenan Asa's yace ina Aysha da sultan?Aneesa ce tace suna daki, jeki ki kirasu, tace to. Tana zuwa ta banke kofa wata harara ta watsa mata sanan tace kizo ana kira, bata jira me zatace ba ta juya.
Murmushin takaici aysha tayi sanan ta kama hannun sultan suka sauka, tun kafin su karasa sakkowa Asa's ya kafeta da sexy eyes dinshi, tana zuwa ta durkusa ta gaida mum, sanan ta kalli Asa's tace INA kwana? Fuskarshi dauki da wani smiling yace lpya ya kk? A hnkli tace lpy kalau, sultan ma yace gud morning dad, kujerar kusa dashi ya jawo yace zoki zauna anan aysha, ba musu ta zagayo ta kusa dashi, plate ta dauko da zubawa sultan abinci ta mika mishi, sanan ta juya zata tafi, da sauri Ahamad ya ruko hannunta cikin husky voice dinsa yace ba yanzu zakici abincin ba? Cikin muryar ta me dadi tace ni nakoshi, me kikaci? Ba komai kawai bana sha'awa ne ta karashe mgnar cikin sigar shagwaba, baki da lpya ne Aysha? Nima bansan abinda yake damuna ba, kawai dai inajin nausea da anorexia ne, kuma kaina yana ciwo, Amma meyasa kikayi abinci bayan baki da lpy? Saida na dora kaina ya fara ciwo, Eyya iam sorry, yanzu ya zaayi kenan? Na karasa cin abinci nazo mutafi Hosp, ko kuma yanzu nan kike so na kaiki idan na dawo naci abincin? Ko kuma bakya son fita na kira Muktar yazo ya dubaki a gda? Duk abinda kike so shi zanyi miki Aysha, ki fadamin wanne zaayi? Kai 😳dama mutumin nan ya iya caring? Dama mgna me dadi tana fitowa daga bakinsa? Anya abinda yake fada har zuciyarsa ne kuwa? Ni kuwa bari na gwada shi, nasan karya yake yaudarar tasa ce ta motsa sbda yaga mum a zaune,,,,,,, Cikin murmushin Jan hankali tace yanzu nakeso muje, idan ka dawo kaci abincin, mikewa taga yayi yace to muje ranki ya Dade, kinada right din da zakiyi duk yadda kike so dani, the only thing I need is your happiness, inason abinda zai saki farin ciki da walwala aysha ko meye shi, Wallahi ji nake kmr ciwon kan naki ya dawo kaina, dariya tayi da har saida fararen hakoranta suka fito sanan tace iam joking, kaci abincin ka na Riga nasha navidoxin, so nausea din ya dena, kuma ita tafi damuna, yanzu ciwon Kaine kawai, shima kuma nasan zai daina. How sure you're cewa zai dena? Wani smiling ta karayi tace zai daina mana, is alright idan be daina ba kimin magana kinji? Tace to a hnkli. mum da tunda taga asas yana yiwa aysha mgna farin ciki ya cika mata zuciya tace amma da kin daure kinci ko kadan ne aysha, cikin nutsuwa tace zanci ne mum, Amma sai anjima, to shikenan Allah ya sauwake tace amin, sanan ta nufi steps zuwa dakinta.
Tunda ya fara yiwa aysha magana su aneesa suka shiga wani yanayi more especially murja da ada take tunanin sonta yake tafi kowa gigicewa, sbda tunda Asa's yake be taba yiwa wata mace mgna cikin so da kauna kmr yadda yakewa aysha a yanzu ba, ji tayi zuciyata ta fara zafi, kan uba, badai Asa's ya fara son aysha dagaske ba? Aikuwa idan hakane to ko shakka banayi asiri tayi mishi, shiyasa tun tuni mum dina take fadamin muje wajen mallam Sule ya mallake min shi amma naki, aikuwa wallahi ya zama dole na farraka su ko ta halin kaka
A bangaran aysha kuwa tana zuwa ta kwanta a daki, tunani ne ya addabi zuciyarta idan dai har idanunta sun nuna mata gskya to ta gano zallar sonta a idon Asa's, kodai da gaske yake yana sona? To amma idan yana sona yaushe ya fara sona? Kuma meyasa yake sona?
Maman Aysha
[24/05 9:21 PM] Mizz Ayuush: [4/30, 12:46] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
2⃣0⃣5⃣➖2⃣1⃣0⃣
Suna gama cin abinci mum ta kalli murja tace anyi inviting dina zuwa wajen waazin da zaayi a legal yau, zamu tafi da karima aneesa da kuma Najwa, ke kuma saiki zauna a gda tunda aysha bata da lpya ko? Murja tace to shikenan sai kun dawo tace to. Cikin shirin su suka fito mum tacewa murja don Allah idan aysha ta farka ki matsa mata taci abinci cikin kissa murja tace to mum sai kun dawo. Suna fita tayi dariyar mugun ta tace nida zata mutu ma ai da naji dadi shegiya, komawa daki tayi tai wanka ta dau make up wasu shegun English wear's ta saka, sanan ta dawo falo ta zauna.
Asa's yana komawa dakinshi wanka yayi ya shirya cikin wata red shirt me karamin hannu da yellow jeans kayan ba karamin amsar sukayi ba, disigner turarensa ya dakko ya fesa sanan ya dakko laptop dinshi ya fara aiki. Chief of securities din gdn shi ne ya kirashi a waya yace yallabai ga wasu mutane suna son ganinka, da har zaice bashi da time, sai kuma yace su barsu su shigo. Guest falo aka kaisu, sanan daya daga cikin securities din suka kai musu ruwan roba da lemo me sanyi, da sallama Asa's ya shiga falon, suna ganinshi suka mike wit respect suka gaishe shi, sanan ya nemi waje ya zauna, daya daga cikin su ne yace yallabai dama daga asibitin yoyon fitsari ne na dambare, nine medical director na asibitin, shi kuma wanan shine HOD nursing dept, muna Neman temako ne yallabai, Sbd a yanzu haka akwai patients dinmu sunfi mutun hamsim, Wanda mun dubasu munga idan akayi musu aiki zasu warke, saidai matsalar mun Dade muna rubtawa gwamnati ta kawo kayan aikin da zaa musu amma har yanzu basuyi responding ba, shine muka yanke shawara zamu hada taro na musamman, zamu gayyaci matar Governor data deputy governor, matan manyan yan kasuwa, matar sarki, da kuma matan 'yan majallisu na jaha ko Allah zaisa su hada mana koda Rabin kudin ne, mika mishi IV card din yayi yace wanan na me dakinka ne yallabai. Karba Asa's yayi yace kmar nawa kuke nema na aikin? 10 million ne yallabai, is alright zatazo insha Allah, to mungode Allah ya kara budi, yace amin, sanan sukayi mishi sallama suka tafi.
Juya card din ya fara yi, wanan na me dakinka ne, su basu San banida aure ba kenan? To wa zan tura kenan? Aysha mana zuciyarsa ta bashi amsa, yes aysha zan tura, tunowa yayi bata da lpya, kawai saiya nufi cikin gda.
A falo ya sami murja tana chartn, kallo daya tayi mishi taji gbnta ya fadi wani mugun sonshi taji ya kara shiga zuciyarta, Allah yayi maka baiwa Asa's, ai wallahi ya zama dole na mallake ka, kota wacce hanya saina aureka bazan taba bari na rasaka ba,,,,murja aysha ta tashi taci abincin kuwa? Ya katse mata tunani, aa har yanzu bacci take, hanyar steps yayi ba tare daya kara cewa komai ba, murja na ganin haka tabi bayan shi. Suna shiga yaga ta rufe windows din dakin, kuma ta kashe A/c, sanan ta dauki wani katon Eskimo ta rufu dashi, da hanzari ya karasa bakin gadon ya zauna, sanan ya janye bargon daga jikinta, wani haddaden kamshin turare ne ya daki hancinta irin Wanda tayi mishi amfani dashi a jalingo, nan take rayuwar da yayi a asibiti ta dawo mishi, cikin shagwaba Aysha tace mayar ka rufeni sanyi nakeji, cikin tausayawa yace haba Aysha, ya zaayi na lullube ki acikin wanan zafin? Kin gafa Dan zaman nan da nayi harna fara gumi, nidai don Allah ka rufeni ta karasa mgnar da kyar Sbd rawar sanyin da take, murja kuwa na gefe a zaune zuciyarta banda tiriiri ba abinda take, hannu yasa ya taba jikin aysha sai yaji shi kmar wuta, ya salm haka jikinki yayi zafi aysha? phone dinsa ya dakko ya fara dialing no Muktar, yana dauka yace kazo yanzu yanzu don Allah, aysha ce bata da lpya, jikinta yayi zafi sosai, yace to gani nan zuwa.
Cikin few minutes ya karaso Asa's yace har kazo? Yace kai me bamu shawarma bata da lpya ai banga ta zama ba, dama Kaine da sai naga dama zanzo. Thermometer ya dakko ya duba temperature din, sai gashi wajen 43, murja ya kalla yace samo karamin baho da ruwa me sanyi tace to, tana kawo wa yace ta dauko karamin towel, mika mata ruwan yayi yace yi mata tepid sponging don Allah, ki tabbatar kowanne kin saka towel din a kowacce gaba na jikinta, sbda idan bazai yiyyu ayi mata pcm inj da wanan temperature ba, zamuje waje idan kin gama saiki mana magana. Suna fita tayi murmushin mugun ta, sanan tace ba wani tepid sponging da zanyi, Allah yasa idan yayi mata allurar ta karasa ta. Waje ta samu ta zauna, in a few minutes tace ta gama, A tare suka shigo, amma daya gwada still ba wani improvement, kawai saiyace taje tayi wanka, Asa's ne ya hada mata ruwan wanka da kanshi, sanan ya riketa ya rakata har bakin toilet din, dayaga tsoron ruwan take kawai saiya jata har har cikin jakuzi din, ya sakar mata shower ba tare da ta cire rigar jikinta ba, wata kara aysha tasa irin ta shidewar nan, saida ya tabbatar ta jige jagwab sanan ya fito ya dauko mata wata gown marar nauyi pink color shiga yayi ya kashe shower din, sanan ya mika mata rigar ya fito ta canja, sanan ya koma ya riko ta suka fito tare.yana kara gwadawa yaga ta dawo 32, sanan yayi mata allurai. Ya bawa asas wasu nasha kuma, kunna A/c dakin sukayi aysha kuwa anayi mata allura bacci ya dauketa. Murja kuwa zuciyata ba karamin damuwa ta shiga, asasa da Muktar sun Dade suna hira a dakin saida Muktar zai tafi nema suka fita, itama murja falo ta koma ta zauna da tunani kala kala a zuciciyarta
Maman Aysha
Maman Aysha
[4/30, 16:19] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
2⃣1⃣0⃣➖2⃣1⃣5⃣
Bayan Asa's ya raka Muktar ya dawo kitchen ya wuce ya damawa aysha coker oats, sanan ya dauki guntun hankali da kwai ya nufi dakinta, har lkcn tana bacci, zama yayi yanata chartn da friends dinshi kusan 2hours tayi tana bacci sanan ta farka, tabata yayi yaji zazzabin ya sauka, mikewa tayi ta shiga toilet ta karayin brush, sanan ta fito flaks din Asa's ya dakko ya zuba coker oats din a cup ya zuba madara da sugar ya mika mata, Iya coker oats din kawai tasha, taki cin dankali zare mata ido Asa's yayi yace saita sha, yanayin yanda yake mata fadan kawai sai abin ya bata dariya kallonta yayi yace oh dariya ma na baki ko? Kin sami kanki yanzu ai shiyasa da dazu ne ko smiling ba zaki iya ba, to ai gani nayi kana treating dina kmr wata karamar yarinya, smiling yayi yace ai dama ke ba babba bace, cikin cool voice dinta tace mishi ina mum? Sun fita unguwa, to Ina sultan? Ya salam sultan yana makaranta ba a dauko shi ba, kinsan driver shine ya tafi dasu mum, ni kuma Wallahi na manta, cikin rudewa aysha tace ankai 20minutes da tashinsu fa, mikewa tayi daga kan gadon yace Ina zaki? Zanje na dauko shi mana, dariya yayi yace har kin warke? Sa hijab dinki muje to, a tare suka sakko daga steps, cikin mugun yake murja tace patient har kin warke? Asas yace rigima dai, wai sultan zata dauko.
A camery 2017 dinshi suka fita, ya bude musu A/c, dubanta yayi yace na fuskanci kina tsananin son sultan aysha, abinda kike mishi koda ace mahaifiyar shi tanada rai iyakacin abinda zatayi mishi kenan, shiyasa nake kara sonki aysha, ban taba soyayya ba sai akanki kuma ina addua Allah yasa daga kanki na rufe kofa, sbda halin ki yayimin, I like all your style Aysha, INA masifar sonki amma is like har yanzu baki amince da sonda nake miki ba, rike hannunta yayi yace Wallahi aysha da gaske nake sonki, kuma kece mace ta farko Dana zuciyata ta fara so a rayuwata, na Dade INA tsoron sharrin mata, na Dade INA yiwa mata kallon mayaudara macuta, azzalumai amma kyawawan dabi'unki sunsa na cire wanan tunanin a zuciyata, don Allah aysha kiyimin alkawari zaki kasance dani har iya karshen rayuwar ki? Kuma kimin alkawari zaki zauna dani cikin gaskiya da rikon amana? Hawaye na zuba a idonta tace nayi maka alkawari insha Allah zan zauna dakai a bisa amana,,,,,,motar su ce tayi packing a kofar jabanul noor, da gudu daya daga cikin malaman yazo yace yanzu driver dayake kawo shi yazo ya dauke shi, kudi masu yawa ya dakko ya bashi, mutumin yanata godiya ya figi motar shi suka tafi, ta rose flower sweet and bakery suka biya ya sayi lafiyayyun kaji dasu burger da ice cream, sanan suka tafi gda. Suna shiga su Najwa da aneesa suka hada ido, take away din da ya sayo aka baje akaci dake dama ba a gama lunch ba.
A weak later
Yau ne ake gudanar da taron da aka shirya a Volvo vaginal fistula Hosp Danbare, bayan an gama break kowa yana zaune Asa's yace aysha inaso kije yanzu ki shirya, akwai taron da zaki wakilceni around 11am, kuma kinga yanzu 10am, so kiyi sauri kije ki shirya, cikin shagwaba Aysha tace nifa bana iya speech a idon mutane, wani lallausan smiling yayi mata yace zaki fara daga yau, murja ce tayi karaf tace ah yaya gskya taje ta kofsa, tunda ni graduate ce koni zanje? Itama aysha graduate ce tayi Bsc nursing a Abu zariya, sbda haka ita zataje, kallon aysha yayi yace idan kin gama shiryawa ki sameni a side dina.
Cikin wata gezna shadda yar wajen 150k ta shirya ash color, dinkin rigar irin 3quarter din nan ne, akayi mata stone work da adon pink tun daga sama har kasa, sanan ta zauna ta Mirza dauri, light make up tayi amma tasa pink Jan baki tasa sarka da Dan kunne pink, shoe and bag ma pink, gyale ma pink dake fara ce sai kayan suka haskata, tunda ta fara sakkowa daga bene suka zuba mata ido, a hnkli mum tace tabarakalla masha Allah, su kuwa su murja kallo daya sukayi mata suka watsar, amma idonsu yace besan zance ba, dole saida suka dago sukaci gaba da kallonta, wani irin kishi ne ya kamasu, nan take murja ta kara jin tsanar aysha a zuciyarta. Da daryarta mejan hnkli ta karaso gunsu tace mum na tafi, kama hannunta mum tayi tace kiyi addua kafin ki fita daga gdn nan kinji ko, tace to mum, Allah ya karemin ke daga sharrin bakin mutane dariya aysha tayi tace amin mum.
Yana zaune yana aikin businesses dinshi da computer sa tayi sallama ta shiga, binta yayi da wani mayataccen kallo, suna hada ido ya nemi nutsuwarshi ya rasa, cikin wani irin yanayi yace anya zan barki ki fita a haka kuwa? Inada tsananin kishi Aysha, kuma nasan dole zaa nuna program din a media, gasky bazaki ba bari nayiwa murja mgna taje. Tunani tayi idan ta bari murja taje to ta hadu da gori, kuma ta ringayi mata iyayi kenan, cikin kissa da shagwaba da ita kanta batasan ta iya ba taje kusa dashi ta zauna, tace haba don Allah saida ka bari na gama shiryawa kace wai ba zani ba, naga bani kadai bace mace a wajen, akwai first lady, matan yan majallisu etc kuma su kaga da auren su ma, ni kuwa da baayi auren bama,,,,,,to ai shiyasa nake tsoron kar wani yayi min snatching dinki, dariyar da take kara mata kyau tayi cikin sigar yaudara tace don't worry iam yours forever, shima smiling yayi yace is alright amma matso kiji wani abu, tana matsowa yasa bakin shi akan lips din ta saida ya tsotse Jan bakin datasa Tass, har saida yaji tana Neman yin kuka sanan ya kyale ta, cheque ya bata na 10million yace idan taje ta basu a matsayin contribution dinta, sanan idan zata fadi suna aysha Ahamad sa'eed sardauna zata ce sbda a matsayin wife dinshi zataje. Saida ya rakata har bakin motor, convey ya hada mata da motoci bakwai masu tsadar gaske, motar data shiga ce ta tsakiya sanan yayi warning din drivers din akan sujata a hnkli, saida yaga fitar su sanan ya koma gda
Maman Aysha
[4/30, 20:56] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
2⃣1⃣5⃣➖2⃣2⃣0⃣
Suna shiga wajen taron securities suka fito da sauri suka bude mata kofa, saida suka rakata har wajen da zata zauna, cikin girmamawa organizers din sukazo suka tareta, sanan suka nuna mata wajen da suka tanadar mata t zauna, kujerar first lady ce ta farko, sanan ta matar sarki, sanan ta Mrs Asa's su kuma matan yan majallisu bangare guda aka ware musu.
MD din asibitin ne ya fara bayani bayan ya gama wasu daga cikin staff din asibitin sukazo suma sukayi bayani, sanan suka fara gayyatar guest dinsu. First lady ce ta fara fitowa tayi bayani bayan ta gama ta bada kyautar 2million sai matar me martaba sarki itama ta bada kyautar 1 million, sai Mrs Ahamad sa'eed sardauna saida tayi bayani sosai akan ciwon vvf da turancinta me dadi, sanan ta fassara da Hausa, bayan ta gama tace tayi donating 10 million naira nan take waje ya dauki ihu da tafi, wasu kuma kabbara kawai suke, commissioner of health ne ya mike yayi jawabin godiya, sanan yace suma zasuyi nasu kokarin insha Allah. Haka akayi taro aka watse aysha ta koma gda.
Dake direct aka nuna program din a gdn television Asa's ya kunna musu sun gani, tunda aysha ta fita tana bayani farin ciki ya lullube Asa's, ba karamin burgeshi Aysha tayi ba, wani sonta yaji yana yawo a jinin jikin shi. Ana gama program din friends dinshi da suka San bashi da aure suka fara kiranshi a waya suna tambayar yaushe yayi aure be fada musu ba, saidai kawai yayi dariya yace a India ya aurota shiyasa beyi gayyata ba, dayaga zasu dameshi kawai saiya kashe phone dinsa
Tana zuwa wanka tayi ta dauro alwala tazo tayi sallar azahar tana idarwa ta shirya cikin wata fitted gown din material green, color din ta karbi skin dinta tana cikin fesa turare saiga Asa's ya shigo, ji tayi gabanta ya fadi sbda yanzu al amarin shi tsoro yake bata, a bakin gadon ta ya zauna yace wato shine kikaje kikai ta zuba kauyanci a wajen ko? Wani lallausan smiling tayi tace ba dole ba kmr ni ace anyi min convey din motoci, ai bakaga kauyanci bama saida naga securities sun bude min kofa, kuma sun takemin baya sainaji kaina ya wani fasu, bansan lkcn Dana canja tfya ba na fara ta takama dariya sosai Asa's yayi😅 yace ni Wallahi tsokanar ki nake kin burgeni sosai Aysha, yanayin yanda kika nutsu a wajen sainaji na kara sonki,,,,,phone dinshi ce ta fara kara yana dauka yaji minister of information ne, bayan sun gaisa ya fada mishi cewa akwai meeting da aka shirya zaayi da manyan yan kasuwa na duniya, a kowacce kasa ana bukatar mutun uku, so kana daya daga cikin Wanda zasu wakilci 9ja, kuma gobe ake so kowa ya tafi, a USA zaayi kuma 2 wks zakuyi, cikin sanyin jiki Asa's yace to nagode Allah ya kaimu goben, yace amin, sanan sukayi sallama. Aysha ce ta kalleshi tace ya naga jikinka yayi sanyi? Tfya ce ta taso min ta sati biyu, ni kuma gashi banaso nayi missing dinki, ko 1 minute banaso nayi ba tare dake ba, INA sonki da yawa Aysha, kinga yanzu da munyi aure da dake zan tafi, gskya INA dawowa zaayi maganar aure, sbda na matsu dake dauriya kawai nake ya karashe mgnar yana mata wani shu'umin kallo, murmushi aysha tayi tace Allah ya kaiku lpya ya dawo daku lpya, yace amin, amma iya abinda zakice min kenan? Cikin shagwaba tace addua fa nayi maka, fisgota jikin shi yayi yace kina nufin ba zakiyi missing dina ba kenan? Kasa magana aysha tayi shi kuwa yayi hugging dinta sosai sun Dade a haka sanan tace sakeni na sauka kasa, kallonta yayi da idonshi daya kada yayi ja, sanan yace don Allah kice kina sona kozan samu relief da radadin sonki aysha, cikin cool voice tace to I Luv you sakeni, oh to nema? Irin na takura miki din nan ko? Tunda hakane bazan sakeki ba, hawaye ta fara tace don Allah kayi hakuri yunwa nakeji, mayaudarin smiling dinshi yayi mata sanan ya saketa. A tare suka jera suka sauka kasa
Maman Aysha
[24/05 9:21 PM] Mizz Ayuush: [5/1, 19:01] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
2⃣2⃣0⃣➖2⃣2⃣5⃣
Washe gari da wuri Asa's ya shirya cikin wasu hadaddun suit, yana gama break ya cewa mum zanje mu tafi mum ayi min addua, tace Allah ya tsare min kai, Allah ya kaiku lpy ya dawo min dakai lpya, yace amin. Cikin kissa su murja ma sukace yaya Allah ya kiyaye yace amin, kallon Aysha yayi yace yan mata ya akayi ne? Ke bazaki yimin addua ba? Zatayi mgna kenan kawai sai hawaye ya fara zuba a idonta, kama hannunta yayi yace zo muje ki rakani kallon mum yayi yace na tafi. Ta side din shi suka bi, saida sukaje bakin kofar da zata sadaka da waje, sanan ya janyota jikin shi ya goge mata hawayen sanan yace kiyi hakuri zan ringa kiranki a waya har sai kinji kmr muna tare, dagowa tayi suka hada ido a hnkli tace kawai dai zanyi manage Allah ya bani hakurin jure rashin ka harna 2 wks, kiranshi aka farayi a waya, abokan tafiyarshi ne kawai saiya saketa yace bye aysha, sai munyi waya
Su murja ne a daki sai kaiwa da komowa take yi cikin bacin rai tace kan uban nan aysha ba karamin asiri tayi wa Asa's ba, Ku duba kuga duk irin shariya, wulakanci da kuma ji dakai da yaya Ahamad yake dashi yanzu ita ya dena yi mata, saima wani janta yake ajiki, kuna gani yaufa agaban mum ya rike hannunta cikin daga murya tace ko Baku kula bane? Aneesa tace mun lura mana, nifa na hakura da Asa's sbda na fuskanci yafi karfina karima da Najwa ma sukace Wallahi muma mun hakura, gobe ma zamu koma gdn iyayenmu hutun ya isa haka, kullum banda bacin rai ba abinda muke fama dashi, gara muje mu samu mazaje daidai class din mu mu aura domin kuwa Asa's yayi mana nisa, murja ce tace kaji zancen banza, ita aysha an fada muku class din Asa's ce? Duk kanmu iyayen mu masu kudi ne, ita kuwa yar talakawa ce, ai itace ma bata dace dashi ba dabadan asiri ba, karima ce tace amma kinsan tana da kyau, so duk irin namijin da takeso zata iya samu, Sbd Dan banzan kyaun ta da class din ta. Dariya takaici murja tayi tace tunda Ku kun hakura shikenan, nidai yanzu nasa kafa, inaji ajikina zamuyi aure da Mr Asa's, kallon juna su aneesa sukayi sukace Allah ya bada SAA.
Da yamma mum ta kira aysha tace jiya munyi mgna da Ahamad akan zai yiwa yan uwan babanshi mgna suje Neman aurenki, kuma kinga wajen yan uwan mahaifin ki yakamata suje, kuma gashi ba ruwan su dake, INA tsoron kar famiyn Baban Ahamad suje su fada musu wata mgnar ta batanci akanki, kuma kinga duk cikinsu ba Wanda beso Ahamad ya auri yarshi ba, shine na yanke decision zamu tafi jalingo dake gobe, ni zanyi kwana daya acan, saina wuce Bauchi dake munada company a Bauchi zanyi wa manajan kamfanin mgna ya samo min address din gdn Ku, zanje na Tara baffaninki gabadayansu nayi musu nasiha, idan naga alama sunyi regrating zanyi miki bayani sai kije garin kiyi kmr sati daya, so kinga kina can kenan zaa je Neman auren, idan kuma suna nan akan bakansu sai aje Neman auren jalingo, amma ke me kika gani? Shawara tayi mum, Allah yasa a dace tace amin. Mum tace bari ma na kira alhaji lawan din yanzu, bugu biyu ya dauka bayan ya gaisheta cikin girmamawa tace dama so nake na tambaye ka ko Kasan gdn marigayi alhaji Aminu maitama? A unguwar jahun suke Eh na sani hjya ai akwai new staff da muka dauka kwanan nan, biyu daga cikin su yan familyn ne, akwai danshi abokina ma, OK, Kasan wani Dan gdn alhaji kabeer, amma fa ya Dade da rasuwa? Eh nasan shi, to shikenan zanzo jibi insha Allah, to shikenan Haj Allah ya kawoki lpya tace amin, aysha ta kalla tace har Baban ki ya ce ya sani, inaji ajikina abin zaizo mana da sauki, nayi miki alkawari insha Allah zan kawo karshen kiyyayar da suke nuna miki aysha, kuka aysha tasa ta kwanta akan cinyar mum tace ngde da kaunar da kike nuna min, Allah ya biyaki da gidan aljanna tace amin
Washe gari su aysha da mum suka dauki hanyar jalingo, aneesa, Najwa da karima kuma suka koma gdn iyayen su, ita kuma murja zataje gda kafin mum ta dawo
Maman Aysha
[5/2, 21:50] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
2⃣2⃣5⃣➖2⃣3⃣0⃣
Da helicopter din Asa's su aysha suka tafi jalingo, a gdn inna habiba suka sauka ba karamin farin cikin ganin aysha sukayi ba, abinci kala kala aka tanadar musu bayan sun huta da daddare mum tayiwa inna habiba bayanin auren Asa's da Aysha da kuma hukuncin da suka yanke na zuwa wajen maitama family. Duk sun goyi bayan hakan, su inna habiba harda rawa da taji ance aysha da Asa's zasu yi aure, aysha na ganin murnar da inna habiba take saita fara muka, inna ce ta fado mata a rai, Allah sarki inna, inama tana da rai taga wanan rana, da baasan irin murnar da zatayi ba. Saida tayi kuka me isarta sanan taje ta gyarawa mum wajen da zata kwanta, ita kuma tayi musu shimfida ita da sultan sbda shi har yayi bacci ma, shi kuwa sadi driver helicopter daki aysha tasa Dr suraj ya kama mishi a hotel
Washe gari bayan sunyi break mum tayi shirin tafya ita da sultan, har bakin helicopter suka rakota ba karamin gdya sukayi mata ba, inna habiba ta hada mata kayan su kuka, daddawa, kubewa, soyayyar gyada amaro etc ta bata sanan sukayi sallama suka tafi
Bauchi
Direct gdn alhaji Lawan suka wuce tarba ta girmamawa akayiwa mum, sunyi mata girki yafi kala goma, cikin girmamawa Mutanen gdn suka ringa zuwa suna gaisheda mum Sbd alhaji Lawan me kudi ne, kuma duk kudin daya samu albarka cin su Asa's yake ci, sbda yakai 20yrs yana yiwa su Asa's managa a kamfanin su na sugar dake Bauchi, tun dad din Asa's yana Raye ya Dora shi kuma daya mutu Asa's be sauke shi ba, sai suka kyale shi yaci gaba da kula dashi.
Bayan sun gama cin abinci mum tace ya rakata gdn maitama family. A gdn babban yayansu su dad din aysha suka je dake dama yasan da zuwansu ya hada kan sauran yan uwanshi wato alhaji hamza da alhaji rabiu.
Cikin karramawa suka karbe su dake alhaji Lawan yayi musu bayani itace mum din Managing director na kamfanin da yake aiki. Bayan sun gaisa mum tace sunana Haj Zainab Sa'eed Ahamad sardauna, nice matar marigayi alhaji sa'eed sardauna, kuma mahaifiyar danshi Ahamad sa'eed sardauna Wanda kuka fi sani da Mr Asa's, don Allah idan bazaki damu ba nazo ne domin nayi muku wata tambaya? Cikin girmamawa sukace muna jinki ranki ya Dade, kunada kani kabeer ko? Eh muna dashi Haj, Amma ya rasu 9yrs ago, allahu Akbar Allah ya ji kanshi, sukace amin, to don Allah zan iya ganin familyn shi? Tare sukayi accident da familyn shi suka rasu, ya salm duk dinsu kenan? Ah ah akwai yarsa guda daya aysha, OK, zan iya ganin ta? Kallon juna sukayi cikin kuskunda alhaji hamza yace tana wajen familyn mahaifiyar ta, Amma a iya sanina ana kai mutun wajen familyn Uwa ne, idan dangin uba ba Wanda zai iya rike shi, Amma meyasa Ku gaku har Ku uku amma aka rasa Wanda zai riketa? Kodayake kuyi hakuri na shiga abinda be shafeni ba, don Allah idan ba damuwa inaso Ku fadamin garin da take naje na sameta, sbda INA tsananin son ganin ta, kuka baffa Haruna ya fara Haj kin taso min abinda yafi damuna a yanzu, tabbas bamu yiwa Dan uwanmu adalci ba, ba abinda beyi mana a rayuwa ba hatta wanan gdn shi ya sayamin, amma sbda wani dalili marar tushe muka juya mishi baya dashi da iyalinsa, a yanzu haka bansan inda aysha take ba, sabda naje jalingo nemanta wata biyu daya wuce sunce suma basusan inda take ba ya karasa mgnar yana kuka, kallon shi mum tayi tace kana nufin yanzu kunyi nadama dakai da yan uwanka? Sosai ma kuwa, ai bamu gama nadama ba ma, sbda har yanzu bamusan halin da yarinyar take ciki ba, sbda tunanin ta harna hadu da hawan jini, munyi nadama marar misaltuwa. Murmushin jin dadi mum tayi tace alhamdulilla dama abinda nakeso naji daga gareku kenan, aysha tana hannuna a tare suka mike, dariya mum tayi tace Ku zauna inaso Ku nutsu Ku saurare ni, tun lkcn da kakar aysha ta rasu na roki alfarma abarmin ita sbda wani hallaci da tayiwa Dana Wanda bazan taba mantawa dashi ba, kuma yanzu haka Ahamad shine zai auri Aysha, shiyasa nazo wajenku, da ace wani bare ne daban zai aureta da bazan taba nemanku ba, dani zan aurar da ita nayi mata duk abinda iyaye sukewa 'yayansu, amma dake Dana ne shiyasa na nemeku. Iyayen Ahamad na bangaran mahaifin shi zasu zo Neman auren Aysha next WK insha Allah, kuma Ahamad yace na nema mishi alfarma awajenku kar bikin ya wuce nan da 2wks, sanan don Allah idan sunzo kuyi musu karba ta mutunci, aysha tana jalingo yanzu, amma zanyi mata waya ta taho nan, idan tazo zata zauna anan har ayi biki. Kuma bama bukatar komai na kayan daki domin kuwa Ahamad ya zuba komai a gdn daya Gina zasu zauna, bude bag dinta tayi ta basu cheque din 500k tace ga wanan Ku karbi bakin dashi, daga baya zan turo muku kudin da zaayi hidimar biki, idan da me mgna acikinku ina saurara. Shiru wajen yayi for some minutes, sanan baffa Haruna yace ba matsala Haj, zaayi yanda kika ce mungode Allah ya saka muku da gdn aljanna, tace amin, phone no ta ta basu, sanan tace duk abinda suke bukata su yiwa alhaji Lawan mgna, sanan tayi musu sallama ta tafi suka dauki hanyar kano
Aysha ce a kwance abin duniya ya dameta, yau kwana biyu da tafyar Asa's amma har yanzu be kirata ba, anya da gaske yana sona kuwa? Sake sake ta ringayi iri iri, daga karshe wahalallen bacci ya dauketa, can cikin bacci taji phone dinta tana ringing, tana picking taji yace 'yan mata na ya kk? Iam sorry zakiga ban kiraki da wuri ba Wallahi mun zama busy ne, Amma fa bana seconds biyu ba tare da nayi tunanin ki ba, ban taba tunanin sonda nake miki yayi min illa ba sai yanzu da nayi nisa dake aysha, kullum dakyar tunanin ki yake barina nayi bacci, kinsan yanzu me nafiso Aysha? Cikin cool voice dinta tace ah ah, so nake najiki ajikina aysha, kishiruwar dumin jikinki ce take damuna aysha, na matsu najimu a manne da juna INA shakar kamshin ki me dadi, na shiga damuwa sosai akanki aysha sbda ban taba jin ina feelings mace ba sai akanki, sauran matana nayi tarayya dasu ne kawai sbda na sauke hakkinsu dayake kaina, sbda haka ni yanzu na yanke decision zaa daura auran mu dake kafin na dawo, so kinga duk ranar Dana dawo dakin matata zan wuce, dariya aysha tayi har saida yaji sautinta, sanan tace Amma dai tsokanata kake ko? Saikace auran yar tsana? Iam not joking aysha, Wallahi iam serious don Allah ki taimaka wa rayuwata ki bani hadin kai, sbda yin hakan shine kwanciyar hnkli na, tro baki tayi kmr yana kallon ta tace kuma haka zaayi bikin ba wani shagali ba komai? Zan tro miki kudi kiyi shagalin da friends dinki, kinsan ni ba kowa zan gayyata ba, Sbd Wallahi aysha har kunyar na gayyaci mutane daurin aurena nake, meyasa? Mubar wanan mgnar, nidai kawai ki amince min a daura auren, don Allah ki tausayamin aysha kinji? A hnkli tace is alright Allah yasa haka shine mafi alkairi, amin aysha na, shiyasa nake kara sonki, I really Luv you aysha, tace I Luv you too, dariyar farin ciki yayi yace bari na barki ki kwanta sai kin jini gobe, I miss you soo much my aysha
Maman Aysha
[24/05 9:21 PM] Mizz Ayuush: [5/3, 20:14] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
2⃣3⃣0⃣➖2⃣3⃣5⃣
Mum ta kira aysha tayi mata bayanin duk yanda sukayi dasu baffa Haruna, kuma ta fada mata cewa ta kirashi a waya tunda tana da no shi, saita fada musu ranar da zata tafi Bauchi. Godiya sosai aysha tayi mata Sbd ko a mafarki bata taba tunanin familyn babanta zasu dawo su sota ba. Kwanan ta biyu a jalingo ta tafi Bauchi tana sauka a tasha tayiwa baffa Haruna waya ya tura sanshi Saleem ya dakko ta a motar shi, tunda suka shiga mota yake kallon aysha a zuciyarsa yace dama nasan aysha tana da kyau, amma kuma sainaga yanzu kyaun ya ninka na da, na Dade INA sonta amma sbda tsautsauran ra'ayin su Abba na hakura, Amma tunda yanzu komai yayi normal ya zama dole na nuna mata soyayya ta. Da wanan tunanin suka karasa gda, dama already abban su Saleem ya Tara gabadaya familyn sbda tarar aysha, suna shiga kallo ya dawo kanta kmr basu taba ganin ta ba, sbda rabonsu da aysha tun batafi 10yrs ba, da faraa aka karbeta Abba yace ta dawo kusa dashi ta zauna, introducing dinta ya karayi sanan ya nuna mata sauran'yan uwanta da bata sansu ba, wasu kuma ta manta su, sanan suka roketa gafara ta yafe musu. Akwai yan mata wasu sun fita wasu kuma mates dinta ne sosai a family din, su suka jata suka shiga ciki tayi salla taci abinci, sanan suka fara janta da hira kowacce acikin su tana kokarin nuna mata caring, harta kasa gane wacce tafi sonta acikin su, Dan Uwa kenan me dadi
Yau kwanan aysha uku da zuwa Bauchi amma idan ka ganta saika rantse tayi shekaru masu yawa sbda ta ware sosai acikin gdn, kuma su safeena sun zagaya ta ita gdjen 'yan Uwa da bata sani ba, ba karamin dadin garin aysha take ji ba saidai abinda yafi damunta yaya Saleem ya takura mata, ko INA tayi yana binta ga wani mayataccen kallo daya ke binta dashi, wani lkcn idan suna zaune ana hira shi yake hanata mgna sbda kallon da yake mata.
Kamar yadda mum ta fada uncles din Asa's sunje Bauchi kuma an saka date din biki nan da 2wks, bayan sun tafi da yamma asas ya kira Aysha a waya yace yayi mata transfer 10million naira tayi hidimar biki dashi, Aysha tace amma kudin yayi yawa, har me zaayi da 10 million? Kiyi duk abinda kike so, idan be isa bama kimin magana a karo, inaso kiyi shalin biki yanda ranki yake so, tro baki tayi tace wane shagali zanyi bayan baka nan, kiyi hakuri aysha ba yanda zanyi ne, Amma su Muktar da sauran friends dina zasu zo, sun Dade suna hira, sanan suka katse.
Tun daga ranar aka fara shirin biki baji ba gani, rana daya zasuyi komai sbda mum tace ana daura aure zasu tafi da amarya, su aysha ne zaune ita da su safeena suna hira, sukace mata to wai aysha ya zakiyi da friends dinki, mu bamuji kin gayyaci ko daya ba, ko baki da friends ne? Dariya aysha tayi tace inada su mana kuma they are wise enough idan sukazo sai kun Rena kanku kuda friends dinku sabda mugayen yan gayu ne, nasiba ce tace a ina suke? Yan GRP din mu ne na Maman Aysha novel, nasan idan sukazo kuma sai kunji kuna sonsu sbda duk yan GRP din ba wacce bata waye ba, kuma suna da tsananin kirki, hamm kudai kawai sai kun gansu.
2 wks later
A yau ne ake kamu da kuma yinin bikin Aysha, hotel din da yafi ko wanne tsada a Bauchi suka kama, Umar m Sharif, Nura M inuwa da kuma gwanja sune mawakan da zasu cashe a wajen bikin, wani hadadden gida aka sauki mum da tawagarta sbda sunzo zasu kwana wash gari kuma su tafi da amarya. Mutanen jalingo ma gda guda aka ware musu, Dr kamal da maryam ma sunzo, Dr suraj da matarsa kuwa kwanan su uku a garin, dashi ake shirya komai na bikin. A hotel din akayi order abinci kowanne mutun daya zaa hada mishi abincin 10k wato me karatu fadin kyau da tsaruwar da bikin yayi bazai fadu anan ba, kawai Ku tambayi members din Maman Aysha grp zasu Baku labari.
Washe gari daruruwan mutane suka saida daurin auren Asa's da aysha akan sadaki naira dubu Dari biyu, bayan anyi reception aka fara kokarin tafya kai amarya, daya daga cikin jirgin Asa's mum tasa aka kawo air port din Bauchi aka Debi mutane yan kai amarya zuwa kano. Kafin a fito da aysha saida su Abba suka zaunar da aysha sukayi mata nasiha me ratsa jiki, sanan aka tafi da ita. Duk yan uwan su aysha ba Wanda basu tafi rakiya kano ba.
Hadadden mother's eve mom ta hada a kano bayan ansha budiri washe gari aka Debi Mutanen Bauchi Dana jalingo aka maida su garuruwan su.
Murja da mom dinta kuwa basu da lbarn komai sai jin daurin aure sukayi, tunda aka fada murja ta zube a kasa sumammiya, dakyar aka samu ta farfado amma fa har yanzu murja na asibiti on admission
Maman Aysha
[5/4, 17:33] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
2⃣3⃣5⃣➖2⃣4⃣0⃣
Mutane duk sun watse sai amarya aysha aka bari a katon gdnta dake sardauna crescent wato me karatu fadin kyau, tsaruwa da kuma girman gdn bazai fadi anan ba, domin kuwa part din masu aiki ma kadai gari guda ne, ballantana kuma part din Mrs Asa's kudai kuyi imagining kawai. Securities din da suke gadin gdn su wajen Dari ne, sbda duk lungu da sakon gdn sai kaga security, masu aiki ma sunkai su ashirin zagaya gdn aysha ta farayi Amma saida ta gaji bata shiga wani wajen ba, garden din gdn ma kadai abin kallo ne. Daki ta koma tayi wanka tayi sallar magrib tayi addua sosai akan Allah ya basu zaman lpya saida tayi sallar isha'i sanan ta tashi daga kan sallaya. Ji tayi zaman kadaici ya isheta, gashi tunda aka fara hidimar biki Asa's be kirata ba, tuno girman gdn tayi kuma gashi ita kadai zata kwana a part dinsu,,,,,karar wayarta tace ta katse mata tunani Asa's ne aikuwa tana dauka ta fashe mishi da kuka, ya salm ji yayi gabadaya tsikar jikin shi ta tashi, ba abinda yake bukata irin yaji aysha ajinkinshi, cikin bedroom voice yace aysha meya faru? Bakai bane tunda aka fara biki baka kirani bafa sai yanzu, kuma kasa an kawoni gda ni kadai, ni gaskiya gdn mum zan tafi kafin ka dawo, ban gane ke kadai ba ina masu aikin gdn? Suna part dinsu mana, ni kuma ina part din mu, smiling yayi yace anan din ne bazaki iya kwanciya ke kadai ba? Eh, kiyi addua ki kwanta ba abinda zai sameki tunda akwai mutane a gdn, kiyi hakuri dani aysha Wallahi na zama busy ne sosai idan muka shiga meeting tun safe sai dare muke fitowa, Amma insha Allah nan da 3days zan dawo, kenan kana nufin kwana uku zanyi INA zama ni kadai a gdn nan? Cikin shagwaba tace ni gsky bazan iya ba gdn mum zantafi, idan kikaje gdn mum bada yarda ta ba ranki zai baci, sbda haka kibi umarni na. Na fahimci ka daina sona yaya Asa's shiyasa ko tausayi na bakaji, Wallahi zan kira mum na fada mata yanzu, bata jira me zaice ba ta katse kiran. Dariya Asa's yayi yace aysha fitina kenan, inama a kusa muke.
Aysha na gama gayawa mum ta kirashi a waya, tsara mum din yayi har saida ta hakura, sanan ta kira aysha ta mata nasiha akan tayi hakuri ta zauna a gdnta, bayan sun gama waya da mum ta kwanta tayi ta kuka saida tayi me isarta sanan bacci ya dauketa, kota kan abinci bata bi ba.
Murja kuwa ana sallamarta daga asibiti gdn mallam Sule suka wuce sukayi mishi bayanin abinda suke so, farantin buga kasa ya dakko bayan yayi duba ya gama yace wai abinda kamar wuya domin kuwa gabadayansu masu inada ne, dukansu suna azkar, Amma zan gwada na gani idan bazai yiyyu ba zanyi miki waya. Cikin tashin hnkli murja tace don Allah mallam kayi mana kokari sosai ko nawa ne zan baka, sanan sukayi mishi sallama suka tafi jiki ba kwari
Maman Aysha
[5/4, 21:08] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
2⃣4⃣0⃣➖2⃣4⃣5⃣
Washe gari ma haka aysha ta wuni tana kuka, tun da asuba Asa's ya kirata a waya saida yayi mata 10missed call Amma taki dauka, sai mum ya kira ya fada mata ta danje taga lpyar Aysha ya kirata bata dauka ba, tace to.
Wajen 5pm mum taje gdn ba karamin murnar ganin ta aysha tayi ba, cikin zumudi aysha tace mum me kike so na dafa miki? Mum tace sakwara da egusi soup nakeso aikuwa da sauri ta shiga kitchen ta Dora mata, kafin sallar magrib ta gama komai har paper soup din ostel Tayi musu, sanan ta hada musu zobonta me dadi. Sultan ma da aka taso su daga islamiya gdn aka kawo shi. Saida sukayi sallar isha'i sanan sukaci abinci, Amma aysha zobo kawai tasha sai hadaddiyar dahuwar kaza da mum ta kawo mata, dama tun ranar da aysha ta amince zata auri asas mum ta fara tsuma ta. Wani irin nishadi aysha takeji yau sbda ganinsu mum da sultan, zama tayi suka ringa hira har sultan yayi bacci sai wajen 9pm mum tace zasu tafi aikuwa nan take gbn aysha ya fadi shagwabe fuska tayi tace don Allah mum ki zauna mu kwana anan, dariya mum tayi tace zanzo wataran amma ba yau ba, Aysha tace ni Wallahi mum dama nan gdn kika dawo da zama tunda akwai enough dakuna saiki zabi duk Wanda kike so ki barmana, dariya mum ta karayi tace ki rufamin asiri, ai zamana daku bazai yiyyu ba, sbda ni inada jama'a, shi kuma mijinki yace baya son hayaniya, to don Allah mum ki barmin sultan ya tayani zama, kiyi hakuri aysha, sultan zaizo amma ba yanzu ba, kuka aysha tasaka shikenan duk watse wa zakuyi Ku barni, ni Wallahi zaman kadaici ya isheni gashi ya hana masu aiki zama anan yace suna gama aiki su ringa komawa part dinsu, rungume ta mum tayi tace kiyi hakuri aysha dama zaman aure ya gaji haka, wanan shine ibadar, nasiha tayi mata sosai harta hakura, sanan mum tace idan da abinda zakiyi kafin ki kwanta kije kiyi INA jiranki, kinga muna tfya saiki kwanta ko? Cikin cool voice aysha tace wanka kawai zanyi, mum tace to je kiyi amma fa kiyi sauri dare ya farayi, tace toh. Da sauri tayi wankan tana fitowa ta dakko wata shegiyar Riga armless pink tasa iya gwiwa rigar ta tsaya mata, hijabin da take salla dashi ta zura dake har kasa yake sanan ta koma falo wajensu mum, tanaji tana gani suka tafi taso rakasu har bakin mota amma mum taki suna zuwa kofar falon karshe mum tace ta koma ciki, securities suna zaune a wajen su dayawa daya daga cikin su ne ya karbi sultan ya kaishi mota.
Su mum na tafiya ta rufe kofar ta danna lock password, tana shiga daki ta debo turarenta na humra wajen kala hamsin amma kowanne saida aysha ta shafa, sabda ita dama naturally haka take tana kaunar kanshi. Tana gama shafawa ta rufe kofar dakin da pin din kofar, zama tayi a bakin tafkeken gadon tayi addua ta shafe ajikinta, sanan ta kashe wutar dake akwai switch a gefen gadon.
Harta fara bacci saitaji kmar motsin mutun a falo, kawai saita tashi a razane da sauri ta kunna wutar dakin tanata dube dube Amma bataga kowa ba kuma tanajin tsoron fita,gashi kuma bata dena jin motsin ba, jitayi gabadaya ta dena jin baccin sbda tsoratar da tayi, agogon bangon dakin ta duba taga 11pm, tabdi har yanzu dare beyi sosai zaa Dade kafin gari ya waye, phone din Asa's ta fara dialing ta rokeshi ya barta ta tafi gdn mum tunda dare beyi sosai ba, amma saitaji sun fara mata turanci alama baya kan Layin. Yanzu kenan haka zanyi ta zama ni kadai a dakin nan? Meyasa Asa's yayi min haka, meyasa yake son takura ni daga yin aure? Can karshen gefen gado ta tafi ta rakabe ta kwanta tanata kuka, kuka sosai take saitaji kmr an bude kofar a hnkli, Amma tsoro ya hanata ta juya ta gani, kawai saitaji an kashe wutar dakin,,,,,,,, innalillahi wa inna ilaihir rajuun ce ta fito daga bakinta, cikin kuka da tsananin fargaba tace waye? Kunna fitilar yayi yace nine aysha, iam sorry nayi zaton bacci kike juyowa tayi da sauri tana mitstsika ido, ganin shine da gaske kawai saita tafi da gudu tayi hugging dinshi, kuma kawai saita fashe da kuka, why do you punish me dis way? Da baka dawo yauba bansan ya zanyi ba, kara rungume ta yayi sosai ajikinshi banda shakar kamshin ta ba abinda yake, dakyar ya jata suka karasa bakin gado romancing dinta ya fara a haukace, sai lkcn hklinta ya dawo jikinta, kokarin kwacewa take daga jikinsa Amma Sam yaki sakinta, cikin fargaba tace sakeni, basarwa yayi kmr ba dashi take ba, cikin muryar kuka me hade da shagwaba tace don Allah ka sake ni, anki a sakeki, haba Aysha bakya tausayi na ne? Da kishiruwar sonki na dawo, meyasa bazaki temaka min da mafi sanyi nasha ba? Kinsan irin azabar da nasha kuwa ta rashin ki? Don Allah kiyi min hakuri koda dumin jikinki ne naji kozan samu relief daga abinda yake damuna pliss aysha🙏🏻 zatayi mgna yasa bakin shi a nata ya fara tsotsa kmr sweet
Maman Aysha
[24/05 9:21 PM] Mizz Ayuush: [5/5, 12:30] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
2⃣4⃣5⃣➖2⃣5⃣0⃣
Yanayin yanda aysha take rokonshi yaso ya daga mata kafa, Amma saiya kasa sbda ya shiga wani yanayi da be taba tsintar kanshi a ciki ba. Ba karamin wahala aysha tasha a hannun Asa's ba, sai bayan ya dawo hayyacinsa sanan ya fara tausayin ta, aysha kuwa banda kuka ba abinda take kwantar da kanta yayi akan kirjinshi yace aysha kiyi hakuri, nasan ke yanzu haushi na kike ji, ni kuma tunda aka haifeni ban taba jin farin ciki irin na yau ba, addua ce kawai a tsakanina dake aysha sbda kin tabbatar min cewa ke yar halak ce, inaso ki sani ban taba jin feelings ba sai akanki, ban taba enjoying rayuwar aure ba sai yanzu akanki sbda sauran matana da nayi tarayya dasu bawai don INA sha'awar su nayi ba, nayi ne kawai sbda na sauke nauyin hakkinsu da yake kaina, Amma Wallahi aysha sai yaune na tabbatar da nayi aure, kuma na fara enjoying life din auren, nagode sosai Allah yayi miki albarka. Rungume ta ya karayi sosai ajikinshi cikin few minutes bacci ya dauketa, dagota yayi yace tashi muje kiyi wanka, cikin muryar bacci tace ni bacci nakeji, ai kuma baa so mutun ya kwanta da najasa, sbda a lkcn duk wani asiri yake samun shiga jikin mutun, idan bazaki iya ba tashi muje ni sainayi miki yana kokarin dagota tace ni don Allah yaya Asa's ka kyale ni haba ka taramin gajiya kuma bazaka barni nayi bacci ba? Wata shu'umar dariya yayi, sanan ya dauke ta cak ya shiga toilet da ita shi yayi mata komai sanan ya dawo da ita daki ya dakko wata gown me laushi purple color ya saka mata, sanan ya fesa mata turare, daukaeta yayi ya mayar da ita dakinshi sbda yafi nata haduwa da komai, shima wanka ya shiga daya fito yasa jallabiya yayi wanka da turare yayi nafila rakaa biyu yayi gdya ga Allah sanan ya koma ya kwanta, saida ya matse aysha ajikinsa sanan ya samu bacci ya dauke shi.
Da asuba Asa's ya farka yaje yayi brush, yayi alwala ya tafi masallacin cikin gdn shi, harya dawo aysha bata tashi ba, da zai kyale ta amma daya tuna falalar da take cikin sallar asuba kawai sai fara tashin ta, a hnkli yake jijjiga ta yana cewa aysha tashi kiyi salla Amma ina saikace gawa, Harshensa yasa a kunnenta ya fara lasa a hnkli aikuwa tuni ta mike dariya Asa's yayi yace jeki yi alwala kizo kiyi salla. Dama kullum brush take fara yi kafin tayi alwala, tana gamawa tazo tayi salla, ta Dade tana kwarara addua sanan bayan ta nade sallaya taje gbn Asa's ta durkusa kanta a sunkuye tace ina kwana? Basarwa yayi kmr badashi take ba, saida ta gaishe shi sau uku beyi responding ba, dagowa tayi cikin muryar shagwaba tace ina gaisheka amma ka kyale ni? Binta yayi da wani shu'umin kallo fuskarshi dauke da murmushi yace yanayin yanda kika gaishe ni ne bemin ba, har kasa fa na durkusa ko so kake saina kwanta? Dariya ya karayi yace aini ba durkusawarki nake bukata ba, to ya kake so nayi? Yawwa yar gari, hugging dina zakiyi kimin hot kiss, sanan kice na tashi lpya, tro baki tayi tace ni gskya bazan iya ba, fisgota jikinshi yayi yace Toni bari nayi miki, hugging dinta yayi ya fara yimata hot kiss sanan cikin husky voice dinsa yace morning my queen ya gajiya?
Dakyar ya Bari aysha ta fita tayi musu break, damma ya zama addicted to abincin ta ne, da bazai bari ta fita ba. Bayan sun gama break kowa ya shiga yin wanka, cikin wata galila da kudinta zai kai 200k maroon color ya shirya, disigner turarensa ya fesa sanan ya dawo falo ya zauna, computer sa ya dakko ya fara aiki, sanan ya kira Sulaiman PA yace ya kawo mishi duk file din da beyi signing ba gda yayi, yace to. Kin shiga wanka aysha tayi kawai ta wuce kitchen, hadadden abinci tayi ta zuba a food wormers, sanan ta koma daki tayi wanka ta shirya cikin wasu shegun English wear's Riga da Wanda, top din 3 quarter ce pink, wandon kuma legis ne be karasa har kasa ba, taje gashinta tayi ta shafe shi da mai sanan ta tufke jelar ta kwanta a gadon bayanta, turarukanta ta fara dakkowa tana fesawa nidai tun INA kirgawa harna dena. Light make up tayi a fuskarta sanan ta fita falo wajen Asa's. Tulin files ta gani a gabanshi yanata aikin yin signing dake ya Dade bayanan, tana zuwa ta kwanta akan carpet ta Dora kanta akan cinyarsa, aikuwa ya kanwar da files din gefe ya fara shafa gashin kanta, film din biki ta kunna mishi yana kallo ga wani irin sanyin A/c me hade da dadin kamshi da yake tashi a falon. Cikin muryar ta me dadi tace wai ya akayi ka dawo jiya bayan gobe nake sarai dakai? Ko meeting din kuka gama da wuri? Bamu gama ba, su sai gobe zasu taho nima karya nayi nace wife dina bata da lpya shine sukace na taho, dariya aysha tayi tace Amma Kasan karya bakyau ko? To ya zanyi? Duk bake kika jawo ba, ni kuma? Eh mana sonki ne ya hanani sukuni gashi kin kirani kinayi min kuka, shiyasa hnkli na ya kara tashi, kinsan INA sonki da yawa aysha, banaso na ganki acikin damuwa. Mikewa yayi yace taso muje kiga wani Abu, hannunta ya kama suka shiga wani daki set din akwatuna kala hudu ta gani different colors, yace ga lefen ki nan ki bude ki gani idan da abinda beyi ba saiki fada min. Budesu tayi ta fara gani, amma set uku kawai ta gani taji ta gaji da kallon kayan sbda yawansu, hawayen farin ciki ne ya fara zuba a idonta, Asa's yace aysha meya faru? Kayan ne naga sunyi yawa, meyasa kake son kayi ta kashe min kudi haka? Dariya yayi yace wai akan wanan kayan kike kuka? To ai baki fara ganin komai ba, kinsan matsayin ki a zuciyata kuwa? Zo muje waje wata mota ya nuna mata da Ku dinta zai kai 20million ya bata key din motar, sanan ya kara Jan hannunta suka koma daki takaddun kamfanin shi na turare dake jgwa state ya dakko yace yabar mata halak malak, zatayi godiya yasa harshensa a bakinta ya fara aika mata da wasu sakkoni
Maman Aysha
[5/5, 14:52] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
2⃣5⃣0⃣➖2⃣5⃣5⃣
Haka rayuwa taci gaba tsakanin aysha da Asa's, soyayya suke nunawa junansu sosai yanzu Asa's ba sosai yake fita wajen aiki ba, yafi zama a gda saida akawo mishi takardun yayi aikin a gda, wani lkcn kuma da computer sa yake yin business din shi. Kullum yana manne da aysha, ko fita zaiyi wani lkcn tare suke fita, harta wajen kitso idan aysha zata shi yake rakata kuma ya zauna a wajen harsai an gama mata sanan su tafi, mutane har mamaki irin sonda Asa's yake yiwa aysha suke, saidai kuma idan suka duba zubin hallitar da Allah yayi mata da kuma kirki da saukin kanta saisu gane cewa ba abin mamaki bane ta cancanci a sota. Kasashe biyar Asa's ya biya musu suka tafi wata biyu sukayi honey moon, Holland suka fara zuwa, sai Switzerland, sai Turkey, sai new Zealand daga nan kuma suka wuce kasa me tsarki sukayi ummara sanan suka dawo gda, akaci gaba da gashi, yanzu watansu biyu kenan da yin aure, idan ka kalli Aysha sai kaji sha'awar ka kara kallonta sbda kyau ne ya hadu da kudi, da kuma kwanciyar hnkli, idan kaga aysha yanzu bazaka ganeta ba, ta kara kyau ta kata gogewa ga gayu ya dadu, ga wani mugun so da Asa's yake nuna mata sbda haka yanzu bata da wani problem.
2 months later
Watan su aysha hudu kenan dayin aure, saidai acikin yan kwana kin nan aysha batajin dadi sosai, domin kuwa bata da kuzari kullum sai kwanciya, kuma ta dena cin komai daga coke sai maltina kadai take iya sha, Amma tuk da haka tana iya kokarin ta taga tayiwa Asa's duk abinda yakeso, shiyasa tuk ta yanda yakai ya gano ko wani Abu yana damunta ya kasa ganewa, Amma fa dauriya kawai take.
Yauma kamr kullum suna zaune a falo aysha ta kwanta akan cinyarsa suna kallon film din king of heart a zee world, wata peech din English gown ce ajikin aysha, shi kuma yellow shirt me karamin hannu ce ajikinsa, da kuma red jeans ajikin rigar an rubuta SMILE da red pen, kallo suke cikin nishadi kawai saiyaji phone dinsa tana kara no murja ya gani, yana dauka tace gani a kofar gdn ka securities sun hanani shiga, cewa yayi ta hadasu, yanayi musu mgna suka bude mata. Aysha ce tace wacece tazo? Yace murja, ji tayi gabanta ya fadi, kokarin mikewa take daga kan cinyarsa kawai saiya mayar da ita ta kwanta, yana wata shegiyar dariya yace murjan kike jin kunya komai? Kafin tayi magana su murja suka shigo da fararsu, waje suka samu suka zauna sanan tace yaya INA wuni? Shan mur yayi yace nayi fushi yau watan aysha hudu a gdn nan amma sai yau zaku zo? Fara ido murja tayi tace kayi hakuri yaya Wallahi abubuwan ne sai a hnkli, shiyasa yau mukazo mu kwashi girkin amarya, saidai kuma naga kmar amaryar tamu batajin dadi sosai, dariya Asa's yayi yace wa ya fada Miki? Kalau take Ku fadi duk abinda kukeso tayi muku, gyara zama murja tayi tace faten doya, pizza, zobo, da kuma paper soup din kifi. Kallon aysha yayi ya mata wani lallausan smiling yace aysha zaki iya kuwa? Cikin dauriya tace ba damuwa ai bakonka annabinka, bari naje na musu. Amma dauriya kawai aysha tayi, sbda tun safe malt ne kawai acikin ta, wata irin muguwar kasala take ji. Haka ta shiga ta farayi musu girki zuwa magrib ta gama hada komai, kifi ne kawai ya rage shima kuma ta gama hada komai na romon, zuba kifin ne kawai ya rage mata saidai fargabar dakko shi take sbda haka kawai taji ta tsani karnin kufi.
Tunda aysha ta shiga kitchen murja ta ware sai yiwa Asa's hira take, dake jinin shi ya dauketa dama tun farko, sai ya biye mata sukayi ta hira su kuwa sauran ba sosai suke mgna ba.
Dakyar aysha ta daure ta zuba kifin ta zuba ishashhiyar albasa kayan kanshi da kuma tafarnuwa, tunda ta zuba taji zuciyarta ta tashi, aikuwa yana tafasayowa kamshin ya daki hancinta sai amai da gudu tazo ta wuce ta shiga toilet din falo, Asa's na ganin haka yabi bayanta da gudu, amai take kmr yan hanjinta zasu fita, tana gamawa ta saki ruwa ya korashi, mikewa tayi zata tafi sai jiri ya kwashe ta, da sauri Asa's ya dauketa ya fito da ita, yama manta da wasu su murja direct dakinshi ya wuce da ita yace bari na janza miki kaya mu tafi asibiti aysha, cikin kasala tace bazan iya tafya ba, Dr Muktar friend din shi yayiwa waya aikuwa yazo da hanzarin shi, yanajin abinda yake damunta yayi setting line, sanan yasa tayi fitsari yana aunawa yaga positive cikin tsananin farin ciki yacewa Asa's congratulation aysha na dauke da ciki wata uku, wani ihu Asa's yasa, sai kuma yace oh my god friend addua fa ya kamata nayi ko? Alhamdulilla yace, Allah yasa me albarka ne, Muktar yace amin, cheque din 2mililon ya bawa Muktar yace ga tukucinka, ba karamin murna Muktar yayi ba, sanan yasa mata dextrose saline suka dawo falo Muktar yana jira ruwan ya kare ya tafi, kasa zaman falo Asa's yayi sbda gani yake kmr wani Abu zai sameta, komawa dakin yayi ya zuba mata ido yanata kallonta ita kuwa tunda akyi mata allurar amai bacci ya dauketa
A bangaran murja kuwa tunda ta fuskanci aysha nada ciki ta shiga tashin hnklin data kasa boyeshi, ko sallama ba tayiwa Asa's ba suka fice daga gdn, gdnsu ta wuce tana huci mum dinta ce tace murja lpya? Bad news mum, yar iskar yarinyar nan aysha ciki ne da ita yanacan yana murna kmr baa taba mishi haihuwa ba, bema San mun taho ba yana can a wajenta, ko kinsan likita da yayi mishi albishir ma 2 million ya bashi, cikin kuka tace mum ki nemomin solution inba haka ba Wallahi zaki rasani, sbda zuciyata tana gaf da bugawa
Maman Aysha
[24/05 9:21 PM] Mizz Ayuush: [5/7, 09:36] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
2⃣5⃣5⃣➖2⃣6⃣0⃣
Saida aysha tayi wajen 2hours tana bacci sanan ta farka a kasalance, Asas baya dakin, kawai saita shiga toilet tayi wanka, tayi brush sanan ta dauro alwala, wasu English wear's tasa Riga da siket, ta shafe jikinta da humra, sanan tayi sallar magrib da isha'i bayan ta idar ta zauna tayi addua saita koma ta kwanta sbda batajin karfin jikinta, Asa's ne ya shigo a sukwane, zama yayi a bakin gadon yace aysha ya jikin? Tace da sauki, me kike so kici yanzu? Tace ba komai, amma dai kinsan dole kici abinci ko? Cikin shagwaba tace toni bana sha'awar komai, sassauta murya yayi yace kiyi tunani de aysha, shiru tayi for some seconds sanan tace kwadon gari nakeso, wata yar iskar dariya yayi yace eh? Gari fa kikace aysha? Gari ai shake ki zaiyi, ni bansan ma ya ake hadashi ba, ni gasky bazan baki gari ba, sbda ban taba ciba kema kuwa bazaki ci ba, tashi muje rose flower sweet and bakery may ba ki sami abinda zakici, shagwabe fuska tayi tace ni shi nakeso, idan bazaka samo min ba kuma shikenan. Phone dinsa ya dauka ya fara kiran mum, bayan sun gaisa yace mum don Allah kinsan yanda ake kwadon gari? Dariya mum tayi tace wa zaici gari? Aysha ce, cikin farin ciki mum tace bari na bawa baba mati ya sayo min garin, idan na hada saikaxo ka amsa ko? Ah ah ai bazamu iya jira ba, bari mu taho gdn naki kawai taci anan. Kallon aysha yayi yace tashi mutafi gdn mum, hijabin da tayi salla ta dauka suka tafi.
Suna zaune mum ta jika ta dakko dakekken kuli kuli ta zuba, sanan ta tambayi aysha manja takeso ko mangyada? A kunyace aysha tace banason mai, iya garin kuli kawai akasa mata ta karba ta faraci kmr kuncen yunwa, yanayin yanda yaga tanaci sai shima ya diba yaci, kasa hadiyewa yayi saida yaje ya zubar, cikin tausayawa yace yanzu wanan shine yayi miki dadi? Janye kwanon garin yayi yace gaskiya bazakici ba, kallon mum aysha tayi tace don Allah kice ya bani, smiling mum tayi tace Ahamad bata abincin ta, da muka samu take iya cin wanan dinma ai saimu gode Allah. Saida aysha taci ta koshi sanan suka yiwa mum sallama suka tafi.
Mum din murja ce tayi wata yar iskar dariyar mugunta ta kalleta tace Neman solution ya zama dole ki kwantar da hnklin ki murja insha Allah very soon zanyi wani Abu, nayi miki alkawari sai kin auri Ahamad ko yanaso ko bayaso, Kima fara daukar kanki a matsayin matar shi, ya zama dole ki shiga gdn. Dariyar jin dadi murja tayi tace shiyasa nake sonki mum.
Asa's ba karamin tausayin aysha yake ba, sbda yanzu abincin ta ya zama kame kame, wani lkcn ma kota fadi abinda take son ci ana kawo mata saitace ta koshi sbda cikinta me tsuri ne, sunje anyi scanning ance yan biyu zata Haifa, murna a wajen Asa's baa mgna. Tunda aysha ta sami ciki baya motsawa ko Ina, kullum yana gida yana kula da ita. Yauma kmr kullum aysha na kwance akan cinyar Asa's cikin tausayawa yace aysha me zakici yau? Don Allah ki daure ki fadi abinda zan samo miki, rashin cin abincin ki ba karamin damuna yake ba, dagowa tayi tace zogale nake so, zugalai kuma? Tace eh, mum ya kira ya fadawa, tace tana dashi a garden din ta zatasa a dafa mata, gdn mum din suka tafi bayan angama hadashi aka kawo mata, dake da baki a gdn su mum din murja ne da sauran yan uwan mum sunata hira da Asa's, saita kasa sakewa taci, daukr plate din tayi zata koma daki kawai saiya riko hannunta yace ina zaki? Daki zan koma, Wani lallausan murmushi yayi mata yace ban yarda ba nafiso kici agabana sbda na tabbatar kinci, oya dawo ki zauna ko kunyar su mum din murja beji ba ya zaunar da aysha a kusa dashi hada ido sukayi suka jijjiga kai, kasa daurewa mum din murja tayi tace Amma wanan rashin kunya dayawa take, agaban mu? Murmushi Asa's yayi yace aysha tashi mu koma side dina, aunty zuhra tace da yafi dai
Maman Aysha
[5/7, 20:07] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
2⃣6⃣0⃣➖2⃣6⃣5⃣
Haka rayuwa taci gaba tsakanin aysha da Asa's, ba lefi yanzu tana Dan cin abinci, abinda yafi damunta yanzu bacci ne, tana yawan yin bacci, saita shafe 3hours tana bacci, kuma idan ta fara baccin kmar gawa ko juyawa batayi harsai ta tashi. Abin ba karamin damun Asa's yake ba Dan dai ba yanda zaiyi ne.
Tafiya ce ta tasowa Asa's zuwa Abja zasuyi meeting da Mr President, da da ita zai tafi, amma daya tuna batajin dadi sosai, kuma kwana biyu kawai zaiyi saiyace zai kaita gdn mum kafin ya dawo. Hakan kuwa akayi saida yaje ya sauketa sanan ya wuce. Yanzu mum tayi sabuwar me girki sunanta liyaratu, degree tayi a catering amma dake aiki yana wahala bata samu ba, shine aka dauketa a gdn mum zaa ringa bata 50k per month. Zata kai 27yrs, Amma batayi aure ba, tanada kirki ga respect asalunsu yarabawa ne mazauna kano. Tunda aysha taje gdn take fama da ita, da tace tana son abu takeyi mata, sanan tanada barkwanci gata da hira. Idan tasa aysha a gaba ta fara yimata hira sai taga ta fara gyangyadi take kyaleta.
Yauma kamr kullum liyaratu tayiwa aysha danwake me dadi aysha tanaci suna hira saiga sultan yace aunty me kike ci? Aysha tace dadin duniya sunan shi, yace to nima zanci, liyaratu ce tayi caraf tace na zuba mishi ya kasa ci, kinga nashi can a kitchen, dariya aysha tayi tace indai dani ne ko bayaso zaici, kinsan da da Uwa sai Allah, dariya liyaratu da mum sukayi, aikuwa sai sukaga yana ci din, saida yaci sosai sanan aka wanke mishi hannu, liyaratu tace lalle akwai shakuwa a tsakanin Ku da sultan, aysha tace sosai ma, ni nayi missing dinshi ma, don Allah mum ki amince min mu tafi da sultan gobe idan zan koma gida, mum tace ai matsalar daga wajen daddyn shine, cewa zaiyi baki da lpya zaije ya dameki, smiling aysha tayi tace tunda haka ne saimu tafi gdn kafin ya dawo, idan yaje gdn ya ganmu dashi ai dole ya kyaleshi, ni bansan meyasa yake haka ba, mum tace Amma badan wani Abu yace abarshi anan ba, tausayin ki yake na tabbata koda ke kika haifi sultan zai iya hanashi zuwa wajen ki, Sbd cikin mijinki ne ya hanashi zuwa, kuma gaki da yawan bacci, idan kun tafi goben ma kwana daya kawai zaiyi ya dawo, smiling aysha tayi tace to shikenan mum.
Washe gari bayan sunyi break mum ta dakko gyalenta tace zanje dubiya asibiti, liyaratu ki kula da gdn da Allah, tace to HAJIYA, mum na tafiya aysha ma ta mike tace nima bari naje na kwanta bacci nakeji. Side din Asa's ta tafi ta kunna A/c ta kwanta, dake tunda akayi aurensu ta daina kwana a dakinta na da.
10:45 am
Mum ta dawo, bataga kowa a falo ba sai ta nufi side din Asa's wajen aysha sbda jikinta ya bata tana can tana bacci, a kofar falo ta hadu da liyaratu tana fitowa daga side din, kallonta mum tayi tace ke kuma meya kawoki nan? Aysha naje na duba sbda tunda kika tafi take bacci, shine naje naga ko lpya, kuma naga har yanzu bata farka ba, mum tace to wanan ya zama last, ba me aikin dayake shiga nan, domin kuwa ba huruminki bane, koda wasa karna kara ganin ki anan kinji ko? Tace to ayi hkri hajiya, sanan tace ki fadawa Laraba ta yago min zogalai a garden yau dambu nakeso, tace to hjya, sanan ta tafi ita kuma mum taje ta kara duba aysha saida ta tabbatar she is normal sanan ta fito daga dakin.
4:20pm dot jirgin su Asa's ya sauka a kano, yana kunna wayarshi yaji kira ya shigo, bakuwar no ce yana dauka yaji ance yallabai barka da yamma, sunana ASP Abubakar, idan bazaka damu ba don Allah INA Neman izini naganka yanzu, yanzu kuma? Gaskiya bazai yiyyu ba domin kuwa daga tfya na dawo ko gda banje ba, kadai sa wani time din amma banda yau, yallabai don Allah kayi hakuri muganka Sbd abinda zamu tattauna dakai yanada matukar muhimmanci in fact abune daya shafi iyalinka, to shikenan mu hadu a gdn mum dina, to mungode yallabai.
A kofar gdn Asa's ya samesu, yana zuwa suka shiga tare, guest falo ya shiga dasu, bayan an kawo musu drinks Asa's yace ina jinku meya faru? ASP ne yace ayi mana uzuri muga madam dinka yallabai, phone dinsa ya dauka yace mum kuzo guest falo keda aysha, ba karamin mamaki mum tayi ba, Amma dai saita taho tana zuwa yace ina aysha? Mum tace yanzu suka tafi ita da sultan, cikin sauri ASP yace ayi mata waya ta dawo, harta kusa zuwa gda taga kiran mum, tana dauka tace ki dawo gda yanzu nan, tace toh, tunani take tayi a zuciyata tace Allah yasa lpya.
Tana zuwa akace su shiga dakin baki, sanan ASP ya fara bayani kmr haka:-
Wanan mutumin sunan shi gidigo, tsohon Dan ta adda ne, an daure shi a gdn yari yafi a kirga, daga baya sai Allah ya shirye shi, tun munasa ran kara kamashi da wani lefin har muka Dena, shine yau yazo min da lbrn cewa wife dinka tayi mishi text akan tanaso yayi kidnapping dinsu ita da danka sultan, akan saika basu 5 billion naira zasu sakesu, idan ka bayar da kudin zata bashi billion daya, mika mishi wayar gidigo yayi yace ga text din ka karnta da kanka yallabai. Asa's yana karbar wayar no aysha ya fara dubawa dake ya haddace ta, ya Dade yana tantance no amma ba wani mistake, saida ya tabbatar cewa no aysha ce sanan ya fara karanta text din kamar haka...........
Maman Aysha
[24/05 9:21 PM] Mizz Ayuush: [5/9, 20:50] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
2⃣6⃣5⃣➖2⃣7⃣0⃣
Gani yayi bazai iya karntawa ba kawai saiya mikawa ASP wayar yace karbi ka karanto mana kowa yaji, yace toh yallabai.
*Assalam sunana aysha Ahamad sa'eed sardauna (Mrs Asa's) na samu number k ne a wajen friend dina, kuma ta tabbatar min cewa ka kware a iya kidnapping, duk da ta fadamin cewa ka dena wanan harkar yanzu, Amma inaso ka temaka muyi business din nan dakai domin kuwa zai kawo kudi sosai, kuma bazaka sha wahala ba. Idan ka dauke mum din Asa's duk duniya ba Wanda Asa's yakeso kmr ni da danshi sultan, Sbd zamu fito anjima da yamma kai kuma sainayi kidnapping din mu, banaso a sami matsala a yau nake so kayi, sbda Abu ne me wahala na kara samun chance din Dana samu yau, idan ka amince zakayi min aikin kayi min flashing, falashiin kawai nace kayi min karka sake ka kirani, saina kika*
Tunda Asp ya fara karnta text din Aysha ta hada gumi, yawun bakinta ya kafe, tunani take mafarki take ko kuwa da gaske ne?
Asa's kuwa jingina bayan shi yayi akan kujera idonsa sun kada sunyi ja kamar borkono, kallon gidigo yayi yace bayan ka karnta text din kuma meya faru? Gidigo yace flashing din nayi mata, saita kirani, ka duba received call zakaga no ta, karbar wayar Asa's yayi ya duba ya gani no aysha ce, sanan ya duba call history yaga sunyi 10minutes, cikin dashesshiyar murya yace nagani, gidigo ne yaci gaba da cewa nayi recording din maganar da mukayi da ita lkcn data kirani, kunna wa yayi saiga muryar aysha tana yawo a kunnen kowa kmr haka.....
*yawwa Dan gari, wanan ya tabbatar min da cewa ka amince kenan, inaso ka zama very careful lkcn da zaka gudanar da aikin, sbda Kasan Asa's ba karamin mutun bane, kuma sanan 5 billion naira zakace ya baka, idan ya bayar zan baka 1billion naira, banason kuskure ko cin amana acikin aikin, inaso komai ya tafi successfully. Muryar gidigo ce ta fito yace Amma bakya ganin 5 billion tayi yawa? Batayi yawa ba, Asas zai iya baka koda trillion ka nema indai akan nida sultan ne, sbda haka karka damu, idan na fito zanyi maka text, Amma fa karka sake ka kirani*
Cikin tsananin tashin hnkli Asa's yace ni kuma irin tawa kaddarar kenan? Duk mutumin dana yarda dashi saiya ha'inceni? Hawaye ne yake zuba a idonshi kamr famfo yace wanan shine karo na hudu da matana sukayi disappointing dina, amma ban taba shiga tashin hnkli irin nayau ba sbda sauran matan da suka ha'ince ni dama ba wani sonsu nake ba, kallon kwayar idon Aysha yayi yace ban taba sanin so ba sai akanki, ke na fara so, ke na bawa amanar zuciyata, ke zuciyata ta amincewa meyasa kika ha'ince? 5 billion nawa take a wajena da har zaki betraying dina akanta? Meyasa kikayi min haka aysha? Meyasa kikace amana ta? Ya karasa magna cikin wata wahalalliyar murya,,,,,,,wallahi banci amanar ka ba yaya Asa's, wallahi duk abubuwan nan da aka fada bansan ko daya aciki ba, wallahi sharri akayi min,,,,,rufemin baki dalla, idan kince text karya ne, recording din da yayi na maganar da kukayi fa? Ko kinaso kice ba muryar ki bace? Rike kafarshi tayi tace tabbas muryata ce, amma kuma wallahi ba dani yayi waya ba, bansan lkcn da nayi wanan mgnar ba wallahi,,,,,,,, wata tsawa Asa's yayi wa aysha yace ya isa, bana bukatar jin komai daga bakin ki, ba wani Abu da zaki fada na yarda dake, iam totally disappointed on you aysha, ni yanzu ko ganin ki banason yi na tsaneki, Asp ya kalla yace ka tafi da ita kayi mata duk hukuncin daya dace, mikewa aysha tayi tace ni kake cewa ka tsana? Ni kake cewa.......jiri ne ya kwasheta ta fadi, da gudu mom tazo ta daga ta, jini ne ya fara zuba daga jikinta, salati mum tayi tace shikenan cikin ya zube
Maman Aysha
[5/9, 21:57] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
2⃣7⃣0⃣➖2⃣7⃣4⃣
Asa's yanajin haka ya mike ya fita daga falon, cikin bacin rai mum tace ina zaka? Zo ka dauketa ka kaita mota, juyowa yayi ya dauketa suka fita, da sauri aka bude mota Asa's yana kwantar da ita a back seat yayi tafiyarsa, a kusa da aysha mum ta zauna, harsu Asp aka tafi asibiti, shi kuma gidigo akace ya tafi sai an nemeshi.
Asibitin Dr Muktar aka wuce da ita, tun kafin su karasa mum tayi mishi waya, suna shiga wasu nurses su biyu suka dorata akan strechter suka shiga ciki da ita.
Rubdugu akayi akanta har saida suka tabbatar bleeding din ya tsaya sanan suka kyale ta, scanning machine Muktar ya dakko yayi mata cikin tsananin fargaba mum tace likita yay? Cikin ya zube ko? Ah be zube ba, treating abortion ne, alhamdulilla mum tace, sanan tace yanzu sai yaushe zata farfado? Any time zata iya farfado wa, sai lkcn mum taji hnklin ta ya kwanta, fitowa wajen su Asp tayi tace inaso ka bani phone din gidigo akwai abinda nakeso na duba, yace to hjy. Text message din ta shiga, ta duba time din da aka tura, taga 10:20 aka tura shi, sanan ta duba no Aysha acikin list din received call taga wajen 10:35 kiran ya katse, kallon Asp tayi tace iam totally confused akan case din nan, ina ganin kmr akwai makirci acikin al amarin nan, Sbd yau da safe na fita around 9:30, naje dubiya, wajen 10:45am na dawo, ina shiga gda naga me aikina liyaratu ta fito daga side din Asa's,,,,,,,bashi labrn duk abinda ya faru tayi, sanan taci gaba da cewa liyaratu ta tabbatar min da cewa tunda na fita aysha take bacci, kuma idan ka duba time din da aka tura text din da kuma wayar da yace sunyi a tsakanin 10am ne zuwa 10:35, kuma aysha bacci take a wanan lkcn. Mikewa Asp wayar tayi ya gani, shima ya gaskata maganar mum, sanan yace ke aganinki suwa kike tunanin zasu aikata haka? Mum tace INA zargin liyaratu me aikina, sbda tana dakin aysha a lkcn da aka turawa gidigo text, kuma ni shi kansa gidigo ma ban yarda dashi ba, Sbd haka Asp inaso ka kama min liyaratu da gidigo kuyi tayi musu azaba harsai sun fadi gskya, Sbd gaskiya ni su nake suspecting, mikewa Asp yayi yace na yarda da hujjojinki, kuma zamuje mu kamasu a yau din nan, amma itama aysha bazata fita daga zargin ba harsai gskya ta bayyana, sbda haka tana warkewa zamu tafi da ita station, mum tace ba matsala.
Yana fita daga asibiti yasa yaranshi su kama mishi gidigo, sanan shida wata woman police sukaje gdn mum suka kama liyaratu.
Asa's kuwa dakinshi ya tafi ya kwanta, ya rasa abinda yake mishi dadi gashi nacecciyar zuyarshi ta dameshi da tunanin ko wane hali aysha take ciki? Duk yanda yakai da cire tunanin aysha a zuciyarsa ya kasa, Sam zuciyarsa taki ta amince mishi da tsanar Aysha, anya kuwa aysha ba tsafi tayimin ba? Wanan wane irin bala'i ne? Meyasa na kasa dena tunanin ta?
Maman Aysha
[24/05 9:21 PM] Mizz Ayuush: [5/11, 20:49] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
2⃣7⃣4⃣➖2⃣8⃣0⃣
Kwanan aysha uku a asibiti aka sallameta, ba karamin kulawa Muktar ya bata ba, dakanshi yaje ya karbo musu drugs din daya rubuta, sanan ya fadawa mum kar aysha tayi aikin komai, sbda an bata bed rest, saida ya rakosu har bakin motor, sanan yace amma yallabai Asa's baya gari ko? Sbda naga tunda aka kwantar da aysha ko a waya be kirani ba, dariyar yake mum tayi tace ai ban fada mishi ba, besan bata da lpya ba Sbd damuwa zaisa a ranshi kuma gashi baya gari, dariya Muktar yayi yace gara da baa fada mishi ba da yanzu nima ya dameni. Kayansu drive da wasu securities su uku suka zuba a motar sanan su mum sukayi wa Muktar sallama suka tafi.
Yau kwanan su aysha biyu kenan da dawowa daga asibi, tunda suka dawo aysha take zuba ido kp zataga asas amma shiru, kmr ma baya gdn. A bangaran su gidigo kuwa tunda aka kamasu ake basu wahala amma fur sunki fadar gskya, Asp ne ya kira mum a awaya yace HAJIYA har yanzu fa suspects dinmu sunki su fadi gskya, duk tambayar da akayi musu sun kafe akan aysha ce ta sakasu, nifa INA ganin da gaske aysha ta aikata abinda ake zargin ta dashi, sbda haka hajya kiyi mana hakuri mu gudanar da aikinmu yanda ya kamata, tunda aysha ta samu sauki zanzo na tafi da ita yau, cikin bacin rai mum tace kai har wani aikin ka ka sani? Ina ganin wahar da kuke basu ba wata me yawa bace, ni su nake zargi 100% Sbd kallo daya nayiwa gidigo na gane cewa he is guilty, ko ka manta ni retired Justice ce? Inaso Ku ninka azabar da kuke musu sau hudu, idan sukaji azaba tayi yawa zasu fada. Asp yace to shikenan hjya, amma fa ina nan akan bakana na kama Aysha, mum tace idan dai kuka ninka wahalar da kuke basu, kuma basu fadi Wanda ya sasu ba zuwa gobe, na amince kazo ka kamata.
Washe gari tunda Aysha tayi sallar asuba ta koma bacci dake ta tashi tayi sallar tsakar dare, bata barka ba sai wajen 10am tana tashi ta shiga toilet tayi wanka ta shirya cikin wata English gown yellow me spaghetti hand, kara taje gashinta tayi ta daure shi da ribom, light make up tayi tana cikin fesa turare phone dinta ta fara kara abbanta ne ya kira daga Bauchi, da sauri ta dauka bayan sun gaisa yace kira nayi inyi miki godiya, mijinki yazo ya gaishe mu yayi mana kyautar kudi masu yawa, kuma yasa an karawa Saleem girma a company shi, tun ranar dayaje nake Neman layinki amma ban samu ba sai yau, jiki ba kwari aysha tace eh akashe wayar take sai jiya da daddare na kunna, to ai ba wata matsala ko? Ah ba matsalar komai Abba, to don Allah idan kinje gdn hjya kiyi mana godiya, na kirata har sau hudu bata dauka ba may ba batasan no ba shiyasa, aysha tace ai ina gdnta ma bari kawai nakai mata Ku gaisa, yace to shikenan.
Asa's ne ya shiga dakin mum zaiyi mata sallama, sai yaga bata, kawai saiya juya zai fito yazo daf da bakin kofa yaci karo da mutun, kamshin turarensu ne yasa suka gane junansu, nan take zuciyarsu ta fara bugawa da sauri at d same time, bude baki aysha tayi zata bashi hakuri kawai saiya rabe ta gefenta zai wuce, sauri tayi tasha gabanshi, cikin sanyin murya tace yaya Asa's don Allah karka hukuntani ta wanan hanyar, Wallahi dauriya kawai nake amma bakaga yanda sonka yake wahalar dani ba, ya kamata ka daure ka bani time nayi maka bayani a nutse, Wallahi bansan komai akan saidar da gidigo yazo da ita ba, kuma ni ban taba ganinshi bama sai ranar da case din ya faru,,,,,,, dalla yimin shiru! ya daka mata tsawa ke yanzu a haukanki kinyi zaton mayaudaran kalamanki zasu kara tasiri akaina? Idan kina wanan tunanin gara ki dena, domin kuwa duk duniya ba wacce na tsana yanzu irinki. Wasu zafafan hawaye ne suka fara zuba a idonta, cikin kuka tace koda ka tsaneni, koda bazaka kara cigaba da zama dani a matsayin wife dinka ba, kayimin alfarma ayi bincike akan case din, bawai sbd inaso naci gaba da zama dakai ba, ah ah inaso ne na wanke kaina akan mummunan zargin da ake min. Ai sedun da gidigo ya bayar basa bukatar bincike, Sbd haka karki karayi min mgna, kuma yanzu zanyi wa Asp waya yazo ya tafi dake,,,,,,,,,idan ka sake ka kirashi to bani bakai, muryar mum ta katse shi, a tare suka juya suka ganta a tsaye, cikin mamaki Asa's yace meyasa kika ce haka mum? Sbda ka kasa fahimtar Aysha, ka kasa ganewa wacece aysha, kayi zama da ita na wattani da yawa amma har yanzu bakasan halinta ba, ka dena hada case din matan ka na baya da wanan, sabda a wancen karan Sadiya da kunnenka da kuma idanunka ka kamata, ita kuma Surayya da idanunka ka kalli video da goje ya dauka lkcn da sukaje mishi da maganar, amma ita aysha har yanzu ba wani kwakkwaran evidence. Dama nasan bayanta kike bi, na fuskanci kinfi son aysha akaina mum, ba haka bane Ahamad, inaso ka sani ni alkali ce, na saba shari'a kala daban daban, sbda haka ni har yanzu sedun da aka bayar basu gamsar dani ba. To kuwa wallahi dole acikin biyu ayi daya, kona kira Asp yazo ya tafi da aysha, ko kuma ya zama dole yau aysha tabar gdn nan, sbda bana son ganin ta, cikin lallami mum tace uhm uhm Ahamad, karfa bacin rai yasa kayi abinda zakazo kana dana sani, kuma ya kamata ka sassauta ma yarinyar nan, kodan cikinka da take dauke dashi, Au wai dama wanan kaddararran cikin be zube ba har yanzu? Mum ce tace Ahmad Kasan abinda kake fada kuwa? Na sani mana, kaddara ce kadai zatasa a haifo min su, ni kuma a haka rayuwata zata Kare, duk 'yayana ba Wanda suke da Uwa ta gari
Maman Aysha
[5/13, 09:40] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
2⃣8⃣0⃣➖2⃣8⃣5⃣
Da nasan cikin be zube ba ai da nasa doctor ya karasa zubar min dasu, na fiso idan na rabu da aysha ace rabuwa mukayi ta har abada, bana sha'awar abinda zai kara shigo min da ita cikin rayuwata, cikin tsawa mum tace Ahamad ya kamata ka saita kalaman da kake fada, ya kamata ka tausasa harshen ka sbda INA guje maka ranar da zakazo kana danasani, ni ba wani Dana sani da zanyi indai akan wanan butulun ne, ke na fuskanci ko kadan bakya son lefinta, na rasa wane irin so kike mata, Sbd har kinfi sonta akaina sbda ta iya makirci, to Wallahi ya zama dole yau tabar gidan nan, kallon aysha yayi yace idan kin cika yar halak inaso yau kibar gdn nan ki koma garinku zan ringa tro miki kudi idan kin haihu kin yaye yaran zanzo na karbesu. Mum ce tace to dunda hakane ka rubuta takardar saki ka bata, zan saketa amma ba yanzu ba, sbda kona saketa yanzu iddarta bazata cika ba saita haihu, Sbd haka idan ta haihun zan saketa, kallon aysha yayi yace ki fadi ko billion nawa kk so zan baki, cikin muryar kuka aysha tace bana bukatar komai a wajen ka, kuma tabbas ni yar halak ce sbda haka ayau zanbar gdn nan, mum ta kalla tace don Allah mum kiyimin izini na tafi gdnmu. Shiru mum tayi for some minutes sanan tace nayi miki, ki shirya kayan ki zanyi wa mallam Ibrahim mgna yazo ya kaiki, kai kuma Ahamad baka taba yimin musu ba, amma yau INA fada kana fada ko? To inaso ka sani daga yau na cire hannuna a case dinka da aysha, kuma ko nan gaba karka sake ka kara sani aciki. Aysha jeki hado kayan naki, tace to. Yar karamar trolley ta dakko ta zura hijabinta na salla red color yayi mata kyau sosai, a falo ta sami mum da Asa's suna zaune shi kuma mallam Ibrahim yana tsaye, aysha na zuwa ya karbi trolley din ya fita da ita, kallon mum aysha tayi tace zamu tafi mum, nagode sosai da kaunar da kika nunamin, a lkcn da inna ta mutu nayi kukan maraice sbda ina tunanin bani da wani gata daya rage min a rayuwata, Amma haduwata dake ta tabbatar min da cewa ba haka bane, kinyi min abinda koda mahaifiya ta tana raye iya abinda zatayi min kenan, na tabbata yanzu duk duniya ba Wanda yakai ki sona, Asa's ne yayi saurin dagowa ya kalleta, ci gaba tayi da cewa nagode Allah ya saka miki da gdn aljanna, murmushin manya mum tayi tace amin aysha Allah ya kiyaye hanya tace amin.
Aysha na fita Asa's ya rintse ido ya dafe kanshi, mum tana kula dashi saida batayi mishi mgna ba, kwala kiran aysha tayi sai gata ta dawo, mum tace zoki zauna anan, duban aysha tayi tace kiyi hakuri dani aysha, nasan zakiga kmr na takura miki, to amma ya zama dole ne, kinsan likita ya baki complete bed rest, sbda treating abortion kika samu, kuma kinsan effects din da suke tattare da kin bin umarnin shi Sbd kema health professional ce, shiyasa na kiraki akan ki janye mgnar tafiya Sbd idan kika tafi cikin ki zai iya samun matsala koda kuwa ajirgi ne, ni kuma Allah ya jarafce ni da son abinda zaki Haifa, Sbd haka don Allah kiyi hakuri ki zauna dani harki haihu. Shiru aysha tayi for some minutes, sanan tace ba abinda zaki sani yi aduniyar nan banyi miki shi ba, koda kuwa zan rasa rayuwata ne akai, sbda haka shikenan na hakura Allah yasa haka shi yafi alkairi. Wata wawiyar ajiyar zuciya Asa's yayi, su Kansu sun kasa gane ta mecece? Phone din mum ce ta fara kara, Asp ne ya kirata tana dauka ya gaisheta wit respect, sanan yace suspects dinmu sunyi mgna, cikin zumudi mum tace alhamdulilla, wa sukace ya sasu aikin? sunanta sameena yar gdn minister of finance, sauran bayani sai kunzo. Kallon aysha mum tayi tace aysha Allah ya wanke ki yau, ansami wadda suka kulla miki sharri, wai wata ce sameena yar gdn minister of finance Cikin tsananin firgita Asa's yace sameena ce ta kulla wanan makircin? Mum tace eh itace ko kasanta ne? Eh na Santa, ta taba cewa tana sona. Phone dinsa ya dauka yace Asp inaso kaje ka kamo sameena yanzu nan, zamuzo police station din yanzu, kallon mum yayi yace muje ko? Tace to. A tare suka fita har aysha suka nufi police station
Maman Aysha
[5/13, 10:31] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
2⃣8⃣5⃣➖2⃣9⃣0⃣
Har cikin gda Asp yaje yasa aka kira mishi sameena ya taho da ita dake indai akan gaskiya ne bashi da tsoro, a motar su ta police aka dakkota cikin fitsara tace uban me nayi muku zakuzo har gda Ku kamani? Asp yace muna tuhumarki da hada baki da akayi dake aka kullawa aysha Mrs Asa's sharri dake dasu gidigo, tana taunar chewing gum tace to ai bani kadai bace, ni biyansu kawai nayi amma duk wani kulle kulle murja kanwar shi ce tayi, ita tazo har gdnmu ta sameni tace tasan irin sonda nakewa Asa's, tun da dadewa, sbda haka zata temaka min na aureshi, ta gama hada plan din komai ni kuma saina biya kudin, Sbd ina mugun son Asa's shiyasa na amince na biya kudin 20 million. Cikin kunar rai Asa's yace Asp jeka dauko murja, cikin few minutes sai gasu, gabanta Asa's yaje ya ringa wanka mata mari saida yayi mata sau goma sha biyu sanan yace duk a cousins dina ba wacce nakeso kmr ke, ba wacce na yarda da ita kuma na saki jiki da ita kmr ke, amma meyasa kika hada makircin da zaki rabani da aysha bayan kinsan itace farin cikin rayuwata? Sbda INA sonka, na Dade INA sonka yaya Asa's, duk wani bugu da zuciyata take da sonka take yi,saidai na duba naga zuciyarka bazata taba son wani ba sai baka tare da aysha, nasan cases din da suka faru a baya, kuma nasani ka Dade kana zargin aysha akan tazo ne domin ta cutar dakai, wanan dalilin ne yasa na hada plan din sbda nasan zeyi saurin tasiri a zuciyarka. Idan ka tsani aysha ni kuma saina shirya duk yanda zanyi na mallake ka.kaji dakikiya jaka mahaukaciya, ke a tunanin ki idan na rabu da aysha zan kara yin soyayya? To bari kiji na fada miki, da ace na saki aysha da bazan kara yin aure ba a duniya Sbd shi is my type, ita kadai zuciyata take so, sameena tace lalle murja kin cika yar iska, Ashe dama kinyi amfani dani ne don ki cimma burinki? Murja tace kwarai kuwa, sbda na shirya plan amma banida kudin dazan biyasu, ke kuma nasan kinada kudi shiyasa na biyo ta kanki. Sameena tace garama da Allah ya tona asiri, Asp ne ya daka musu tsawa yace a shiga dasu ayita cin ubansu kafin a shigar da case din kotu. Aysha ce tace inada mgna, indai sbda ni zaa shiga kotu INA rokon alfarma a kashe case din anan, domin kuwa Wallahi ni na yafe musu, ina musu addua akan Allah ya shiryesu su fara yadda da kaddara mekyau da kuma marar kyau, Asa's ne yace idan ke kin yafe Toni bazan yafe ba, sbda sun wahalar dani, sun sani acikin damuwa, naji bazaa je kutu ba Amma don Allah Asp inaso kuci uban yaran nan harsai sun gane kuskurensu, sameena ce tace kai kake nakayi ni nasan ayau zan fita daga wajen nan, Sbd ko nawa ne dad dina zai iya biya, Asa's yace kin manta koni waye shiyasa kike wanan mgnar naga ta yanda uban naki zai fitar dake, kallon Asp yayi yace duk lkcn da uban wanan yarinyar yazo beli kayi min mgna, Asp yace to shikenan yallabai, sanan suka tafi shida aysha da mum.
Tunda suka shiga mota yake satar kallon aysha har sukaje gida, dakinshi ya koma ya kwanta yana tunanin da wanne ido zai kalli aysha ya bata hakuri, yayi wa aysha rashin mutunci marar misaltuwa, ya fada mata bakaken maganganu da baa taba fada mata irinsu ba, yanzu ta ina zai fara bata hakuri kenan? Me karatu Ku bawa Asa's shawara ta ina ze fara?
Maman Aysha
[24/05 9:21 PM] Mizz Ayuush: [5/14, 12:03] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
2⃣9⃣0⃣➖2⃣9⃣5⃣
Washe gari da safe aysha ta fito cikin wata Arabian gown pink ta daure karamin gyalen ta kasan gashinta ba karamin kyau tayi ba, kasa ta tafi zata karya, mum da asas ne zaune a falo, tun kafin ta karasa sauka kamshin turarenta yaje musu, lkci guda suka zuba mata ido suna kallonta, tayi zaton tazo last step, Ashe second to d last ne, tana Dora kafarta ta zame, ta tafi zata fadi Asa's ya tafi a sukwane ya rike ta, tallafo ta yayi ya zaunar akan kujera, yace sannu aysha, ko kallonshi batayi ba bare taji responding, juyawa yayi ya kalli mum yace Wallahi bakiga yanda gabana ya fadi ba, cikin shan mur mum tace uhhmm, gaban aysha yaje yace me zakici a kawo miki? Basarwa tayi kmr bataji me yace ba, mum tace wanan ba huriminka bane, ka tafi inda zaka don naga alama ka takura mata ko aysha? Aysha tace yawwa Wallahi gara ya tafi kam, kallon kwayar idon aysha yayi ya sakar mata wani shu'umin mayaudarin murmushi, sanan yace kina nufin bakya son ganina kenan? Tace eh, to shikenan bari na tafi, harya fara tfya sai kuma ya dawo cikin shagwaba yace to ai ni yau ba inda zani, so nake na zauna na huta a gda, kitchen ya shiga ya dakko flaks din kunun gyada da Kofi ya zubawa aysha yasa mata sugar ya gauraya sanan ya mika mata, kin karba tayi, saiya marairaice yace nasan fushi kike dani, kiyi hakuri ki karba kisha koda bazakiyi min mgna ba pliss, Cikin shan mur tace wa ya fada maka zansha kunu? Ka dauke abinka banaso, kinaso aysha, na sani da kunu kawai kk break fast, kar fushin da kike dani yasa kiki cin abincin, kiyi hakuri kisha baby's dinmu aysha, kaddararrun yaran da kake bakin ciki da rashin zubewarsu kake so yanzu aci abinci Sbd su? Sauri yayi ya kalli mum, ita kuwa saita mike ta tafi daga wajen, dawowa kusa da aysha yayi yace tabbas na tafka babban kuskure, Amma don Allah aysha kiyimin uzuri, Wallahi rashin sani ne yasa nayi miki haka, don Allah ki gafarceni aysha ni kaina yanzu inajin kunyar ace wai kalaman nan daga bakina suka fito, mikewa aysha tayi ta nufi hanyar dakinta, da sauri ya rike hannunta yace ya zama dole kibar dakin ki na upstairs ki dawo kasa sbda is very risk ki ringa hawa sama kina sakkowa, cikin kuka aysha tace sakar min hannu, ko bakasan nima yanzu na tsaneka ba? To idan baka sani ba inaso yanzu kasani, karka ga don naci gaba da zama a gdnku kayi tunanin zanci gaba da zama dakai, na riga na cireka a raina, zama dakai ba shida wani amfani tunda bazaka iya bada saida mekyau akaina ba, mum ce ta fito tace Ahamad saketa, to mum don Allah ki roketa ta koma part dina na gdn nan Sbd kinga dazu da ta fadi zaa iya samun matsala, tunda batason ganina nizan koma gidana, don Allah mum? Shan kunu mum tayi tace ba nace karka kara sani a case din Ku ba? Marar kuya fitsarrare, da kana da kunya ma ai bazaka iya yi mata wata mgna ba da wuri haka. To inaso kasani zamana aysha take a gdn nan ba zaman ka ba, kuma tunda tace bata sonka inaso ka rubuta takardarta ka bata kuma Wallahi karka sake kayimin musu bana bukatar jin komai daga bakinka, fitamin daga gida. Karka sake ka dawo gdn nan ba tare da takarda ba. Ji yayi zuciyarsa tana wani irin tafasa, cikin tsananin bacin rai ya fita.
Har Asa's ya fita aysha tana kuka dakyar mum ta rarrashe ta tasha kunun daya zuba mata, ba abinda yake konawa aysha rai irin kiran cikinta da yayi kaddararre.
Asa's kuwa yana fita ya samu minister a kofar gda, karasawa yayi suka gaisa, sanan Asa's yace nasan akan case din yarka kazo, mu koma station din nima yanzu can zanje. Suna binshi a baya sukaje har police station, sawa yayi aka fito dasu gabadaya sun fita hayyacinsu, parents din murja ma sunzo, saida ya bari suka gaisa da iyayen su sanan yace amayar dasu, yana jira yaji minister yayi mishi gadara, amma ga mamakinsa saiyaji yana rokonshi yayi hakuri a sakesu, kallon shi asas yayi yace tun jiya naso asake su, amma sai sameena ta cika baki sbd tana gadra kanada kudi, sassauta murya minister yayi yace kasan yaran yau ka haifesu ne baka haifi halinsu ba, don allah kayi hkuri mr Asas, kafin yayi mgana mum din murja ta fara bala'i wato kudi yasa ka zama marar mutunci ko? Munayi maka magna Amma kmr zugaka muke? Tunda kayimin haka zaka iya yiwa hajya ma haka tunda dani da ita duk daya ne, ba tare da ya damu ba yace nifa banason hayaniya, wanan fadan naki bashi zaisa na hakura ba, kuma inaso kisani kasancewar murja causin dina ne yasa aka sassauta mata, da bare ce da yanzu NASA an wulakanta min su, kinsan kudi ba karya bane. Zanyi tunani zuwa nan da next WK nagani ko zan iya hakura, kallon minister yayi yace yallabai kayi hakuri, ba karamin lefi sukayi min ba makircin da suka kulla ya jefani acikin matsalar da bansan yaushe zan fita daga ciki ba, Asp ya kalla yace sai mun kara waya.
Mum din murja ce ta kalli minister tace meyasa kake lallabashi bayan kinada power da zaka iya ja da kowa a 9ja? Inda mune muke da power dinka ai da yanzu anyi an gama, Amma kana binshi a hnkli yana maka rashin kunya, bayan ka haifeshi. Murmushin manya minister yayi yace banida wani zabi daya wuce nabishi a hnkli, domin kuwa ya fini kusanci da Mrs President, Mr Asa's yana daya daga cikin masu arawa Nigeria kudi idan aka shiga matsala, so kinga kenan ba karamin mutun bane. Ni yanzu temako daya zakiyi min, tunda mum dinshi yar uwarki ce, kiyi mana jagora muje mu roketa, nasan ita kadai ce zata iya yi mishi magana sbda kinga 'yayyanmu ne basu da gaskiya.
Hakan kuwa akayi, a tare suka tafi gdn mum, suna shiga mum din murja ta zube agaban mum tana wani irin kuka me ban tausayi, tana rokon mum akan ta temaka ta roki asas, shima minister ya kwantar dakai sai rokon ta yake, kunya ce ta kama mum, ace babban mutun kmr minister yana rokon ta, kuma ga yar uwar ta sai kuka take, tausayin su taji ya kamata, kawai saita dauki phone dinta ta fara kiranshi, yana dauka tace Ahamad inaso kaje kasa a fitar da yaran nan yanzu nan, umarni nake baka idan kuma ba haka ba zaka hadu da fushi na, wit respect yace to mum, don Allah kiyi min afuwa idan na hadu da fushinki ai rayuwata ta wargaje, zansa asakesu yanzu ma kuwa, Amma fa nima sai aysha tayi hakuri ta yafemin tukun, sbda sune sukayi causing din duk abinda ya faru, kiyi hakuri don Allah mum bawai naki bin umarnin ki bane, ya kamata nima aimin adalchi akan case din
Maman Aysha
[5/14, 13:31] Maman Aysha: Gaskiya tafi kwabo💵💵
2⃣9⃣5⃣➖3⃣0⃣0⃣
Cikin mugun bacin rai mum tace kazo gda yanzu ka sameni. Cikin few minutes saigashi yazo, yana shiga mum ta dauke shi da mari har sau biyu, cikin bacin rai tace Dan iskanci INA baka umarni kaima kana bani? Aysha dake gefe saida taji mari ajikinta, duk irin wulakancin da Asa's yayi mata bataji sonshi ya ragu a zuciyarta ba, duk abinda take mishi dauriya kawai take. Durkushewa Asa's yayi a kasa idonshi sun kada sunyi ja, cikin kuka yace haba mum don Allah, yanzu lefina kika gani? Bancancanci wanan hukuncin daga wajen ki ba, meyasa kika dena tausayi na? Meyasa kika dena sona? Ya kamata kiyimin uzuri, kinfi kowa sanin halin dana tsinci kaina a baya, be kamata kiga lefina ba Dan na yarda da abinda akace Aysha ta aikata, idona ne ya rufe a lkcn shiyasa na kasa gane gskya. Kallon mum yayi yace idan har keda aysha kunyi hakuri kun yafe min zansa a fitar dasu, idan kuma Baku yafe min ba nima Wallahi bazan fito dasu ba, sbda bazai yiyyu nasa asakesu suci gaba da rayuwar jin dadi, ni kuma rayuwata tana cikin kunci ba.
Minister ne ya kalli mum da aysha yace don Allah kuyi hakuri Ku yafe mishi, tausayin Asa's ne ya kama mum, dake tsakanin da Uwa sai Allah, kallon Asa's tayi tace shikenan mun hakura, magana ta wuce kaje kasa a sakesu, da sauri yaje yayi hugging din mum yace nagode, kallon aysha yayi saiyaga ta hade girar sama data kasa, jiki ba kwari ya cewa su minister muje station ko? Sukace to, godiya sosai suka yiwa su mum, sanan suka tafi. Suna zuwa ba bata lkci sukasa aka fito dasu, kwana biyu kacal sukayi amma gabadaya sun fita hayyacinsu. Kudi masu yawa Asa's ya bawa su Asp sanan ya tafi, su kuma kowa ya dauki dansa suka tafi asibiti sbda azabar da suka sha. Liyaratu da gidigo kuwa ance sai iyayen su sunzo
Asa's na fitowa daga station gdn shi ya koma yayi wanka ya shirya cikin wata yellow shirt da red jeans, An rubuta SMART da red paint aciki, Yellow facing cap yasa me tsada, sanan ya manna black glass a idonshi, yayi wanka da turare, direct gdn mum ya tafi a karamin falo nacan ciki ya samesu ita da aysha, wit respect ya gaida mum, sanan ya kalli aysha yace yan mata ba gaisuwa? Kara turo baki aysha tayi, zama yayi akusa da ita yace haba aysha, har yanzu baki dena fushin dani ba? Tashi mum tayi ta basu waje, cikin unique voice dinsa yace don Allah aysha kiyi hakuri, ko kinaso na margaya kwanan nan ne? Idan kikaci gaba da fushi dani zan iya haduwa da heart attack, kinga daga nan kuma se mutuwa twins sun zama marayu kenan, aiko baka mutu ba twins marayu ne, tunda ka kirasu da sunan kaddara ai basu da wani muhimmanci a wajen ka, sauri yayi yasa hannu ya rufe mata baki da hannun shi, don Allah ki dena fadin irin wanan mgnar Aysha, Wallahi duk duniya ba abinda nakeso kmr twins,
banida wani buri daya wuce naga sun fito duniya, bacin rai ne yasa nace haka don Allah aysha kiyi hakuri, Wallahi duk duniya ba Wanda yakaini sonki, ko mum bata kaini sonki ba Allah, kiyi hakuri sharrin shedan ne da bacin rai yasa nayi miki haka. Kuka sosai aysha take, kawai saiyayi hugging dinta yana rarrashinta, kwacewa tayi daga ajikinshi ta tafi daki da gudu tana kuka. Ji yayi gabadaya jikinshi yayi sanyi, wata irin nadama ce take damunshi, gaskiya beye mata adalci ba kam, to amma ba yanda zaiyi ne.
Mikewa yayi ya shiga dakin mum, a sanyaye yace aysha har yanzu taki tayi hakuri, na rasa me zanyi mata, mum tace aikin rarrashi zakayi tayi harta hakura, sunkuyar dakai yayi yace to shikenan zan tafi gdnsu imran, don Allah kije ki tayani bata hakuri, ta tafi daki tana kuka, mum tace to
Yana tafiya mum ta shiga wajen aysha, har lkcn tana kuka, cikin nutsuwa mum ta fara mgna, kiyi hakuri aysha nasan Ahamad ya bata miki, Amma a bisa rashin sani yayi miki, sbda mata sun Riga sun horashi da yaudara, zan fada miki abinda baki sani ba, kafin Ahamad ya aureki saida ya auri mata dai dai har guda uku, Amma duk mata ukun ba wacce bata ha'ince shi ba tun daga lkcn ya tsani mata a duniya,,,,,,,,, nan dai mum ta zauna ta bata lbrn komai sanan tace duk duniya ba wacce Ahamad yakeso kmr ke, domin kuwa da baya sonki da aranar da gidigo yazo da mgnar case din Ku nayi imani da a take a wajen ze sakeki, amma kinga be sake ki ba, ko ko maganganun daya fada bacin rai ne yasa yayi miki haka. Aysha ta tausayawa Asa's sosai, sai yanzu ta gane abinda yasa yake zargin ta, kallon mum tayi tace shikenan mum na hakura Allah ya kara rufa asiri ya karemu daga sharrin makiya, mum tace amin.
Mum na fita daga wajen aysha ta kira Asa's tace matar ka ta hakura, sai kaima kazo ka kara bata hakuri, saida ya biya ta yahuza suya yayi sayayya, sanan ya tafi gdn wajen mumya fara zuwa yakai mata gasassun kaji, sanan ya shiga part dinsa. Fitowar Aysha daga wanka kenan tana tsaye tasa wata yar bingilgilar rigar bacci, dake cikin yan biyu ne ya turo sosai, tana cikin fesa turare saiga shi ya shigo dakin, harara ta watsa mishi, ji yayi gabanshi ya fadi, amma saiya waske ya fara wakar me ciki uhm gani nan tafe me ciki Wallahi banison sunan nan, yanayin yanda yake rawa yana tsokanar ta kawai sai abin ya bata dariya, yana ganin haka yaje yayi hugging dinta yana mata hot kiss
Maman Aysha
[5/14, 16:32] Maman Aysha: Gasky tafi kwabo💵💵
3⃣0⃣0⃣➖3⃣0⃣5⃣
Tunda ga wanan ranar su Asa's da aysha sukaci gaba da gudanar da soyayya su yanda ya kamata, ya dauke matarsa sun koma gdnsu ko aiki ya dena fita sbda yanzu cikin aysha ya girma sosai, yanda EDD dinta ya nuna saura 2 wks ta haihu, kuma Dr Muktar yace bazata iya haihuwa da kanta ba saidai ayi mata C/s.
1 WK later
Asa's yayi musu visa zuwa USA har mum da sultan sbda a can zaayi mata aikin, tana zuwa washe gari akayi mata dake elective C/s ne, kyawawan yara mace da namiji aka fito dasu, hammm zo kaga murna wajen mum da Asa's, harna kasa tantance waye yafi murna acikin su, kwanan su biyu a asibiti aka sallame su, suka dawo gdn shi na garin sukayi 3 days, ana gobe suna suka koma 9ja. Washe gari aka radawa yara suna Ahamad da Aysha ana kiran Ahamad da junior ita kuma little aysha. Sunan kawai aka rada, amma bikin sunan sai next WK zaayi, shiri sosai Ahamad da aysha suke dinkuna ma kadai sunyi yakai kala nawa, Iv cards ya buga yake ta rabawa, gayya sukayi sosai
A WK later
Yaune ake gudanar da bikin sunan twins, a compound din gdn shi zaayi bikin amma fa ya zuba securities kamar banza, duk Wanda zai shiga saiya nuna gate pass sanan a barshi ya shiga. Decoration akayi wa wajen Dan ubansu irin Wanda saika rantse event centre ne, fadin kyau da haduwar da aysha da Asa's sukayi ma bata lkci ne, sultan da twins ma ba karamin kyau sukayi ba, duk inda ka wulga hadaddun mutane masu ji da Kansu. Abinci kala kala aka shirya, gasassun raguna kuwa a rataye kowa yaje ya yanki yanda ransa yakeso. Bayan kowa yaci abinci ya koshi Asa's ya karbi loud. Speaker ya fara bayanin godiya, bayan ya gama aysha ma tayi. Hadaddun senovias suka rabawa mutane taro ya watse. Bayan duk an tafi Asa's ya kira mum da kannen dad dinshi, yace yanaso yayi magana dasu, takardu ya dakko yace kona mutu na bawa Ahamad junior kamfanin takalma na dake kasar Malaysia, ita kuma little aysha na bata kamfanin Asa's textile dake kasar Holland, Sukace to Allah ubangiji ya saka da alkairi, Allah ya kara budi yace amin, Aysha ce tayi murmushi tace yayi mantawa, zuba mata ido sukayi suji mantuwar da yayi, a nutse tace ya bawa sultan kamfanin shi na waya dake kasar China. Cikin farin cike sukace masha Allah yasa zasu mori abinsu akace amin, Sanan sukayi sallama suka tafi
Ana watse wa masu aiki suka gyara gdn kmr baayi taro ba, daki aysha ta shiga tayi wanka tayiwa su twins ma ta lallaba su sukayi bacci, sanan ta shirya cikin wata fitinanniyar rigar bacci tana cikin fesa turare saiga Asa's ya shigo cikin shirin sa, kamo hannunta yayi suka zauna a bakin gado cikin unique voice dinsa yace meyasa kika yanke hukunci bada yarda ta ba? Fara ido tayi tace sbda na isa, haka kawai kanata rabon kamfani banji kace gana Dana ba, dariya Asa's yayi yace kinsan kuwa duk yafi nasu twins tsada? Dariya tayi tace na sani mana, ai hakane ya kamata sbda shine first born, kuma shine Dan gaban goshi na, inaso kasani son sultan a jinina yake, koda na haifi yaran nan banji sonshi ya ragu a zuciyata ba, saima karuwa da yayi, dariyar farin ciki yayi yace shiyasa nake tsananin sonki aysha sbda gaskiyarki da kuma rikon amanarki, gaskiya nafi duk mazan duniyar nan SAA, nagode Allah daya mallaka min ke a matsayin matata, smiling din dayake kara mata kyau tayi tace aini ce ya kamata nayi maka godiya Mr Asa's, kayi min komai a duniya, Sbda ka tsallake yayan masu kudi da masu mulki a aureni a lkcn da bani da wani gata,,,,,,,,sauri yayi ya toshe mata baki yace banaso na karajin wanan mgnar a bakin ki, inaso kisani kece farin cikina kamr yadda hydar ya zama farin cikin Fatima, ba abinda ba zanyi miki ba a duniya aysha, saidai idan banida shi
zata kara magana ya hade bakinshi da nata ya fara tsotsa
Alhamdulilla anan na kawo karshen wanan lbri na gasky tafi kwabo, kuskuren dana fada aciki Allah ya yafe min.
*I dedicated this novel to my lovely sis yaya Asiya Bashir Ahamad and her friend Aunty Ruky bello tanx for d Luv and care*
Ina mika godiya ga dukkan fans dina Wanda na sani da wanda bansani ba, more especially Maman Aysha group members and Room 5 SON members, nagode da kulawarku Allah yabar zumunci
Saimun hadu a sabon novel dina
Maman Aysha
0 Comments: